SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)

Abinda zuciya ke so page 1

by @smauta

BISMILLAH DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI NI SM AUTA MAMALLAKIYAR LITTAFIN SAFIYYA NA SAKE DAWO MAKU DAWANI SABON LITTAFINA MAI SUNA SOMEONE'S HEART'S DESIRE 🥹❤️ WANNAN LITTAFI DAZAN RUBUTA ƘAGAGGEN LABARI NE IDAN SUNA KO MU'AMALA TAYI KAMANCECENIYA DA NA WANI/WATA TO ARASHI NE,THIS BOOK IS FREE, WANNAN LITTAFI KYAUTA NE………………TO CHAT ME ON WHATSAPP ***


SOMEONE'S HEART'S DESIRE 🥹❤️




Lily Lily Lilily🗣️haka nakejin muryar magidanciyar mata tana kwalama lily kira harta iso bakin kofar dakin nasu tana fada kamar zata auri baki,ina dalili yarinya bacci kamar kasa ko wacce kwaron bacci ya cijeta idan kika bari nadawo baki tashi daga baccin nan ba cikin gidan nan nidake ne…….


Wacce ake kira da lilyn ce ta farka jin fadan da akeyi a gaban kofar dakin su ta kalli gefen gadonta wayam alamun bakowa sai ita kadai,zumbur ta mike zaune tana mutsuke ido saukar ruwa taji a bayi yasa tagane da mutum a toilet din……


Bakin toilet din ta iso tace sarah sarah wacce ake kira da sarah tace meye,lily tace ohhh meye ko bari inshigo ciki zaki gane meye sarah tace dan Allah karki shigo kewai ko kunya bakiji ki kalli mutum zindir,lily tace ehhhh a haifeki gabana kicemun haka za'ayi maki aure ai kije gaban wani katon zir mezangani inba shegen nononki ba mai kama da lemun tsami……..

Inda sabo sun saba kullum fada kamr kaji amma yan uwane masu son junansu dole dama a samu irin hayaniyar nan ta sako da sako tana bikin mirror sarah ta fito daure da towel tace lily me kikace uwaki nace a tare suka kwashe da dariya……..



Ba uwaki zakice ba uwamu zakice banza kawai kinsan nace maki 9 fa ki tasheni ashe baki tasheni ba saida naji sababin mama na farka har 12 tayi inata bacci,ke waye zaki ba sakon tashin ki,na tasheki wlh kikaki tashi nikuma na kyale ki…….



Dagaske kike wai ni wlh banji ba kai Allah ya yayeman wannan bacci Abby dai yace babanmu na biyo wai idan yana bacci baisan inda kanshi yake ba,ummm yanzu dai ki shiga wankan kafin mama ta dawo wlh,lily ce ta matso kusa da sarah tace yar kanwata kinsan me?bansani ba wlh kuma banso inji danke ba alheri zaaji da gurinki ba kullum bala'i……..


Dalla ba wannan ba,bari dai in fito wankan mu tattauna masoyiyar suka ba juna hannu suna tafawa raff kai daga ganin wannan soyayyar dake tsakanin su ta ginu tun yarintar su gwanin sha'awa abunsu…….



A parlour lily ta samu sarah da ya adam suna kallon tv kallo daya tayima gefen ya adam ta dauke kanta shima haka,da salon tsokanar fada ta canza murya sarah baby i want tall to you please can you came?ta kalli sarah tana wani irin fari da idanu a ran sarah tace nashiga ukku dangerous ta fito fa😂😂😂💔 


Inajinki sarah kawai tace har lily tayi gaba ta dawo tace bakiji me nace ba?can you came?ko bakijin turanci ne ki taso sirri zamuyi ko dole sai na tsaya tsakiyar parlour na fadamaki sirri na kowa baki ehhhh?satar kallon ya adam sarah tayi taga gaba daya hankalin shi na gun tv yanajin komi take sarai ya gane so take ya tanka ta…..



A lokon kitchen suka tsaya gani meye,maye kuwa kawai so nake ki baro masa parlour waike lily meye haka dan kinga ya adam na kyaleki a gidan nan duk wata bolar ki kanshi gaskia banjin dadi,ehhhh kwareman baya shegiya ki nunaman rikona ake gidanku,uwarku ɗaya ubanku ɗaya nunaman yan ubanci….


Sarah ta rike hannunta kedai baki gajiya da wannan maganar wlh to koda ake rikon ki ai kinfi yan gidan ma gata nidai bansan wannan maganar lily tai mutsul tace daman mana kince haka,banda iskaci ina yayarki ina magana kinayi,kemai yaya ki kareshi wani ya adam yen yen yen yen…..



In banda mutuwa tayiman yankan kauna da ina zaki ganni gidanku ma har a matsamun ehhhh itadai sarah na tsaye tana kallon ikon Allah itafa ta dade da gane lily nada aljannu amma mama da abby sunki yarda kullum cewa suke tsiwace gareta,tsiwa har yanzu kingama University kuma service amma kullum abu kara ma gaba gaba yakeyi?…….



Wallahi idan bazaki fadaman kiran meye ba zan tafi ni ban shirya jin wannan iskanci na aljannunki ba,oh nice keda aljani like kawai ma banida hankali ko?mama ce take fitowa daga dakin ta tanajinsu tace lily idan na karajin magana a bakinki irin wannan kinsan dukan sakwara a gidan shine zan maku ku dukan ku…….




Mama ina wuni da ban wuni ba kinganni baki tashi sallah asuba akan lokaci ba breakfast ma bazaki tashi kiyi akan lokaci ba,har lokacin cin abincin rana yayi kinci abincin ko kin tsaya surutun ki na mutuwa tayi maki yankan kaunar?…..



Sai lokacin ma ta tuno tanajin yunwa wlh ita idan tana tsiwa gaba daya ma Rayuwa ta manta wa take da ita zaki wuce kokuwa saina zo wurin ina amfanin wannan rayuwa kullum kuna girma amma ƙasa kukeci haka za'ayi maku aure mazajen ku suyita fama daku nidai duk wacce mijinta ya kawoman kararta ban yafe ba…..



Lily tayi karaf tace mama ba wanda zai kawo maki wata kara kedai kuyimana auren lokacin da zamu zage mu nemi ladar waya gani sai lokacin wani kololon bakin ciki yaji ya kara taso mashi jin wannan ficikar yarinyar abinda take cewa,bai gama tsinkewa da lamarin ba sai dayaji sarah tana daria wallahi mama lily aure take so……



Waya hanata ta fiddo mijin harda ke din duk ku tafi gidanjen ku in huta da sababi da dogon baki kullum cikin magana nake ina dalili,ran adam ne ya ɓaci ya mike tsaye hanyar kofa ya nufa mama tace sai ina baiko dago kanshi ba balle ya kalli maman tashi kawai yace am coming taf taf taf ya takala benen ya haye sama zuwa dakin shi……




Shigar shi dakin keda wuya yahau safa wal marwati tsakiyar dakin da yake wani fankacece an zuba mashi kaya irin na kawa daka gani kasan dai wannan gida na masu hannu da shuni ne,gaban mirror yazo ya tsaya ya dafe goshin shi ba abinda ke mashi ringing irin maganar lily da take cewa kuyimana auren mana…….



First thing daya fara fado mashi a rai irin yadda last week yaganta da wani namiji a bakin gate ya rike mata hannu and yazo ya fada kiri kiri yarinya ta shafa ƙwallin abada tace karya yake ba the worst part din kuma abby ya yarda da maganar ta mamansu ta rufeshi da fada kmr zata ari baki tana cewa sheri zai mata……..



Kara dafe kanshi yayi dayaji yana barazanar tarwatsewa a daidai wnn lokacin,meyasa komi lily zatayi yakejin zafin shi har cikin ranshi tuni ba tun yau ba tun lily na karama yakejin wani irin zafin kishi a kanta wanda baisan na meye yayi tambayar har ya gaji duk answer daya ce zaace maybe sonta yake bai sani ba,turarukan gaban mirror yayi watsi dasu kasa yace nooooooooooooo karya ne karya ne ni adam bazan tabason wannan yarinyar ba,batada kunya……….




Ya saka wannan ta fidda wancan ya samu ya kwanta har bacci yayi nasarar yin gaba dashi,a bangaren lily kuwa dadi ne ya kashe ta ganin yabar parlour tasan maganar da tayi ne ya baƙanta mashi rai dama tayi da biyu ne kuma kwalliya ta biya kudin sabulu yanzu ma suna kitchen itada yar uwarta suna girkin rana,koda suka taso gidan masu kuɗi mama tayi tsayin daka abincin gidan sukeyin shi……..



Bata yarda masu aiki na masu aninci ba shiyasa sun bala'in iya girki duk wani nau'i na snacks shima haka,da safe ne kawai mama ke breakfast sauran kuma lily da sarah keyi,kmr kullum lily na dafa white rice sarah na miyar sunata firar su ta yan mata,wayar lily ce tayi ringing da sauri tabar wurin gas tazo ta dauki wayar ta……



PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR SMAUTA TAKU CE💃💃