MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 15

by @maimunabala209

MATAR GIDA 015



SHUUKRAN/022



P15




Daga haka Ammi ta kashe wayarta,a hankali Ɗalha ya zare wayar daga kunnesa jiki babu kwari ya ajiye wayar kan tebir dake gabansa Salame ce kaɗai hope ɗinsa gashi Ammi ta ce ita kadai ce a gidan bayan wasu ƴan mintina Ɗalha ya tashi ya fita daga office ɗinsa bai tsaya ko ina ba sai office ɗin Muhsin bayan sun gama gaisawa ne Ɗalha ya cewa Muhsin ya yi masa rakiya gidan rediyo zai bada cigiyar Amirah,wani irin kallon rainin wayo Muhsin ke masa kafin daga bisani ya fashe da dariya sai da ya yi me isarsa kafin ya ce ''abokina abin ya kai ga haka'' a takaice Ɗalha ya ce ''to ya zan yi kafa san halin Ammi sarai,ka tashi kawai mu tafi ƙila in taji sanarwa a gidan rediyo da talabijan ta dawo'' fuskar Muhsin dauke da murmushi ya ce ''lallai da sauran ka,Mallam ka dage da addu'a kawai Allah ya daura ka kanta ya huci zuciyarta kawai ta dawo ko dan yaranta'' Ɗalha ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya kafin ya ce ''haka nake fata'' a hanyar su ta dawowa daga gidan rediyo da talabijan ne kiran Unaisa ya shiga wayar Ɗalha a karo na babu adadi Muhsin dake zaune kujerar gefen driver ya mayar da dubansa ga Ɗalha ya ce ''Mallam ka amsa kiranta mana tun ɗazu fa take ta faman kira'' Ɗalha ya yi shiru ya cigaba da tuƙin da yake Muhsin ya gyara zama tare da mayar da hankalin sa kan Ɗalha sosai ya ce ''Mallam nan da ƴan kwanaki za'a daura maka aure da yarinyar nan me yasa baka son daukar kiranta?" shiru Ɗalha ya yi kafin a hankali ya sauka daga kan kwalta ya samu waje gefin kwalta ya yi parking mota shi dai Muhsin binsa kawai yake da ido kamar yau ya fara ganin sa,ba tare da kallon inda Muhsin ke zaune ba ya dauki wayarsa ya kira layin Unaisa bugu ɗaya ta amsa kira nan ta shiga jiro wutar masifa tana faɗin ''ni zaka wulaƙanta Ɗalhatu?to wallahi ka sani in za ka cigaba da yin haka zan iya fasa auren ka,tunda ka sake matarka gaba ɗaya ka fita hayyacin ka sai wulakanci kake min kala kala ni na ce ka saki matarka?wallahi ka kiyaye ni ka dai ji na faɗa maka,ka san kana son mata haka me yasa ka sake ta?'' galala Muhsin ya yi yana kallon Ɗalha cike da mamaki ganin murmushi ma yake da alama duk maganganun da Unaisa ta faɗa masa bai ji zafin su ba,fuska dauke da murmushi Ɗalha ya ce ''Allah ya ba ki hakuri yanzu dai me ki ke buƙata me ki ke so?" cike da rashin kunya Unaisa ta ce ''kana nufin bazan kira ka ba sai ina buƙatar wani abu?" cikin kwantar da murya Ɗalha ya ce ''a'a ba haka na ke nufi ba wai dai tambayar ki kawai nake ko da abinda ki ke bukata'' shiru Unaisa ta yi na wasu ƴan mintina kafin ta yi magana cike da isa ta ce ''kayan da zan sa ranar daure aure da kuma dinner nake son zuwa ƙarɓa na yi magana da tilan ya ce ya gama'' Ɗalha ya ce ''nawa ne ƙudin?" cike da gadara Unaisa ta ce ''dubu ɗari biyu ne da ashirin'' Ɗalha ya ce ''an gama ranki shi dade amarya ba kay lai...'' bai kai ga ida zancen sa ba Unaisa ta katse wayar,Muhsin da ya gama cika da mamaki ya ce ''ikon Allah daman ka iya ririta mace haka?" Ɗalha bai tanka sa ba ya mayar da hankali kan transfer da yake yiwa Unaisa bayan ya tura mata kuɗin ne ya ajiye waya kafin ya kunna mota har sannan bai yarda ya haɗa ido da Muhsin ba Muhsin dai sai bin Ɗalha da ido yake baki buɗe can Ɗalha ya hau kwalta da mota ne Muhsin ya ce ''ikon allah..ita fa a tunanin ta kai mutumin kirki ne,yanzu fa da ka auro ta zaka fara mata tsawa kamar yadda ka ke yiwa Amirah'' sai a sannan Ɗalha ya yi magana cikin yanayi na jin haushi ya ce ''Mallam ban son iskanci ni ɗin mutumin banza ne ko me ka ke nufi?"Muhsin ya yi murmushi ya ce ''a'a ni ban faɗa ba'' daga haka ya ja bakinsa ya yi shiru,ganin hanyar da Ɗalha ya nufa yasa Muhsin faɗin ''ina kuma za ka kai mu?" Ɗalha ya ce ''ɗinki zan ji ƙarɓo tun ranar juma'a ya ce min ya gama sai yanzu na tuna'' Muhsin ya yi shiru bai ce komai ba 
















Karfe sha biyu na rana daidai Amirah ce zaune cikin palorn ɗakin da Rumaisa ta sauke ta tana kallon wani a shirin a talabijan daga gefin ta Rumaisa ce zaune tana yankan salak shinkafa da wake da mai da yaji zata yi yau,ana tsaka da shirin ne an ji hutun rabin lokaci yadda aka fara haska tallace tallace Amirah da Rumaisa duk hankalin su na kan talabijan kawai sai ganin hoton Amirah suka yi an haska ana cigiyarta ana rokon duk wanda ya ganta ko yasan inda take ya kira layin waya da aka bayar,daga Amirah har Rumaisa sun yi mutuwar zaune ita dai Amirah hawaye ne ya ciko idanunta lokacin da mai sanarwa ya ce ta tafi ta bar ƴaƴa bakwai ciki harda ƴar shekara ɗaya da wata shidda,bayan an gama haska hoton Amirah ne Rumaisa ta mayar da dubanta ga Amirah taga kuka take bata hanata kuka ba kawai ta mayar da hankali kan yankan salak da ta ke,misalin ƙarfe biyu na rana Rumaisa ta shigo ɗakin da Amirah take ta tarar Amirah zaune kan darduma da alama bata daɗe da idar da sallah ba,hakan yasa Rumaisa ta samu waje ta zauna,bayan Amirah ta shafe addu'a da take ne ta mayar da hankalin ta kan Rumaisa ta ce ''sannu da aiki har kin girkin kenan''ta yi magana fuskarta dauke da murmushi Rumaisa ta mayar mata da murmushi ta ce ''yauwa sannu'' daga nan shiru ne ya biyo baya na wasu ƴan sakanni Rumaisa ce ta fara magana inda ta ce ''Amirah ki yi hakuri zan yi maki katsalandan mun yi magana dake jiya kin faɗa min cewar mijinki ya sake ki ne saboda zai ƙara aure'' Rumaisa ta yi shiru na wasu ƴan sakanni tana nazari kafin ta daura da ''tsakani da Allah babu yadda za'a yi ba ƙi yiwa miji laifin komai ba kawai dan zai ƙara aure ya sako ki dole akwai dalili,ko rashin kunya kike masa ne Amirah?" cike da juriya Amirah ta ce ''a'a'' Rumaisa ta ce ''kin nuna kishin ki a fili ne?" nan ma Amirah ta ce ''a'a'' cike da ƙaguwa Rumaisa ta ce ''ok pls faɗa min mai dalilin sakin ki da ya yi'' da ƙyar Amirah ta ce ''kazanta''cike da mamaki Rumaisa ta ce ''kazanta fa ki ka ce? ke ɗin ƙazama ce?" Amirah ta yi shiru zuwa yanzu ta gaji da kuka hakan yasa yanzu ma bata yi kuka ba sai zafin da zuciyarta ke mata Rumaisa da ta gama cika da mamaki ta ce ''a lallai na yarda da ake cewa namiji in ya so sake mace akan gishiri ma sai ya sake ki ya ce kin manta ba ki zuba masa gishiri cikin ruwan wanka ba'' Rumaisa ta yi shiru tana ƙara mamakin abinda Amirah ta faɗa mata can ta ce ''tsakani da Allah a sani na da ke wallahi ke ba ƙazama ba ce,kawai dai iskanci ne irin nasu na maza'' numfasawa Amirah ta yi kafin ta ce ''yaran ne sun yi min yawa kuma ina fita aiki shi yasa kullum cikin aiki nake ban cika samun lokacin kaina ba sau da yawa yana dawowa gida ya tarar yaran sun ɓata gida,da na gama gyara gida suke ɓatawa,in na ce su yi taya ni aikin gida irin su shara da wanke wanke wallahi sai na yi ta magana basu yi ba'' shiru Amirah ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta daura da ''wankan yamma da mata ke yi kafin miji ya dawo gida su yi kwalliya suna jiran miji ni sai sha biyun dare nake samun daman yin wanka,kin ga kuwa babu yadda za'a yi na yi kwalliya sha biyun dare amma..''bata kai ga ida zance ba Rumaisa ta ce ''ba ki shan maganin mata ne ko aski ne ba ki yi? in ban yi kuskure ba wannan ƙitson da ke kanki bai yi sati ba lallai dai ga faratan ki duk jajaye,to tsakani da Allah ina ƙazanta a nan?" Amirah ta yi shiru Rumaisa ta daura da na tambaye ki kina shan maganin mata ko ba ki sha?" cikin sanyin murya Amirah ta ce ''ina sha'' Rumaisa ta daura da siya ki ke ko kuɓewa ki ke haɗawa da madara,da kuka da madara,ko kina cikin masu cewa fruit da ruwan ɗumi ya ishi su?" Amirah ta yi ƙasa da murya ta ce ''ban cika siya ba haɗawa nake da kaina'' baki buɗe Rumaisa ke kallon ta kafin ta ce ''da ƴaƴa bakwai ne ki ka tsaya a iya kuka da kuɓewa da fruit to wallahi ansha da ke,to ba dole ya yi aure ba'' lokaci guda jikin Amirah ya yi sanyi ta ce ''to ya zan yi'' wani irin murmushi Rumaisa ta yi kafin ta ce '' a gaskiya ya kamata mu riƙe faɗawa kanmu gaskiya kin yi aure shekaru tara zuwa goma amma ba ki iya cire ƙuɗaɗe ki siya magunguna masu kyau da inganci ba,kuka da kuɓewa da fruit suna da mutukar tasiri amma fa ki sani namiji yana son canji ba kullum ya ji abu ɗaya ba,in ba ki da ƙudin siyan magani wannan abu ne daban amma ke kina aiki kina ƙarɓar albashi'' nan dai Rumaisa ta cire kunya ta shiga yiwa Rumaisa lecture sosai kan zamantakewar aure ta kuma bata shawarar yadda zata sa yaranta su yi mata aiki ba tare da sun sata magana ba








SHUUKRAN/022