MARYAMA

Page 48

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

48...

Bari muyi tsokaci kadan akan post na jiya kafun mu cigaba. Nasan da yawanku sun tsinewa Maryama walau a zuciya ko a fili bisa abinda ta aikata na gujewa Sadeeq duk da dumbin soyayya da ya ke gwada mata, tabbas Maryama ta aikata mugun butulci amma ya kamata mu fahimci cewa lallai bakin uwa ba karamin abu bane, Sadeeq ya gujewa mahaifiyarshi, yaki yin biyayya ga abin da take so, ya zabi Maryama wacce da haduwarsu duk wattani ne a kan mahaifiyarshi da ta reni cikinsa ta haifeshi ta shayar dashi gami da bashi tarbiya,uwa uba da soyayya irinta uwa marar yankewa,amma ta zana mashi layi akan Maryama yaki ji saida ya tsallake wannan layin,so dole ya dandani sakamako irin na bijirewa mahaifiya...

Ita kuma Maryama, dama duk zuciyar da ta tasirantu kan kwadayi da buri sai ka same ta da dabi'ar rainuwa.shi buri haka yake,idan kayi burin samun naira goma, sai Allah ya nufeka da samunshi,tofah daga lokacin da ya shigo hannunka zaka daina ganinshi da daraja burinka taya zaka mallaki ashirin?wannan yana daya daga cikin sharrin kwadayi da buri musamman idan kana kutsa kai cikin masu abin, to kullum fa saika hadu da sama da abin da ka sani...Allah ya sa mu dace...

Sadeeq ya kasa gaskata abin da kunnuwanshi ke jiyo mashi daga bakin Maryama ke fitowa, ya kasa aminta da abin da idanunshi ke gane mashi cewa wannan Maryama ce ba canzata akai ba,a hankali yaji jiri yana kwasarshi bai yi aune ba yaji ya fada saman kujerar dake bayanshi, "Ya Allah"ya furta yana dafe goshi,a daidai lokacinne kuma yaji karar rufe kofarta ta fita daga palon.

"So its reallity ba mafarki na ke ba,?" ya tambayi kanshi, kamar wanda ya zare haka yakebta sambatun kiran "Plssss Maryama karki tafi, kar ki barni dan Allah, I love you!I love you!! I love you!!! Idan ba ke rayuwata bata da wani amfani"...Saidai duk yadda zuciyarshi ke tunzurashi ya tashi ya bita,gangar jikinsa ta ki bashi hadin kai,haka ya cigaba da zama a wajen yana sambatu kamar wanda notin kanshi ya fara sacewa.

(Shin anya kuwa Maryama ba kyawunta ne jarabtarta ba?.)

A zuciyata da ruhina ina jin babu dadi akan abin da na yiwa Sadeeq, ko ba komai shine tsanin da na fara takawa ya kaini ga nasara,shine bangon da na jingina har na daga kafata na leko tsakiyar duniya. bayan Hamma j..Da sauri na rumtse idanuna ina jin faduwar gaba, duk sadda zan tuna da shi ko Iyayena,na kan tsinci kaina cikin wani irin yanayin da ban san yadda zan kwatanta maku ba,anya zasu yafe min?abin da nake yawan tambayar kaina kenan, da zarar na yi irin wannan tunani maganganun siyama ke fado min a rai, (Idan kin gama karatu kin samu aiki kinyi kudi, sannan kika auri hadadden miji kamar Sadeeq kika dawo kika rushe wannan kangon gidan naku,tsaff zasu yafe maki balle ma idan kin hada masu da kujerar makkah)wannan tunani shi yake rage min tashin hankalin da nake shiga duk sadda irin haka ya bijiromin.......amma kuma matukar ba hakan nai mashi ba bazai taba barina wajen cimma wannan abin arziki mai cike da tarihi da ya tunkaro ni ba...

Da wannan tunanin na iso makaranta,lokacin da na shiga dakinmu,turusss na yi ina karewa Chioma dake ta narka kaya cikin wani lafcecen akwati kamar mai kaura daga nahiyar baki daya, "Haaaan, Chioma mai kike aikatawa haka?" .

Na fada cikin harshen turanci kamar yadda muka saba magana da ita fuskata dauke da madaukakiyar mamaki.

Bata san na shigo ba sai da na yi magana ta dago da hanzarinta ta kariso wajena gami da rike hannayena duka biyu fuskanta kamar gonar auduga ta ce, "Guess what Marama,?" girgiza mata kai nayi don na kasa fadin koda kalma daya ne.

"Zamu wuce Dubai da Abdallah".Ta fada tana murmushi, tamkar ta watsa min ruwan zafi a kirji haka naji.

"Ban fahimceki ba Chioma"na fada a rude bakina yana rawa kamar zai fado kasa.

"Hmmmm dazu kawai ya kirani wai idan na amince zai sama min biza mu wuce dubai,tsabar dadi bansan lokacin da kwalla kara ba,shi ne fa kika ga ina hada kaya yanzu."

Hannunta dake rike cikin nawa na cire hadi da zama bakin gadona ina dafe goshi na da duka hannun.

"So me hakan ke nufi? me Abdallah yake nufi?ko ya dauka bazan amince bane shiyasa ya aikata min haka? Kai ina ba haka bane kawai yayi niyyar yaudaranki ne dama Maryama, zuciyata ta bani amsa,"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, na furta ina kokarin maida kwallar da ta cika min idanu.

Zama Chioma ta yi bakin gadon gami da dafa shoulders dina tace, "What happened Marama?you look so tensed".

Bazan iya jurewa ba dan haka na fashe da kuka ina fadin, "Chioma Abdallah ya ci amanata, ashe dake yake son tafiya shi ne yazo ya shirya min karya, ya sani na sake abin da na dafe ashe yaudarata yake yi".

Da yake da turanci na yi maganar duk taji, galala ta yi da baki, kafun ta rufe bakin da hannu irin taji abun mamaki dinnan tace, tana nuna ni da yatsa, "You mean...You mean kece Abdallah yace zamu tafi tare?" ai tun bata karisa ba ta rungumoni tana ta dariya hadi da fadin, "Haduwata dake alkhairi ne Marama, dama ya sanar dani akwai wacce yake son mu tafi tare but yet bata amsa mashi zata je ko bazata ba, saidai matukar bata amince ba, a cewarshi nima bazan jeba dan itace fitilar tafiyar, so ashe kece,"

Riketa na yi nima ina sauke ajiyar zuciyar samun reliefe na ce, "kwarai kuwa ni ce,".

"So what are we waiting for? yi maza ki kirashi kice kin amince" tana fadan haka ta fara janyo akwatuna na wai zata shirya min kaya, wannan shine matakin farko na shiga ta gararin rayuwa, matakin daukar darussan dake cike makil da wagga duniya tamu mai abin al'ajabi...

Babu bata lokaci muka kimtsa,visa da passport namu duk ya kammala da nufin zamuje makaranta ne a can, duk wani harkar cuku cuku Abdallah ya sanshi dan haka baisha wahalar samar mana takardun bogi na makarantar ba wanda dasu ne aka buga mana biza da paspo dinmu.

Ranar wata laraba muka nufi airport nida Chioma, Abdallah yana legas kuma ta can ne zamu wuce dan haka daga patakwat zuwa legas ma jirgi muka bi,sanye nake cikin abaya fishall pink as usual, dan gaba daya kayana abaya ne tunda nazo patakwat dan bazan iya sanya irin kayayyakinsu ba mai bayyana tsiraici, atamfa kuma idan ba kar ace na yi karya ba, bantaba ganin mace sanye da shiba.

Lokacin da jirginmu ya sauka a Murtala Muhammad International airport dake lagos, tsaye muka samu Abdallah a airport din shida wasu mutane da kallo daya na musu naji basu kwanta min a rai ba, yawancinsu suna sanye ne da wando three quarter irin manya manyan nan da riga armless, bakake ne kirin jibga jibga babu alamar annuri a fuskarsu sunkai su hudu, sai oga Abdallah dake tsaye a tsakiyarsu jikinsa sanye da wando jeans baka sai farar shirt na kamfanin polo mai tsayi da fadi kana ya daura wani katon rigar sanyi a kai idanunshi sanye da glasses kana wuyanshi dauke da wani katon sarka irin na maza, yatsun hannunshi kuwa duka akwai zobe irin tafka tafka dinnan a jiki,tun daga kan matattakalar yake hango su, a ranshi yana kissima abubuwa dayawan gaske...Ganin sun karaso ne yasashi sakin murmushi mai dan fadi,da muryarshi irin ta tatattun yan duniya yake welcoming dinmu, "Muje ku dan huta a masauki kafun lokacin tashinmmu zuwa Dubai ya yi dan jirgin dare zamu bi".

Ya fada murmushi dauke saman fuskarshi. bayan motar muka shiga nida Chioma shi da daya daga cikin wadannan mutane marasa kyan gani suka shiga gaba, sauran ukun kuma suka shiga dayar motar,muna tafiya yana ta nuna mana garin lagos, tabbas ya amsa sunanshi na cunkus dakin tsumma da bahaushe ke mashi kirari. A harabar wani hadadden hotel muka sauka daga kai na yi Ina karewa wannan waje da ya tsaru iya tsaruwa na yi, EKO HOTEL AND SUITE, naga an rubuta, hanya Abdallah ya nuna mana muka fara shiga cikin hotel din, a reception suka tsaya suka karbi rooms keys da suka ajiye,lifter muka hau ya kaimu 5thfloor inda dakunan da su Abdallah suka kama suke mudai muna biye dasu a baya sai kalle kallen abubuwan mamaki muke kuma mun kasa cewa ko uffan yayinda ni tsoro ke rubuce karara saman fuskata.

Wani babban daki yasa makulli ya bude yayinda sauran boys din nashi suka yi gaba, da hannu ya nuna mana da fadin "ku shiga ku huta, tunda ba jimawa zamuyi ba shiyasa na kama muku daki daya,"..babu musu muka shiga dakin,iya haduwa ya hadu babu ce kawai babu a dakin nan,zama mukayi bisa kujerun dake zagaye gefe guda kamar palo. Rolling na kaina na cire ina daure kaina da gyalen, Chioma da ke bin dakin cike da zalama da kallo. 

bayan kamar minti ashirin, wata ma'aikaciyar hotel din tayi knocking, Chioma ce ta je ta bude kofar sannan ta shigo dauke da wani babban tray abinci ne a jere a kai kala kala, duk da yadda yawuna ya tsinke da ganin abincin,amma na kasa cin ko da lauma daya ne dan wani irin fargaba ne ya dirar min lokaci daya.

Da kyar Chioma dake kwasar gararta ta tirsasa ni na sha drink da wani snacks da ban san ma minene ba, bayan mun gama ni na fara mikewa na yo wanka hadi da daura alwala dan azahar ta gabato fitowata na samu Chioma ma daure da towel tana jirana dan haka ta fada bandakin, a gurguje na dan shafa mai sama sama na maida rigar da na cire dan a airport muka bar kayanmu na kabbarta sallah. knocking aka kuma yi Chioma da ta fito yanzun daure da towel ta nufi kofar ta bude, daya daga cikin mutanen dazu ne, cikin harshen turanci ya ce mata, "Oga na san ganinki a daki mai lamba ...." daga haka ya juya ya koma inda ya fito,da dan rawar jiki ta mayar da kayan da ta cire itama komai bata shafa ba ta fita,lambar dakin da ya sanar da ita nan ta kwankwasa babu bata lokaci kuwa aka bude ta shiga ciki.

Dakin sakk irin wadda suke ciki ne bai da wani bambanci dan haka ta samu waje ta zauna, hira Abdallah ya fara mata cike da jan hankali da tambayarta hanya sosai ta sake dashi kafun wani da badashi aka je daukosu a airport ba ya shigo dakin hannunshi dauke da glass cup guda biyu, daya ya mikawa Abdallah daya kuma yaba chioma, girgiza kai tayi tace ,"yanzu nuka gama yin lunch sir iam okay".

Na sani ai, wannan ba abinci bane so chill kawai madam,"cewar Abdallah yana kashe mata idanu daya,tunda Chioma tasha drink din nan bata kara sanin inda kanta yake ba,..Ina idar da Sallah babu zancen azkar bare addu'a wanda na manta rabona da yinshi na mike gami da zama cikin daya daga kujerun dake wajen, tun ina irga sakwan har na fara minute har hour, babu Chioma babu labarinta, cike da zullumi nake zaune har time na la'asar yayi na shiga bayi na dauro alwala,na fito. zaune na ganta saura kadan in ruga da gudu amma nayi karfin halin karasa shigowa na ce ina kallonta, "Chioma meke faruwa,baki da lafiya ne? Ina kika je?".

Na mata tambayar ganin yadda fuskarta yayi jajawur hakama idanunta dake tsaye tarwai babu alamar zata kifta su, bata kalleni ba ba kuma ta ce min komai ba, daga karshe ma ja tayi ta kwanta anan saman kujerar da ga haka kuma bacci ya dauketa, Sallah na yi ina ta ta'ajjubin mai ya sami Chioma,....Har dare tana kwance a wajen bata motsa ba, jirginmu karfe takwas zai tashi dan haka karfe bakwai wani yaron Abdallah ya shigo da wani cup a hannunsa, sosai na fara tsorata da yanayinsu, amma sai na dake, baice min ba nima bance mashi ba.

Kan Chioma ya daga gami da bude bakinta da karfi ya tura mata ruwan dake cikin kofin sannan ya sake ta ya fita, bai dade ba kuwa ta farka tana mika gami da hamma sai kuma ta ware idanunta a kaina ta ce, "Marama ya kikai tagumi,har yanzu bamu tafi bane?".

Murmushin yake na mata na ce,"kina bacci zamu ciccibeki mu tafi ne,?"

Mikewa tayi da sauri tana fadin, "Jesus,sai kuma ta rike cikinta da sauri ta da dade a haka kafun ta shige bayi ta dan watsa ruwa, abincin da aka kawo na dare ma banci ba Chioma dai ta dan tsakuri kadan itama da haka muka wuce airport dan lokaci ya kusa, lokacin da na zauna akan seat nawa Chioma a gefena yayinda su Abdallah da sauran tawagarshi na mutum uku ke bayanmu,.

Wani irin hawaye ne suka gangaro min a cikin raina na ce, "Kuyi hakuri Innarmu, Baffanmu idan nayi kudi zan dawo, na tabbata kuma zakuji dadin arzikin da zan yi. Hamma ja...Rumtse idanu nayi da karfi, duk sadda na tunashi wani irin girgiza kirjina keyi, "wane hali yake ciki?"shine tambayar da nake yawan yiwa kaina kenan.

Tunda muka fito na lura da yanayin Chioma sai kara ta'azzara yake yi bata cewa komai sai cikinta da take yawan matsewa da taune lebe ga idanunta da suka kada jajawur kamar garwashin wuta, da haka jirginmu ya lula sararin samaniya hawayen dake cigaba da tsiyaya cikin idanuna wanda bansan dalilinsu ba, na dadi ne ko akasin hakan na sa bayan hannu na share su,tafiyar 7hours 32minutes ne daga lagos zuwa Dubai dan haka tsakar dare sosai muka iso filin tashi da saukar jirage na kasa da kasa dake Abu dhabi.Taxi guda biyu ne ya dauko mu daga airport muda kayanmu zuwa wani anguwa da bazan iya tantancewa ba saboda yanayin gajiyar danai. 

Wani katafaren gida muka shiga wadda a take ya gusar man gajiyar da nai na hangame baki ina kallon ikon Allah da irin dukiyar da aka narkar a wagga gida. Zuwa lokacin jikin Chioma ya kara tsananta dan haka cidakk wani da naji Abdallah yana yawan ambata da John ya dagata har cikin gidan direct dakin da aka tanada domin mu aka shigar da ita, Abdallah ya sanar min in zauna da ita zuwa Safiya zata warware gajiyar hanya ne, da safen za'a raba mana daki. Ba don na amince wai gajiyar hanya ce ba na gyada mashi kai kawai.

Bayan kamar minti talatin da zuwanmu Chioma ta fara wani irin girgiza mai ban tsoro yayin da bakinta ya fara fitar da wani irin kumfa kore kore.Hannu na daura akai na ce, "Na shiga uku, Chioma!nan na ringa jijjigata amma ina sai karkarwa take da jan numfashi tamkar numfashin nata zai bar gangar jikinta.

A birkice na fita daga dakin ba tare da na san inda zan nufa ba, burina kawai inga Abdallah kar Chioma ta mutu, turrus na ja na tsaya jin wani irin dariyar da ya kece dashi marar dadin sauraro daga cikin wani daki dake daura da inda na tsaya, jikin kofar na kawo ina kai kunnena daf dan jin ko Abdallah yana ciki, amma da sauri naji wani irin abu kamar guduma ya sauka a kahon zuciyata jin abinda suke fada daga cikin dakin suna dariya, a hankali naji kafafuna suna neman rasa garkuwarsu na daukar gangar jikina da sukayi, take wani irin zufa ya yanko mi duk kuwa da irin sanyi da rabar ac dake busowa ta ko ina na gidan babu shiri na sulale na kai kasa ina rike bakina da hannu dan kar kukan da nake shirin kurmawa ya fito..............