SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)
Abinda zuciya ke so page 5
by @smauta
SOMEONE'S HEART'S DESIRE 🥹❤️
Watarana adam da abokinshi Imam suna rubuta waec daga primary section lily ta debo zugarta har senior section azo wurin yayanta tun daga class dinsu ya hango ta da wasu yara yake cewa a ranshi Allah yasa ba bugun su tayi ba akazo wurin kawo kara bakin class ya fito ya taresu lily ya adam duk duniya itace mutum ta farko data fara kiranshi da ya adam kudina sun fadi kabani inaso in siya bigbom kallonta yake tsaf kmr ba tare sukazo school ba uniform din nan tai masu kaca kaca…….
Imam dake bayanshi ne ya zaro 200 ya mikama lily fafur taki ansa imam yayi juyin duniya ta ansa taki tace ya adam zai daketa wata dari biyun ya fiddo a aljihu ya mika mata sannan ya daure fuska tamau yadda zataji tsoron shi yacemata karya sake ganin ta tazo nan itadai buƙatar dara kasawa kudi ya bata ko gobe saita dawo haka ta ayyana a ranta,ta gefen imam zai wuce shi yace adam yarinyar nan tamun dan Allah kubani ita mana munayin candy kaga china zantafi karatu wlh in tafi da ita idan takai js3 haka kawai ina aureta idan ta girma zaayi cikakkiyar mace yana murmushi irin na tashen balagar nan😂😂😂🤭…………
Wani tuƙukin bakin ciki ne ya kama adam bai tankama imam ba ya rabashi ya shige class table dinshi ya samu ya zauna yanajin kanshi na daukar mashi chargy ohh kallonta ma imam yayi har yasan za'ayi cikakkiyar mace abinka da yarinta a wannan lokacin ya rasa gane meke mashi dadi,wani zazzabi zazzabi yake neman rufeshi bai daddara ba yasake zuwa yamashi maganr lily shifa dagaske sonta yake zuwa ɗaya adam yaima imam saiga idonshi ji kake gabbbbbbbb……….
Dambe ya kaure na maza ana ba hammata iska mai hakuri bai iya hakuri ba,naushi yake kaima imam ta ko ina abokansu dakyar suka shiga tsakani na abinda adam keyi sai huce yana kiran stay away from lily imam ban hada kannena da kowa ba wallahi sai in kashe kowa ya nemi shiga gonar kannena,ina ruwanka da ita primary 4_5 can you imagine kana maganar auren ta i can't take it……….
Dakyar aka samu aka daidaita fadan nan ya koma seat dinshi yanata huttai ya rasa meke mashi dadi koda akazo ɗaukar su tareda lily tanada mashi surutu kamar yadda ta saba yayi banza da ita har suka iso gida har magriba maganar imam naci mashi rai yazo ya samu anana lily homework a parlour fada yashiga ma lily kan karta kara zuwa section dinsu abun har daurema Amina yarfillo kai yaso yayi yau adam ne akaji dashi da yar lelen shi lallai tayi laifi,bayan ya koma dakin shi mamarta ta kara gargadin ta kan zuwa section din nasu……..
Tun daga lokacin adam ya fara canza ma lily sakin fuskar da yake maka lokaci guda ya dauke ba ruwanshi da ita tsakanin su kullum concrete warning ne,abinka da ita kuma mai kunnen kashi sai ta fara ganin ya takura mata shima ta sakashi cikin sahun wanda take tsigalewar ko gida baison wannan kutsun wasa da takeyi ita kadai ai yanzu abun sai ya karu kamar ana kona mata kai har saida baban lily yashiga maganar……..
Bayan shafe shekaru kusan biyar a lokacin adam yagama degree dinshi a kasar china yajona da masters ɗin shi kan zane zane wato architecture,yaune suka samu labarin mummunar gobarar da tashi gidansh lily wanda aka samu asarar rai da dukiya😭😭😭😭😭😭😭😭😭 Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Allah yayima baban lily rasuwa tareda mahaifiyar ta a lokaci daya ba abinda zamuce saidai muce Allah yajikansu da rahama Amin……….
Wannan mutuwa ba ƙaramin kada adam tayi ba bayan Wada daya da rasuwar yasamu isowa Nigeria yayi kuka kamar zai zare yayi kukan dashi kanshi baisan yanayi ba iyayenshi dasuka nunamashi fatan dunia yau ya wayi gari babu su wayyo Allah sai da kyar da addu'a aka shawo kan adam ya natsu,a lokacin kuwa lily tazama abun tausayi batacin komai kullum kuka haka mama ke kokarin kula da lily yadda zatayi ma sarah haka zatayi ma lily har takai mama batama ta sarah lily ce gabanta bata yarda ace lily tayi wani abu acikin gidansu…………
CIGABAN LABARI
Wannan kwalliyar da kikeyi tunda safe wai ina zakije wohoho sarah kin cika tambaya wlh ai kinsan ban fara yawon bariki ba balle ki tsareni da tambayar ina zanje clearance zanje kokin manta ne,sai lokacin sarah ta kalli calendar wayarta tace kawai kiceman clearance zakije shine sai kin tsaya jeraman magana,lily tayi wani farr da ido tace tooo abar hali aci me dalla jeki wurin mama ki ansoman kudin adaidaita bansan shegen surutu idan baki zuwa kuma ki fadaman sarah tace Allah baki hakuri…………
Kicibus sukayi da sarah ta anso kudin kai yayata wnn wanka yayi anya clearance din nan kadai zakije nasanki fa mishau ce ɓadda musulmi karaf a kunnen adam,lily tace eh to inasa rai daga rijiyar zaki idan nagama clearance din zan wuce club in kurbi giya ko kwalba biyu ce zaki bani guri shegia kosaina halbaki dan aljanna fa zaya kaini idan banyi kwalliya ba ya kikeso in fita,ohhh shine kikaima mama 419 kudin adaidaita kmr kinyi gabanta kuwa……….
Kinsan bakida power wurin mama zatace karya kike kinga gashinan yana kirana ma a waya wlh nasan yazo mezan siyomaki?duk idan lily ta fita sai tayima sarah tsaraba kamar yar yarinya hakanan Allah ya dora masu son junansu sarah tace choco milo bazan siyo wani choco milo ba fadi wani abun da to kije ten to ten kisawoman pounded yam dinsu,yar son banza keda wnn pounded yam din taki dai………
Koda tashigo parlour bata lura da ya adam dinba saida takusa fita kofa taji kmr ana kallonta ilai kuwa shine kyar idonshi cikin nata daburcewa tayi ta fara kame kame ya ya ya adam ina kwana iskan daya debota bai kara kalla ba balle tasa ran asa gaisuwar nan tasan shi dama da gaba balle anyi abun nan duka yau kwana ukku sai tafi wata baya ansa gaisuwar ta………
Tana fita parlour tace kama kanka dama ba dan Allah na gaidaka ba ya wani mutsuke fuska sai kace wanda akaba sakon mutuwa kai ina dalili ina dan mafari Allah ka nunaman ranar da zan gama service din nan inyi aure uban kowa ma ya huta idan nabar gidan ya isa ya kara ganina tazuru kawai🤣🤣🤣ahhh ahhh lily kina gatsar yanayi ya adam dinne tazuru………..
PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏......SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE..........