SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)

Page 9

by @smauta





Suna nan zaune a parlourn yanata duba aikinshi a kan waya ita kuma gaba daya rayuwar ta na wurin sarah tana so ta kirata tana tsoron bala'in shi,sai wurin goma na dare yace mata zakici abinci?kamar ya tona ranta wlh dama wata wahalallar yunwa takeji,ummmm bai kara cemata komai ba ya mike zumbur ita ta biyo bayanshi tinkis tinkis suka nufi calido……………..





Yana kallonta ta gefen idon shi yadda take satar kallon shi suna shiga suka samu wurin zama balasti kunga yadda sukayi wani mugun match duk wanda ya wuce saiya kara kallon su wanda bai sansu ba mata da miji kawai zaka kira su,sai wani kalle kalle take kamar mai jin tsoron wurin………




Ke meye haka villager seat properly baki taɓa zuwa nan din bane gyada kai tayi yace karya kike nan ma nasan kunzo ya galla mata harara,kan kace kwabo an cika masu table da kayan ciye ciye kota kanta baibi ba ya fara saving kanshi a hankali take komai dan gaba ɗaya ta tsargu itadai burinta daya ya maidata gida koda za'a dake ta na ta yarda………



Sun dauki lokaci anan sannan suka taso koda taga suna nufar motar shi wani dadi ne ya ƙumeta amma kashhhh akwatin ta ya fiddo mata,ba bakin magana yana gaba tana binshi a baya har dakin a parlourn ya ajiye mata shi ya zauna itama ta kama gefe daya ta zauna tana zaman jiran tsammani…………





Jim jim jim jim alamun yana kiran waya kuma a speaker bata gama tunanin wa yake kira ba saida taji muryar babani tana cewa Assalamu alaikum, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un duk inda hankalin lily yake so dubu to ya tashi tasan wacece babani sarai,satar kallon ta yayi yaga yadda take gwalo ido kamar taga abin tsoro…………..




Lafiya lau suka gama gaisuwar su sannan yace babani na'am adamu baki fara bacci ba ko,idona biyu adamu ummm dama ƙara na kawo maki to adamu inajin ka duk da baka tabaman hakan ba amma yanzu dakayi hakan nasan abun ne yaci tura,ya daga ido ya kalli lily dake hawaye tana hada hannayen ta alamun roko karya fada mata………….





Kayi shiru ina jinka me akai maka adamu bakomai dama lily ce sai yayi shuru me tayi kuma wannan ja'irar diya badai ita ka kawo karar ba eh itace,baka bata dan bara'uban kashi ba Adamu fin karfin ka tayi a'a babani tadaina jin maganar kowa ne naga kuma bayayi amma idan kice kila taji maganar taki shiyasa nace maki na kawo maki kara amma kuma fa bance kiyi mata danyen hukuncin nan naki ba,muddin kikaiman haka zamu bata fada dai nakeso kima ta………





Tsaf ya zayyana mata komi abinda kawai bai gayamata ba kamata dayayi taje restaurant,babani fada take kamar zata ari baki ina take yal kundun ubar dama bahillace da shegiyar taurin kai,yawon duniya tace zataje to Allah bata saa ai gata ga duniyar nan kaki mata dan bara'uban bugu kuma yanzu zan kira yar uwarta yafindo in gayamata ai tasanta sarai dama kabar ta taje gembu yafindo saita kusa kasheta ita ai bata daukar wannan iskancin nata saimu nan…………….




Kefe babani kinji matsalar ki nibance ki kira kowa ba banasan da ita ba naki kiranta nasan hukuncin da zatai mata bamai sauki bane shiyasa na kiraki amma kina kiran aunty yafindo gaskia mun bata babani,to naji kaidai wannan son ƙanne naka ba'a ganeshi yanzu ina take fatimar yal buhun uba?…………..




Shi kanshi saida ya murmusa wai yal buhun uba,samun kanshi yayi dayi mata karya kawai baisan taya ma bakinshi ya shirgo karyar nan ba,tana gidan abokina nakaita nace su rikeman ita ta kwana gobe da safe zanje in dauke ta sai ta tafi gembun,ba gidan ubanda zataje kace tasa kafa ta fito baban naku ma baisani ba,ya dago ya kalli lily da tayi sumar zaune jin ya gindira karya wai tana gidan abokinshi bayan hotel ya kawota………….






Eh babani ba wanda yasan ta fito ina saratu tana gida na baro kayiman arziki adamu ka daukoman yarinyar nan ka kawoman ita yanzu,ya kalleta ta kara marairaice mashi tana kuka yasan yadda babani ta dau zafin nan indai yakaita yanzu bugu ne harna banza saitaci shi,yace ban iya driving kirjina ke zafi ulcer ta tasoman saidai gobe da safen in kawota………….




Ai wnn shirmen banza ne bari in kira baban naku gwara daka gayaman da wuri adamu wannan yarinya karta dauko mana magana muna zaman lafiya yarinya marainiya amma tana nema ta fitinemu to bari in kira baban naku yaimata aure kawai kowa ya huta,kishingide ya adam yake saida ya tashi zaune jin babani ta ambaci aure,Allahumma ajirni fi musibati ya maimaita a ranshi kit ya datse wayar……………….




Da sauri lily tazo gaban shi ta tsugunna dan Allah ka dubi girman Allah karka kaini gidan babani wallahi kasheni zatayi,eh lily gwara ta kashekin mu huta da ɗaukar magana,gidan babani zaki koma da zama gidanmu dadi ne yai maki yawa kike ganin tsana ce zaki koma inda zaki gogu dan dole ki russuna ma na gaba dake dan dole kinsan babani bata wasa da yaro tashi daga gabana ki dauki kayanki ki shige kafin in tashi nima in tattakaki…………





Kwance take kan gado ta saka wannan ta warware wancan kuka zatayi me zatayi oho daga cikin dakin tanajin muryar shi sama sama takuma gane sarai da abby ne yake waya innalillahi ita yanzu da wane ido zata kalli abby ko mama uwa uba Sarah, wayar ta ta jawo ta hau kiran sarah,na kwance taga mai kiran itama tai zuciya bazata dauka ba,tagaji da iskancin lily da kullum take ganin gidansu ake musguna mata…………..



Wani sabon kuka ta kece dashi tagane sarah ma fushi take bata taba kiranta bata ɗauka ba sai yau,ta juya nan ta juya nan ta rasa meke mata dadi a duniya ina zatasa kanta taji dadi ita Fatima,bacci ya fara daukar adam ya tashi ya kashe wutar parlourn da komai ya zare key din kofar ya fita yana mai rufota ta baya yasan taurin kanta tana iya tashi ta fice ba tareda sanin shi ba……..





Wani dakin ya kara kamawa yaje boutique din wurin ya siya kayan bacci da wanda zai saka gobe duk abun bukata sannan ya koma dakin dayake facing na lilyn,kayan jikinshi ya cire nan na tsaya nayi kallon hallita haka ya adam yake kakkarfan kato in garman namiji da kowace mace ke burin samu a mallakin mijinta…………………


WASHE GARI DA SAFE 




PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹..SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……