MATAR GIDA PAGE 13
MATAR GIDA 013
SHUUKRAN /022
P13
Shiru ta yi tare da ƙorawa ruwan dake cikin pool ido sosai ta yi nisa cikin tunani,wata murya da bata san ko na waye ba ya katse mata tunani,a hankali ta ɗago manyan idanunta ta zuba masa wani matashi ne da a ƙalla zai yi shekaru talatin da tara zuwa arba'in a duniya kallo ɗaya Amirah ta yi masa ta dauke kai,kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci baya cikin hayyacin sa a buge yake,kujerar dake fuskantar Amirah ya ja ya zauna ya ƙoreta da ido ita dai bata sake kallon inda yake ba,fuskarsa dauke da murmushi ya ce ''baiwar ya aka yi ne?" Amirah ta yi shiru bata ce komai ba nan ya daura da ''gaskiya kin haɗu fa,ko zan iya samun number ki" sai a sannan Amirah ta mayar da dubanta garesa cikin sanyin murya ta ce ''bawan Allah ina da aure,tare da mijina nake,in babu damuwa ko za ka iya ƙyale ni'' wani kallon rainin wayo ya yi mata kafin ya ce ''wani mijin?" Amirah ta dauki kofin juice dake gabanta ta kurɓi kaɗan daga ciki, gaba ɗaya ta gama tsorata daidai lokacin da ta ajiye kofin ta jiyu muryar matashin ya ce ''karya kike tun ranar Lahadi kike hotel ɗin nan ban taɓa ganin ki da wani ba,ke kadai ki ka zo'' shiru ya yi yana ƙare mata kallo fuskarsa dauke da murmushi ya ce ''number ɗakin ki 1321 hawa na uku'' sai kuma ya daura da ''kullum karfe biyar kina fita siyan abinci,l have been wathcing you all this while'' Amirah da ta gama tsorata da lamarinsa ta dauki wayarta ta fara danna trying to be calm,matashin ya ce ''ko dai akwai wanda kike jira?ina nufin ko akwai wanda ya ajeyi ki ya biya maki kuɗin daƙi kafin ya zo?" ya ƙare magana tare da kafe ta ido,a hankali Amirah ta dauki ƙaramar hand bag ɗinta ba tare da ɓata lokaci ba ta bar wajen shi kuwa wannan matashin sai faman dariya yake tare da ɗaga murya yana faɗin ''zan ziyarce ki da dare''
Bayan komawar Amirah ɗaki bata zauna ba saida ta kulle ko ina a ɗakin ta tabbatar ta kulle ko ina kafin ta samu waje bakin gado ta zauna tana mayar da numfashi,sosai ta tsorata da lamarin wannan mutumin,dole ta bar hotel ɗin kafin dare,wannan tunanin yasa ta tashi ta fara haɗa kayayyakin ta,cikin ƙanƙanin lokaci ta gama haɗa kayanta,ba tare da ɓata lokaci ba ta fita daga ɗakin sanye da dogon hijab har ƙasa,bayan ta rufe kofar ɗakin tana shirin barin wajen kofar taga wannan matashin ya fita daga elevetor da sauri Amirah ta dauke kai kamar bata gansa ba,jakar kayanta da take riƙe da shi ta ƙara ɓoye cikin hijab yadda ba zai gani ba,gaba ɗaya kanta ya kulle hakan yasa ta tsaya nan wajen kofar ɗakinta,idonsa a kanta ya nufo har inda take tsaye zuwa yanzu Amirah ta gama tsorata jira kawai take ya taɓata ta kurma masa ihu,amma sai ta ga ya buɗe daƙin dake kusa da nata hakan yasa Amirah sauke wata doguwar ajiyar zuciya bayan ya buɗe kofar ɗakin ne ya mayar da dubansa gareta ya ce ''karfe tara zan shigo ki shirya kafin nan''ya ƙare magana yana sakar mata wani irin murmushi,bayan Amirah ta tabbata ya shiga ɗakinsa ta nufi elevetor da wani irin sauri,bayan fitar ta daga elevetor ta yi checking out hotel room kafin ta bar harabar hotel ɗin, gaba ɗaya bata cikin nitsuwa,tafiyar mintina goma ne daga hotel ɗin zuwa bakin kwalta,bayan fitarta bakin kwalta da ƴan mintina ta tare abin hawa,nan me adaidaita ya tambayeta ina zata shiru ta yi tana nazari,sake tambayar ta me adaidaita ya yi a karo na biyu nan ma shiru ta yi na wasu ƴan sakanni tunawa ta yi da ƙawarta Rumaisa dake aure a unguwar Malali rabon Amirah da ita tun haihuwar Rayyan,bata da tabbacin har yanzu Rumaisa na garin Kaduna ko a'a ita kaɗai ce ƙawarta a nan garin hakan yasa ta cewa me adaidaita ya kaita Malali,tafiyar mintina ashirin da biyar ne daga inda me adaidaita ya dauko Amirah zuwa unguwar Malali har kofar gidan Rumaisa me adaidaita ya kaita bayan fitarta daga adaidaita ta biya me adaidaita,tsayawa ta yi kofar gidan Rumaisa na wasu ƴan mintina tunawa da irin wulakancin da Ɗalha ya yiwa Rumaisa ranar sunan Rayyan yasa Amirah taji gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi,tun daga wannan ranar Amirah ta yanke duk wata alaƙa tsakaninta da Rumaisa da ma sauran ƙawayen ta gaba ɗaya bisa umurnin Ɗalha,ko kiranta Rumaisa ta yi bata ɗaga kiran saboda Ɗalha ya ce ko waya ta yi da Rumaisa bai yafe mata ba,hakan yasa ko kira ɗari Rumaisa za ta yi mata bata ɗaga daga karshe Rumaisa ta hakura ta daina kiran Amirah gaba ɗaya, jiki babu kwari Amirah taja kafarta zuwa cikin gidan,sallama dauke a bakinta ta shiga gidan, gida ne irin ta masu karamin karfi ɗakuna huɗu ne a gidan kowanne da parlour da kuma bayi a ciki sai kitchen da bayan gida dake waje,dake can ƙarshen farfajiyar gidan babu laifi gidan na da girma farfajiyar ma tana da girma daidai misali,a hankali Rumaisa ta ɗago jin murya kamar ta Amirah hannunta riƙeY da buta,galala ta yi tana ƙarewa Amirah kallo cike da mamaki ta ce ''wa nake gani haka kamar Amirah'' Amirah ta ƙirkire murmushi da bai kai ciki ba ta ce ''ni ce'' Rumaisa ta faɗaɗa murmushi ta ce ''sannu da zuwa maraba'' ta faɗa tare da ajiye butan dake hannunta ta yunƙura ta miƙe tsaye tare nunawa Amirah hanyar ɗaki bayan shigarsu ɗaki ne Amirah ta ajiye jakar kayanta bisa ɗaya daga cikin kujerun parloun,Rumaisa ta mayar da dubanta gareta ta ce ''ki shiga ki yi alwala bara naje na yi sallah'' a kunyace Amirah ta amsa da ''to'' kamar yadda Rumaisa ta faɗa mata hakan ta yi tana cikin sallah ne wata budurwa da bazata wuce shekaru ashirin a duniya ba ta shigo parlourn bakin dauke da sallama,bata tsaya ɓata lokaci ba ta wuce bathroom dake cikin dakin ta dauro alwala kafin ta fito ta shimfiɗa darduma gefin Amirah ta tayar da sallah bayan ta idar da sallah ta mayar da dubanta ga Amirah ta gaishe Amirah cikin girmamawa ganin Amirah ta girme ta nisa ba kusa ba yasa ta shiga nitsuwa ganin yadda ta takure kanta ne yasa Amirah mayar da dubanta gareta ta ce ''yaya sunanki''kamar jira take ta ce sunana Yasmin ƙanwar me gidan ce ni'' Amirah ta ce ''masha Allah'' daga haka bata sake cewa komai ba ita dai Yasmin ta cigaba da danna wayarta
Karfe takwas da rabi Rumaisa ta shigo ɗakin hannunta riƙe da flask ɗin abinci zuwa yanzu ta canza kayan jikinta daga lace zuwa wata doguwar rigar barci yadin rigar mai taushi ce sosai ja ta daura farin hijab a kai,tun ɗazu Amirah na jin yadda Rumaisa ke fama da yaranta wajen wanka da cin abinci da kuma homework,bayan ta ajiye flask ɗin ne ta samu waje ta zauna nan suka ƙara gaisawa da Amirah shiru ne ya biyo baya Amirah na son faɗawa Rumaisa Ɗalha ya saketa amma bata san ta inda zata fara ba,ita ko Rumaisa har yanzu mamaki take saboda tun jiya ana ta posting a group ɗinsu ana cigiyar Amirah ita a tuaninta ma Amirah bata garin amma to me yasa ta baro gidan mijinta kuma me yasa bata tafi gidan iyayenta ba,jin shirun nasu ya yi yawa ne yasa Yasmin fita daga ɗakin ta yi hakan ne dan ta basu waje su samu damar magana,bayan fitar Yasmin ne Rumaisa ta mayar da dubanta ga Amirah ta ce ''dama kina garin nan?" Amirah ta yi murmushi bata ce komai ba can Rumaisa ta ce ''jiya naga an yi posting a group mijinki da ƴan uwanki suna neman ki'' Rumaisa ta yi shiru tana ƙarewa Amirah kallo da ta ƙurawa tiles ido gaba ɗaya ta ƙasa hada ido da Rumaisa tsabar kunya,bayan wasu ƴan sakanni Rumaisa ta ce ''kin yi yaji ne?" murya can ƙasa Amirah ta ce ''a'a'' tana ƙoƙarin hana kanta kukan da ya taso mata,cikin raunanniyar murya Rumaisa ta ce '' me yasa za ki bar gidan mijinki da ƴaƴanki ba'a san inda ki ke ba har iyayen ki babu wanda yasan inda kike,me ya yi zafi haka Amirah? na san ki da hakuri da juriya ya aka yi ki ka yi rauni haka?" Amirah ta yi shiru hawaye da ta daɗe tana ɓoye ya samu damar zuba a hankali ta kai hunnu ta fara share hawayen, har yanzu Rumaisa ta ƙasa fahimta dalilin da yasa Amirah zata tafi ta bar yaranta wai har ana cigiyar ta a ƙafan sada zumunta,hawayen da ta gani a fuskar Amirah ya sa ta yi tunanin ko aure Ɗalha zai yi,ba tare da wani dogon tunani ba ta ce ''zai maki kishiya ne?" Amirah ta amsa da ''eh'' cikin muryar kuka,wani irin tsaki Rumaisa ta yi kafin ta ce ''kawai dan zai yi aure sai ki bar masa gida har yaranki,tsakani da Allah'' tun sanda Ɗalha ya saketa bata taɓa shiga yanayin da ta shiga yanzu ba,tun bayan sakinta bata samu damar yin magana da kowa ba iyaka da dare ya yi ta rungume matashi ta yi kuka har barci ya dauke ta,yau ya zama rana na farko da zata fadawa wani Ɗalha ya saketa zuciyarta ta yi mata wani zafi haɗe da nauyi ji ta yi kamar an daura mata dutse a kirji da ƙyar ta ke fesgar iska,gaba ɗaya ji tayi numfashinta na niman yankewa da kyar ta samu ta saita kanta cikin wata iriyar murya me cike da ƙunci da baƙin ciki ta ce ''saki na ya yi''
SHUUKRAN/022