SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)
Page 7
by @smauta
Kamar zata tashi sama haka ta juya ta wuce ko motar bata rufe mashi ba,ta riga sarah isowa dakinsu gaban gado ta tsugunna ta fashe da wani irin kuka mai kara har tana bubbuga kafar ta kasa,lily you have to strong karki bari yaga gazawar ki,duk abinda zaiyi ya bata maki rai shi zaiyi ki gode Allah ma da bai fadama abby kedai kinsanshi sarai………….
Ansa hijab din kisa mutafi,ta fuskar nan tata ta datayi jawur ta dago ta kalli sarah tace in tafi ina? billahillazim ko zai kasheni yau saidai a fitar da gawata a gidan amma idan nabishi mun fita kece ba sunana lily ba kuma ki koma ki gayamashi ban fitowa muddan saina saka hijab bazanje ba………
Lily ya adam kikema wnn rashin kunyar abun naki fa ya soma yawa ya adam matsayin uba yake garemu fa,kedai yake matsayin uba amma niban taba mashi kallon uba ba wlh a yayana yake kuma yayan wanda na tsana tsana ta ƙarshe a duniyar nan to shine,ba ragi tsakanina da duk wanda zai nuna yana hassada da farin cikina na rasa uwata da ubana ma waye zan rasa a duniya dazai tadaman hankali wallahi babu shi………..
Kuma bari kiji in gayamaki muddin mukaci gaba da wannan zaman a gidan nan wallahi za'a wayi gari babu ni cikin gidan nan ta mike tsaye saratu kalleni da kyau tsaye nake da kyau zaune da kyau wallahi zuciya ta ta fara rayaman in fita inyi zaman kaina in samu yanci na,haba nagaji nagaji nagaji kullum da bala'in dazan tashi dashi sbd ya adam bai taba kauda kanshi gareni…………
Na rantse da Allah gidan nan zan bari zaman kaina zan fara abinda yake gudu inyi kenan to wallahi zan fita ina nemi mazan dakaina koban nemesu ba kyauna zai kawomansu,kome na kawo sai anyi kutunkutun ya hana aure na kawo wanda nakeso an hana sai nan da 6 month ni bazaa tsaya a saurari uzuri na asan me nakeso asan meyasa nakeso inyi aure ba nifa macece kamar kowa jini na yawo a jikina ina iya bakin kokarina wurin killace kaina amma ba'a gani……………
To zaman gidan nan ya kareman daga indai ina numfashi lokacin daukar ma kaina yanci yayi koda za'a kasheni wlh,sarah sumar tsaye tayi tana kallon ikon Allah gaban mirror dinsu taja stool ta hau ta fara sauko akwatina daga sama sarah ce ke kuka wiwi tana rike lily na fisge hannun ta,kayanta kawai take kwasa tana zubawa yanzu tafiya zakiyi kibarni eh sarah zan tafi dan in kwatar ma kaina yanci,kwatar yancin shine zaki tafi neman maza………
Jikinki ko nawa ke za'a zaga koni karki kara sa hannunki jikina ko in ratsa maki mari🙄duk wannan drama da akeyi adam na bakin kofar su yanajinta sumar tsaye yayi lilyn ke wnn kalaman😂😂😂ta hada komai nata tasss ta fara jan akwatin ta sarah na biye da ita tana bata hakuri karta tafi………..
Lily kiyiman rai karki tafi idan kika tafi ina zan saka kaina ke kadai gareni yar uwa a duniyar nan wani kallon ukku saura kwata taimata,nice zance haka amma ga dan uwanki nan kinada shi ke baki laifi wurin shi nike laifi ta bude kofar sukai kicibus idanta cikin nashi ba alamar tsoro ko shakka tareda lily a lokacin,Sarah ce ta biyota lily karki bata idasa ba adam yace barta ta tafi hanya ya bata tawani figi akwatin ta tayo kasa………….
Sarah kuwa zubewa tayi kasa tana kuka adam ne da kanshi yazo ya tada sarah ya kaita kan gado ruwa ya bata daya ganin a bedside dinsu, cigaba da lallashin sarah yayi yana bata hakuri ya adam dan Allah kace ta dawo gida karta tafi,zata dawo sarah karya take ba inda zataje ki kwanta karki sake ki fito ina zuwa…………
Koda ya fito tsakar gidan mai gadi ya hanga yana maida kofa ya rufe alamun ta fita motar shi kawai ya shiga ya bata wuta ya saki horn da sauri mai gadin ya bude mashi full light yayi motar tashi sannan ya cillo kanta waje😂😂😂😂kai sai damu wlh😂😂😂😂😂😂😂😂😂…………….
Tafe take tana sauri ga dare dan wurin 8:45 lokacin ga akwatin tana ja ko ba'a gayamata tasan waye tunda taji karar bude gate full light dayayi kuma yake hasketa yasa bata ganin gabanta ga kuka tsayawa tayi cakkkkk ita batai gaba ba ita batai baya ba shikuma bai rage hasken motar ba……………
Yakai minti ashirin a haka saida ya tabbatar hasken motar yagama da idonta sannan yazo daf da ita ya sauke glass keeeeee,karka karacemun ke idan ba zaka kirani da lily ta ba ka kirani da fatima sunana na yanka duk wnn rashin kunyar idonta na rufe kuma tana zubar da hawaye………..
A karo na farko da tunda yake a rayuwarshi ya kira sunanta na yanka gatsal yace FATIMA ita kanta saida taji gabanta ya fadi tashiga bude idonta amma inaaa wasu taurari take gani suna mata yawo ga tsananin bacin rai,ya jefo mata tambaya ina zaki je?ba wai tace inda ake kaunata,ina kenan? gembuuuuu………….
A daren nan zaki je gembu ko yawon neman mazan zaki fita,a dake itama lily ta bashi ansa duk wanda kasuwar shi ta budeman dashi zan fara kawai taja akwatinta zatayi gaba amma bata gani sosai sai gata ƙasa rikicaaaa wani murmushi da baisan lokacin da yayi ba yazo mashi sai lokacin ya bude motar ya fito akwatin nata ya kama itama ta kama ta rike wallahi ba zan koma gidan nan ba……….
Yace kashhhhh basai kin rantse harta bishiyoyin gidan suma sun gaji dake da halinki ba gidan zan maidaki ba inda kike buƙatar zuwan zan kaiki ya fige akwatin yasa maka mata a boot har lokacin tana nan kasa ya dawo bai tsaya mata magana ba kawai taji ya dauketa cakkkkk ya bude gaban motar ya sakata sumar zaune tayi tun tana yarinya rabon da ai mata irin wnn ɗaukar kenan sai yau😂😂😂🙄🙄🙄🙄…………….
Kamar jira take tashiga rera mashi kuka cikin motar duk digon kukan ta har cikin ranshi yakejin shi badan yaso ba kuma baiji dadin da lily take ganin zaman gidansu da yadda yake da ido akanta hakan takurawa ce,kawai ya lura tanada rawar kai dole sai ansa ido sosai a kanta hakanan kuma yakejin bai yarda da saurayin nan nata ba,yana fara tunanin saurayin ta yaji ranshi yayi wani irin baci lokaci guda taji ya kara speed din motar………….
Wayyo Allah karka kashemu 😂💔 wallahi ban shirya mutuwa yanzu ba saina haihu ya adam ka tsaya in sauka ina baijinta gudu yake shararawa a titinan GRA,yakai minti ashirin yana gudun saida rai ya farajin zuciyar namashi sauki kan zaɓaɓɓen kishin ta daya taso mashi,wuri ya samu yayi parking ya kifa kanshi da steering mota,tun yana tari a hankali har ya fara cin karfin shi yana dafe kirjin shi…………….
Duk yadda ranta yake ɓace da yayan nata data lura da halin dayake ciki ta gigice gasu kan titi ya adam ta kira sunanshi yafi so nawa amma ko gezau hannunta tasa ta dago kanshi ya taho luuuu kamar zai fado mata wani ihu ta kurma a motar nashiga ukk dan Allah karka mutu dan Allah ka tashi……………
Ruwan dake gefen ta bude marfin ta jona masa a baki ba bata lokaci yacigaba da ansar ruwan nan makwal makwal saida ya shanyeshi tassss ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya,kanshi a langwabe idonshi ma a rufe yace lily na'am so kike ki kashe ni??????????????
PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏..SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……