HASASHEN SOYAYYA

Hs 35

by @legendspen

_Page 35_

Sai da Bhatool ta kwashe sama da awanni uku sanan ta tashi, Yaya Karima ta gani a ɗakin ita kaɗai a hankali ta kira sunanta. "Yaya." Da sauri Yaya Karima ta ta so zuwa bakin gadon, sanan ta ce. "Bhatool, kin farka?." 

"Yaya ina Senate?." Ta tambaya. "Ya fita yanzu."

"Waye ya bugeni?." Bhatool ta sake tambaya. "Wani ne kuma ya tafi, ya jikin naki?." 

"Kai ne kawai ke ciwo, zan shiga banɗaki." Kama ta Yaya Karima ta yi ta shiga da ita banɗakin, suma cikin banɗakin Senate ya shigo. "Ta tashi ne?." Ya tambaya. "Eyh ta ta shi." Yaya Karima ta ba shi amsa bayan sun fito. "Bhatool ya jikin naki?." Kau da kai ta yi ba ta bashi amsa ba, kamar ba shine abinda ta fara tambaya bayan ta tashi ba. "Ki yi hakuri kin ji." Ya faɗa kamar zai yi kuka. "Bazan ƙara ba." Ya sake faɗa, sai a lokacin ta ce. "Da sauƙi, mu tafi gida." 

"Tom Bhatool, amma yanxu Mom ta ce wai mu huce gidanta mu kwana biyu." Ya faɗa. "Eyh, kam hakan zaifi." In ji Yaya Karima, dai-dai lokacin Abdul ya shigo, bayansa kuma gayen da ya buge ta ne; Ahamd ya shigo. Lokaci ɗaya Senate ya haɗe rai, kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa. "Bhatool kin farka?." Abdul ya tambaya. "Eyh Abdul na farka, waye wannan?." Ta faɗa tana kallon Ahamd dake bayansa. "Ina ruwanki?." Senate ya katse ta, turu baki ta yi gaba kamar za ta yi kuka. "Shine wanda ta bugeki." Abdul ya faɗa, dai-dai lokacin shi kuma ya ce. "sannu ya jikin?." 

"Idan zaka dinga fita da mota kana kula Malam, kawai ka bugeni." Abinda Bhatool ta faɗa kenan, murmushi ya yi sanan ya ce. "Tom in sha Allah na gode, ya jikin naki?." 

"Malam baka da damuwa da jikinta, as you see gashinan ta warke so leave us please." Senate ya faɗa. "A'ah Senate, mene haka kuma?." Yaya Karima ta faɗa tana mamakin Senate, mene na fushi har haka. "Komai fa da ya faru ba ni da laifi, ubangiji ne ya tsara hakan tun kafin yanzu, dan haka babu amfanin ka dinga jin haushi na."  Ahamd ya faɗa.

Ta shi Senate ya yi ya fice gaba ɗaya, Anas yabi bayanshi yana mamakin wanan baƙin kishi irin na Senate. "Senate wai mene haka kake yi?." Anas ya faɗa mai bayan sun fito waje. "Anas baza ka gane ba, bana son ganinsa kwata kwata a kusa da ita." 

"To ai ba kusa da ita ya ke ba." Anas ya ba shi amsa. "Ya zo inda muke ma bana so wallahi, nifa Abdul ɗin ma yanzu bana son yadda yake shige mata wallahi." 

"To mahaukaci, ƙaninta ne dai uwa ɗaya uba ɗaya, kuma a yadda kake gani Bhatool tafi son Abdul akan kowa cikin gidansu." 

"Amma wanan faɗan da suke fa?." Senate ya tambaya. "To ai faɗan shine nuna soyayyar, akan Abdul; Bhatool za ta iya haƙura da rayuwa da kai." 

"Bakada hankali kai fa Anas." Senate ya faɗa. "Ka ga koma mene yanzu kawai mu shiga." Kama hannun sa Anas ya yi suka shiga ciki, lokacin kuma Ahmad ya juyo zai fita. "Allah Ya bata lafiya." Ahamd ɗin ya faɗawa Senate. "Amin." Ya amasa ba tare da ya kalleshi ba, Senate ya shiga Ahmad ya fita. 

"Mene wanan kuma kike ci?." Senate ya tambayi Bhatool. "Apple ne." 

"Wane ya baki?." 

"Ahamd ne ya kawo." 

"Waye kuma Ahamd?."

"Wai wanan tambayar kuma na lafiya ne." Bhatool ta faɗa, Yaya Karima dai miƙewa ta yi ta basu waje, sai da ya jira ta fita sanan ya ce. "Waye Ahamd?." Kuka ta fashe da shi, tana faɗin. "Ni gaba ɗaya na yi hasashen soyayya mai kyau a gidanka, amma ban samu ba sai faɗa."  Ta shi ya yi ya dawo kusa da ita sanan ya ce. "Bhatool wane faɗa na yi miki?." 

"Gashinan, ka ce wannan ka ce wannan." 

"Bhatool ni fa mijinki ne, ina da haƙƙin tambayar ki komai." 

"To shi wannan ɗin da ka tambaya, wanda fa ya buge ni ne." 

"To Bhatool daga buge ki kuma sai ya hau kawo miki Apple kina ci." 

"Sha'awa ya bani fa." Ta faɗa. "Ba sai kice ni na siyo ba."

"Tun da ga shi a kusa kuma mene na sai an wahalal da kai, kawai yanzu kaje wajen likitan assalamemu mu tafi gida, banason warin asibitin." 

"Tom." Ya faɗa tare da tashi. 


Sai wajen ƙarfe 12:30 na dare suka isa gidan Mom, kai tsaye sashen Senate suka nufa dan acan zasu zauna. Sai washe gari suka fito ɓangarensu Mom, kallo ɗaya Dad ya yi wa Bhatool ya gano sahibarsa a cikin ƙawayar idonta, da mamaki ya kalli Mom sanan ya ce. "Yaushe suka zo kuma?." 

"Nan suka kwana, Bhatool ɗin ce ba lafiya." 

"Ya salam! Me ke damunta." Ba ta sami zarafin bashi amsa ba su ka ƙaraso wajen. "Ina kwana Dad." Bhatooɗ ta faɗa. "Ina kwana Mom." Ta faɗa duka a tare. "Lafiya ƙalau Bhatool, ya jikin?." Mom ta faɗa, Dad kuma ya ce. "Daughter me ke damunki?." 

"Zazzaɓi." Senate ya faɗa. "Kunga likita ko?." Ya tamabaya. "Eyh, daga asibitin mu ka yo nan." 

"Okay Allah ya ƙara lafiya." 

"Amin Dad."

"Zauna mana Bhatool." Mom ta faɗa tana nuna mata kujerar kusa da ita, zama Bhatool ta yi shi kuma ya tsaya a tsaye. "Kai kuma ba zaka zauna ba ne?." Mom ta tambaya. "Na ga ita kawai kike so." 

"Kai dalla ka zauna, yanzu ka girma." Mom ta faɗa, shi dai Dad bai ce komai ba, sai can ya ce. "Bhatool ya mutanen gidan naku?." 

"Lafiya ƙalau Dad." Ta faɗa kan ta a ƙasa. "Ma sha Allah." Daga haka suka fara cin abincin, sai bayan sun gama ne Bhatool ta miƙe za ta tashi Dad ya ce. "Ki zauna mana mu yi hira." Dawowa ta yi ta zauna. "Ba fa a hira sa surikai." Mom ta faɗa tana dariya. "To aini bana surukunta ka da ita, 'ya nake da ita." Ya faɗa yana dariya, sai kuma ya ce da Bhatool. "Mahaifinku ya yi shekara nawa da rasuwa?." Daman abinda yake so ya tambaya tun-tuni kenan yake wanan kwana-kwanar. "Tun ban kai shekara biyar ba, yanzu kuma shekarata ashirin da ɗaya." 

"Ya kai shekaru sha-shida kenan?. Ya faɗa yana mamakin yadda akayi wanan tsohon lokacin Habiba ba ta nemeshi ba. "Eyh, Dad." Ta faɗa. "Allah ya jiƙansa da rahama." 

"Amin Ya Allah." Suka amsa baki ɗayansu, daga haka ya dinga jan ta da hira sama-sama wanda duk neman bayanai ne a kan Umma. 

Haka zaman Bhatool da Senate ya fara tafiya gidan Mom, komai yadda ya kamata. Kulawa da Soyayya tana samu a wajen Senate kamar yadda ya fara mata a farko, babu wata matsala ko wata damuwa har ta fara mantawa da wani abu ya taɓa faruwa tsakaninsu na saɓani, Amrah ta kirata a waya ta faɗa mata ba ta da lafiya tana gidansu Senate.

thanks for the comments, it mean alot