MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 14

by @maimunabala209

MATAR GIDA 014


SHUUKRAN/022





P14



Baki buɗe Rumaisa ke kallon Amirah dake faman kuka kamar ranta zai fita tun barinta gidan Ɗalha sai yau ta samu ta yi kuka son ranta,bayan wasu ƴan sakanni Rumaisa ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya kafin murya can ƙasa ta ce ''ki yi hakuri Amirah ki dauki sakin da ya yi maki a matsayin ƙaddara babu bawa da baya haɗuwa da kaddara,ki yi hakuri ki daina kuka ki yi addu'a domin ita ce mafita gareki'' daga haka Rumaisa ta yi shiru tana ƙara jaddada lamarin sakin da Ɗalha ya yiwa Amirah,Amirah ta dauki a ƙalla mintina ashirin tana rera kuka yadda ta daura kanta a cinyar Rumaisa ita dai Rumaisa bata hanata kuka ba,bayan wasu ƴan mintina Amirah ta yi shiru ta shiga sauke ajiyar zuciya,ganin haka yasa Rumaisa yiwa Amirah nasiha da rarrashi Rumaisa ba ita ta bar ɗakin ba sai karfe goma saura nan dan mijinta ya dawo gida ne yasa ta yiwa Amirah sallama daga haka ta fita daga ɗakin zuwa ɗakin mijinta yadda Amirah ta wuce bathroom dake cikin ɗakin ta yi wanka bayan fitarta daga wanka flask ɗinda Rumaisa ta shigo mata da shi ta bude taga tuwon shinkafa ne da miyar ganye sarving kanta ta yi kafin ta samu waje ta zauna ta fara cin abinci bata ci da yawa ba ta je ta ƙoshi hakan yasa ta rufa sauran daga haka ta wuce bathroom ta wanke baki da hannu,kwanciya ta yi kan gado dake ɗakin bayan wasu ƴan mintina Yasmin ta shigo ɗakin yadda ta kwanta a ɗaya bangaren
















Karfe shidda da mintina hamsin na safiyar Laraba Ɗalha ne zaune cikin parlour tare da yara yana zuba masu abinci cikin plate wanda zasu ci a gida kafin su tafi makaranta kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yau ɗin yana cikin farin ciki,dalili kowa shine yau ya gama wa yaran shirin da wuri,insha Allah zasu tafi makaranta kafin karfe takwas,tsayawa ya yi a kansu suna cin abinci gudun kar suyi faɗa ita dai Fauziyya tana manne da shi sam taƙi zama ta ci abinci ita dole Dady zai bata duk yaran suna cin abinci da cokalin amma banda Suhail dake ci da hannu a cewar sa cokali zata ƙona masa baki amma in yana ci da hannu to hannusa ne kawai zai masa zafi amma abinci bazai ƙona sa a baki ba,Ɗalha bai bar wajen ba saida ya tabbar sun gama cin abinci kafin ya wuce ɗakinsa ya cire kayan da zai sa ya daura kan bed kafin ya wuce bathroom ya haɗawa kansa ruwan wanka,fita daga bathroom ɗin ya yi ya mayar da dubansa ga Fauziyya dake riƙe da plate ɗin dafa duka na taliya tana tsaye kusa da gado,ganin ta tsaye kusa da gadon yasa ya dauke ta ya daura ta kan kujerar dake gaban madubi ya ce ''ki zauna a nan ki ci abinci sannan kar ki tashi ki je ko ina har sai kin gama cin abinci'' alama ta yi masa da kai cewar ta ji,ba tare da wani dogon tunani ba Ɗalha ya shiga bathroom,kamar yadda ya faɗa mata hakan ta yi nan kan kujera ta zauna ta ci abincinta bayan ta gama ci ne ta kalle hannunta taga duk ya ɓaci da mai da kayan miya nan take taji tana son wanke hannu ga shi Dady ya ce kar ta je ko ina ta zauna cikin ɗakin nan ta shiga dube dube, idonta ne ya sauka kan kayan da Ɗalha ya fidda da niyyar zuwa office da su ba tare da ɓata lokaci ba Fauziyya ta sauka kan kujerar da Ɗalha ya daurata ta nufi inda ya zuba kayan ta kafe farar shaddar da ido kamar wacce aka yiwa wahayi kawai ta dauki rigar farar shidda ta shiga share hannunta da shi haka ta yi ta share hannu da rigar har Ɗalha ya fita daga bathroom ya tarar da ita tsaye,zaro ido Ɗalha ya yi tsabar mamaki bai san sanda ya ce ''kan uba me zan gani haka Fauziyya?" ita kowa Fauziyya ta wangale baki tana dariya ta ce ''na iya wance hannu Dady'' Ɗalha bai san sanda ya dafe kai ba ya ce ''na shiga uku wayyo Allah nagode maka'' ita dai sai faman dariya ta ke tana faɗin Dady na iya wance hannu karɓar rigar Ɗalha ya yi daga hannunta yana ƙarewa rigar kallo Fauziyya ta ce ''Dady ji ka wanke rigar na sa maka miya hannu na ya yi kyau'' Ɗalha ya sauke ajiyar zuciya tare da ajiye rigar bai sake bi ta kan Fauziyya ba dake ta faman zuba masa surutu,wasu kayan ya duba ya shirya kansa,daukar Fauziyya ya yi zuwa bathroom ya wanke mata hannu da baki kafin ya fita daga ɗakin hannusa riƙe da Fauziyya ganin su Sudais ya yi zaune cikin parlour sun ƙorawa talabijan ido,shiga parlourn ya yi ya kalle tv yaga carton suke kallo hakan yasa ya daka masu wani uban tsawa ya ce ''me ku ke yi har yanzu baku sa uniform ba?" duk suka mayar da duban su ga mahaifinsu suna kallonsa kamar yau suka fara ganinsa,Rayyan ya yi karaf ya ce ''saboda ba a wanke mana ba'' Ɗalha na shirin magana Suhail ya ce ''me yasa baka wanke mana uniform ba Dady har na islamiyya fa ba'a wanke ba kowanne ranar talata Mumy ke wanke mana uniform da mun dawo daga makaranta'' shiru Ɗalha ya yi yana bin yaran da kallo Suhail ya daura da ''me yasa baka wanke mana ba?yanzu me zamu sa mu tafi makaranta?'' a sanyaye Ɗalha ya samu waje ya zauna nan cikin parlour murya can ƙasa ya ce ''bazan iya ba...na gaji ina ki ka shiga Amirah zan yi duk wani abinda ya dace dan na dawo dake kafin hidimar yara ta kashe ni'' Suhail da ya kafe mahaifinsa da ido ya ce ''da wa ka ke magana Dady?" jiki babu kwari Ɗalha ya tashi ya nufi inda yake ta tabbacin uniform ɗinsu yake ya kwashe uniform ɗin,kitchen ya nufa ya zuba uniform cikin injin wanke kallon agogo ya yi yaga karfe bakwai da mintina ashirin,injin zai dauki a ƙalla mintina arba'in kafin ya gama wanke kayan da daurewa har busar da su,waje Ɗalha ya samu ya zauna cikin parlourn,Allah ya taimake Ɗalha carton ɗin da suke kallo ya dauki hankalinsu sosai hakan yasa basu sa shi magana ba, Rayyan da Afef ma basu yi faɗa ba Suhail ne kaɗai na rinƙa sintiri zuwa kitchen shan ruwa amma  ba ruwa yake zuwa sha ba,abinci da ya yi saura  cikin tukunya yake zuwa ci,bayan Ɗalha ya gama sa masu uniform ne Suhail ya kalle sa ya ce "haka zamu sa uniform ɗin ba'a goge mana ba?"  kuma basu gama bushewa ba akwai sanyi  a takaice Ɗalha ya ce ''eh'' tare da banka masa harara
















Karfe takwas da mintina ashirin Ɗalha ya gama shirya yaran kowanne su ya dauki jakar makarantar sa tare da jakar abincin sa yau ma kamar kullum kowanne riƙe da jakar lunch box ɗaya banda Ummu Abiha dake riƙe da extra lunch box,bayan duk sun fita ya rage Sumayya,Ɗalha ya kunna mota yana shirin fita daga gidan Sumayya ta fito riƙe da wando extra a hannunta bayan wanda take sanye da shi,fuskarta a haɗe jira take a yi mata magana ta fasa kashi kallo ɗaya kawai Ɗalha ya yi mata bai ce komai,bayan shigar ta motar ne Sudais ya ce ''Dady kafar Rayyan babu takalmi,ya ɓatar da takalminsa'' wani mugun kallo Rayyan ya rinƙa yiwa Sudais dan ya tona masa asiri,Ɗalha ya mayar da dubansa ga agogo dake daure tsintsiyar hannusa yaga karfe takwas da rabi daidai,kawai ya tada motarsa sun fita daga gidan,ta cikin madubi ya rinƙa kallo yaran ta bayan mota,yau tun kafin su kai bakin kwalta Ummu Abiha ta buɗe lunch box ta fara cin abincin dake ciki,Sumayya ko na riƙe da dayar wandon kamar wani zai kwace mata ga Rayyan kafafunsa babu takalma,muryar Suhail ne yasa Ɗalha mayar da hankali kan tuƙin da yake inda ya ce ''wa kake kallo Dady?" Ɗalha bai tanka sa ba ya cigaba da tukin sa, basu suka kai makaranta ba sai karfe tara daidai yau Ɗalha bai yi wahala shiga yiwa head mistress magana ba,bayan ya zuba yaran ya ja motar sa 











Karfe tara da mintina ashirin Ɗalha ya yi parking mota a harabar kamfani daidai lokacin kira ya shiga wayarsa bai tsaya duba mai kiran ba ya yi wucewarsa office, bayan shigarsa office ne ya duba mai kiran yaga Ammi ce sai da zuciyarsa ya kusa bugawa shiru ya yi ya ƙorewa screen ɗin wayar ido yana shirin kiran Ammi kiran Unaisa ya shiga rabon da su yi waya tun daren littini tun jiya take faman kiran sa bai ɗaga ba yanzu ma ya zuba wa wayar ido har kiran ya katse bai amsa ba,bayan kiran Unaisa ta tsinke ne Ɗalha ya yi kira layin Ammi bugu ɗaya Ammi ta amsa kiran,cike da girmamawa Ɗalha ya gaishi ta,Ammi ta yi shiru bata amsa ba,hakan yasa Ɗalha yin shiru yana nazarin abinda zai faɗa mata bayan wasu ƴan sakanni Ammi ta ce ''Amirah ta dawo?" wani ɓoyayyar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke cike da tsoro ya ce ''a'a'' yana shirin magana ya ji Ammi ta kashe wayarta,Ɗalha ya ƙorawa wayar ido bayan ya cire wayar daga kunnen sa,jiki babu kwari ya sake kira layin Ammi amma bata dauka ba,sai da ya yi mata kira huɗu amma bata ɗaga ba hakan yasa ya hakura ya ajiye wayar,shiru Ɗalha ya yi akwai maganar da yake son yiwa Ammi yana son ya roƙeta ta tura masa Salame ɗaya daga cikin ƴan aikinta ya samu ta taimaka masa wajen kula da yaran,har ga Allah ba zai iya cigaba da kula da yaran shi ƙadai ba,daga ranar Lahadi zuwa yau Laraba gaba ɗaya ya gaji har ya fara tunanin ƙila jininsa ya hau saboda rashin hutu ga kuma caza masa kai da yaran ke yi,bayan dogon tunani ya sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya murya can ƙasa ya ce ''Amirah jarumar mace ko ya take kula da yaran ita kaɗai oho'' shiru ya yi tare da rintsa idanunsa kafin a hankali ya furta ''rabbi ka bayyanar min da matata duk inda take ya rabbi ka kare min ita,Allah ka dawo da ita cikin aminci ya Allah ka huci zuciyarta'' a hankali ya kai ya hannu ya dauki wayarsa ya kira layin Ammi sai da wayar ta kusa tsinke kafin Ammi ta amsa cike da nitsuwa Ɗalha ya ce ''barka da hutawa Ammi'' murya babu yabo babu fallasa Ammi ta ce ''barka dai lafiya ka ke ta faman kirana haka?Ɗalha ya yi shiru bai ce komai Ammi ta daura da ''na tambaye ka ko matarka ta dawo ka ce a'a kaga kuwa babu wata maganar da zan yi da kai'' cike da girmamawa Ɗalha ya ce ''Allah ya huci zuciyarki Ammi mun kai cigiyarta gidan rediyo da talabijan ko Allah zai sa a dace'' Ammi ta yi shiru bata ce komai ba,cikin kwantar da murya Ɗalha ya ce ''Ammi in babu damuwa dan Allah ko za ki iya turo min ɗaya daga cikin ƴan aikin ki ta taimaka min wajen kula da yaran'' Ammi ta yi shiru kamar bata ji abinda ya faɗa ba bayan wasu ƴan sakanni ta ce ''lyan Salame ta je ƙauye jinyar mahaifiyarta,yanzu haka Salame ce kaɗai a gidan'' shiru Ammi ta yi kafin ta ce ''kar ka je komai za ka iya kula da su tunda uwarsu ƙazama ce''







SHUUKRAN /022