BABAN KAWATA

Chapter 19

by @smauta

Meyasa baka dawo da ita ba?oga nayi nayi ta biyoni taki kuma suma yan uwan nata sunce ba inda zataje nabar mata wayana idan tana buƙatar wani abu ta kiraka,leave sum sum Idris yabar gaban khalil kanshi ya dafe sosai Innalillahi wainna ilaihir rajiun ashe dai dagasken take kakarta batada lafiya meyasa zuciya ta takasa yarda dake manar,nayi maki kallon karya kike kin dawo ne abuja nemana,ya Allah karkasa in zama nine silar rabuwar manar da farin cikinta🥹🥹🥹🥹🥹



Karfe tara na dare manar na zaune tsakar gidan maman Ibrahim taci kuka tagaji ta kira wayar kaka yafi so shurin masaki amma amsa daya ce wayar a kashe take🥺misalin karfe tara na dare maman Ibrahim ta fito daga daki manar damuwa bazatasa kaka su dawo ba kiyi hakuri gobe da safen har kaduna sai kuje da Ibrahim kiyi hakuri lafiya akaje nemama kaka kin ji.......



Jakar kayanta da envelope ta kudin da khalil ya bada a bata ta kalla wayar idris ce tun dazu ake kira sarai tagane mai kiran ta kin dauka tayi mezai cemata a wannan halin datake ciki a yanzu, hankalin khalil gaba daya baya tare dashi kar manar taje ta cutar da kanta Idris ya aika aka kirawo shi ka tabbata wayar ka na hannun manar eh oga Allah yasa lafiya,ina kira bata dauka bari in kirata ds dayan layi na...........




Wayarsa dake aljihu ya ciro ya saka number shi ya danna kira kira kusan biyar ba'a ɗauka ba sai na shidda manar ta dauka shima dan taga number ce,hello hajia Idris kirjin ta taji ya buga ta saisaita natsuwar ta Idris ka koma gida lafiya ko?eh hajia dama oga ne yace yanata kira ba'a dauka ba,yana ina ta jefa masa tambayar gamunan tare dashi ɗil ta katse wayar da hannu yayima Idris alamun ya tafi kawai..........




Number ya sake dailing ta dauka muryarshi da ta daki dodon kunnen ta yasa lokaci daya zuciyar ta ta karye ta sakar mashi kuka mai tada hankali kasa cemata komai yayi dan a yanzu ba abinda take bukata sai kukan bawani lallashi da zaiyi tasiri a kanta mintin su ashirin a haka sannan yace MANAR da shashshekar kukanta ke daga masa hankali ta ansa shi,ki daina kukan nan kinji in turo gobe a dauke ki????





Saida ta ciro wayar a kunne ta duba ta kalli sama ta tabbatar ba mafarki take ba tace in dawo wurin ka bansan wane hali kakata take a ciki ba ita kadai ce gatana a duniya itace farin cikina bazan iya barin suleja ba,bansan inda kaka suke ba wayar ta a kashe na rasa tudun dafawa,manar kinada ni komai zaizo maki a sauki ganinan zuwa....................





Gashinan zuwa a wannan tsohon daren zaice mata gashinan zuwa wata zuciyar tace mata subul da baka ne kawai yayi,kayan dake jikinshi ya sauya zuwa manyan kaya harda babbar riga yana zuma wannan fitina nen kamshin nasa a harabar gidan ya fito Idris ya taso dauko mota,ba musu ya shiga layin jeran motocin ogan nashi ya zabo narkekiya guda daya a owners corner ya kame saida suka halba titi Idris ya rissina oga ina mukayi wayar sa na hannunshi yana turama jude number idris a saka mashi tracking yace masa suleja..............




Idris bai kara cewa uffan ba ya cigaba da tsalala gudu akan titi suna gab da shiga suleja aka fara wani irin mamakon ruwa wanda dole tasa saida sukayi parking a gefen hanya, cigaba da kiran wayar idris yayi amma bata shiga ranshi ne ya bashi sbd ruwan da akeyi ne sun dauki kusan hour kafin ruwan ya tsagaita suka cigaba da tafiya,har kofar gidansu manar idris ya faka oga munzo ga gidan nan amma ita tana cikin wancan gidan sai lokacin ya dago ta cikin glass ya karema unguwar talakawan kallon tsaff gidan da Idris ya nuna masa ya kalla sauka kayoman sallama da mai gidan...........





Ba musu idris ya fita har kofar gidansu Ibrahim layin shuru an tafka uban ruwa mamako bubbuga kofar gidan ya fara shuru ba wanda ya ansa duk bugun kofar daya manar na ji tsaf har lokacin zaune take dangalgal kan kujerar dakin maman Ibrahim,daga can taji baban Ibrahim na cewa wanene a wurin kofar nan tocila dinshi ya kunna ya nufo soron gidan nashi.............






Addu'a manar take Allah yasa ba khalil bane wata zuciyar tace anyi wannan ruwan bazai iya baro Abuja ba a daren nan yanzu wurin 12 na dare,malam lafiya daga ina baban Ibrahim ya kashe ma idris ido da haske kome yake faruwa yana kallo ganin sai ja inja ake da baban Ibrahim yasa khalil ya sauko da kanshi............





Assalamu alaikum baban Ibrahim ya ansa tareda mika mashi hannu kamar yadda yayi mashi bayan sun gaisa ne ya gabatar da kanshi a wurin baban Ibrahim nazo wurin manar ne na kirata tace bata san inda kakarta take ba,to ranka ya dade maganar ba'a san inda kaka take ba gskia ba haka bane dan kuwa mudai da hannun mu muka kai kaka babbar asibitin garin nan daga bisani aka maidata asibitin kaduna yanzu haka tana can.............





Kuma bakomai bane ya kara tunzura wannan ciwo sai bacewar jikar ta manar yau kimanin kwana uku kenan daga tafiya abuja saida waya da kaya dan ta samu kudin magana aka nemeta kaura wambai tun ranar ciwon kaka ya tsananta cikin daren muka kaita asibiti bata san ma inda kanta yake ba gaskiya har aka tafi da ita kaduna bata gane wake kanta,baban Ibrahim dama kaka halin da take ciki kenan kukaceman lafiyar ta🥺🥺🥺🥺🥺




Daga bakin kofar datake masu laben ne ta fito tana rizga kuka mai tsuma zuciya,gogan kuwa kafeta yayi da ita kyar yana kallon yadda take kuka kamar zata cire ranta a karo na ba adadi kenan dayaji tausayin manar ya lullube shi ruffff rai da rayuwar sa 🥱🥱🥱🥱🥱🥱