24
Chapter 24.
"Ni da gidana har akwai wanda ya isa ya hana ni shiga inda na ga dama?" Ta girgiza kai, kana cikin dakiya da son ɓoye zallan tsoron da ya gama mamaye zuciyarta ta ce. "To me kake so, me kake nema a nan?"
"Na zo amsan abin da ke shi ke nawa." Gaban ta ya faɗi. "Wani abu?" Ya ɗan murmursa. "Kina bani mamaki wallahi, a yadda na ke ganin ki kyakkyawa da iliminki da wayewarki ban ɗauka zan sha wahalar shawo kanki har haka ba, a yadda kike wayayyiya nan ya ci a ce kin fahimci abin da na ke so daga gare ki tun farko." Ya dan ja tsaki.
"Ni har kin sa ina rena wayonki."
Duk da ta fahimci inda ya dosa bai hana cikin rawar murya ta ce. "To me kake nufi me kake so?"
"Yauwa kina jina, ina nufin ki bani gishiri na ba ki manda na ke nufi, ki bani jikin ki ni kuma na yi maki alqawarin komai da kike so na jin dadin rayuwa zan ba ki. Kuma karki damu da iyalina ba abin da Binta za ta miki, idan ma kika ce nan din bakya so to ni me kama mike wani gidan ne, har mota zan siya miki ki faɗi komai da kike so ni me cika miki ne. Kawai abin da na ke so da ke ki bani haɗin kai komai ya tafi yadda kamata, ni kuwa zan canza miki rayuwa. Ke kin ganki Kuwa?" Sam baki yi kama da yar wahala ba dubi fatar ki yadda take luwai luwai so soft, kyau ne Allah ya kashe ya baki dan haka ki san yadda za ki anfani da shi ki waye mana kina abu kamar wacce ba a birni take ba."
Tunda ya soma magana Nazli ta koma can lugu bayan gas ta tukure wuri guda idanuwan ta kuwa sun cika taf da kwalla jikinta kuwa tuni ya soma ɓari, sake maze roƙon mopper da ke hanunta ta ce.
"Dan Allah ka yi haƙuri kar ka cutar dani, wallahi aiki ne ya kawo ni gidan ka ba wani abu ba. Ni ba zan taɓa aikata abun da kake nema na da shi ba, kuma kai ma da kake yi ina rokon Allah ya shirye ka ya fidda hakan daga ranka ya ganar da kai gaskiya, na roƙe ka da ka barni bana so idan aikin ne baka so to na rantse ni me bari ce ko yanzu ka ce ba ka bukatar mu a gidan ka zamu bar ma shi amma kar ka min abin da zai sa na tsane ka, na ƙi yafe maka duniya da lahira."
Guntse fuska ya yi, kana wannan karon babu wasa cikin muryarsa ya ce. "Karfa ki nemi ki rena mini hankali, kin ga na yi miki kama da wanda ya ke son tuba a yanzu ne da za ki nema min gafara, wato ko. Dan kin ga ina bibiyar ki ta lalama shi ne kike ƙoƙarin kawo min iyayi to bara ki ji daga ke har uwar ta ki ba wanda ya isa ya hana ni yin abin da na yi niyya a yau ba idan da akwai kuma to nuna min shi. Kaya ne na gani kuma sai na maida kwalamata, ke ban da abun ki har kin samu ana lallaɓa ki kina botserawa?" Ya ja kwafa, daga haka ya nufo ta gadan gadan, ihu ta saka tare da fisge fisge daga riƙon da ya kai mata sai da riƙo bana wasa ba ya yi mata, tattara karfin ta ta yi ta gantsara masa cizo a damtsen hannunsa na dama.
Ƙara ya saki tare da hankaɗe ta gefe yana yarfe hannu cikin zafin cizon, Nazli na ganin wannan damar ta miƙe cikin azama da gudu ta nufi ƙofa tare da murɗe key sai dai ko kan ta kai ga bude ƙofar ta ji ya damƙi gashin kanta tare da yin baya da ita ya jawo ta gabansa.
Kana ya ɗauke ta da maruka zafafa hagu da dama. "Ke har kin isa ina bin ki kina jana a ƙasa?" to wallahi yau ko mutuwa za ki yi sai na samu abin da na ke so, idan kin ga kin fita daga hannuna yau to bayan na biya bukata kenan."
Daga haka ya saɓata a kafaɗa, da hannu ɗaya ya buɗe ƙofa ɗayar hannun kuma ya riƙe ta tsam a kafaɗansa duk fisge fiszgen ta a banza sai kuka take tana ƙiran sunan Ammie.
Har sama cikin ɗakin sa ya kaita ya kulle ƙofa kana ya juyo ya taka cikin ɗakin, kan gado ya yi wurgi da ita. "Gwara ma ki taimaki kanki ki mu yi komai cikin lumana da da daɗin rai da wannan yunƙiri na ki dan ba mai ceton ki a hannuna yau, da zai fi miki ma ki saki rai ki kwashi garima yarinya ki ji abin da ake ji kema."
"Ƙarya kake wallahi ba zan taɓa yarda da kai ba, sai dai ka kashi ni amma ba zan taɓa bari na haɗa jikina da ƙazamin na ka ba, idan kai jahillci da son zuciya sun rufa ma ido to ni na san me na ke darajar kaina da ta addina. Wallahi sai Allah ya saka min ba zan taba ya fe maka ba mugu kawai."
Murmushi ya yi. "Wai ashe dama haka kike da baki?" I like it. Sai na ji kin sake burgi ni."
Ganin ko a jikinsa zagi da ta ke aika masa ya sa ta rausayar da murya ta ce. "Dan Allah ka yi wa Allah da manzon sa ka yi haƙuri ka kyale ni, ka tuna duk abin da ka yi wa dan wani to za a yiwa na ka. Kana da ƴa kana da mata kana kuma da ƙanwa karka sa Allah ya kama ka da su, kar ka ja masu masifar da ba su san musabbabin ta ba. Kar ka yi sillar jefa rayuwata cikin wani siraɗin dan Allah ka barni na tafi."
Jikinsa ya ɗan yi sanyi da maganganun ta a hankali ya matso bakin gadon dab da ita ya tsuguna gaban ta, har ta yi zaton nasihar ta ce ta shige shi sai ta ji yana fadin.
"To ki bari na yi sau ɗaya!, sau daya kawai za ki bari na yi daga baya sai mu roki Allah zai yafe mana saboda shi gafurur rahim ne komai ka yi ka tuba to zai amsa maka."
Ɓakin ciki, takaici game da dana sani ne suka mata kawanya idon ta sai zuban ruwa. A sadda ta ke farin cikin ya dawo kan hanya za ta ƙubuta daga gare shi sai kuma gashi ya zo da wani bato. A hankali ta soma ja da baya jin ya ja jallabiyar jikinsa ya cire ya haurawa kan gado.
"na fa faɗa miki ki kwantar da hankalinki ba da karfi zan miki ba, ki saki jiki kawai yarinya dan ba abin da za'a fasa."
Jin tana ɓata masa lokaci shi kuma a matse ya ke ya sanya shi nufo ta da zafin nama zai cafke ta amma ta yi tsalle ta dare ƙasan gado.
Zagaye ɗakin suka soma tana gudu shi kuma na kokarin cabko ta har daga ƙarshe ta yi nasarar shiga banɗaki ta maida ƙofa za ta rufe ya yi saurin riƙewa. Da ƙarfi ya tura ƙofar ta buɗe har yana gurje mata ƙofa, jan hannunta ya soma tana tirjewa kawai ya soma ra bata da kayan jikinta a nan wurin dama tuni hijabin Ammie da ta shigo da shi ya yi na sa gefen daga ita sai shimmy da da zani da ta daura a sama.
Jin hannunsa a inda bata yi zato ba ya sa ta kwallara ƙara har Ammie da ke boysqouter sai da ta ji, hatta Hajiya Binta da ke danno hancin motar ta cikin gidan a daidai lokacin sai da ta ɗan tsagirta da jin wannan ihun.
Gaban ta ya faɗi, ko ƙarasa parking bata yi ba ta fice ta nufi cikin gidan da sauri. Hakan ce take a wajen Ammie da dama tun ɗazu take tunanin abin da ya tsayar da Nazli har haka da ba ta zo ba. Haka kurum hankalinta ya ƙi kwanciya da jin ihun kuwa tsam ta miƙe ta nufi cikin gida.
"Ni za ki tonawa asiri?" Cewan Alhaji Badamasi tare da wanka mata mari. "Wallahi ko mutuwa za ki zai na yi abin da na ke so." Zuwa lokacin ƙarfin ta ya ƙare ta soma sarewa dan Alhaji Badamasi ya fi karfin ta ta ko ina, tana ji tana gani ya kai ta kasa dai dai sanda ya ke kokarin cimma manufarsa a kanta Allah ya taimake ta idon ta ya faɗa kan igiyar shower da ke sakale kan bathtub ta dage da karfin ta sai da ta rintse idanu ta daddage ta kwada masa a kai dai dai kyarsa. Ji kake
"Ahhhh!!! Ya furta, daidai sanda Ammie da Hajiya Binta suka yi cikubus a falon gidan, suka bi juna da kallo ba tare da ko wannen su ya furta komai ba suka haura sama da sassarfa suna rige rigen shi ɗaki.
A hankali slowing ya kai hannu bayan keyarsa ya shafo Jin dumin abu na sauko masa. "J..jini!." ya furta cikin inda inda, sai kuma jikinsa ya soma saki.
Da ganin haka Nazli ta hankade shi gefe cikin tsoro ta ja da baya tare da ɗaura hanaye biyu bisa kai ta tana furta. "Inna lilahi wa inna ilaihir raji'un, na shiga uku.!!" Ganin yadda ya yi baya ya faɗa ko motsi bai yi, ga jini da ya malala ƙasan ties kamar an yanka rago.
"Na shiga uku, wayyo Allah na dan Allah kar ka mutu kar ka mutu ka bar ni da haƙƙkin kisa, ni ban kashe ka ba."
A daidai sanda Ammie da Hajiya Binta suka yi nasarar shiga ɗakin. Ihuun da ta ji a kanta shi ya fargar da ita tsayuwar Ammie da Hajiya Binta a kanta, wanda suka yi mutuwar tsaye da abin idanuwan a zare cikin dimuwa da gigita da mummunan gani da suka yi, Hajiya Binta ta kuma kwallara ƙara tare da sakin jaka da mukulin motar a hannunata ta nufi Alhaji da gudu ta soma jijjiga sa jin baya motsi.
"Wayyo Allah ta kashe shi, shi kenan ta kashe shi ta kashi min miji. Jama'a taimako!!!........✍️✍️✍️✍️✍️
END OF BOOK ONE