MATAR BELLO

3

by @aishaangel

*MATAR BELLO.*
_The Bride Who Brought Chaos_

By Aysher Angel

Page 3

*When What Was Meant to Be Joy Became Trouble?*


WhatsApp ***



Yusrah ta danne dariyar dake taso mata tace, "Mai gida ba motar ɗaukar shanu bace ba, mahaukaciya ce amaryarka ta janyo mamu." Ya kalli inda Bulkuma take yace, "Billy mi yasa kika janyo mamu mahaukaciya a gida?"

Bulkuma tace, "A'a bani na janyota ba, naga tana bin yara ne suna kwarata shine nayi dariya ita kuma ta biyoni."

Yusrah ta murtuƙe fuska tace, "Kika dai janyo mamu ita."

Bulkuma ta murguda baki tace, "A'a kada ki ɗaura min tsaɓa a kai, bani na kar zomon ba, ko ratayarsa ba'a bani ba, kune kuke kirana mahaukaciya shine da Allah ya tashi nuna maku iyakarku sai ya nuna maku mahaukaciyar ganin idanunku kukaga samfurin haukan da kuke ƙaƙaba min."

Yusrah tace, "Dalla yiwa mutane shiru, sai surutu cacaca kamar akuya." Bulkuma ta ɓata fuska kamar zatayi kuka tace, "Ni ba akuya bace, kuma kema sai naje na kawo maki mahaukaciya tayi maki dukan akuyoyi."

Bello yana jin haka yayi sauri ya kamo hannunta yace, "Kiyi haƙuri ki barni haka idan ba so kike kuyi takabata ba."

Ta turo baki tace, "Ba wannan Yusrar bace take ce min ina surutu cacaca kamar akuya ba, to kodai ta maida kalmominta akan kanta ko kuma fita zanyi inje in ɓallo garke-garken mahaukatan akuyoyi suyi dabdalar safe a kanta."

Yusrah ta tuno yadda aka lakadawa Zuhra shegen duka, muryarta tana rawa tace, "Yi haƙuri amaryar Bello bake bace cacaca kamar akuya, ni ce cacaca kamar akuya."

Bulkuma tace, "Kinyi kyan kai, da kinyi taurin kai da na nuna maki aiki da cikawa." Ta miƙe fuu ta tsallake Zuhra dake kwance tana wayyo-wayyo ta shigewarta daki.

Bello yana dafe da kugunsa yace, "Musa ka cuceni kace min kwaila duniya ce, gashi nayi auren kwailar amma babu abun da nike gani sai lukutar bala'i."

Yusrah tace, "Ohh dama shine ya zugaka ka ƙaro aure, annamimi ina nan gidan zai tarar dani inyi mashi wankin babban bargo."

Bello yace, "Taimaka min in koma parlour." Ta bamka mashi harara tace, "Ban taimakawa, ka kira shi Musan da ya zugaka kayi auren sai yazo ya taimaka maka."

Ta miƙe fuu ta shige ciki, ta shige dakinta ta ɗauki waya tana kallon yadda aka kirɓi Zuhra tana kwasar dariya kafin daga bisani ta ɗaura bidiyon akan ticktock bayan da ta saka blur a daidai saitin Zuhra.

Bidiyo ya tafi viral, mutane suna ta dariya domin wasu sun ɗauka shirin barkwanci ne aka shirya.

Washegari daƙyar Zuhra ta shirya ta wuce school tana tafe tana cije baki yayinda baki daya jikinta yake mata ciwo.

Sun fito lectures taga ƴan course dinsu sunyi tsintsima a back bench na threater suna ta dariya, ta ƙarasa wajen tace, "Asiya miye kuke kallo haka?"

Asiya tana dariya tace, "Wata mahaukaciya ce take casa wata mata."

Zuciyar Zuhra ta buga da karfi tuna baƙar wahalar da tasha jiya a hannun mahaukaciya, tace, "Matsa in gani."

Tana leƙa ta hango falon gidansu, anyi blur dinta ne shiyasa ma basu gane itace ake kirɓa ba, cikin ranta tace, "Kutuma, kenan Yusrah daukota tayi bidiyo ta yadawa duniya aiko bazai saɓu ba sai na rama, itama sai mahaukaciya tayi mata shegen duka na ɗauki bidiyo."

Ko lectures dinsu ta ranar basu gama ba ta hau bus ta kamo hanyar gida, ta samu Yusrah zaune a parlour tana kallo a system, Bulkuma tana kallon cartoon, mai gidan kuma a kofa suka haɗu dashi zai fita.

Tana ajiye jikarta a daki ta fito ta shiga dakin Bello ta dauko master key ta kulle dakin nasa, ta lallaɓa ta kulle dakin Yusrah da na Bulkuma, da kofar kitchen da duk wata kofa da za'a bi a gudu ya rage kofar shigowa parlour ce kaɗai ya rage.

Ta bazama cikin unguwa neman mahaukaciya, ta hango wata karfaffar mahaukaciya zaune a gefen hanya tana wasa da ledoji tana dariya. Ta ɗaga murya tace, "Ke mahaukaciya."

Mahaukaciyar ta juyo ta kalleta sai kuma ta juya ta cigaba da wasan ledoji tana faɗin, "Yarana ku kyaleta bata da hankali."

Zuhra ta ɗauki roba ta jefeta dashi tace, "Ke mahaukaciya dake nike."

Mahaukaciya tayi mata banza, ganin wankin hula zai kaita tsakiyar dare ta warware mayafin dake saman kanta tayi kundunbala ta isa inda mahaukaciyar take ta janyota ta wanka mata mari ta ƙara wanka mata mari sannan ta Ingizata ta kwaso ƙasa ta watsa mata tace, "Ke mahaukaciyar banza da wofi."

Mahaukaciya ta kalli inda ledojin suke taga anyi dama-dama dasu, ta dubi inda Zuhra take tace, "Ni kika kashewa ƴaƴa."

Zuhra wacce ta tattare bujenta ta zama ready tace, "Ehh kuma nace maki mahaukaciyar banza, mahaukaciyar wofi."

Mahaukaciya tayi kukan kura tayo kanta suka raba tsere.

Bello ya shawo corner kenan ya hango Zuhra a guje mahaukaciya ta biyota, ya zaro idanu yace, "Kai! Mi kuma ya haɗa Zuhra da mahaukaciya?"

Tuna arangamarsa da mahaukaciyar jiya ya saka ya koma inda ya fito ya zauna a bakin titi yana maida lumfashi yana kitsa dabdalar cakwakiyar lukutar bala'in da za'ayi a gidan.

A guje Zuhra ta shige falon ta faɗa dakinta ta maida kofa tayi locking.

Bulkuma da Yusrah suna hango mahaukaciya a guje kowace tayi hanyar dakinta saidai a rufe suka tarar da kofofin, suka rankaya dakin Bello suka tarar dashi a rufe, kofar kitchen a kulle.

Mahaukaciya ta cigaba da ralli dasu a falon suna gudu suna ihun neman taimako gashi babu hanyar tsira.

Bulkuma tayi sa'a tayi wuff ta ɓoye a bayan kujera, mahaukaciya ta taɗo Yusrah ta saka bulalar bedi ta cigaba da zaneta, Yusrah tana ihu tana wayyo-wayyo yayinda bulalar take shigarta musamman da ya kasance material marar nauyi ne a jikinta.

Zuhra ta saita camera ta window na dakinta tana naɗar bidiyo tana dariya. Bulkuma dai idanu sun raina fata tana makale a bayan kujera tana mutsu-mutsu da idanu kamar beran da mage ta saka a corner babu hanyar tsira.

Mahaukaciya tana dukan Yusrah tana faɗin, "Ni kika kashewa yara ko? Yau sai jikinki ya gaya maki."

Dukan da Yusrah tasha yafi wanda aka yiwa Zuhra sau biyu da rabi.

Saida Bello yaga fitar mahaukaciyar sannan ya shigo gidan ya samu Yusrah kwance tana kuka da hawaye shabe-shabe.

Bulkuma tana rabe a bayan kujera tana haɗa zufa.

Yace, "Zuhra mi ya hadaki da mahaukaciya?" Tace, "Yara ta biyo hanyar da nike tayo kaina na tattare zanina na arto a guje."

Ta fakaici idanunsu ta buɗe kofofin.

Yusrah tasha baƙar wahala ba kaɗan ba, da rarrafe ta shige ɗakinta ta haɗa ruwan zafi tana gasa jikinta tana ihu, har zazzabin dole tayi, saida likita yayi mata allura ta samu tayi barci.

Suka zauna a parlour zugum-zugum.

Washegari babu wanda ya fita gidan kasancewar Zuhra bata da lectures shi kuma mai gidan har lokacin bai koma kasuwa ba, idan su Garzali sun tambaya sai yace ban gama amarci ba, idan sunce zasu zo cin girkin amarya yace babu ruwansa idan su Zuhra suka tado masu aljannu.

Yusrah tana kwance tana wayyo-wayyo aka kirata ta ɗaga, tayi jim sannan tace, "Bani da lafiya ne shiyasa amma yanzu zan hau sai in tura maki lasa-lasan dake akwai sai ki zaɓi wadanda kike so, amma ni ina Katsina su kuma kayan suna Kano."

Tayi jim sannan tace, "Okay babu damuwa, yanzu zan tura maki hotunan." Ta gama tura hotunan kenan ta shiga status can ta hango status din wata customer ɗinta na jiya ne lokacin da mahaukaciya take jibgarta, an saka mata blur ne shiyasa ba za'a gane itace ba.

Ji tayi zazzabin dake damunta ya ware, ta warware kallabin dake saman kanta tayi ɗamara da shi, saida ta saki ashar sannan tace, "Kan kaza-kaza, ashe yau za'ayi yakin duniya na tamanin a gidan nan."

Bello ya ɗan dubeta yace, "Lafiyarki?" Ta nuna Zuhra tace, "Wannan munafukar matar taka zaka tambaya, jiya ta ɗauki bidiyona ta ɗaura a ticktock."

Bello yace, "Wani bidiyo?" Zuhra tayi karaf tace, "Bidiyon lokacin da mahaukaciya take tara mata na jaki." Ta miƙa mashi wayarta tace, "Duba ka gani ya tafi viral mutane dariya suke a comment section, barkwanci mai citta da tafaranuwa da masoro."

Bello ya amsa ya duba, ya dubeta a fusace yace, "Mi yasa zakiyi haka?"

Kanta tsaye tace, "Saboda itama lokacin da mahaukaciya ta jibgeni ɗaukar bidiyo tayi ta ɗaura a ticktock din shiyasa nima jiya na bazama a unguwa na tsokalo mahaukaciya tazo itama aka lakaɗa mata na jaki na ɗauki bidiyo na ɗaura."

Ta lalubo bidiyon ta nuna mashi, tace, "Tayi min shiyasa na rama MUGUN ABU JAKADA."

Yusrah ta lailayo ashar ta lailaya sannan tace, "Shine kika gayyato mahaukaciya ta dokeni." Zuhra tace, "Eh ramuwar gayya wacce tafi ta gayya zafi."

Yusrah tace, "Amma ai dukan da aka yi min yafi wanda aka yi maki."

Zuhra ta kyalkyale da dariya tace, "Wannan ribar kafa ne kika samu."

Yusrah ta fusata tace, "Ribar kafa ko? Aiko zakiga ribar kafa ganin idanunki." Ta nufi hanyar kofa, Bello ya tare hanya yace, "Ina zaki kuma?" Tace, "Mahaukaci zan nemo yazo ya rama min dukan da nasha jiya idan kuma ban samu ba in nemo ƴan daba suzo suci ƙaniyar kowa da kowa."

Babu shiri Bello ya kulle kofar yace, "Babu inda zakije, kinyi mata ne ta rama shikenan 1-1." Yusrah ta fusata tace, "1-2 dai domin dukan da aka yi min yafi wanda tasha sau biyu da ɗoriya don haka ko ka bani hanya in fita in nemo mahaukaci ko kuma in nuna maka hauka ganin idanunka."

Ya murtuƙe fuska yace, "Babu inda zakije." Ya koma akan kujera ya zauna.

Yusrah ta sheke da dariya tace, "To shikenan ka hutar da ni neman mahaukaciya, nima zan iya komawa mahaukaciya mai lasasi, sai na shayar daku giyar nadama, sai kunyi nadamar tsokaloni, yau sai anyi yakin duniya na ukku a gidan nan."

Ta shiga kitchen ta ɗauko taɓarya ta nufi tvn bango gadan-gadan ta rotsata, ta fasa ihu tana tarwatsa dukkanin abun da ya tari gabanta, tayi kansu suka tarwatse kowa ya nemi hanyar tsira, gida ya rikice babu abun da yake tashi sai ihunsu da ƙarar fashe-fashen da Yusrah takeyi.

Makota suka shigo sulhu, Yusrah ta tayar da aljannu, aljannun Zuhra suka tashi, wata makociyarsu da ta shigo rabo itama aljanunta suka tashi.

A ranar babu wanda yayi barci a unguwa, mutanen unguwa sunga lukutar bala'i ganin idanunsu har dare ana abu guda, duk wata mai aljannu a layin saida suka tashi, har wadanda ba'a san suna dasu ba, unguwa ta rikice.

Bello yayi tagumi hannu biyu-biyu, yayi zuru-zuru dashi, ya kira Musa yana ɗagawa yace, "Musa ka cuceni kace min auren kwaila duniya ne, gashi ni tunda na auri kwailar babu abun da nike gani sai lukutar bala'i, jaraba ta yau daban ta gobe daban, tunda na auri yarinyar nan babu wanda ya ƙara barci da idanu biyu a gidan nan, mai gadi kansa ya gaji ya tattara ya gudu, gashi yanzu ta tsolako bala'i a tsakanin Yusrah da Zuhra sun tayar da aljannu matan unguwa sai zubewa sukeyi."

Ya tsinke wayar, yayi nadamar auren Bulkuma yafi sau shurum masaki, ya aureta a zuwan ya samu kwaila mai sakashi dariya da wautarta, gashi a karshe wauta ta juye ta sakashi a hannun ƙaƙanikayi. Shin mi ya faru a baya? Shin wannan wacce irin amarya ce Bello ya auro?

Nima, ni da readers muna buƙatar sanin wacce irin amarya ce wannan, shin ya aka yi aka kwana a ragaya? Don haka mu koma baya WATANNI GOMA DA SUKA WUCE domin jin yadda aka yi aka kwana a ragaya. Kafin nan kuma sai mu dawo mu dasa domin jin irin dabdalar cakwakiyar da za'a cigaba da bugawa a tsakiyar gidan Bello, angon Bulkuma, Mijin Zuhra da Yusrah 🤣🤣🤣🤣.


*******


WATANNI GOMA DA SUKA WUCE


MAHUTA, KATSINA

Karfe shidda na safe, gari yayi shiru kowa a makota yana bacci amma ban da Gwoggo Saude, ta kasa barcin kwata-kwata saboda gudun kada Bulkuma ta fita ta janyo mata masifar da zata hanata barcin dare, ta ɗauki kujera ƴar tsugunno ta zauna gefen kofa, ta kasa ta tsare tana faman gyangyaɗi.

Bulkuma tayi lamo a daki tana barci amma wannan shirun ba na daɗi bane, shiru ne na guguwa mai zuwa da karfinta.

Gwoggo Saude ta jingina da bango tana faman gyangyadi.

"Hmmmm..." ta ja numfashi mai nauyi, kanta na ɗan faɗuwa ƙasa, sai ta firgita ta ɗaga kai da sauri.

"A’ah! Ba yau ba..." ta sanar da kanta tana mai tunawa kanta ƙaramin yakin duniya na ulli da za'ayi a gidan idan ta bari Bulkuma ta janyo faɗa. Domin kuwa ta san abu ɗaya tak, idan Bulkuma ta fita da sassafen nan to fa labari ya gama lalacewa.

Ta ɗan leƙa cikin gida tana wani tunani domin shirun da taji yayi yawa kada fa yarinyar nan haura katanga tayi ta fice, ta zabura.

"Bulkuma..." ta kira a hankali. Amma shiru babu amsa.

Ta sake kira, wannan karon da ƙarfi kaɗan, "Bulkumaaa!..."

Bulkuma ta gyara kwanciya ta amsa da, "Na'am Gwoggona," da wata murya mai cike da kasala kamar wadda aka taso daga mafarki mai daɗi.

"Na'am, me ya faru ne?" Ta sake faɗa.

Gwoggo Saude ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, "Alhamdulillah tana ciki."

Ta gyara zama da kyau akan kujera ƴar tsugunno tana gadin kofa kamar soja da yake tsaron iyakar kasa.

"To yau kam sai in ga ta yadda zaki fita ballantana har kin janyo min faɗa matar mutane tazo kawo min ba'asi har tana nema ta kai min naushi a muƙa-muƙi," ta yi magana a hasale, tana ƙoƙarin buɗe idanunta da karfi domin barcin nema yake yaci ƙarfinta.


Mintuna kaɗan suka wuce, iska mai sanyi ta busa ya sakar mata da barci, barci yayi daɗi ta wuntsulo daga kan kujera ta kwara kai, ta buɗe idanu da sauri tana waige-waige a tunaninta wani dogon barcin tayi, a tamanin tayi hanyar dakin da Bulkuma take kwance, tana hangota a dakin ta sauke ajiyar zuciya.

Ta dawo bakin kofa ta dasa aikin zaman gadi, barci ya sake saceta kamar wacce ake jefa dashi.

Kanta ya karkata gefe yayinda ta fara jin kamar ana kiran sunanta daga nesa.

"Saude... Saude..."

Ta buɗe ido da sauri tana furta, "Na'am?!"

Amma shiru. Ta kalli hagu, ta kalli dama, babu kowa.

Ta dafe kai tana sakin siririn tsaki, "Kai barcin safe da dadi yake amma ina ji ina gani wannan yarinyar ta haramta min shi, babu damar in gyangyaɗa sai ta fita ta nemo min faɗan da zai shafe tarihin dadin barcin safen."

"Wallahi idan na sake barin wannan yarinyar ta fita da sassafe nan, sai dai in manta da barcin dare gaba ɗaya," ta faɗa a ranta tana mai juyawa gefe.

Bulkuma wacce Gwoggo take kira da ‘Ƙullin kuli boton tsakar gida’ idan aka bari ta fita to fa gidan ba zai sake samun salama ba har sai dare ya raba tsakiya domin wani neman ba'asin mantawa ake dashi sai karfe goman dare.

Ko jiya, ta lumshe ido tana tuna abin da ya faru jiya da safe.

JIYA DA SAFE

Kamar abun arziki Bulkuma ta fito tana faman washe baki, Gwoggo Saude dake faman wanke-wanke tace, "Bulkuma, ina zaki je haka da sassafe?”

Bulkuma ta juya da sauri kamar yaron da aka kama yana aikata laifi dumu-dumu, ta ce, "Ba wani waje zan je ba, nan kusa zan leka."

"Nan kusa? Ina ne nan kusa ɗin?" Gwoggo Saude ta tambaya tana mai miƙewa tsaye.

"Wallahi kasuwa ce kawai, nan kasuwa zan je, in dawo nan da nan."

Gwoggo Saude tace, "A wajenki take kasuwa kawai amma ni a wajena tashin hankali ne gangariya domin ban san adadin ƙarar da za'a kawo min ba, ko mai gari bai kaini amsar korafin jama'ar gari ba, sai kace wacce ta haife duniya, da kike cewa kasuwa kawai, idan kin je, sai kin dawo da labari uku: na rigima, na neman ba'asi, da na ƴan amsar ramuwar ɓarnar da kikayi masu."

Bulkuma ta turo baki, "Ni kuma Gwoggo, kina yawan zargina ne kawai, wai ni kullum rigima nike kawowa."

Gwoggo Saude ta ɗaga hannu, "To me ya faru jiya?"

Bulkuma ta yi shiru kamar wacce ruwa yaci, babu baka sai kunne.

Gwoggo Saude ta cigaba da faɗin, "Ba ke ba ce kikaje kasuwa sayayya ba, daga mata ta faɗa maki kudin kaya kikayi mata ihu ɓarauniya saida aka gama lakaɗa mata na jaki sannan kikace ba barauniya bace kudin kayan ne sukayi maki tsaɗa."

Bulkuma ta fashe da dariya tana tuna yadda matar ta ƙirbu a wajen mutane, duka tasha kamar sakwara a turmin daka, bugu tasha ba kaɗan ba barinma dama barayi sun addabi kasuwar da ƴan ɗauke-ɗauke shiyasa shi kanshi bugun da biyu aka yi mata shi.

Ganin tana dariya Gwoggo Saude ta fusata tayo kanta, tayi baya tana faɗin, "Ai gaskiya ne fa... ta rage min kudin mana, abun da yake naira dari tace min ɗari biyar tana min kallon sabuwar shigowa kasuwar zata wanki gara shiyasa nayi mata ihun ɓarawo na nuna mata na fita sanin gari."

"Don tayi maki tsada sai aka ce kiyi mata ihun barawo, haka kawai kin saka an kusa kashe matar mutane, haka ina ji ina gani na miƙa akuyata aka siyar aka yi mata magani da daurin karayar hannu da kafa bayan da na gama bayar da hakuri kamar zan ari baki."

Bulkuma ta ɗaga kafaɗa tace, "Ni dai ba zan bari a cuce ni ba."

Gwoggo Saude ta buɗe ido tana mai dawowa daga duniyar tunanin, ta ja tsaki.

"Yau kam ba zaki fita ba," ta faɗa a fili.

Sai dai kafin ta gama faɗin maganar kofar gida ta yi ƙara ƙiiiirrr, ta zabura tana faɗin, "Ke don ubanki dawo," sai daga baya ta ankara ashe iska ne ya kaɗa kofar


A DAKI

Bulkuma ta buɗe ido ɗaya a hankali, ta saurara taji shiru, ta ƙara saurarawa taji shiru amma duk da haka bata yarda tayi ɓuruntu ba domin ta tuna warning da Gwoggo Saude tayi mata akan yau lock down ne, babu shiga babu fita.

Ta tashi a hankali tana tako da sanɗa kamar ɓarawo.

Tana dosar kofa ta hango Gwoggo Saude ta jingina da bango tana kwasar barci har da munshari.


Ta tsaya tana dariya ƙasa-ƙasa, "Yau ake yin ta, Gwoggo da shirinta ta tashi."

Ta juya a hankali ta ɗauki ɗan ƙaramin tabarma ta shimfiɗa a ƙasa kusa da bango ta kwanta kamar wadda ba ta da niyyar fita.

Gwoggo Saude tayi firgigit tana waige-waige ta hango Bulkuma kwance akan tabarma, ta hauri kafarta tana faɗin, "Ke mi kikeyi a nan?"

Bulkuma tana lumshe idanu kamar mai barcin gaske tace, "Zafin cikin dakin ya koroni na dawo nan, ke kuwa Gwoggo mi ya faru kike barci a bakin kofa?"

Gwoggo Saude ta murtuƙe fuska tace, "Ban sani ba, zakiyi min shiru a nan ko kuma sai nayi maki ɗan banzan dukan da zai saka ki tuna dalilin da kyau."

Bulkuma naji zancen duka tayi lukus, Gwoggo bata cika dukanta ba amma idan ta tashi ba dukan wasa takeyi ba, tara mata gajiya takeyi da kyau.


Bayan minti biyu, barci ya ƙara kwasar Gwoggo Saude.

Bulkuma ta buɗe idanu ta kalleta ta miƙe a hankali, tana ɗaga ƙafarta ɗaya bayan ɗaya tana sanda kamar ɓarawo.

Ta buɗe kofa kaɗan, kofar ta ɗan yi ƙara ƙiiiirrr, Gwoggo Saude ta motsa. Bulkuma ta tsaya cak tana muzurai.

Gwoggo Saude ta ɗaga kai kaɗan sai kuma ta sake sunkuyar da shi.

Bulkuma ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, ta buɗe ƙofar da salo irin na ƙwararriyar ƴar gudu, ta fice fitt.

Ta rufe ƙofar a hankali kamar babu wanda ya taɓa budeta.


Gwoggo kuwa sai bayan mintina biyu sannan ta buɗe idanu ta gyara zama da sauri. Ta kalli ƙofa ta ga a rufe. Ta ɗan yi murmushi tana mai faɗin, "Yau dai na yi nasara..."

Ta jingina da bango cikin jin daɗi, barci yana kwasarta har kofa ta buɗe kasancewa sakayawa Bulkuma tayi.

Ladiyo ta zo wucewa ta ce, "Gwoggo Saude, Bulkuma ta wuce ƴar yara da gudu fa."

Gwoggo Saude ta miƙe tsaye da firgici kamar wacce aka tsikara tace, "Meyyy?!!!"

Ta duba ƙofa. Ta duba cikin gida. Ta sake duba waje. Ta dafe kai tana faɗin, "Wallahi wannan yarinya ba mutum bace, aljana ce!" 😭

Tayi zaman daɓaro a ƙasa tana jimamin abun da zaije ya dawo, "Shikenan... sai mu jira labari."

********

A bangaren Bulkuma kuwa tana fita a gujen nan sukayi arangama da Jamila ƴar gidan Ladi mai kalwa, rubbar nika dake a saman kan yarinyar tayi dandamalin dama-dama a ƙasa.

Bulkuma bata tsaya ganin aika-aikar da tayi ba ta ƙarawa gujenta iska.

Jamila tana kuka wi-wi ta tattara fasashiyar robar tayi hanyar gida.

Jamila ta shiga gida idonta cike da hawaye tana kuka shabe-shabe har da majina.

Ladi ta dafe kirji ganinta rike da ɓaraguzan roba, ta kalleta ta kalli ɓararriyar roba da ke a hannunta.

Tana hau salati tana tafa hannu, "Yanzu da na baki nikan shine kikaje kikayi min ɓari."

Jamila tayi baya da sauri tana faman girgiza kai tace, "Wallahi innarnu ba ɓari nayi ba."

Ladi ta zuciya kamar zata kai duka, "To uban miye ya samu roɓata ta koma ɓaraguzai marassa mamora?"

"Ɓare min shi aka yi."

Saida Ladi ta lailayo ashar ta lailaya sannan tace, "Wani marar kunyar yaron ne yayi maki haka. Inje mu dambace da uwarsa."

Jira kawai take a faɗa mata suna ta suri mayafi taje ta tambayi dalili, saidai ace bata da haƙuri.

Jamila ta ɗaga kai idonta cike da hawaye tace, "Bulkumar tsallaken tudu ce..."

Ladi ta suri mayafi, ta ɗaga hannunta cikin gaggawa tana maganar kamar zata ari baki, "Wuce mu je wajen uwarta in ji dalilin da ya saka tayi maki wannan ɓarnar da gangan din."

Jamila tayi turus, Ladi ta fusata ta daka mata tsawa, "Don ubanki taka, muje!"

Jamila tace, "Inna mu tausayawa matar nan. Kada yawan kai ƙarar Bulkuma ya saka ta har ta hadiyi zuciya ta mutu."

Ladi ta ɗan yi turus tace, "Hakane kuma da wannan don wannan. Matar nan bata da damuwa ko kaɗan, amma waccen ifirituwar yarinyar daga riko ta zame mata Allah ƙaƙai. Shi Malam Garban da take ɗiyar ƙanwarsa, ya buge da neman kudi ya gudu ya bar saude tana ta shan wahala. Haka shekaran jiya yarinyar can tayi wa wata mata ihu ɓarawo, ta saka aka yiwa matar dukan tsiya, har aka ƙarya mata hannu da kafa. Kai da ace ni ce Saude da ta tuni na watsar da ɗan mangoro na huta da kudaje."

Ta dauki buhu ta auno wata masarar ta ɗaura mata a kai bayan da ta buge mata warning, "Ko mafarkinki kada yabi ta wajen gidansu waccen yarinyar, kiyi zagaye ki kai min nikana lafiya ki dawo min dashi lafiya, don na rantse idan aka ƙara min ɓari bazan yarda ba."

Ita kanta Jamila ba zata yi gigin bi ta hanyar gidansu Bulkuma ba, a cewarta zaman lafiya yafi zama ɗan sarki, ko da yawon mayar da nika aka barta an cuceta.

********

A Gidansu Bulkuma Kuwa.

Gwoggo Saude ta miƙe jiki a sanyaye, ta leƙa kofar gida saida gabanta ya yanke ya faɗi hango garin masara yayi dabgaro a dandamalin ƙasa. Tun daga nan jikinta ya bata akwai damuwa, ta fahimci wannan aiki ba na kowa bane sai Bulkuma.

Ta koma cikin gida ta auna masara mudu ɗaya ta zuba a buhu koda ƴan neman ba'asi mun zo ba sai tayi wahalar awo ba.

Ta fara kiciniyar damun kokon safe, ta gama ta zauna akan tabarma, idonta na leƙa kofa, tana jiran wadanda aka yi wa aika-aika su zo neman ba'asi ta bayar da haƙuri.

A wannan halin ne Iya Mairo tayi sallama, da sauri Gwoggo Saude ta miƙe tana faɗin, "Don Allah kiyi haƙuri don yau ne ka haifeshi baka haifi halinsa ba, ga masara nan kiyi hakuri bani da kudin nika da na baki."

Iya Mairo tayi turus tana faɗin, "Hala mutuniyar ce ta janyo faɗa kike jiran bayar da haƙuri, to bani tayi wa ɓarna ba, ni zuwa nayi ki ara min wannan kwallar taki in nunawa Aminu idan yaje kasuwar birni ya siya min irinta."

Gwoggo Saude tace, "To..." Ta juya zuwa dakinta ta dauko kwallar ta kawo mata.

Iya Mairo ta amsa tana ƙara mata jajen shegen rashin nutsuwar Bulkuma da ya saka kullum take aikin kwara kai da masu talla ko nika ana zuwa tambayar ba'asi.

A zahirin gaskiya Bulkuma bata da mugunta ko rashin kunya, bata da neman faɗa, saidai bata da nutsuwa ko kaɗan, ga ƴar banzar wauta, kullum cikin gudu take shiyasa bata da rabo da cin karo da masu talla da ƴan kai nika.

Sannan fa ita tace duk wanda yayi mata kan kara sai tayi mashi na itace ya shekera ya shekare yana amfana, shiyasa matar nan ta kasuwa da ta nemi ta raina mata wayo ta siyar mata kaya da mugun tsaɗa ta buga mata ihu ɓarawo.

Bugu da ƙari duk idan taga abun dariya sai ta dara a cewarta faɗan da babu kai ciki dadin kallo gareshi.

Akwai ranar da Kuluwar Mas'udu tana cacar baki da facalarta har ana buga kwano da bango ana surfawa juna zagi ta uwa ta uba, zuciya takai wuya kiris ake jira a daku. Bulkuma ta shiga kallon faɗa ta hau waka tana rera 'Bamu rabawa saidai mu ƙara zugawa, bugi cikin, mari kuncin, wawuro kafafun'

Suka zuciya suka janyota suka saka a daka suka mata shegen duka suka wurgota waje, ta dawo gida tana kuka shabe-shabe da fuska a jeme an haɗa mata jini da majina. Gwoggo Saude tayi kamar bata lura ba.

Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)