MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 16

by @maimunabala209

MATAR GIDA 016


*SHUUKRAN/022



P16


Washe gari bayan idar da sallar asuba Ɗalha ya fita daga ɗakinsa zuwa ɗakin yara,tun bayan tafiyar Amirah ya daina fita sallar asuba a masallaci a gida yake sallah ɗaya bayan ɗaya ya tada yaran ya umurce su dasu je suyi alwala suyi sallah shi kuma ya wuce kitchen dan ɗaura masu abinda za su tafi makaranta da kuma wanda zasu ci a gida,daren jiya bai kwanta ba sai karfe sha biyu ya rage aiyukan gidan sosai yanzu dankalin turawa da ƙwai da soya masu sai tea,na rana kuma farar shinkafa zai dafa,ya yi miyar shinkafar tun daren jiya,bayan shigar sa kitchen ya wuce pantry inda ya dauko wasu fararen robubi irin wanda ake aikin kitchen da su,ɗebo dankali da kwai ya yi ya zuba ɗaya roba,ɗaya robar kuma ya auna shinkafa gwangwani biyar ya zuba a ciki,bayan fitarsa daga pantry ya dauki pot ya tare ruwa a fanfon kitchen da mamakin sa yaga ruwan baya zuwa,kashe fanfon ya yi ya sake kunnawa amma ruwa bai zuba ba,hakan ya nuna ruwa a ƙare a tanki,wani dogon tsaki ya yi kafin ya fita daga kitchen ɗin bai tsaya ko ina ba sai wajen switch ɗin borehole ya kunna switch ɗin dan yin pumping,daga haka ya koma ciki dan cigaba da aiki,bayan shigarsa ya dauki dankali ya fara ferewa nepa suka dauke wuta,a hankali Ɗalha ya ajiye wukar dake hannusa sai yanzu ya tuna duk ranar alhamis nepa ke dauke masu wuta in sun dauke sai safiyar juma'a suke dawo da wutan,cike da takaice Ɗalha ya dafe kansa murya can ƙasa ya ce ''oh my God yanzu ya zan yi?" tunawa ya yi da babu mai cikin inji bare ya kunna ya cigaba da pumping ruwa,ya tuna ranar juma'ar da ta gabata Amirah ta tambayesa ƙudin mai ya ce mata bai da  kudi,jiki babu kwari ya fita parlour ya zauna kan kujera one siter kallon agogon dake manne bangon parlour ya yi yaga karfe shidda da mintina goma,taɓe baki ya yi tare da sauke doguwar ajiyar zuciya, karfe tara ake buɗe gidan mai hakan yasa ya gyara zama tare da runtsa idanuwansa












Bai dade da zama ba Ummu Abiha ta shigo parlorn daga ita sai rigar bacci,ta naɗe rigar sama ta sa hannu ta riƙe yadda rigar bazai sauko ba fitarta kenan daga bathroom, bayan shigar ta parloun ne taga Ɗalha zaune kan kujera ya rufe ido kamar me bacci hakan yasa ta ƙaraso har inda yake zaune ta shiga kiran sunansa tana ''Dady..Dady..Dady'' a hankali Ɗalha ya buɗe idanunsa kafin ya gyara zama ya mayar da dubansa gareta,murya can ƙasa ya ce ''me ya faru Ummu?"sunkuyar da kai Ummu Abiha ta yi kafin ta ce ''Dady na gama popo ina son yin tsarki amma babu ruwa a bathroom''shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni yana tunani can ya ce ''oky'' ya faɗa tare da yunƙurawa ya miƙe tsaye,kitchen ya nufa ya dauki gorunan ruwa biyu kafin ya fita daga kitchen bayan fitarsa ya tarar da Ummu Abiha inda ya barota kallon ta ya yi kamar yadda itama take kallonsa ya ce ''muje'' babu musu ta bi bayansa har cikin bathroom ɗinsu Ɗalha ya shiga ya dauki buta kafin ya buɗe gorunan  ruwan ya zuba mata cikin buta,ya miƙa mata butan ta sa hannu ta ƙarɓar,barin ɗakin ya yi zuwa nasa ɗakin inda ya ga Fauziyya zaune kan bed da alama bata daɗe da tashi daga bacci ba,ya ƙaraso har inda take zaune ya miƙo mata hannu kamar jira take ta faɗa hannusa da sauri tana goga ido cikin hausarta da baya fita ta ce ''Dady tea'' murmushi ya yi kafin ya sumbaci kuncinta ya ce ''ok my princess'' daga nan ya fita daga ɗakin, bai tsaya ko ina ba sai kitchen,da ruwar gora ya haɗa mata shayi bayan ya daura ruwan a wuta ya yi zafi,bathroom ɗinsa ya wuce da ita ya wanke mata baki kafin ya zaunar da ita cikin parlour ya bata kofin, ƙarɓar kofin ta yi ta fara sha









Ɗalha na zaune nan cikin parlour hannusa riƙe da wayarsa yana kiran layin Amirah tun daren jiya yake ta kiran layin amma wayarta a kashe yanzu ma sau huɗu ya kira layin amma wayar tana kashe hakan yasa ya hakura ya ƙorawa tv ido,yana nan zaune Sumayya ta shigo parlour tana tura baki,kafeta da ido Ɗalha ya yi yana jiran jin abinda zata faɗa,har inda yake zaune ta ƙaraso ta ce ''Dady kaga Ummu Abiha bata flushing ba ni kuma ina son shiga tiolet'' ta ƙare magana kamar zata yi kuka Ɗalha ya ce ''ok je bathroom ɗina,babu ruwa a gidan ne'' maƙe kafaɗa Sumayya ta yi ta ce ''ni dai a'a'' cikin kwantar da murya Ɗalha ya ce ''ki je bathroom ɗina na ce zan kawo maki ruwa a can'' ba da son ranta  ba ta wuce bathroom ɗin Ɗalha kamar yadda ya faɗa mata,itama ruwan gora ya zuba mata a buta amma ita fitsari ta yi,Ɗalha na shirin barin ɗakin Suhail ya shigo ya ce ''Dady yau baza mu je school bane? na je kitchen naga baka dafa mana abinci ba'' Ɗalha ya ce ''eh baza ku tafi ba ni ma bazan tafi aiki ba'' Suhail ya kafe Dadyn sa da ido cike da mamaki ya ce ''amma fa kullum muna zuwa makaranta me yasa yau baza mu tafi ba'' a takaice Ɗalha ya ce ''saboda bazan kashe kaina ba'' Suhail ya ƙarasa shiga ɗakin tare da kallon mahaifinsa dake mayarwa Sumayya wando ya ce ''mutawa za ka yi in ka kaimu makarantar?" wani irin tsawa Ɗalha ya yiwa Suhail ya ce ''get out'' da wani irin sauri Suhail ya fita daga ɗakin sosai ya tsorata da tsawan da Ɗalha ya yi masa 








Karfe tara da rabi Ɗalha ya fita siyan mai dan yin pumping ruwa,sosai ya jawa yaran kunne cewar kada wani ya yi ɓarna ko faɗa,amma bayan dawowar sa daga siya mai yaga gidan duk a hargiste kaman sun yi yaƙi Rayyan da Afef dai sau uku suka faɗa kafin ya dawo,Ummu Abiha kowa kayan kwalliyar Amirah ta kwashe daga ɗaki ta yi jeri da su a nan parlour ta zauna gaban kayan kwalliyar sai faman surutu take da kayan kwalliyar, Sudais da Suhail na can gefi suna wasa da toys ɗinsu Afef dai ya ruƙube a gefi yana kuka ciki ciki inda Rayyan na tsaye kansa yana aika masa harara,Ɗalha ya dauki a ƙalla mintina uku tsaye cikin parlour yana ƙarewa yaran kallo har ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya girgiza kai kawai ya nufi hanyar kitchen yana daf da shiga kitchen ne idonsa ya sauka kan Sumayya da ta ɓoya karkashin daining table tana shan madara Ɗalha bai san sanda ya ajiye galon ɗin hannusa ba ya ce ''ke uban me ki ke a wajen?" a takaice Sumayya ta basa amsa ta ce ''madara nake sha'' cike da mamaki Ɗalha ya ce "me ki ka ce?" Sumayya ta sake basa amsa hankalinta kan gwangwanin madara ta ce ''yunwa nake ji Dady babu abinci a kitchen'' Ɗalha ya ce ''oky bani madarar'' babu musu ta fita daga ƙarkashen tabir ta miƙo masa gwangwanin tana lashi yatsun hanunta, karɓa ya yi ya shiga kitchen nan ma ya tadda Fauziyya zaune cikin pantry ta haɗa garin tuwo da mangyaɗa  wuri guda tana ƙwaɓawa,gaba ɗaya indomie dake cikin kwali ta zuba su nan ƙasan pantry,Ɗalha ya ji kansa ya fara juya masa tsabar ɓacin rai gaba ɗaya sun rikita masa lissafi bai san da wa zai fara ba ta ina zai fara ya dauki a ƙalla mintina huɗu tsaye kofar pantry yana kallon Fauziyya a hankali ta waigo ta ga Dadyn ta tsaye yana kallon ta kawai ta sakar masa dariya ta ce ''Dady na yi tuwo''







SHUUKRAN /022