Matukar Ina Raye 1
by @mrsisham12
MATUƘAR INA RAYE
Writer — MRS ISHAM
*** whatsapp.
~BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM~
Page 01
Iskar hunturu mai sanyi tana kaɗawa a hankali, tana ɗauke da ɗan ƙurar da ta lulluɓe sararin samaniya. Titunan garin sun yi duhu, sai hasken fitilun gidaje da na motocin da ke wucewa lokaci zuwa lokaci suke karya wannan duhun. Duk inda ka kalla, akwai wani irin hazo mai duhu da ya rufe komai. Hasken fitilun tituna ba ya haskakawa yadda ya kamata, sai dai ya fito cikin ƙurar kamar wani ɗan ƙaramin haske da ke ƙoƙarin yaƙi da duhun dare. Gidaje sun rufe ƙofofinsu da tagoginsu.
Tafiya ta ke a hankali, hannunta ɗaya riƙe da wayarta, ɗayan kuma ta matse gefen mayafinta da yake ƙoƙarin kubucewa saboda iska. Idanunta suna yawo daga wannan gefe zuwa wancan, kamar wadda take fatan ganin wani mutum a duk lokacin da ta ɗaga kai.
Amma babu kowa.
Ta tsaya tana duba wayarta, sai dai babu kira balle saƙo. Ta ɗaga idanunta sama, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
“Waheeda…”
Ta furta sunan a hankali, hawaye na zubowa daga idanunta. Ta sa hannu ɗaya ta share su.
“Ya Allah… ina ne inda wannan yarinyar ta shiga? A ina zan samo ta?”
Ta tambayi kanta, kuka na ƙoƙarin kubuce mata. Wani dakali ta hango, jikinta a sanyaye ta ƙarasa wurin, ta zauna, sannan ta soma rera kuka.
A lokacin hunturu, abin da aka fi buƙata shi ne abin da zai bayar da ɗumi ga jiki. Ba jiki kaɗai ba, hatta cikin mutum yana buƙatar wani abu mai ɗumi domin ya ji sauƙin sanyin da ke ratsa kowane sashe na jiki, ciki da waje.
Majalisa ce. Magidanta da samari suna zaune a kusa da wata wuta da suka hura, tana ci a tsakiyar inda suke zaune, su kuma sun kewaye ta suna jin ɗumin da ke ratsa jikinsu. Ga kuma shayin da suke sha suna hira cikin natsuwa, kowa hankalinsa kwance.
“Kamar ina jiyo sautin kuka,” wani saurayi daga cikinsu ya faɗa.
Hakan ya sa suka yi shiru, suka kasa kunne. Ai ko ba ƙarya ya yi ba, tabbas su ma kunnuwansu sun jiyo musu wannan sautin kukan.
Wani magidanci ya furta, “Je ka dubo waye yake wannan kukan, sannan ka zo da shi.”
Bayan tafiyarsa da ’yan mintuna, sai ga shi ya dawo majalisar tare da ita. Da mamaki suke kallonta, suna tambayar kansu me ya fito da ita a wannan lokacin na dare da sanyi.
“Yarinya, ke kuwa me kike yi a nan? Daga ina kike? Yaya sunanki?”
A maimakon ta ba su amsa, sai kawai ta sanya kuka tana rufe fuskarta da gefen mayafinta. Jikinsu ne ya yi sanyi, tausayinta ya kama su. Hakan ya sa suka bukaci ta zauna, sannan suka samu suka lallashe ta har ta yi shiru.
“Amma ke ba ’yar wannan unguwar ba ce, ban taɓa ganinki ba.”
Kai ta gyada masa alamar eh. Mutumin ya jinjina kai.
“Sani, ba ta shayi ka ji,” ya umarci matashin da ya zo da ita.
Bayan ya ba ta shayin, sai matashin ya ce, “Kanwata, na san ba ƙaramin abu ba ne zai sa ki bar gida a wannan lokacin. Tabbas babban al’amari ne. Ki sanar da mu. Kin ga duk kin saka mu cikin damuwa.”
Ta ɗago idanunta da suka kumbura saboda yawan kuka, ta kalle su sannan ta furta, “Neman ta nake yi. Babu inda ban duba ba, amma sam babu ita a kowane lungu da kusurwa.”
Kallon juna mutanen suka yi. Wani wanda ya fi su manyanta ya ce, “Wacece ita? Tabbas tana da matuƙar muhimmanci a gare ki, tunda har kika iya fitowa cikin irin wannan dare ba tare da tsoro ko fargaba ba domin neman ta. Tabbas ta kasance ta musamman kuma mafi soyuwa a gare ki. ko za ki iya ba mu labarinta?”
Murmushi ta saki lokacin da ta ji ya ambaci kamar ita ɗin ta musamman ce. Ta dube shi ta ce, “Tabbas ita ɗin ta musamman ce, Baba. Waheeda ta kasance yarinya ta musamman, mai cike da abubuwan al’ajabi. Zan ba ku labarint. Fatan za ku iya jure saurara.”
__________________ ✦✦✦✦✦✦✦✦ __________________
“WAHEEDA! Ni kam yau wa kike nufi zai yi waɗannan wanke-wanken? Kin san yau girkin uwarki ne ko?”
Mama Sadiya ta ƙarasa maganar cikin masifa, tana tsaye a bakin ƙofar ɗakinsu tare da yaye labulen gaba ɗaya.
Kamar daga cikin mafarki Waheeda ta ji muryarta. Ta farka tana yatsina fuska saboda bacin rai, domin babu abin da ta fi tsana kamar a tashe ta daga barci.
Ta zauna tana gyara dankwalinta da ya zame saboda rintsawar da ta yi, sannan cikin fuskar ɓacin rai ta ce,
“Haba Mama Sadiya. Ai ko barcin mutuwa nake yi, ya kamata ki bari ki ga ko zan farka ko ba zan farka ba. Amma saboda waɗannan wanke-wanken da kullum ranar girkin Umma ni nake yi, shi ya sa kika zo kika tashe ni?”
Mama Sadiya ta saki baki tana kallonta. Duk da ba yau aka fara ba,inda sabo kowa a gidan ya saba da rashin kunyarta.
Ta ce,
“Lallai wuyanki ya yi ƙwari. Wannan rashin kunyar da kika yi min a kunnen tsohonki mara kunyar banza da wofi”
Waheeda ko kallonta ba ta yi ba. Ta miƙe ta fara tattara ɗakinsu, wanda yake a birkice kamar ɗakin mahaukaciya.
Ƙaramin ɗaki ne, babu plaster balle fenti, amma jakunkunan Ghana Must Go sun kusa cika shi gaba ɗaya. Ga kuma tsofaffin katifu guda biyu da suka bazu a ƙasa, waɗanda suka tsufa suka lalace.
Sai da ta bar Mama Sadiya a bakin ƙofa, sannan ta fito cikin tsakar gidan tana karewa ko'ina kallo. Gidan ya yi matuƙar hargitsewa, babu ko shara, ga kwanukan wanke-wanke a baze ko'ina kamar babu mutanen da ke zaune a gidan.
Siririn tsaki Waheeda ta ja tana riƙe da kugunta. Duk duniya babu abin da ta tsana sama da wanke kwanuka, bare kuma irin yawan kwanukan gidan nasu. Abin ka da gidan yawa, kwanuka sun bazu tamkar na gidan biki da aka ci aka watse.
Cike da tsiwa ta isa bakin ɗakin mahaifiyarta, ta tsaya tana girgiza jiki kamar wacce take shirin yin dambe.
"Kam bala'i! Duk wannan uban wanke-wanken ni ake so in haɗa in wanke? Yasin, ba zan wanke duka ba. Iya wanda aka ci abinci yau kaɗai zan wanke, tunda yau ne aka shiga girkin Ummarmu. Ehen! In ba mugunta ba, kwanukan tun na shekaran jiya ba a wanke su ba, aka tara ana jiran jaka ta wanke. To ni babu wata katuwar da zan wankewa kwanuka"
Wasu 'yan mata biyu, waɗanda shekarunsu ba za su gaza sha takwas ba, suka fito suna wurga mata harara, ita ma tana mayar musu.
Ɗayarsu ta ce,
"Wai ni kam Waheeda, me yasa sam ba ki da kunya? A duk gidan nan akwai sa'arki ne? Mu da muke yin wanke-wanken mutuwa muka yi?"
Waheeda ta yi saurin cewa,
"Yaya Salma, kin san Allah ki yi shiru. Ban yi da ke ba. Waɗanda nake yi da su ai sun san kansu. Ikilima da Rabi ne za su yi wanke-wanken jiya da shekaran jiya amma suka ƙi yi har girkin Ummarmu ya shigo. Don haka, na yau kaɗai zan wanke."
Umma, wacce take cikin ɗaki tana jin duk abin da ke faruwa, ta girgiza kai ta fito cikin sanyin murya.
"Waheeda, wato ni ban isa da ke ba kenan? Me yasa kullum kike son jawo min magana ne?"
Waheeda ta turo baki tana matsowa kusa da ƙofar tana kunkuni.
"Ni dai wallahi ba jakarsu ba ce. In ke kina musu shiru, ni ba zan yi shiru ba."
Umma ta girgiza kai kawai tana gode wa Allah, ta zuba mata ido. Ita ba mace ba ce mai son hayaniya, shi ya sa kishiyoyinta suke mata cin kashi yadda suka ga dama.
Salma ta yi tsaki, ta dubi Ikilima da Rabi da suke tsaye turus suna kallon Waheeda.
"Amma ku, saboda tsabar iya shege, kun san jiya ku ne da aiki amma ku ka ƙi yin wanke-wanke, kuka tara wa Heeda saboda ita ce jakarku ko? To ba za ta wanke ba, shegun yara masu kama da Iblis!"
Kamar wacce aka harbo daga ɗaki, Mama Jamila ta fito tana nuna Salma da yatsa.
"Wallahi ni ban haifi Iblis ba. Sai dai uwarku ce ta haifi Iblis, ga ta kuwa a gabanki tana addabar rayuwar kowa daga gida har cikin unguwa."
Salma ta yi tsaki tana hararar Mama Jamila.
"Ni dai kanwata ba Iblis ba ce. Kuma ko mutuwa za a yi, ba za ta wanke kwanukan nan ita kaɗai ba. Don haka kowace katuwa ta ɗauki kwanon da ta ci abinci ta wanke."
Zuwaira, wacce take tsaye a gefen Salma, ta ce,
"Malama dakata mana! Kar fa ki yi wa uwarmu rashin kunya. Kin san uwa ba ta fi uwa ba. Wallahi sai mun haɗu mu yi muku dukan tsiya, babu abin da ya sha min kai."
Umma ta ɗaga murya.
"Salma, Waheeda, ku zo ku wuce ciki. Bana son magana. Kun ji na faɗa muku. In ba so kuke ku ja min zagi da wannan sanyin safiyar ba"
Waheeda ta yi wani irin tuma kamar za ta kai bugu. Ta ja siket ɗinta sama kaɗan, ta cire dankwalinta ta ɗaura a kugunta.
"Babu wacce ta isa ta zagar mana Ummarmu mu ƙyaleta dai-dai nake da kowa a gidan nan. Duk wacce ta ce min kule sai na ce mata cass! Ehen, babu babba babu yaro."
Tana gama faɗar haka, gidan ya rincabe da cacar baki. Kowa na ƙoƙarin kare uwarsa da kuma nuna kuskuren ɗaya. Yadda suke zagin juna sai ka ce ba 'yan uwa ba ne, alhali duk suna ƙarƙashin mutum ɗaya ne. Hayaniya ta mamaye gidan tamkar ana cikin kasuwa.
Gyaran murya yayi daga bakin ƙaramar ƙofar gidan da aka yi wa labule da tsohuwar buhu. Gaba ɗaya suka yi shiru suka juya.
Yana tsaye a bakin ƙofar, hannunsa riƙe da butar ƙarfe, asuwaki na bakin sa, sanye da wata babbar malum-malum wacce ta sa ya yi kama da zai tashi sama.
Mugun kallo kawai Baffa yake wurga musu kafin ya ajiye butarsa a ƙasa. Ya ƙaraso tsakiyar gidan yana kare musu kallo ɗaya bayan ɗaya, sannan ya ce,
"Wannan wani irin masifa ce kuma? Wai ni kam in tambaye ku mana, duk cikin unguwar nan ni kaɗai ne mai mata uku da yara,kullum babu zaman lafiya a gidana? Ni kenan an gama da kwatanta gidana ana cewa gidan Baffa Ardo gidan masifa? To ku saurara, duk ranar da na sake jin wata faɗa a gidan nan, na rantse sai ko wata mata ta tattara kayanta ta koma gidan iyayenta! Shashashu kawai marasa kan gado!"
Cike da tsiwa Waheeda ta ce,
"Baffa, wallahi ka yi musu magana su daina zagin mana Ummarmu. Don sun ga ba ta magana ne, sai kowacce ta kwaso rashin mutuncinta ta zo ta sauke a kanta. To wallahi ba zai yiwu ba!"
Baffa ya zuba mata ido yana kallonta kafin ya yi mata dakuwa da hannu.
"Kin ci gidan ku. jakar ubanki na ce, kin ji? Wato ke ce fitsararriya ko?"
Waheeda ta kau da kai gefe ba tare da ta ƙara cewa komai ba.
Umma kuwa, duk hayaniyar da aka yi, ba ta ce uffan ba. Ta girgiza kai kawai ta juya ta shige ƙaramin ɗakinta.
Salma da Waheeda suka bi bayanta bayan sun gama hararar Zuwaira.
Suka same ta zaune a kan gadonta na ƙarfe mai spring, ta buga uban tagumi. Su ma suka zauna suna ta kunkuni, ita kuwa kallonsu kawai take yi ba tare da ta ce komai ba. Har lokacin ana jin muryar Baffa yana ta surfa bala'i a tsakar gida.
Salma ta ce,
"Kai, shi ma dai Baffa yana da uban mita wallahi."
Nan take Umma ta kai hannu ta daki bakinta.
"Dan ubanki Baffa kike cewa yana da mita, Salma? Wai ku kuna da hankali kuwa? Ni ban isa da ku ba kenan? ba komai, rayuwa ce. Idan baƙin ciki ya kashe ni na faɗi na mutu, sai in ga yadda za ku yi."
Nan take jikinsu ya yi sanyi.
"Ki yi haƙuri Ummarmu, ba za mu iya jure cin ƙashin da ake miki ba ne."
Ta galla musu harara.
"Ni ake zagi ko ku? To Waheeda, ki fita daga idona in rufe. Kin ji na gaya miki? Baki da aikin yi sai ja min magana a gari, kowa yana kuka da ke kamar shaidan. Iskancinki ya ishe ni. Bari Baba Karami ya shigo gida, sai na zauna da shi na faɗa masa duk wani iskancin da kike yi. Tunda ni kin raina ni, shi ai na san yana daidai da zamaninki."
Waheeda ta turo baki tana bubbuga ƙafa.
"Wai ke Ummarmu, komai sai ki ce za ki faɗawa Baba Karami. Mutumin da ya tsane ni, idan ya kashe ni ai shikenan."
Wani murfin tukunya da ke gefen Umma ta ɗauka ta wurga mata.
Da gudu Waheeda ta fice daga ɗakin ba shiri, Salma kuwa ta fashe da dariya ganin yadda ta arce. Kallon da Umma ta yi mata ne ya sa ta haɗiye dariyar ta yi shiru.
Waheeda ta zauna dabas a bakin ƙofar ɗakin Umma tana ƙananan koke-koke kamar jaririyar goyo. Sauran mutanen gidan kuwa babu wanda ya bi ta kanta, kowa ya kama gabansa.
Baffa ya fito yana ciro wata tsohuwar wayar keypad daga aljihunsa, ya matso da ita kusa da fuskarsa yana duba lokaci.
Sai ya ce,
"Wai ni kam yau me kuke nufi ne? Ban fa karya ba, na ga kuma baku da niyyar yin komai."
Mama Sadiya ta harare shi ta yi tsaki.
"Aikin kenan ai ba kunya, ba tsoron Allah. Ka ce a ba ka abinci, sai ka ce kana kawo ƙwayar gero cikin gidan nan."
Baffa ya washe baki.
"To Sadiya, in banda abin ki. Ku ai kuna sana'a, yanzu ku ne masu gidan. Sai abin da kuka ba ni."
Mama Jamila ta ce,
"To sai ka je wajen matarka ta gaban goshi, Mandiya. Ita ce da girki yau. Mu ma babu abin da muka ci, ita muke jira."
Ko tsayawa ya gama sauraronta bai yi ba. Ya nufi ƙofar ɗakin Umma, ya tsaya gefen inda Waheeda ke zaune tana kuka, ya yaye labulen.
"Haba Gimbiyar Mata!"
Haka yake kiranta, shi ya sa kishiyoyinta suke ƙara tsanarta, domin Baffa yana matuƙar son Umma saboda haƙurinta da zurfin ciki.
Ya ce,
"Ya za ki bar bayinki da yunwa, Gimbiyar Mata?"
Mama Jamila, wacce ta kasa kunne, ta yi wuf ta ce,
"Ah ah wallahi a gidan nan babu bayinta. Tunda kai ka mayar da kanka bawa, sai ku je can ku ƙarata ta yi ta jan ka kamar rakumi da akala."
Umma ta yi murmushi bayan ta saurari dukansu, sannan cikin sanyin murya ta ce,
"Baffansu, ka yi haƙuri. Ba wai haka na so ba. Awara da doyar da Salma ta yi jiya sam ba a yi ciniki ba. Babu wani kuɗi kirki da ta dawo da shi sai tulin awarar da ta rage. Duk a cikin gidan nan aka cinye su tass."
Baffa ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya zaro tsohuwar takardar naira dubu ɗaya daga aljihunsa ya wurga wa Salma.
"To shikenan. Ga wannan, sai ki sayo ko kamu a zuba wa kowa ya sha yadda zai isa. Ba sai an sayi sugar ba. Wanda ba zai sha haka ba, ya haƙura. Wanda ke da canji a cikinsa, ya siya abin da yake so."
Nan take Waheeda ta dakata da kukanta, ta miƙe zumbur ta ɗaga hannu ta ɗaura aka ta sa ihu.
"Wayyooo Allah! na shiga uku na lalace, Za su kashe ni Wannan wata irin jaraba ce? Ko mu muka kawo shan koko duniya iyaka kenan! Yau ko yunwa za ta yi ajalina, aradu ba zan sha kokon da babu suga ba"
Dube-dube Baffa ya fara yi ko zai ga wani abu a gefensa da zai kwankwasa Waheeda da shi. Nan take idanunsa suka sauka kan wata guga. Aikuwa, da sauri ya rarumo ya nufi kanta.
A sittin Waheeda ta fice daga gidan, tana sakin wani sabon ihu kamar wacce aka yi wa mutuwa. Tana isa bakin ƙofa ta ce:
“Wallahi Baffa, ka ba ni yobe in sayi dankwalin Hausawa. Ni dai ba zan sha wannan kokon nan na fama ba. Kullum sai shan koko da sharɓar miyar kuka, kamar mayu”
Cak ta bugi wani mutum da ke tsaye a bakin ƙofa. Da sauri ta ja baya tana kallon fuskarsa.
Wani irin tsoro ya bayyana ƙarara a kan fuskarta da ta gane wanda ta buge. Ta yi ƙoƙarin sulalewa ta gudu, amma kafin ta motsa ya damƙo hannunta gam, yana watsa mata muguwar harara.
Murya na rawa ta ce,
“Baba Karami… don girman Allah ka yi haƙuri. Ka yi min rai.”
Don’t forget to comment and like plus reshare.