MATAR BELLO

2

by @aishaangel

*MATAR BELLO.*
_The Bride Who Brought Chaos_

By Aysher Angel

Page 2

*When What Was Meant to Be Joy Became Trouble?*




WhatsApp ***



Bayan doya ta dafu, Bulkuma ta koma ciki ta ɗauko cooler ta zubawa Bello ta kai mashi dinning table sannan ta zuba sauran a katuwar cooler ta bararraje a parlour tana ci tana kallo.

Yusrah tace, "Gayyar dangin mayunwata kawai." Bulkuma cikin ranta tace, "Ki fara girbar abun da kika shuka ɗazu tukunna kafin mu ɗora fitinar gabanta."

Bello yana dawowa ta ɗauko abincin ta kai mashi falo har da ɗauko mashi ruwan gora, ta washe baki tace, "Angona ga abinci na girka maka, kayi haƙuri jiya ba kai nayi wa dariya ba, buje nayi wa dariya."

Yusrah ta fashe da dariya jin abun da Bulkuma ta faɗa.

Bello yayi mata wani mugun kallo babu shiri ta tsuke bakinta tayi gum. Bulkuma tace, "In zuba maka?" Ya ɗan kalleta ai yadda yake da wani bahagon ciki idan yaci jagwalgwalon yarinyar nan sai ya kusa mutuwa akan hanyar zuwa asibiti.

Ji yayi tace, "Bello ga abinci." Yace, "A'a kici ke kam, ni Yusrah ce zata girka min." Yusrah ta saki murmushin jin daɗi ita matar so.

Hawaye suka taru a idanun Bulkuma wato kyamarta ma yake yi, tana amaryar amma yana gudun abun da ta girka aiko sai ta fanshe a wajen matarsa.

Bello da baisan wainar da ake toyawa a ran Bulkuma ba ya kalli Yusrah yace, "Masoyi a tashi a dafa min abinci mana da yunwa na dawo." Yusrah tayi siririyar dariya tace, "An gama ranka ya ɗaɗe." Ta tattara wayarta ta nufi hanyar dakinta tana wata shegiyar tafiya ita a dole matar so.

Da yanga ta kutsa kai amma a tamanin ta fito tana ihun gobara, ganin gudu ta tade kafafu tayi warwas a ƙasa, amma bata damu ihu take daga zaune tana faɗin, "A kawo min agaji, gobara a dakina."

Bulkuma ta fashe da dariya.

Bello ya miƙe a rikice yana faɗin, "Gobara kuma? Innalillahi wa inna ilaihi raji'um."

Hankalin Bulkuma a kwance tace, "Ba gobara bace, jahilci da jarabar da ta alakantani da shi ne na nuna mata samfuri domin ta gani ganin idanuwanta, gashi kuwa ta gani hayakin girkin Bulkuma ya sakata hawayen masoyi."

Yusrah ta fusata tace, "Ke jahilar banza da wofi," tayi kukan kura tayi kan Bulkuma. Bulkuma tayi sululu ta saka mata kafa, sai ga Yusrah tayi warwas a ƙasa tana ihun, "Wayyo kuguna, wayyo kafata, wayyo kwankwasona."

Zuhra da shigowarta kenan komai ya wakana, ta kwashe da dariya har da riƙe ciki. Yusrah ta fusata tayi kanta suka kacame da faɗa, abunka da wacce aka kayar dandanan Zuhra ta kaita ƙasa ta falfala mata mari. Bello yana magana sukayi mashi banza.

Yusrah taji duka ta fara cizo da yakushi, Bello ya shiga tsakani yana rabo, Yusrah ta shammacesu tayi kamar ta hakura ta zagaye kitchen tayi wuff da muciya tayo kan Zuhra gadan-gadan, Zuhra ta goce, muciya ta sauka akan Bello, yayi warwas a ƙasa.

Yusrah ta ɗaura hannu a kai tana faɗin, "Na boni na sheme shi." Zuhra tace, "Kuma wlh idan ya mutu sai an daureki." Bulkuma tayi wuff tace, "Tare da ke, ai tsaɓar mugunta ce ta saka kika goce aka samu bawan Allah."

Yusrah ta daka mata tsawa, "Yiwa mutane shiru munafukar banza da wofi, ai duk kece kika tayar da wannan bala'in, jahila mai farar kafa."

Ganin sunyi kanta zasu ladaka mata na jaki ta gudu dakinta ta kulle, a ranta tace, "Haka kawai su huce haushi a kaina."

Amma a zahiri saida ta ƙara kunnasu, faɗi take, "Bani rabawa saidai in ƙara zugawa, bigi cikin, naushi hancin, kayar da kafafun." Sukayi mata banza.

Saida aka yayyafawa Bello ruwa sannan ya farfado yana sabbatu, "A ina nike, zaune nike ko a kwance, Zuhra miƙar da ni zaune." Zuhra tace, "Mai gida a zaune kake." Yace, "Ina motar da ta bankeni."

Zuhra ta danne dariyar dake cinta a ciki tace, "Mai gida ba mota bace, muciya ce waccen dangin bala'itattun ta buga maka, kuma ba zamu yarda ba dole wadda ta aikata ta karɓi hukunci, ka korata gidansu." Yusrah ta miƙe fuu tana faɗin, "Saidai ke a koraki, aniyar kowa ta bishi."

Zuhra tace, "Eh aniyar da kikayi amfani da ita kika sheme mijina ta koma maki kema a shemeki."

Tuni Yusrah ta koma dakinta ta wangame kofa ta kunna fanka ta cire ledojin da aka cusa mata a window, hayakin ya fita ta kunna turaren wuta ta zauna tana cizon yatsa, "Tur, wai a ce ni Yusrah na tsaya kishiya ta lakaɗa min na jaki koda yake bugewar da nayi ne ya saka tayi galaba a kaina."

A parlour kuwa, Zuhra ce ta taimakawa Bello yayi wanka ya kishingiɗa, ta shiga kitchen ta dafa mashi shinkafa da miya sai kuma pepper chicken ko kuma tace kaza mai miya-miya kamar yadda Bello yake cewa.

Tayi serving dinsa, yayi cokali ɗaya daɗi ya kai mashi har tsakiyar kai ya lumshe idanu ya buɗe yace, "Allah yayi maki albarka." Ta sakar mashi murmushi tace, "Amin, bari in kira amaryarka tazo muci tare." Ya jinjina kai yana cigaba da kwasar lakwadar dadin girkinta.

Bulkuma ta fara gyangyadi taji knocking, ta laɓe gefen kofa tace, "Koma waye ya koma inda ya fito, bazan buɗe ba haka kawai a karyawa Gwoggona ni."

Zuhra tayi dariya tace, "Calm down amaryarmu, Bello ne yace ki fito muci abinci." Kamar ba zata fito ba sai kuma ta buɗe kofa ta ɗan leko kanta kaɗan ta hango Zuhra da Bello akan dinning table.

Zuhra tace, "Amaryarmu ki ƙaraso kici abinci kada yayi sanyi."

Har Bulkuma ta fara ci da cokali, ganin ba koshi zatayi ba ta ajiye ta cigaba da zuba loma da hannu tana faɗin, "Nifa bazan iya gulmar ci da cokali ba, ai sai mutum ya shekara ya shekare yana ci bai koshi ba."

Zuhra tayi dariya tace, "Aci dadi lafiya." Bulkuma tana kwasar girki daɗi yana kai mata har tsakiyar kai, zata iya rantsewa bata taɓa cin abinci mai daɗin wannan ba, tana ci tana zuba santi.

Zuhra tana mata dariya. Bulkuma tace, "Na gode Aunty, ke kina da kirki, ita waccen gayyar bala'itattun ɗazu da na tambayeta abincina cewa tayi ita ba baiwar gidan ubana bace ba, wai inje in nemo kalgo da sabara da na saba ci a kauye, har tana kira min jahilci da jaraba, aiko nayi mata aikin jahilci da jaraba, nayi mata girkin hayaki wajen taga kuma nasa leda na toshe tagar dakin."

Zuhra ta kwashe da dariya tace, "Kinyi min daidai, gwara da kika koya mata hankali, kin burgeni da kika sakawa marar kunyar kafa tayi zaman daɓaro a ƙasa."

Suka kyalkyale da dariya.

Bello yace, "Zuhra ina rabaki, aka ce idan kaga gemun ɗan uwanka yana ci da wuta shafawa naka ruwa."

Zuhra tace, "A'a fa, barni in more dariya, mugun abu tayi ya koma mata, MUGUN ABU JAKADA ne."

Bulkuma ta zage taci abinci ta more ta koma daki ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita.

Throughout karshen wunin ranar matan gidan suna busy, Zuhra kanta ya ɗauki zafi ta tusa tulun takardu a gaba tana fidda assignment. Ita kuma Yusrah ta samu order na wata atamfa ta anko ga riba zata samu kaca-kaca, tana ta kiran waya tana cigiyar inda za'a samu atamfar, sai wajen Magriba gab da almuru sannan ta samu atamfar har an gama komai, an tura mata kudade ta tura, zuwa da safe za'a aika atamfofi daga Kano zuwa Damaturu.

Suna gama cin abincin dare kowace ta kama hanyar dakinta, saboda tsaɓar gajiya da barci har wani dishi-dishi suke gani musamman Zuhra da tasha rubutu da research, suna yada kafadunsu barci yayi awon gaba da su.

Bello yayi wanka a dakinsa ya zura jallabiya ya leƙa dakunansu ya samu duk sunyi barci har ya nufi hanyar dakin Bulkuma yana kitsa yau sai yaci amarci da ita sai kuma ya tuna yadda tayi mashi fashin kwakwa a joystick.

Da sauri ya dafe wajen ya haɗe yawu mukyut ya juya ya koma dakinsa tun bata illata masa kayan aiki ba.

Bulkuma wacce bata saba kwanciya da wuri ba sai juye-juye take ta kasa barci, ta miƙe zaune tana tunanin zuci, da zaman banza gwara aikin kishiya koda yake babu mai katon kan da zatayi wa aiki, gwara ta shirya ta fice dandali, ita kitsa a nan garin ma ba za'a rasa dandali ba.

Tayi wanka ta ranbada kwalliya tasha farar hoda kamar wacce zataje tashe, zani daban, riga daban.

Ta sayi rake a karshen layi tana sha tana neman dandali, har ta gaji ta juyo bata samu dandali ba, akan hanya taga wani shago an kunna kallo, almajirai da yara suna zazzaune suna kallo, ta zauna tana ta kallo har goma da rabi na dare, tana tafe tana tuna cakwakiyar film din tana dariya saying, "Yoh ni Bulkuma amaryar Bello, sha biyun dare marecen kura."

Mai gadi yana kwance akan tabarma har ya kai china a duniyar barci ya jiyo motsi, yana buɗe idanu yaci karo da ita tasha farar hoda tayi butu-butu kamar yarinyar aljana, a take ya saki fitsari a wando yana ihun aljana.

Ihunsa ne ya tayar da mutanen gidan daga barci, Zuhra da Yusrah barci ya fara musu daɗi ihun mai gadi ya tayar dasu, suka yo waje daga dakunansu sukayi cirko-cirko, tsoro ya cika masu zuciya jin yadda yake ihu yana faɗin, "Wayyo Aljana!... Aljana!... Aljana ce!... Gata can!..."

Bello ne yayi karfin halin isa inda yake yace, "Wace Aljana kuma!?" Bala mai gadi yana ihu yana nuna bayan flower yana faɗin, "Aljana!..."

Suka juya sukaga wayam, ruɗewa ta saka ba ya nuna inda Bulkuma take daidai. Bello yace, "Babu kowa a wajen can."

Bala mai gadi bawan Allah har zawo ya saki a wando kuma ya gama yarda aljana tunda ya nunawa amma suna cewa basu gani ba.

Bulkuma kuwa haushin kiranta da yayi aljana ne ya saka tayi mukus taki motsi ballantana su fahimci inda take, kusan mintina talatin ana abu guda, Bala mai gadi ya suma ya farfado yafi sau biyar.

Zuhra da Yusrah suka tsure ganin abun na gaske ne, har sun fara gane-gane suna tsoratar da kansu da kansu, sukayi inda Bello yake a guje suna ihun aljana mai kai tara.

Sai daga baya suka gane Bulkuma ce yake nunawa, Bello ya fusata ya daka mata tsawa, "Ke! Ke wacce irin shashasa ce kina gani mutum yana suma amma shine kikayi shiru."

Ta zumburo baki tace, "Eh ina sane na barshi, don kuturun wulakanci ya rasa wacce zai danganta da aljana sai ni, aikin banza, aikin wofi, kadan ma ya gani, ni dashi mun kulla, ya rinƙa ganin aljannu kenan."

Da takaici ya kashe Zuhra bata ce komai ba ta juya fuu ta wuce ciki.

Yusrah tace, "Ban yafe ba barcina mai daɗi da aka katse min," ta juya fuu ta shige ciki, shima Bello a fusace ya koma ciki.

Bulkuma ta kalli inda Bala mai gadi yake ta buga tsaki tace, "Aikin banza aikin wofi." Ta buɗe kofa ta shige ciki tana sababin ya mayar da ita aljana.

Kowa ya watse aka bar mai gadi zaune tame-tame a cikin zawo yana maida lumfashi.

Babu jimawa cajin inverter ya ƙare gashi babu wuta, barci yaki yiwa matan gidan daɗi.

Zuhra ta miƙe tana jan tsaki ta buɗe window ta watsa ruwa ta kwanta amma still barcin babu ɗaɗi.

Itama Yusrah zafi ya addabeta ya hanata barcin, ta buɗe window tayi wanka ta kwanta amma har ila yau barcin babu ɗaɗi, ba kamar na ɗazu da iskan fanka da na Ac yake bugawa ba.

Shi kanshi Bello kasa barcin yayi sai faman juye-juye yana jan tsaki, gashi fankarsa ta kasa mai caji ya manta bai sakata caji ba.

Ita kuwa uwar gayyar Bulkuma tana kwanciya barci yayi awon gaba da ita, barci tayi sosai har da munshari.

Sai gefin asuba sannan aka maido wuta, barci ya fara masu dafi suka jiyo kiran asuba, Zuhra tana da lectures na safe don haka tana ji tana gani barcin yana mata daɗi amma dole ta haƙura da shi, ta tashi ta shirya ta wuce school tana jin kamar ta fasa ihu saboda takaicin yadda barci yana mata daɗi aka tayar da ita.

Haka ta wuni a makaranta tana gyangyadi, tana ta layi kamar ƴar maye, ta jawa Bulkuma Allah ya isa yafi sau shurum masaki.

Itama Yusrah da take gidan bata samu barcin safen ba tunda asubar fari mai kaya ta fara jera mata kira aka zo aka samu matsala a wajen saka kaya mota, instead of a sakasu a motar Damaturu sai aka saka a motar Gombe, tayi wujiga-wujiga, haka tayi ta fama sai gab da almuru sannan ta samu kaya suka isa Damaturu, mai kaya ta amsa, sai a lokacin ta samu sawaba, tayi wuru-wuru kamar wacce aka yi wasan kura da ita, ga barci da yake damunta, tayi Allah ya isa yafi sau shurum masaki akan bukulun barci da aka yi mata.

Karfe sha biyu na dare Bello ya gama kallo a parlour ya leƙa dakin Bulkuma ya tarar dashi wayam babu ita babu alamarta, hankalinsa ya tashi matuƙa gaya, yana tambayar kansa 'ina ɗiyar mutane ta shiga a wannan tsohon daren.'

Zuhra ya fara tayarwa, "Ina Bulkuma take?" Ya tambayeta.

Tana hammar barci tace, "Tana dakinta mana." Yace, "Na duba bata dakinta." Zuhra ta waro idanu tace, "Na'am." Yace, "Shiyasa nike tambayarki idan kin san inda take." Ta ware hannuwa tace, "Ban sani ba amma ka duba compound watakila tana can." Yace, "A tsakar daren nan." Ta yatsine fuska na haushin tayar da ita barci da yayi tace, "Since she is not here, she might be somewhere in the compound, so go and check." Yace, "What?" Tace, "Cewa nayi tunda bata a nan akwai yiyuwar tana compound din." Tana gama faɗin haka ta bamko kofarta ta koma tabi lafiyar gado.

A rikice Bello ya fice compound ya duba ya ƙara dubawa har mai gadi yana tayashi amma babu Bulkuma babu dalilinta.

Ya koma ciki ya tayar da matan gidan, Yusrah tambaya take, "Mi ya faru?" A kufule Zuhra tace, "Sarauniyar gidan ce ta ɓata."

Yusrah ta taɓe baki tace, "Na tambayeki ne, ki bari wanda na tambaya ya bani amsa," Sannan da gadara tace, "Duk cikar gidan nan da batsewarsa akwai wata sarauniyar gidan da ta wuce ni."

Zuhra tace, "Calm down Hajjaju, mun san wacece ke, sarauta ko ta kobon sisi babu a gidanku."

Yusrah ta daka mata tsawa tana faɗin, "How dare."

Ya daka masu tsawa ganin zasu tayar masu faɗa a wannan halin da yake ciki na tashin hankalin na ɓatan Bulkuma. "Kuyi min shiru a nan, ku barni inji da tashin hankalin ɓatan yarinyar nan. Baku ganin dare ne kuke ta ihu."

Yusrah da Zuhra sukayi cirko-cirko a compound yayinda Bello da Bala mai gadi suka fita nemanta a zagayen unguwar amma babu ita babu alamarta.

Mai gadi ya rantse akan shi bai ga fitarta ba amma duk da haka bazai iya cewa ba ta fita ba domin kuwa shi da kansa shaida ne akan yadda yarinyar takd ficewa a gidan kamar iska, tana sulalewa kamar aljani ba tare da ya lura ba.

Yusrah ta gaji da tsayuwa ta nufi kofa fuu tana faɗin, "Tsayuwa bata ganni tunda lokacin da danginta suka kawo amanarta bance na amsa ba don haka wanda ya amshi amanarta sai yaje yayi nemanta, barci na zanyi har da munshari."

Bello ya fusata ya tureta har ta kusa faɗuwa ya ɗannawa kofar shiga falon makulli yace, "Sai muga ta inda zakiga shiga ciki ballantana kuma har kiyi barcin munsharin."

Tace, "Ahaf ai ni ba bakuwar tsanani bace a nan ma sai inyi barcina har da saleɓa."

Duk don ta cunsa mashi bakin ciki akan tayar da ita da yayi barci ta kishin kishingiɗa a wajen kofar shiga parlour tayi likimo kamar tana barci amma ba barcin takeyi ba.

Bello sai zufa yake yi, hankalinsa idan yayi dubu to a tashe yake, tashin hankalin gangariya.

Da gadara Zuhra ta kalli inda Yusrah take kishingiɗe tace, "Tusa a shara kawai." Yusrah ta buɗe idanu tace, "Kika ce?" Tace, "Ban sani ba sai shegen son kira kamar tsohuwar zawara."

Kafin ta samu zarafin mayar da raddi Bulkuma ta turo kofa ta shigo hankalinta a kwance tana tafe tana waftar rake tana wake-wakenta na sha biyun dare marecen kura.

Yusrah ta sauke ajiyar zuciya, ta wafce makulli daga hannun Bello ta buɗe kofa.

Bello ya dakawa Bulkuma tsawa yace, "Daga ina kike?"

Hankalinta a kwance tace, "Yawo mana daga nan kuma sai na tsaya nayi kallo a bakin titi." Ranshi ya ɓaci yace, "Kina matar auren kike fita yadda ranki yake so, ina tvn dake gidan nan miye amfaninta da har zakije waje kallo."

Tace, "Ɗazu da nazo falon nace ka kunna min cartoon korata kayi shine naje bakin titi inda suke kunna kallo inda ba za'ayi min gadara akan tangaraho ba."

Ya fusata yace, "Ke daga yau kika ƙara fita sai na zaneki."

Tace, "Ohh su sauran matanka su fita amma ni sai in tule a gida kamar garar kunya, to ai saidai ka haɗemu mu ukkun ka zane tunda kowace a cikinsu fitarta take kanta tsaye," tana gama faɗin haka ta juya fuu ta shige ciki har da bangaje Yusrah.

Zuhra tace, "Tofa wannan shine karfin hali sata lahira koda yake laifinka ne, yarinya ta fice a salamainin dare ta tayar mamu da hankali amma maimakon ka falla mata mari sai ka tsaya kuna cecekuce."

Bulkuma ta leƙo tace, "Da kike cewa ya mareni to naji kuma tunda ke kika sakashi marina ki kwana da sanin duk ranar da ya mareni a jikinki zan fanshe, kuma kada ki ƙara kirana yarinya, sunana Bulkuma, yarinya tana bayan gyatumarta ana mata rirriga. Ke kuma Yusrah da kike lafewa bayanta to ɗazu cewa tayi taji dadin abun da nayi maki."

Ta juya ta koma ciki fuu ta bamko kofa.

Yusrah ta kalli Zuhra tace, "Ashe gulmata kikayi." Zuhra ta bamka mata harara tace, "Ni Zuhra nafi karfin inyi gulmarki, ce mata nayi naji daɗin yadda ta koya maki hankali, katuwar banza kawai kin zauna yarinya ƙarama ta kaiki ƙasa."

Ta juya inda Bello yake tace, "Kai kuma daga yau sai yau idan mahaukaciyar amaryarka ta ɓace kada ka ƙara tayar dani tunda ba tare dani aka baka shawarar aurota ba," ta juya fuu ta shige ciki ta bamko kofa fiye da yadda Bulkuma ta bamko.

Yusrah ta buga tsaki tace, "Haka kawai muna zaman zamanmu ka auro mamu jaraba, to kai da ka auro jarabar saidai ta ƙare a saman kanka, ina faɗa maka duk ranar da ka ƙara tayar min da hankali akan waccen jarababbiyar yarinyar sai na haukace tuburun anyi yakin duniya na bakwai a cikin gidan nan," ta juya fuu ta shige ciki itama saida ta bamko kofa.

Bello ya rasa yadda zaiyi sai yayi tagumi kawai, yafi ƙarfin mintina talatin a wajen kafin ya miƙe ya shiga ciki.

Mai gadi kuwa tun kafin rigimar tayi nisa ya tattara inasa-inasa ya ƙarawa wandonsa iska, fitinar gidan Bello tafi karfinsa gwara ya gudu da kafafunsa tun kafin yarinyar ta ɓace da gaske a rataya mashi laifi.

Washegari mutanen gidan barci suka sha sosai har karfe goma na safe basu tashi ba, yayinda Bulkuma tun bakwai na safe ta tashi ta kunna cartoon tana kallo ta kure Ac tana kallo tana washe baki.

Tun kallon yana mata daɗi, har yunwa ta fara addabarta, gashi gidan har lokacin tsit yake kamar babu kowa a cikinsa kasancewar har lokacin mutanen gidan basu tashi ba, barcinsu yayi nauyi kamar masu barcin mutuwa. Ta jima tana jiran ko ɗaya daga cikin matan gidan zata tashi a girka abun sakawa kofar salati amma shiru babu alamar kowa.

Da ta gaji da jiran gawon shanu ta miƙe ta shiga daki ta ɗauko kuɗi daga cikin waɗanda Gwoggo Saude ta ba ta. Ta ɗauki cooler da ƙaramin jug, ta fita zuwa bakin titi inda ta siyo koko da ƙosai.

Ta dawo ta zauna ta dararrashe a parlour tana ci tana kallonta, a haka barci yayi awon gaba da ita.

Bello ya farka yayi wanka ya zura jallabiya ya fito parlour ya samu Bulkuma kwance a parlour ga jug da cooler a gabanta ya ɗauka ya duba yaga alamun koko da ƙosai ne.

Ya kira sunanta bata motsa ba sai motsi da tayi da laɓɓanta sai kuma ta gyara kwanciya ta cigaba da barcinta. Ya sake kiran sunanta shiru, ya saka hannu ya girgiza kafaɗarta, nan take ta ɗan motsa jikinta kaɗan, ta buɗe idanu kaɗan tana kallon falon kamar ba ta gane inda take ba. Ta lumshe idanun nata ta sake buɗewa, tana ɗan murza su da hannu, fuskarta cike da kasala da nauyin barci.

"Hmm... me ya faru...?" ta faɗa da muryar dake nuni da barcin bai ida sakinta ba.

"Waye yaci ƙosai da koko?" Ya tambaya fuskarsa babu walwala.

Ta miƙe zaune, saida ya ƙara maimaita tambayar sannan tace, "Ni."

Ya murtuƙe fuska yace, "Saboda ki kira min talauci ki saka a zageni a unguwa shine zaki fita ki siyo koko da ƙosai a bakin titi."

Tayi rau-rau da idanu, ya daka mata tsawa, "Kada ki sake kiyi min kuka a nan!." Ta mayar da hawayen tace, "To ya kake son inyi ne? Tun karfe bakwai na safe nike zaman jiranku amma shiru babu wanda ya fito ni kuma gaskiya bazan cuci kaina in zauna yunwa ka kasheni na fita na siyo koko da ƙosai."

Yace, "Shine ba zaki iya zaman jira ba." Ta jinjina kanta tace, "Kwarai bazan iya zaman jira ba, ku cikinku na ƴan gayu ne ni kuma nawa cikin na ƙauye ne."

"To ina kika samu kuɗin siyen kokon?"

"Wanda Gwoggo ta bani ne."

Yace, "To shikenan amma daga yau kada ki ƙara fita siyen koka da kosai idan kinji yunwar da safe ki shiga dakina ki tayar dani in dafa maki tea da bread."

Tace, "Kai ai shayi da burodi ba ya riƙe ciki, tuwo dumame yafi rikon ciki sosai da sosai."

Ya murtuƙe fuska yace, "To shi garemu, gidan nan ba'a cin tuwo." Tace, "To shikenan sai in rinƙa maleji dashi amma burodin katoto nike so mai kwakwa irin wanda Baffa yake tafo mamu dashi daga Taraba."

Ya jinjina kai kawai, ya shiga dakunan matan gidan ya tayar dasu, a tare suka fito, suna ido hudu da juna suka murtuƙe fuska suna harare-harare da jan tsaki.

Suna juyowa suka ci karo da Bello ya hakimce fuskar nan tasa a murtuƙe, babu shiri kowace ta gyara yanayin fuskarta.

Yusrah ta saki murmushin dole tace, "Yayata ina kwana?" Zuhra tace, "Lafiya lau, ƙanwata. Kin tashi lafiya?" Yusrah tace, "Lafiya lau yayata."

Bulkuma ƴar nema tuni ta fara kyakyata dariya, dariya take har da riƙe ciki ganin yadda matan gidan suke zuba dirama. Ita fa idan taji labarin abun dariya da kafarta take zuwa ta gano ballantana wannan da ya sameta har inda take, dariya take har da kwolla.

Bello ya daka mata tsawa, "Ke! Dariyar uban mi kikeyi mamu a nan?"

Tana cigaba da dariya tace, "Yadda ka murtuƙe kamar fuskar shanu da yadda matanka suka rikice suna gaisuwar dole shi ya sakani dariya."

Ya daka mata tsawa a karo na biyu yace, "Fice ki bamu mutane."

Ta miƙe tana gunguni, "Don mugunta shine ka lallaɓa kayi min wayo ka raboni da gidan Gwoggona, kuma kawai don naki yarda ayi iskanci shine kake tayi min tsawa, ai ha haka mukayi da kai ba."

Da tsawa yace, "Bulkuma ki ɓace min da gani tun kafin jikinki ya gaya maki." Ta nufi hanyar dakinta, ya nuna mata kofa yace, "Fice compound kiyi kneeldown a tsakar rana."

Ta nuna Yusrah da Zuhra tace, "Ai suma da suka tashi harare suka rinƙa yi wa juna don haka saidai su fito muyi kneeldown din a tare."

Zuhra ta fusata ta nunata tace, "Ke ɗan uwarki nice zanyi kneeldown din." Bulkuma ta murgada baki tace, "Ehh tunda ɗaya muke a gidan kuma yadda yake takamar nayi laifi kema kinyi laifin."

Yusrah tayi mata tsawa tace, "Dalla fice kije kiyi kneeldown ki amshi hukunci, mu munyi maki kalar mahaukata ne."

Bulkuma ta riƙe kugu tace, "Eh matsoraciyar banza da wofi, ranar da nayi ihun Bomb nan kika fito kafafunki da lemar fitsari, wa ya sani ko fitsarin kwance kikeyi mijinmu yana rufa maki asiri."

Zuhra ta sheke da dariya tana kallon Yusrah tace, "Haba ko nace shiyasa kullum sai anyi wanki ashe kayan fitsarin kwance ake wankewa."

Bulkuma tace, "To ƴar iya wa ya kasa dake ballantana har ki ɗauka, marar karfi kawai wacce sai idan anyi wa mutum lis sannan take kassarashi."

Zuhra tace, "Uwarki ce matsoraciya." Bulkuma tace, "Ba dai uwata saidai uban uwar mai zagi." Zuhra ta fashe da kuka tana faɗin, "Ranka ya ɗaɗe kana ji yarinya tana zagina amma shine ka zuba mata idanu."

Yusrah tayi karaf tace, "Ke mi ya saka kika fara zaginta, ai ba zanen kugu kika fi wani ba da har kike tunanin zakiyi zagi ba'a rama ba."

Zuhra ta shammaci Bulkuma ta zuba mata cable a gadon baya har sau ukku, Bulkuma ta gantsare a wajen jin an ƙara wata wani ta arta a guje tana jan Allah ya isa, "Allah ya isa kuma da yardar Allah sai an rama min."

Zuhra tace, "Kuma kina dawowa gidan nan sai nayi maki dukan tsiya, dangin Jaraba kawai." Bulkuma tace, "Ni ba dangin jaraba bace, saidai ke Allah ya hadaki da jaraba, kuma dukana da kikayi ban yafe ba."

Zuhra tace, "Ki turo mai karfin gidanku ya rama maki, na bugeki na bugi banza da wofi, mahaukaciya kawai." Ta yunƙura kenan Bulkuma ta arta a guje.

Tana fita ta yanki hanya tana tafe tana share hawayen mahaukaciyar da suke kiranta da shi, ta murguda baki tace, "Ba dai mahaukaciya ba, idan Allah ya yarda sai sunga mahaukaciya ganin idanunku."

A bakin layin gabansu ta hango yara suna jan makauniya, idan ta bisu su watse sai wahalar da ita sukeyi tayi wujiga-wujiga.

Bulkuma ta fashe da dariya tana nuna mahaukaciyar, mahaukaciya ta fusata ta nufo kanta, Bulkuma tace kafa mi naci ban baki ba, ta tattara bujenta ta arta a guje, ita gudu mahaukaciya gudu.

Bello yaji shiru-shiru Bulkuma bata dawo ba ya miƙe ya nufi hanyar fita falon yana addu'ar Allah yasa dai ba fita tayi ba.

A kofar sukayi arangama, Bulkuma tayi fit ta shige falon ta bamka dakinta ta danna lock yayinda Bello yayi arangamar kwara kai da mahaukaciya dama gata da katon kai, ta bangajeshi yayi zaman daɓaro a ƙasa yana ihun, "Wayyo kaina, wayyo kuguna, wayyo kwankwasona, ku taimaka min nayi arangama da motar gingimari."

A parlour kuwa, Yusrah tana hango shigowar mahaukaciya tayi wuff ta shige dakinta ta danno lock.

Mahaukaciya tayi wuff da Zuhra ta wurgar da ita tsakiyar parlour ta cigaba da tsula mata cable, "Ni kuke kira mahaukaciya mai lasisi, jikinku zai gaya maku."

Sai ta bugeta ta bugeta sai ta fashe da dariya tace, "Hhhhh ƙarya suke, ni ba mahaukaciya bace, da hankalina na iya kirgar lamba, daya, ukku, sha tara, talatin, tamanin da tara, dari, kin gani babu wahala."

Sai kuma ta cigaba da tsula mata cable, ihu Zuhra take tana neman taimako, "Wayyo Allah ku taimaka min, jama'ar gidan nan ku taimaka min."

Amma daga Bulkuma har Yusrah babu wanda ya fito, haka kawai su fito a haɗa dasu, ita Yusrah sai ɗauko waya tayi tana ɗaukar bidiyo ta kofar window dinta tana dariya.

Bulkuma ta buɗe kofar kaɗan ta buɗe murya tace, "Zuhra kika ce min mahaukaciya, kika ce min in aiko mai karfin gidanmu ya rama min, to gaki ga mai karfin gidanmu gidan mahaukata tana rama min."

Tana gama magana ta maida kofa ta rufe ta haye kujera tana leƙowa tana gutsirar burodi tana dariya.

Saida mahaukaciyar nan tayi wa Zuhra lis sannan ta juya a guje ta fice, Bello yana ƙoƙarin miƙewa ta bangajeshi ta fice ya koma rujub yayi zaman ƴan bori a wajen.

Ya taƙarƙare ya fasa ihu, "Wayyo kuguna, kuzo ki taimaka min nayi arangama da motar kwasar shanu."

A guje da Bulkuma da Yusrah suka fito suna mashi sannu.

Zuhra dake kwance tana wayyo-wayyo da hawaye shabe-shabe a fuskarta tace, "Ohh wato nice banzan sharar bola shine kukayi banza dani."

A wahalce Bello yace, "Ina motar ɗaukar shanun tabi?"

Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)