SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)

Page 10

by @smauta


WASHE GARI DA SAFE 


Kamar yadda babani ta umarta haka akai,Abby mama Sarah duk sun hallara gidan babani bacci mai nauyine ya dauki adam bai tashi da wuri ba,sai wuraren goma ya tashi da sauri ya shiga yai wanka ya fito ya shirya tsaf a gefen lily ma tayi wanka tsaf ta zauna parlour fuskar nan tata luhu luhu alamun ana buɗe kofar parlour taji yasa ta dago kanta idonta cikin na ya adam ta sunnar dakai ƙasa ina kwana lafiya,ina kayanki?suna ciki dauko su tafiya tayi ta dauko akwatin ta let's go…………






Yana gaba tana biye dashi har reception yaje yayi check out sannan suka fito a wani mini Cafe ya tsaya sandwich da hot coffee ya siya mata ya dawo take ansa tayi muryar ta kasa kasa kamr ba lily ba tace thank you, coffee ta fara sha taji wani zaɓaɓɓen dadi tana sha tana cin sandwich saida cikinta ya fara dauka sannan ta gane wace hanyar ce suke bi,barin komai tayi tafarama ya adam magiyar karya kaita gidan babani…………….




Bai saurare ta tafiyar shi kawai yakeyi,har ya iso gidan babani mai gadi ya bude masu gate suka shigo ya kashe mota amma kimmm taki fita daga motar muje sai lokacin ta samu courage bata ida tsinkewa ba saida taga motar Abba a parking space shikenan yau kashin ta ya bushe………..




Yana gaba tana biye dashi kamar zata shige bayan shi duk an hallara parlour gaban babani yayima kanshi masauki ina kwana babani Adamu lafiya lau,duk ya gaishe da iyayen nashi suma suka ansa sai lokacin lily ta ida isowa parlourn jikinta na kyarma tace babani ina kwana ba yabo ba fallasa ta amsa Abby mama ina kwana,mama kadai ta ansa gaisuwar ta abby kuwa ranshi ya baci da ita matuka…………




Adam bude mana da addu'a,abby ne ya fara magana lily na'am abby dago kanki ki kalleni ta kasa dagowa ta kalleshi babani ta cafe dan ubanki ba magana ake maki ba,mu zaki jawoma magana a kaf dangin mu ba wanda yake fetsarar da kikeyi dan kinga ansa maki ido,to bari kiji in gayamaki kin baro gidansu Adamu kenan har abada zaki dawo nan wurina da zama inga karyar iskanci………..





Inga dan iskan da ke hure maki kunne munafukar banza,ke adamu bai isa yai maki fada ba,waiba magana nake maki ba?ba abinda lily keyi sai kuka sarah na tayata shikam Abba ya cika yacika yai fammmm aljihu yasa ya hannu ya fiddo kudi ya watso mata maza dauka ki tafi gembu kar in kara ganin ki gaban abby tazo kuka take tana mashi magiya………..



Kina tunanin duk abinda kikeyi bansani ba tsiwa da rashin kunyar ki duk ina kauda kai amma yau ke ke buɗe baki kice zakiyi zaman kanki kisa kafa kibar gida ba tareda izinina ba?idan da adam bai biyoki ba da kina tunanin mezai faru wasa da dariyar da nake maki ne yasa kikejin ke kin isa kinkai kin kawo lily????




Abby kaiman rai dan Allah wlh kuskure ne da bacin rai caraf babani tace ke har kinada ran wanda zai ɓaci kawai daga koma ki sako hijabi har yazama abun takura idan bakisa hijab ba haka zaki fita da wannan shaggun nonuwan naki kina girgiza ma maza su,a'a babani dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan kara ba a'a bari in kira yar uwarki kila ita kinji maganar ta……….




Sautin kukanta ta kara tasan wacece yafindo tsaf gobe ta hayo mota tazo kano tai mata shegen duka ta koma dan Allah karki kira ta wallahi ba zan sake ba nayi alkawarin idan na kara kome kikamun ninaja,kima kara gidan jin daɗin naki zaman ya kare a can nan za'a barki shara da mopping sun isheki wallahi zakisan dani kikeyi ubanki zanci laada waje………




Lily albasa batai halin ruwa ba Isyaku ba haka yake ba uwa uba mamanki ko na tabbatar hakurinta zai kaita aljanna amma ke kinaso ki fitini kowa to bandani babani muddin ina numfashi sai na rissina ki dan dole ma bada arziki ba,kuma wane dan iska ne yake hure maki kunne………..




Sai lokacin adam ya dawo hayyacin shi ba magana nake dake ba babani bakowa Alhaji najib ne waye ya haka babani tawani gatsina baki,ta kalli Abby kasanshi eh babani shine wanda mukai maganar nan dake ohhh to to to to nagane wanda yazo nan ya kawoman kayan arzikin nan eh shi……….




To kanajina ko ka kirashi kace idan dagaske yakeson yarinyar nan ya turo mana magabatan shi dan bazamu bari yarinya ta fetsare gaban idon mu ba komi kenan kuma zan kira yafindo in ƙara tuntubar ta akai dukkan abinda tace Allah yasa albarka,ka binciko kowaye ko eh babani dukkan nayi alhamdulillah baida wata matsala to Ma Shaa Allah…………..





Kawai dai naso tagama bautar kasar sannan tayi auren a'a ayi auren tagama a gidanshi,ke kuma ta juyo kan sarah me kike jira mama tace result take jira ya fito sai tashiga itama bautar kasar to Allah sa albarka yaimaki zabi nagari karki kuskura ki biye halin wannan ja'irar kinaji haka dai kowa yaima lily fata fata hatta mama dai saida ta gurje ta tasss,adam ko ya kasa ko motsin kirki jin ana maganar auren lily………….




Sai yanzu yake yarda da zuciyar shi dakuma maganar abokan shi akan lily kenan son lily yake,yasan idan za'a mutu kuwa lily bazata so shi ba koda shine autan maza,a ranshi shima yace ina koda sonta zaiyi ajalina nima bazan taba furta inasonki ba lily tsumul ya mike ko sallama bai musu ba ya fice ba inda ya zarce sai gida ya rasa me mashi dadi duniya……………….


KURMAN SO BALA'I NE YA ADAM😭😭😭😭😭



PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏......SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……