SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)

Page 8

by @smauta






Dan Allah kayi hakuri wallahi ko ƙuda ba zan iya kashewa balle mutum hannun shi ya dora a kirjin shi yagane sarai jikinta yayi sanyi yace gashi zaki kasheni lily saka ido da nakeyi maki yasa kike ganin kamar takura maki nakeyi………



Kina tunanin yawon duniyar da kika fito yanzu ribace zaki samu mace lokaci gareta iskanci ba ado bane ga mace, yarinya karama kamarki kike ikirarin zaki fara yawon dunia idan kikayi a bakin yan Amin ya kenan?munaji muna kallo zamu ganki da wancan namiji gobe mu ganki da wancan??………





Da sun gama yayinki su watsar dake?kyau din da kuke takama dashi ya ƙare tun da akayi dunia ake karuwai kuma har dunia ta tashi bazaa daina ba,kuma kullum cikin haihuwar kyakkyawan mata ake ba kece farko a kyau ba kuma ba kece ƙarshe ba amma kisani shi abinda zaki fita ki fara akwai lokacin da zaki kai babu mai kallon ki balle yai maki kallon sha'awa…………




Akwai lokacin da zaki kai wanda suke rubibinki ko nemansu kikai bazasu kulaki ba lily ta kasa dake suke nema lokacin zakice zaki tuba ki komama Allah,bayan tarin zunubi da kuma dauka idan ta maki kyau ki ƙare ba ciwo idan tazo maki abaibai ki dauko ciwo lokacin zaki nufo mu mu yan uwanki………





Rayuwa a kullum juyawa take karki sake ki kara sama ranki iskanci ado ne ba ado bane lalata ce lalata kuma mafi muni mafi kyama ga al'umma da wurin Allah kusan me kikeyi,ki dinga tsarkake bakinki kafin kiyi wata magana saboda kina iyama kanki baki da kanki Allah kuma ya jarabce ki, yanzu da kika kwaso kaya kika tsallake yar uwar ki kin kyauta kemai taurin kai sbd nace ku koma ku sako hijabi?





In'ina ta fara yace shut up,me kike nufi ke baki isa ai maki fada ba?dududu nawa kike ganin ke kin girmi fada saboda kin girma kina da saurayi yana gayamaki abinda kanki bai kamata ya daukeshi ba shiyasa kikeji daidai kike da kowa kikejin ke kin isa aure kin san matsalolin dake cikin aure ko dadin shi kawai kikeji a baki,kije ki samu orientation kan aure kafin kisama kanki son aure………..







Duk wannan maganar da yake lily kuka kawai take tana nadama kan abinda tayi ta rasa ina zatasa kanta ita tunda ta girma basu taba magana ta hankali kamar yanzu ba itada ya adam shiyasa kullum sarah tace saukin hali gareshi amma ita bata ganewa,shurun da taji yayi ne yasa ta dago kanta suka hada ido da sauri ta sinnar da kanta shiko ya kafeta da ido kallonta kawai yake yadda fuskar ta tayi jawur kyau ma ta kara mashi…………






Yanzu daganan ina zaki je? Ya jefo mata tambayar ummmm ummmm kinji sarai kinji me nace daganan ina zakije?lily tace gida zan koma wane gidan?
Tayi shiru,kinsan bansan ina magana ana kyaleni ko? gidanmu inane gidanku?gidan abby bazaki koma gidan nan ba yadda kika fito bada izinin su ba kuma bazaki koma ba muje in kaiki tasha ki tafi gembun, tsoro ne ya kamata yana niyyar tada mota ta rike mashi hannu gammmm ta saki wani marayan kuma dayakejin shi har kasan ranshi……………..





Menene dan Allah ka maidani gida idan ka kaini tasha yanzu bansan yazanyi ba,a'a kinsani wanda ya fito daga gida da option biyu ko yawon dunia ko tafiya gembu yanzu na rage maki hanya kice bakisan yadda zakiyi ba🙄 gembu kam sai kinje ta da kafarki sakar mun hannu kara rike hannun tayi tana rera kuka,magana nake dake ko?dan Allah ya adam kayi hakuri nifa bakiyiman komai ba……….





Hanya zan sakaki ta zuwa gembu idan kinje ki gaisheman da aunty yafindo duk lokacin da zaman can din kuma ya isheki just give me a call zanzo in dawo dake amma yanzu kam gidan abby kin baro shi,kara rushewa tayi da kuka yace daina kuka ki gidan mijin naki zan kaiki?kunya ta rufe ta kamar kasa ta bude ta nitse ba mgn nake dake ba?to ya adam ai ba'a daura auren ba,eh ba'a daura ba amma kike binshi yawon restaurant mayya😂😂😂😂…………..





Shiru tayi ba dake nake ba wane abinci ne a duniya bakici shi amma saboda maita kika bishi restaurant har ana maki take out,ya adam wlh sarah ta aikeni sai kuma tayi shuru uhumm inajin ki samun kanta tayi da kasa yimashi karya ta gayamashi gaskiya yadda abun ya faru,ya numfasa yace kirashi kice ya baki address na gidanshi za'a kawoki daki tafi yawon dunia gyara musan gidanshi kike tunda kin fasa zuwa gembun………..





Dan Allah ka rufaman asiri,asirinki a rufe yake shima wnn option din kinki shi oya let's go muje in kaiki Tahir ki kwana sai kiji yadda yan bariki keji kema magiya take amma bai kara ko kallonta ba taga dagaske fa Tahir din suke dumfara kuka take kamar ranta zai cire a bakin gate din Tahir ya kalle ta tsafffff,idan nakarajin kince uffan a motar nan ranki zaiyi mummunan ɓaci…………….






Yana gaba tana biye dashi reception sukaje yayi lodging VIP itadai tana tsaye tsoron Allah na baibaye da ita kawai😂😂💔 yau fa ta debo ruwan dafa kanta keys din dakin ya mika mata hannunta na kyarma ta ansa ya galla mata harara,yana gaba tana biye dashi har kofar dakin dakin, bismillah ya bata hanya ta bude dakin akwai parlour sai bedroom guda daya a ciki da toilet…………..





Kofar ya maido ya rufe ya kalleta tsaf yafa gane gaba daya a rikice tace a ranshi yace ga tsoro ga iya shege kenan😂😂shiga kiga ko ina yayi maki ko a canza wani wurin?zatayi magana yace wuce shiga tayi dakin komai neat ta fito,tana dai tsaye ba baki sai ido, yayi da kai tayi mashi alamu shiko wata dariya ke cinshi ya dake………………




PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏...SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……