AMARYAR GADO

CHAPTER 5

by @xayyeesherthulhumaerath

AMARYAR GADO

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

AISHA SANI ABDULLAHI

Xayyeesherthul-humaerath

©️2026

 

Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske. 

 

Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.

 

SHAFI NA BIYAR

 

Ba shiri ya furzar yana kallon Farida, ita kuwa taɓe baki ta yi sannan ta tashi tana jefa masa maficin a jiki ta tafi abunta.

Ya ɗau tea din ya kai baki da nufin ko zai kawar masa da ɗandanon cikin indomie din, nan ma firgice ya zubda harshensa har yana dadewa.

Cikin fushi ya tashi, kafin ya karasa Farida har ta rufe kofar dakinta.

Ya murɗa kofar taki budewa kwafa ya yi yana fadin,”Wallahi duk abun da kike ji dashi na takaki, yadda kike baka haka kike da bakar zuciya, kin ci bashin da sai kin azabtu wajen biya.” Yana fada ya shige dakinsa, toilet ya nufa kai tsaye yana bude baki, da sauri ya dauki brush dinsa yasa toothpaste ya fara wankewa.

 

Farida kuwa na kan gado, hannunta ɗauke da waya tana kallon hoton Ahmad.

 

“Yah Ahmad ka tafi ka barni  bayan ka sabarmin da kanka? ka sa an haɗani da wancen yaron, ta yaya zan iya rayuwa da shi? Wallahi ba zan iya kallonsa a matsayin miji ba, yaron da na yi wa wanka? Na wankewa kashi kuma na goya sa a bayana, wai ace shi ne mijina? Aa aa wallahi ba zan iya wannan rayuwar ba.” Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.

 

Yana fitowa daga toilet ya dauki key yana fita wajen gidan.

 

Daukar mota Sufyan ya yi ya fice daga gidan.

Yana cikin driving ya ciro waya ya kira Habib.

“Hello, kana ina ne?”

 

“Ango,ango kar kace min har an gama barje amarcin an fito.” Cewar Habib.

Tsaki Sufyan ya yi ,”ka fada mun inda kake bana son shirme.”

 

“Gani nan na danzo shakatawa ne cikin Varlaine Lounge.”

Yana gama fada ko amsa Sufyan bai basa ba ya katse kiran.

Varlaine Lounge wajen shakatawa da maza da mata suke haduwa domin cin duniyarsu da tsinke a Rayfield.

Yana zuwa ya yi ordern abinci aka kawo masa ya fara ci, bayan ya ci ya fara zukar shisha kamar yadda Habib ke yi.

 

“Wa ya naga ranka ne a ɓace haka?”

Sufyan ya yi tsaki.

“Wallahi sai na gyarawa Farida zama, sai na yi duk abun da zai sa araba auren nan, na rantse ko rufe idanuna na yi na ganta ji nake kamar in sheke kaina.”

 

Habib ya ce,”In fada ma gaskiya? Wallahi in kuka jera da Farida za ana zaton mamarka ce, ta yi biyunka fa? Wannan hadi ma dai sam bai yi ba ysn an cuceka kana dan matashinka handsome guy son kowa kin wanda ya rasa yadda mata ke tururuwa wajenka a ganka da wannan tunkuzar ai ta kare maka sai dai ka ji ana ga Sufy Handsome da mamarsa.” Ya karasa maganar yana kyalkyalewa da dariya.

Cikin dagin murya Sufyan ya dakatar da shi, “Wai ya kake son kara min wani haushin ne kan wanda nake da shi?”

 

Habib ya hadiye dariyarsa yana, “Ni wallahi hangota kawai nake ina kallonka, amma ka gane kar ka damu fa, kawai ka sha shagalinka ko in kira maka Falilah ne? Daman sai kirana take wai ta yi missing ɗinka.”

 

Sufyan ya girgiza kai yana ɗaukan glass cup ɗin da ke gabansa.

 

Daga waya Habib ya yi ya kirata. Ba a fi minti goma ba kuwa sai gata, tana zuwa wajen Sufyan ta nufa tana wata irin ƙarairaya.

 

Falilah farace, kyakkyawa, zubin Fulani; ga diri, ga kyau ta ko’ina. Ta haɗa komai, gata yar ƙwalisa, yar gaye. Tana ɗaya daga cikin ’yan matan da ke bala’in son Sufyan.

 

Jansa ta yi ya tashi, suka shige ciki, Habib na zaune yana dariya ya ɗaga musu hannu yana faɗin, “A wataya da kyau, a ji daɗi lafiya.”

 

Misalin ƙarfe shida daidai Inno ta koma wajen Farida. Tana zuwa ta tarar da Farida zaune a falo tana kallo.

 

Inno na shiga ta tsaya turus tana kallon Farida, ta taɓe baki, “Ni na shiga Ukuna ni Innojo! Farida, wai me kike nufi damu ne? Yammar Allah, ba za ki tashi ki kintsa ki gyara jiki ba kafin mijinki ya dawo? Ke dai an yi husumammiyar diya wallahi.”

 

Farida ta ce, “Inno, ni fa na yi wanka.”

 

Inno ta buɗe baki, “Gidanku na ce, karɓi gidanku! In zo da safe in tarar da ke da wannan kayan, yanzu ma kice min wai kin yi wanka? Karya kike. Wai ma kin yi muku girkin dare kuwa?”

 

Farida ta yi shiru, sai can kuma ta ce, “Ai ya ce tea za mu sha.”

 

Inno ta washe baki, “Ah, wannan da kyau ai. To yanzu maza tashi mu je ki yi wanka. Kin san fa masu jiki irin naku, in ba gyara akwai matsala. Ahto, taso maza.” Inno ta faɗa tana riƙe hannun Farida.

 

Ba yadda Farida ta so ba haka ta tashi suka shiga ɗaki.

 

Inno ta ce, “Yawwa, shige. Ki wanke hammatar nan fa da gefen damtsenki da ƙasan kirjinki, duk a dirza da kyau don ƙamshin su fita. Ko kuma ma in zo in miki ne kawai?”

 

Farida ta bata rai, “Aa, ni zan yi abuna da kaina. Akan me za ki min wani wanka da girmana?”

 

“Ah, shi ne kike bata rai? Ke yar nan, ni fa taimakon rayuwar aurenki nake saboda gudun husuma. Kin san wasu matan fa da warin jiki suke kashe mijinsu. Ni kuma da raina ba zan bari a yi wannan a badakalar halin Alhaji Audu ba.”

 

Shigewa toilet ɗin Farida ta yi, ta share Inno, ta fara wanka abunta.

Inno na tsaye a bakin ƙofa ta ce, “Ince kina da ruwan almun da za ki goga a hammatar? In ba ki da shi fa ki fada, in sa a sayo miki, yan abubuwan nan da kuka raina suke riƙe aure gam.”

 

Haka Inno ta dunga sambatunta, Farida bata kulata ba.

 

Tana fitowa Inno ta ce, “Daga hammatar in ji.”

 

Ta karasa maganar tana ɗaga hannun Farida tana shinshinata. Ta tabe baki.

 

“Ba laifi, amma dai tabbas sai na nemo miki alimun domin kawar da husumar hamamin hammatar nan. Ina jin gado kika yi wajen Kulu, don ita ma na lura wani lokacin ina jiyo ɗanshin warin nan a kanta.”

 

Farida ta ƙara murtuke fuska ta ce, “Inno, ni fa ki daina saka Mama cikin maganarki.”

 

“To, to uwata, hanani faɗan gaskiya. Ki nane mini baki kin ji ko? Maza ga kayan da na ciro miki, ki saka.”

 

Inno ta karasa maganar tana miƙawa Farida kayan, plain zani ne da T-shirt ɗin riga.

 

Farida ta kalleta.

 

“Haba Inno, barci fa zan yi, ta yaya zan iya barci da waɗannan kayan?”

 

Inno ta murde fuska ta ce, “Gidanku yanzu ke matar aure ce, haka ake yi. Sanya su maza.”

 

Bayan Farida ta sanya ne, Inno ta tasata gaban madubi sai ta yi mata kwalliya. Asali Farida ba mai son kwalliya ba ce, shi ya sa hasali ma bata yi kuma bata iya ba.

 

Hakan ya sa Inno ta ɗauki kwalli ta dambara mata jagira har kusan kunne, ta ƙara murza mata baki da baki da goshi, ta dambara mata farar hoda. Farida tsayawa ta yi kawai tana kallon ikon Allah, maimakon ta yi kyau sai ta ƙara muni da ta yi.

 

Ta sa hannu za ta goge, Inno ta bige mata hannu tana cewa, “Gidanku, ina gyara miki aure kina son ɓatawa.”

 

Tana gamawa ta ɗauki dankwali ta yi mata wani ɗauri irin na ’yan da, wanda ake yi kamar jirgi, sannan ta yafa mata gyale, aka fesa mata turare.

 

“Yawwa, ko ke fa. To mu je falo mu jirasa.”

 

Farida ta fara fita, Inno ta jafko hannunta.

 

“Ya Ilahi! Ni Innojo, wai kwakwalwar kifi gareki ne, Farida? Ni dai baki gajeni ba, aradu kawai kamanninki kika ɗauko. Ina tafiyar da na koya miki jiya?”

 

Ta karasa maganar tana janta, suna tafiya tare a hankali, suna fitowa daga ɗakin, daidai lokacin da Sufyan ya shigo gidan.

Akan Farida idonsa ya fara sauka, gabansa ya yi mummunan faɗuwa, sai da ya ga Inno na washe baki ya gane ashe Farida ce.

 

“A barka da zuwa, Sufuyanu. Maza karasa ki masa sannu da dawowa,” Inno ta fada tana tura Farida.

 

Bata karasa ba ta tsaya tana yi masa kallon banza.

 

Inno ta ce, “Maza ki karasa mana, wai baki gansa ba ne?”

 

Farida taki motsawa. Inno ta yi dariya.

 

“Kila wai a dole kunya ko? To ai duk mun yi.”

 

Ta karasa ta ja hannun Farida ta zaunar da ita gefen Sufyan.

 

Matsar da jiki Sufyan ya yi, shi ma yana binta da mummunan kallo.

 

Inno ta ce, “Ya haka? Kai, yanzu ta yi wanka fa. Kuma in ma tunanin hamamin hammata kake, na shinshina sama-sama ne. Kuma gobe da kaina zan shiga kasuwa in siyo mata alimun tana gogawa, kafin jiki irin wannan ya saurin gumi.”

 

Inno na magana, Farida na ji kamar ta damketa ta taska mata mari a kumatu don takaici.

 

Dariyar mugunta Sufyan ya yi yana cewa, “Ai ko dai irin wannan sai da alimun, in ba haka ba sai su kumburawa mutum ciki.”

 

Kwafa kawai Farida ta yi ta kallesa ba tare da ta ce komai ba.

 

Inno ta ce, “Wallahi kuwa. Yanzu ke Farida, tashi ki je dakinsa ki jirasa, zamuyi magana.”

 

Hada baki duka suka yi, “Dakinsa? Dakina?”

 

Inno ta ce, “E mana, ko ha tare kuke kwana ne?”

 

Dukansu suka yi shiru.

 

“Maza jeki, zai zo ya sameki a can. Zaku sha shayin, dan ba sai kun kara fitowa falo ba.”

 

Tashi Farida ta yi don dole ta shige dakin Sufyan. Tana zuwa ta rabe gefen gado.

 

Inno ta ce, “Ka ga Sufuyanu, ka ji tsoron Allah. Ana rike darajar aure. Batun tsaftar nan fa, kamar yadda na mata kai ma zan yi maka. Ana yi ana durza ko ina, duk da dai jikinka ba irin nata bane, amma a kiyaye, a kula.”

 

Sambatu Inno ta dunga zuba masa.

 

Farida, tun tana rabe gefen gadon, bata san lokacin da barci ya yi awon gaba da ita ba.

 

Sufyan ya raka Inno ta tafi. Ya shiga dakin kawai ya jiyo sautin gwarti, Farida na sharba barcinta abunta.

 

Tsaki ya sake cikin fushi, ya ja kafarta ya fusgota kasa.

 

Jinta da ta yi a kasa ne ya sa ta farka.

 

“Wannan wani irin iskanci ne? Za ka janyoni kasa?”

 

“Ra’ayina ne hakan. Ki fita min a daki,” ya fada yana kokarin kwanciya a gadon.

 

Kafin ya ankara, shi ma sai jinsa ya yi ta ja kafarsa ya fada tim a kasa.

 

A firgice ya tashi ya nufeta, dambe ya kaure…