SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)

Abinda zuciya ke so page 4

by @smauta

Page 4


WACECE LILY 
Asalin sunanta shine fatima Isyaku amma ta taso ana kiranta da lily sbd kyaun halitta da Allah yayimata tun tana yarinya shiyasa mahaifiyar ta Aminatu take kiranta da lily,lily yarinya ce mai wayon tsiya sosai tun tana yarinya tanada kaifin basira ga surutu shiyasa takeda tsananin shiga rai asalin mahaifiyar lily yar taraba state ce fulanin gembu lily ta biyo mamarta fari da kyau ga tsawon gashi……….



Mahaifinta kuma haifaffen dan garin kano ne ya taso daga shi sai yayanshi abby mai suna Ahmad iyayen su kansu yan asalin kano ne sun taso tare shida dan uwanshi duk da akwai tazara ta kusan shekaru goma tsakanin su mahaifiyar su da suke kira babani ita suka budi ido suka sani domin tun isyaku na ciki Allah yaima mahaifinsu rasuwa cutar cancer,haka suka taso cikin maraici bana wahala ba sbd babani mahaifiyar su yar kasuwa ce sosai Allah bai ragesu da komai tun daga karatun boko har na islma duk tayi tsayin daka ta basu……..




Da girma ya fara riskar su saita kaisu kasuwar sabon gari wurin kaninta da yake harkar gwal alhaji lawali a gurin shi suka koyi kasuwanci tun basu iyaba har suka goge sosai a harkar gwal ana nan ana nan lokacin yayesu yayi babani ta tattara duk kudinta da wani gidan su da mahaifinsu yabar su ta saida aka zuba kudin a kasuwa ko a zamanin da din sun zuba kaya dan ba karamin kudi suka narka a shagon ba……..




Daga Ahmad sai Isyaku kanenshi suke zama a shagon kasuwa gaskiya ce da rikon amana kafin shekara karkuso kuga yadda Allah ya dafa masu a harkar kasuwancin su,duk abinda aka samu ribar ukku ake rabata babani ahmad sai Isyaku karami,har kasuwancin su ya bunƙasa sosai takai abby shike zuwa Dubai da kanshi a buga masu gwal irin wanda suke so,daganan ne fa babani tace to zamanshi haka bazaiyiyu ba ya fiddo mata yayi aure……….




Abby a lokacin baiso yayi aure ba amma babani ta matsa mashi lamba har Allah yasa watarana yana shago saiga mama da ƴan gidansu sunzo siyan zobe abu kamar wasa ya taya lokacin tana aji shidda makarantar secondary dokar gidansu kuma idan kayi candy baka wucewa saidai gidan mijinki idan ya yarda……..



Nan fa abby ya sanar da babani halin da ake ciki ya samu mata ummalkhairi yar gidan malam na tsamiyar boka murna wurin babani ba'a magana ta fadama dangin mahaifinsu aka shige gaba akan komai da ummalkhairi tagama makaranta za'a daura masu aure abby yashiga idasa ginin shi daya fara…….




                               *************

Bayan shekara goma da auren abby har sun haifi dansu daya wanda yaci suna Adam daga lokacin Allah bai kara basu haihuwa ba tun mama na damuwa har tazo ta hakura ta fawwalama Allah komai, lokacin ne abby yake aiken kanenshi wurin abokin kasuwancin sa dake taraba gembu anan Allah ya hada jinin Isyaku da Amina yarfillo, lokacin zamani yacigaba an fara rike waya haka Isyaku yasaima aminar shi waya suna gaisawa lokaci bayan lokacii……….



Komai ya canza abby da ɗan uwanshi sun bude katafaren Company na ƙera gwala gwalai a cikin birnin kano Nigeria,sunyi kudi bana wasa ba har lokacin Allah bai kara basu haihuwa ga bikin kanen shi Isyaku na sawo kai,ya zauna da ɗan uwanshi Isyaku yace cikin gidajen su ya zabi daya kafin su gama nasu ginin dayakeso su hadu wuri daya shi da Isyaku sai babani hakan akayi kuwa wani gidansu dake nasarawa sultan road Isyaku zai zauna da Amina yarfillo………..



 lokacin adam yanada shekara goma cif a duniya yana matakin ajin primary na huɗu yaro black beauty mai hazaka da basirar zane zane, lokacin ne kuma akasha hidimar bikin kawun shi wanda a duniya ko iyayen shi basu nunamashi son da Isyaku yake nunama Adam komai na Adam Isyaku, haihuwar shi kawai sukayi amma shike tafiyar da rayuwar shi,dakuwa yayi aure rabin rayuwar Adam gidan Isyaku ta dawo akayi dacen mata Amina mai hakuri da juriya suka hade kansu itada mama ba fada tsakaninsu na kishin sauri saima soyayyar juna kmr jini daya,ana nan Amina ta fara laulayin ciki murna wurin mama karkuso kugani kullum mama tana gidan sbd laulay take mai tsanani………





Abinka da wacce an kawoka gari bakasan kowa ba Mama ce uwarta itace ubanta yaya sama yaya ƙasa haka amina ke kiran mama wanda hakan ba karamin dadi takeji ba,tun ciki na karami har ya fara fitowa sosai, Adam kullum yana damun Amina akan dan Allah idan zata haihu ta haifo masu baby girl wacce zata dinga wasa da ita, Allah maji rokon bawa ranar da Amina ta haihu kuwa ta samɓalo yarinyar fara jawur kmr tayi kaki ta ajiye………




Tun a asibitin Isyaku yasama yarinya suna Fatima amina yarfillo tace za'a dinga kiranta da lily tun kafin sukoma gida saida babani tasa aka kawota asibitin taga yar sabuwar jikallen ta adam konan dacan baya matsawa baya bari na a taba mashi lily kar a dauketa dashi ake renon lily idan ta fara kukan daren ta rutsum baya bacci idan yana gidan, school kuwa tsaraba kala kala yake kawoma yar kanwar shi wata sosai ce mai karfi Allah yasama adam akan lily saidai kashhhhh rayuwa bata daure baaaaaa😂🥹…………….




Bayan haihuwar lily da shekaru ukku tanata gudunta ko ina aka wayi gari mama na dauke da ciki Innalillahi murna wurin family nan karma a tona amina yarfillo itama da ita akasha rainon cikin mama har ciki ya isa haihuwa ta samɓalo yarinyar ta mace abby yayimata halaccin da bazata manta ba ya sakama yarinyar suna saratu sunan yayar mama da Allah yaimata rasuwa bayan auren su……..




Hakanan suka cigaba da rainon ƴaƴansu cikin kulawa da tarbiyya kowa na gidansu amma bai hanasu haɗa kan yaransu ba, Adam gaba daya ya koma gidansu lily da zama tunda mama ta haihu amina yarfillo ta anshe adam tace taji da sabon goyon ta hakan kuwa akayi shima yanason zama gidan saboda kanwarshi lily ko kuda ya taba lily indai gaban adam ne sai yaji dalili a lokacin adam yashiga js2 lily na nursery school dinsu daya kowane abokin adam sunsan lily itama haka zataita kuka ma auntie's dinsu akaita wurin yaya🥹……….




A kwana a tashi ba wuya wurin Allah adam sun kusayin candy a yanzu lily na primary 4 Sarah na primary 2 dukkansu school din su daya,yadda Adam yake kaunar lily haka itama lily ta taso da soyayyar yar uwarta sarah baby a lokacin lily tazama terror a school din nan ba wanda zaacema lily Isyaku bai santa ba,uwa uba ka tabo sarah ranar zaaga tashin hankali gata da mugun kokari amma wasa da fada baya barinta tayi abinda ya dace kullum cikin kawo kashedinta ake wurin yayanta adam saidai ya basu hakuri danshi baya iyayima lilyn shi fada,har yan class nasu suna tsokanar da adams lily😂🤭kai wnn suna yayi……….



PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹ANCE TUN RANAR GINI RANAR ZANE BAZAN DINGA LONG RUBUTA BA SBD MATSALA TA IDO KUYI HAKURI DA WANNAN......SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……