SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)

Page 6

by @smauta




A kofar gate dinsu ta samu dan aljanna zaune cikin mota yanajiran fitowar gimbiyar da takun nan nata kamar batason taka kasa ta bude motar huuuuu dan aljanna na'am matar dan aljanna barka da fitowa wannan kwalliyar duk ta clearance ce??



Wani fari ta karayi da ido tace a'a kwalliyar mijina ce wani dafa kirji alhaji yayi yace washhh, wallahi duniya baka gane da sauranka sai ka samu yarinya kamar ki, Allah ko hmmm wani abun ma sai an daura,na fiki son wannan ranar amma yazanyi gidanku sunce ba yanzu amma da yau da gobe duk ta Allah ce………





Ummmm dan aljanna kenan nima fa kaina nagaji da zaman gidan nan,kaima kuma nagaji da yadda kullum kake yawo wuri wuri siyan abinci babban mutum kamar ka amma ace bakada natsuwa a gidanka,ina sonka tsakani da Allah kuma inaso in shiga rayuwar ka ne badan komai ba saidan kaima kazama cikakken magidanci yadda kowa yake alfari da gidanshi kayi fira da iyalin ka,kaci abinci kuma ka samu natsuwa…………


Lokaci daya dan aljanna ya karajin son lily namashi kawanya a dukka sassan rayuwar shi har inda zatayi clearance ya kaita yana zaune a mota yana zaman jiranta can saigata ta taho tana tafe tana bala'i kedawa kuwa,baki abun magana nida wa kuwa in banda mutanen nan ku tara mutane wuri ku kasa saka koda pan ne a wuri kaji zafin da nakeji kuwa🥹…………




Sorry my wife indai zafi ne yanzu za'ayi maganin shi bari in ƙara maki karfin ac haka kuwa akai kan kace me hatta tssane,daganan sai ina?ten to ten yarinyar can tabani sakon pounded yam, murmushi yayi kefa me zakici yasan ansa daya ce kullum dai tace mashi takoshi da mamakin shi sai yaji tace biryani…………




Wani irin dadi yaji a ranshi yau rana daya lily ta saki jiki dashi zasuje restaurant cin abinci tafiya sukayi mai ɗan nisa kafin suka iso ten to ten dama shi wurin zuwanshi ne abinka da babban mutum dan danan ya saye hours din wurin sbd zai shigo yaci abinci shida yar gwal saida aka gama setting komai sannan suka shigo daga ciki………




Suna zaune lily natama dan aljanna yaukin nan nata da a rayuwar shi ba abinda yakeso sama da ita kan kace kwabo an cika mata gaban ta da kayan alatu,ta fara tsakura shiko gogan sakin jiki yayi yana nakar abincin shi, lily ce uwar iyayi ta bude wnn ta zuba wnn tanadai ta maintaining steeze dinta🤣…….……..




Sun kusa share hour a wurin bakowa saisu kadai hakan ba karamin dadi yayima lily ba dama abinda yasa kullum idan yayi requesting suje cin abinci take cewa a'a kenan sbd mutane,amma indai haka zai dinga mata ai wlh zata dinga boyewa ne ta fito suje cin abincin nan🤣🤣…………




Take out dinta na pounded yam suka gama jira aka kawo dan Allah yayi paying bills dinsu yana riƙe da ledar milkshake ita kuma tana sabe data abincin fitowar su keda wuya daga kan da zatayi karaf cikin idon ya adam,gaban lily ne yace wani dammmmmmm a karo na farko kuma a rayuwarta dataji yau rana kenan taji tsoron ya adam…….





Kallo na biyu bai kara mata ba ya rufo kofar motar shi ya dunfaro inda take,jikinta ne ya fara karkarwa ta kasa gaba ta kasa baya dan aljanna tuni yakai mota bai lura da bata biye dashi ba ya adam ya kusa zuwa daf da ita ta saki ledar hannunta dan ta sadakas mugun bugu ne zai mata a bainar jama'a………




Dan Allah kayiman rai ya adam bazan kara ba yadda ta kira sunanshi da sigar shagwaba saida yaji wani tsauuuuu har tsakiyar kanshi amma mummunan kishi ya hanashi barin yajin dadin hakan,kallonta baiba ya rabata yashiga cikin restaurant din kanshi na wata irin sara mashi,me lily takeso ta maida kanta ne?ya tambayi kanshi ba ansa……….




Da gudu ta kwashe ledojinta ta arta da gudu sai cikin motar dan aljanna dan Allah kayi sauri ka kaini gida lafiya lily?nidai ka kaini gida ba lafiya wlh subhanallah bazan iya magana ba muje kawai idanunta na fitowa waje sosai dan tasan ya rigata zuwa gidan bala'in da zata tarar babba ne amma ayi a gabanta tasan yadda zata kare kanta ne yawwa……





A kofar gidansu ya ajiye ta ko sallama kirki batai mashi ba ta kwashi kayan ta tayo cikin gidan koda tashigo parlour bakowa dakinsu ta haura kirjin ta na dukan tara tara,sarah na zaune ta idar da sallah rufewar kofar dakin bammm dataji yasa tagane ko wacce kuma a wane hali take……..




Kan gado ta fada rikicaaaa sarah nashiga ukku na yau nabani da sauri sarah ta kalle ta minene ke?ya adam ya ganni da dan aljanna,to sai me naga dai har gidan nan yake zuwa kuma wanda zaki aura ne idan ba'a ganki dashi ba wa kikeso a ganki dashi?a ina ma ya ganki?………



A ten to ten mana mun fito nida dan aljanna tsaf ta kwashe duk yadda akai ta fadama sarah mtswwwww yau kin bani mamaki lily ni hankali na ma tashi yayi ko wani wurin ya kaiki ya adam ya ganki,shike da wnn tashin hankalin,ke banza ce kindai san halinshi waya na kalli yadda ya nemi ya kasheni kinsan abby zaije ya fadamawa ko………





To bari in baki shawara hajia uwar daba naga kan naki yau yayi cover idan yaje ma ya fada masu yadda kika saba kekeshe kasa kice baki ba yauma haka zaki mashi ki kekeshe kasa kice nice nabaki sako ki sawoman pounded yam,idan za'a mutu ki tsaya kan hakan nikuma koda an kirani zance eh hakane,sannan kice kema a ten to ten din kuma hadu daya ganki ne kuka fito tare zaya maidoki gida……….




Lily ta kalli Sarah da kyau taga ba alamun wasa a tare da ita,kara bata courage sarah tayi har taji tashin hankalin da tashiga ya ragu sosai,Sarah ta bude ledojin dauka wnn kije ki kaima mama da hannunki kice sawo mata kikayi kin biya ten to ten karkiji tsoro haka akai kuwa lily da kanta takaima mama abincin ta fadamata taje ten to ten sawoma sarah pounded yam itama ta sawo da ita………





Godiya mama tayi sannan tace yar bautar kasa su uniform din ba'a ciresu daria tayi zan cire mama lbr na tsaya waccan yarinyar,ummmm kudai kuka sani koda ta dawo har sarah ta fara cin nata ohhh baki bari na muci tare kaiiii kedai baki koshi ceman kikayi fa an cika maki table komai kuma saida kikaci wnn dinma sai kinci?……….




Fadi barnar baki kudin mijina kice bazanci ba zama tayi tasa hannu tanaci tana zagin sarah kmr ba itace tashigo gidan nan ba hankali tashe tun tana jiran dawowar ya adam taji shiru har Abby ya dawo gogan bai dawo suna kitchen ana girikin dare taji horn daga ita har sarah dukkansu bakin window suka leka dan suga mai shigowa………..





Ilai wanda suke tsammanin kuwa shine ya shigo,suna ganin kalar shigar jikinshi suka gane daga site yake yasha hular kwanon shi da Boot a kafar shi,lily gabanta ya kara tsinkewa shikenan yaran gidansu tagani sun daga bayan motar shi anata fitowa da provision dama shike masu provision yanzu………..




Baro kitchen din sukayi su duka suka dawo parlour za'a shigo da kaya kitchen din,saida aka gama kwashe komai sannan ya nufo hanyar part dinsu,koda ya shigo kallon farko da lily ya farashi tana makale a dinning ko motsi batayi sarah ce tayi ta maza tace yaya sannu da zuwa,kayan hannunshi ta ansa yana gaba tana biye dashi har dakin shi……….



Yagane sarai me sarah ke nufi dan kar yaci uban kawarta ne yasa aka fara mashi ladabin shaggu🤣🤣kafadar ta ya dafa thank u hajia saratututun mama duk ranar da yakejin yan tsokanar shi haka yake mata tayi daria Allah ya huta gajia amin ta sakai ta fito, murmushi yayi sosai yace yaro yaro ne a haifeku gabana ni zakuyima wayau🤣………….





Lily na kitchen sarah ta shigo har gaban lily ke fadi ganin sarah waike miye haka kinwani rikice saifa yagane ki,ni wlh banga wani fushi da yayi ba har tsokanata yayi,amma kinaji na gaidashi yaki amsawa wannan ai ya saba ka gaidashi yayi shiru dallah ki kwantar da hankalin ki ke dai kiyi yadda nace kawai malama…………..





Bayan sallah magriba daga abby sai mama a parlourn shi sunacin abinci suna firar su ta tsaffin masoya ya adam yashigo cikin kananun kaya yanata zuba wani sihirtaccen kamshi,Abby ya kalleshi sai ina?badai gidan sirikai zakaje da kananun kaya ba😁kai abby ya sosa kai kawai………..




Ammm mama dama nazo ince maki zan dauki yaran can zamuje wani wuri,ina zakuje abby ya tari numfashin shi?siyayya nakeso in musu,kudin da aka biyaka ne yau duk saika karar dasu daria yayi a'a kudin nan fa abby ko shekara zaayi bazasu kare ba,zauna inason magana dakai………..





Samun waje yayi ya zauna abby ya fara cewa kaga dai yadda Allah yasa maka albarka a wannan zane zane naka companies da yawa suna aiki dakai ka girma adam kayi aure banga abinda kake needing a duniya wanda bakada shi ba,tun muna shaida juna nidakai ka fitar da mata,ammmm In Shaa Allah abby zanyi nagode toh shikenan Allah yasa albarka yadda kake farantaman nida mahaifiyar ka kaima Allah ya baka wanda zasu faranta maka kaji adam ya sunne kanshi yace Amin………….




Parlour mama ya dawo fuskar nan ba annuri ko daya a samanta kowa ta dafe wayar ta tana chat sukaji shigowar shi,lily da itace karshen gaidashi yau itace farkon cewa ina wuni lafiya kawai yace mata………



10mnt ku duka ku sameni a mota ya juya ya fice ko ansar su baiji ba,lily ta kwalalon idon nan sarah ina zai kaimu kin tambayi kaza hanyar rafi? Tare dai duk aka bamu command din🤣🤣kila filin kaci uwaka zaaje ku goge raini ita kanta lily saida tayi dariya dakinsu suka shiga dan su shirya a gaggauce………….




Tunda suka fito idonshi kan lily dayaga ta kara mashi wani irin haske ga wani gyale duk sunsha kmr zasuje biki,itako tun a hanya take ma sarah magiyar tashiga gaba dan Allah,ko sukazo kawai sarah ta rigata bude bayan motar ta shige🤣🤣kasa motsi tayi takai minti ukku tsaye ta budo motar wani kanshin ta ya daki hancinsa………




Ke gaban lily yace rasss,ummm ku koma kusa hijab gasar kyau zaku fita kome ku baceman daga gani kafin in tattakaku anan🙄🙄



PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹...SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……