SANADIN HIJIRA

Page 48

by @ummufadeela01

*SANADIN HIJIRA*

      BY

Ummu Fadeela


Chapter 47/48
Duk yadda ya so kubutar da ita daga ukubar Mom ya kasa dan ta kasa ta tsare, har dai ranar da ta kama za a yi wa Elisha aiki.
Misalin karfe shiga na safe ta shigo dakin shirye tsaf sai baza kamshi take. Ina takure jikin gado, zuwa yanzu na rigada na sadaukar, sai dai ban saduda ba; ban daina addu'o'i ba, ban daina rokon Allah ya dauki raina kafin wannan lokaci ba... "Wuce ki yi wanka ki shirya, ke ake jira." Ban musa ba na mike ina tangadi kamar zan kifa, ruwa na watsa sama-sama na fito. Ko mai ban shafa ba ta tasani gaba dole na yi breakfast, na zura doguwar riga ja na yi yafa gyalen rigar, duk na yi wujiga-wujiga muka fito.


Yana zaune kujerar da ke facing kofata, ya matse hannayenshi tsakanin cinyarshi kamar mai jin sanyi, ya kafe kofar da ido. Geffan kuwa Elisha ce kwance cikin tsananin ciwon da ya kuma tasar mata cikin dare kamar ba za ta rayu ba, sai murkususu take yi. Kallon second biyar na mishi a karon farko. Ya rame a fuska, idanunshi sun yi zuru dake nuna yana fama da rashin bacci, lebenshi sun bushe har wani fari-fari suka yi. Da hanzari na kawar da kaina gefe lokacin da ya nufomu. "Mommm!! Plsss."


Daga mishi hannu ta yi tana kuma murtuke fuska, "Daga Lisha mu tafi, na gama magana." Sosai ta damke hannuna har cikin motar, sai da ta tabbatar na zauna a gaba, shi ma ya shiga bayan ya kwantar da Lisha a baya, ita ma ta zauna ta ce, "Danna lock." Jiki a mace ya danna. Duk bayan second daya sai ya dago ya kalleni, ambaton Allah nake a zuciyata ina share hawaye a hankali. "Ya Allah ka sanya ina cikin wadanda ka yi wa tanadin babbar rabo ranar lahira." Na fada lokacin da wata nurse ta sanya min wata rigar marasa lafiya ruwan ganye, kana ta daura min hula mai kama da leda a kaina, ina ji ina gani ta min wani allura, daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba.


"Ka ga angon Badar, soja marmari daga nisa! Wai me ke faruwa ne ka yi wani iri da kai? Kasan kuma da wuri ya kamata mu shiga tunda abun da ya kawomu kenan..." 


Yamutsa fuska Al'ameen ya yi dafe da kanshi, "Ni kaina ban sani ba Musty. I felt like something bad yana shirin faruwa da ni, kamar dai..." 

Sai kuma ya yi shiru yana cigaba da kallon Musty dake fuskarshi ke bace kadan wanda bomb ya bata mashi a Borno. Ko ina ya warke a jikinshi amma tabon fuskar tana nan. "Matso ka ji." 

Matsowa Musty ya yi, Amin ya kama hannunshi ya daura saitin zuciyarshi. Da hanzari Musty ya jaye hannunshi. Cije lebe Al'ameen ya yi yana mikewa. 

"Keep saying Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un," cewar Musty dake bin bayanshi ganin how weak Al'ameen is. Gyada kai kawai ya yi suka fito daga apartment da aka sauke su cikin hospital din, nan suka hadu da sauran suka rankaya hospital compound dan fara halartar kwas na musamman da ya kawo su kasar.


Dukkansu sun yi cirko-cirko a dakin da za a gudanar da aikin. Fannah da Elisha suna kwance kan wani gado mai biyu, yayin da likitocin suka zagaye su; bakin likitocin da suka zo ake jira su fara gudanar da aikin. 

Mom sai kai-kawo take a bakin dakin operation din, yayin da Jack ke zaune ya yi jugum idanunshi jajur, wani bala'in tausayin yarinyar ke rufto mishi.


Cike da takun mazantaka suka nufo wajen, dukkansu sanye da uniform na tiyata light blue riga har kasa da hula da facemask. Baka ganin komai sai idanunsu, hanya aka basu duk suka shiga. Al'ameen yana jin nauyin jikinshi yana daduwa.


Bayani mai tsayi babban likitan ya fara musu matsayinsu na masu koyan aikin, wanda ya daukesu mintuna talatin cifff, kafin aka fara fitar da kayan aiki, nan ma yana nuna musu kowanne da amfaninshi.


Daidai lokacin da za a fara gudanarwa, a lokacin ne kuma allurar da aka min ta saki jikina. Juyi na fara yi ina ambaton sunan Allah. 


Cakk likitocin suka tsaya cike da mamaki, yayin da jijiyoyin da ke kai sako wa kwakwalwar Al'ameen ta tsaya daga aikinta jin muryar da ta daki dodon kunnuwanshi...


A hankali na juyo ina bude idanuna da suka yi min nauyi, basu sauka ko ina ba sai kansu. Kuri na yi ina binsu da kallo. "Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka amshi addu'ata ka dauki raina kafin wannan al'amarin." Na fada cike da rauni ina jiran jin ta ina zasu fara tambayata '*MAN RABBUKI*'. A zatona mala'iku ne, sai dai maganganun da na fara ji cikin harshen turanci, babban likitan yana surfa masifa da tambayar wa ya yi min allurar, shi ya kada min 'yan hanji da tabbatar min lallai har fa yanzu a duniya nake, kuma a raye, amma wadannan sune zasu karasa kashe ni yanzu, mummunar mutuwa...


Da hanzari Al'ameen da ya yi suman tsaye ya zare facemask dake fuskarshi ganin an tunkari yarinyar da nufin yi mata wata allurar. Juyin da zan yi idanuna suka sauka cikin nashi, lumshe ido na yi na bude na kuma kallonshi, still shi dinne ba gizo yake min ba! 

Da azama na yi wani wawan tsalle na dirko saman gadon na ruga bayanshi a guje, na makale shi gam, na sanya hannayena duka biyu ta gabanshi na hardesu a kirjinshi. Cikin kyarmar jiki da ta muryar na ce, "HE... HEL... HELP...!"