SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)

Abinda zuciya ke so page 3

by @smauta



Anan tsugunne abby ya barshi ya wuce direct dakinshi ya koma ya dauko car key's dinshi ya nufi farfajiyar gidan su motar shi kirar Mercedes ya nufa yashiga zuciyar har ci take da wuta a lokacin ya buga wani irin mugun horn da duk lokacin da yayi shi kowa yasan ba lafiya an taɓa damo sarkin hakuri da sauri malam shazali mai gadi ya wage mashi gate ya cilla motar a guje Abby da mama suna tsaye bakin window tun horn dinshi na farko……

Sai lokacin mama taji ba dadi a ranta ta kalli Abby da murmushi yayi mata kadan yace Allah ya tsare da sauri mama tace Amin,gefen lily itama tana makale bakin window tana kallon fitar adam din kwance take jikinta yayi tsami taji wannan gigitaccen horn ta leka taga wane dan albarkan ne,tabe baki tayi ta galla ma gate dinsu harara kamar yana kallon ta😂😂😂😂……..



Bai zame ko ina ba sai shagon abokinshi yaje bayan sun gaisa yace yana a bashi iphone 17pro max abokin nashi ne yace bayan ta hannunka kuma,dan tsaki yayi baisoma ya tuna da abinda ya faru,ahhh kaifa miskili ne ceman zakayi amaryar tamu za'a gwangwaje sai dakai arch Adam mtswww kaifa ka cika dumi sufyan wlh zan tafi nan take aka haɗa mashi komai ya fiddo wayar shi yayi payment har bakin mota sufyan ya rakoshi yanata tsokanar shi……..




Inda sabo adam ya saba da iskancin sufyan tunda yayi aure yake ganinsu yara, adam ne bai koma gidansu ba sai wurin 2 na dare yashigo gidan,yasan yanzu kam gidan kowa yayi bacci da mamakin shi yana buɗe kofa lily yagani kwance akan kujera tana waya da wayar sarah,ledar hannunshi ya kalla yaji wani makokon bakin ciki ya taso nashi, yanzu da kudin shi zaisai wayar da zata ringa sheke aya da ita?wata zuciyar tace kai never😂😂😂😂dani da masu karatu in bakason wayar a bamu🥱🥱.........


Bangaren lily kuwa har wani kara narkewa take abunta cikin kujera tana waya da Alhaji najib dinta,bai kara mata kallo na biyu ba ya wuce sama direct dakin shi wani uban tsaki ta buga ta galla mashi harara sarai yajita kuma yasan dashi take a mamakin ta sai taga ko juyowa baiba, toilet dinshi ya shige ya sakar ma kanshi ruwa yakusa 40 manta sannan ya fito kugunshi daure da towel daya kuma yana goge sajen fuskar shi……..







Washe gari da safe kuwa wayar abby ce ta tashi adam, Assalamu alaikum abby ina kwana Lafiya lau kana ina ne?ina daki office fa banjin dadi bazan samu shiga ba kaje asibiti?a'a ina wayar danace ka siyo gatanan kazo ka kawomun zan fita office to abby da saurin shi ya diro a gado ya fada toilet fuskar shi kawai ya wanke yayi brush wata ash color jallabiya ya sako kafar shi da bathroom slippers hannun shi rike da sabuwar wayar ogiya lily😂😂……..



Lily ce tsugunne gaban abby gefen fuskar ta yayi ja sosai abinka da farar fata ko ba'a fada mata ba tasan waye ya shigo parlour sbd kanshin shi na lokaci guda daya karede parlourn abby da kamshi,gaban abby ya tsugunna ya sake gaisheshi ba yabo ba fallasa ya ansa hannun shi ya saka ya ajiye ledar wayar gaban abby,sai lokacin lily ta dago da fuskar ta ya adam ina kwana iskan daya debota ma bai kalla ba balle tasa ran zai ansa gaisuwar ta………



Da shirin abby na office ya muskuta yace ke lily meya hadaki da yayanku?kama hannunta tayi tana murzawa tanajin gaba daya idonshi a kanta duk karyar ta sai samun kanta tayi da wani matsanancin tsoro ya lullubeta lokaci guda,a karo na biyu abby yace ba magana nakeyi dake ba,ah dama abby mama ce ta sakamu girki to muna kitchen nida sarah wlh ka tambayi sarah abby ya katse numfashinta cemaki nayi meya hadaku kinaceman a tmby Sarah?…….



Nima abby bansan menayi ba kawai yazo ya rufeni da duka nashiga store na rufe ina bashi hakuri amma yaki saida ya cire kofar store din sarai abby yasan shakiyyancin diyar tashi yace adam din bashida hankali dazai tasaki gaba yaita duka?zaki fadaman gaskia kosai na tashi na sassaba maki,jikinta ne ya hau kyarma sai ta kwace da kuka wlh abby nidai ban mashi komai dama kwana biyun nan sai yayita hararata……….



Tashi ki bani wuri abby ya korata har tuntube take ta fice a parlourn sai lokacin ya dago idon shi cikin na abby ya sake sunkuyar dakai,Adam na'am Abby masani duk abinda zai kai ka daga hannu ka saki lily ba karamin abu bane,kanshi ya jinjina abby ya kara dacewa saika rage zafin zuciyar nan taka akan mata,lily da sarah har yanzu yara ne baka tunanin hukuncin da kayima lily yayi yawa imagine har yau da safe fuskar jawur kai kanka da kake namiji adam ban taba maka irin wannan dukan ba…….




Lily marainiya ce bayan maraici diyar kanena ce uwa daya uba duk duniya banida kamar Isyaku ya tafi yabar man matar shi da lily itama Amina maman lily tabi Isyaku bawai banso a tsawatar ma lily bane a'a shi hukunci kala kala ne anayin na farko da lalama idan aka kara wani sai ayi da fada matakin karshe shine duka adam ko dukan da kayi mata yayi yawa………





Yau lily ke kallon idona taceman zata koma gembu wurin yan uwan mahaifiyar ta,saboda ka tsaneta a karo na ukku kenan daya dago kanshi ya kalli abby yace abby nine na tsaneta?kaima ka yarda wannan abun danayi tsanace bazance kafini son lily ba amma abby inada yakinin a yanzu ba wanda yakaini son lily abby yadda nakejin sarah haka nakejin lily duk abinda zanyima sarah shi zanyima lily sbd dukkansu kannena amma unfortunately lily batada kunya abby batajin magana ko kadan imagine lily ce abby take kissing wani banza a banza a waya yana maganar numfashin shi na sarkewa saboda azaba……..




Shuru abby yayi na dan wasu lokuta jin me lily ta aikata,cikin ranshi kawai yake nanata Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Allah amanar dana dauka akan yarinyar nan Allah ya bani ikon sauke nauyin ta, Allah ya tsareman mutuncin yarana maza da mata kusan sakanni bakwai ya dauka kafin ya dawo daidai,adam ka tabbata abinda ka fadaman hakane jinjina ma abby kanshi kawai yayi……..




Ba wanda ya kara cewa komai saida mama tashigo abby ya sallami adam ya zayyana duk abinda ya faru Mama shuru tayi kamar mai nazari sannan tace,a nawa tunanin abby mezai hana tunda tanada wanda takeso ya kagara kuma ayi auren nan kaine ka hana kawai ka aurar da ita inaga hakan zaifi mana kwanciyar hankali abby,karyazo muna ganin shi babban mutum wata rana ya yaudare mana yarinya…………



Hakane maman yara, Allah ya fishi ki bani sati biyu inaso in ƙara bincike akanshi sosai kafin magana mai karfi tashiga tsakani,wannan wayar ta lily ce ki bata ki kara jamata kunne kuma,namakara office ban fita ba,sai lokacin ta kalli agogo har kusan 12 ahhh wannan wuce makara ma kuwa da office dinane kana cikin yan dukan makara abby yayi daria yace to ta Allah kuma ba taki ba, tsakani da Allah soyayyar mama da abby tana burgeni duk da gasu sun manyanta amma ba abinda ya canza na bama juna kulawa………..





Kwana biyu da fadan sai yau mama tabama lily wayar ta shima dan taga ƙarshen wata yazo ya kamata ta duba yaushe take clearance,gaba daya sarah da lily mama ta zaunar a daki tayi fadan tayi fadan ƙarshe tabi da nasiha sosai jikin lily yayi sanyi da nasihohin da Mama tayi masu harda hawayen ta😂ahhh nikuwa nace wanda yagaji bai saba ba wai lily da kukan nasiha😂😂😂😂😂💔……..




Dakinsu suka dawo sarah nata kiciniyar budema lily wayar amma ita ko murna batayi waike menene haka lily ahhh mefa kawai wayar bataiman ba nace mashi inason iphone ne Samsung ya fasaman Samsung zai siyoman salon in aje wayar ko ya aje tashi wani yayi macanza azo aita kace nace,sarah ta kwashe da dariya in banda abinki inake ina ganin wayar ya adam balle har macanza ta hadaku kuma shi tashi black ce naki silver fa,wannan dan rigimar da gangan zaizo yayi macanza niko wlh bazanyi shuru ba inkuwa ranar sama da kasa zata hade…………




Dafe baki Sarah tayi tace kinsan tsakiya bakida komai😂💔 keni wlh nagaji da zaman gidan nan aure kawai nakeso ki zauna nan har sainayi aure na haihu naga ke bakida niyyar aure ni wlh jiyama na fadama dan aljanna kawai yazo ai magana a wuce wurin,barin bude wayar sarah tayi tace kike serious waike da gaske wannan tsohon zaki aura???……..



Tsoho sarah aike kikaga tsoho ni yaro nagani danye shakaf ni da in auri saurayi gara banyi aure ba wlh me suka sani banzayen sai zafin kai idan kinason kiga so kiga kauna kiga ruwan kulawa nemi mai mata sarah tace ke Alhaji najib fa ya haifeki wannan ba yaran shi bane kika nunaman a hoto ba?sune mana ko autar shi ta girmeni yace autar ma 30 years gareta nikuwa 25 nake kinga ko ta girmeni sosai……



Shine zaki fada mashi sarah bazaki gane ba wallahi bala'in son shi ni kadai nasan irin soyayyar da yake bani tun yanzu ke inaga nashige ciki wayyo dadi ta wani wuntsila saman gado ba abinda sarah keyi sai dariya ke yanzu akan tsaran abby kike wnn makyarkyatar duwawun?kwarai soyayya ai gaskiya ce sarah na samu abinda nakeso shima ya samu abinda yakeso matar shi tayi watsin iska dashi fa,nikuwa Allah ya kashe ta bani meyayi saura?in rike wuta kawataaaa🔥🔥kun rantse da Allah lily da sarah kawaye ne yadda suke cafketa a dakin nan😂………



Ni kuwa in kinga na auri tsoho to kaini akai amma da hankali na da wayau ban auren tsohon kingin wata ta gama dashi da lily ke siɗi zaki samu,siɗi kikace wlh nafi karfin siɗi gidan dan aljanna,ai yadda nace haka za'ayi duk yadda na dama haka za'a sha ta daki kanta tace tunanin ki wannan kwanyar a banza take aiki,mata yanzu sun zama abinda suka zama daka mijinka yanada kudi kuma yana sakar maki kudi saiki farajin ke kin girmi aure,dan aljanna ai yana hakuri,kullum mata baki wnn kasa baki waccan kasar shi kadai cikin gida uwa aljani bai isa da gidanshi ba, wallahi na aure shi zan shayar da ita ruwan mamaki yadda kikasan ana tarairayar jariri haka zan mashi ko ya samu ya dawo cikin hayyacin shi,sarah tace Allah wlh kuwa,za'a barsu ne suka kwashe da dariya………



PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹....SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……