LULLUƁIN BIRI

64

by @halimahz


Parlon ya nutse cikin wani irin shiru mai nauyin gaske. Ba shiru irin wanda babu magana ba, shiru ne da kowanne numfashin da mutum ya sauke yake da ma'anarsa. 

 

Baffa ya jingina bayansa da kujerar, ya haɗe hannayensa duka biyu a saman cikinsa. Kansa a ɗan sunkuye, amma idanunsa a rufe suke. Duk wanda ya san Alƙali ya san idan ya kasance a haka, to yana tattara dukkan abin da ya ji ne, yana auna shi da hankali, ba da zuciya ba. 

 

Sai bayan wasu daƙiƙu masu tsawo ya buɗe idanunsa. Kai tsaye ya kalli Turaki. 

 

"Muhammad." 

Muryarsa ta fita a hankali. Turaki ya ɗago kansa. 

 

"Na'am Baffa." 

 

"Ka tabbatar duk abin da ka faɗa min gaskiya ne?" 

 

Bai yi wata-wata ba ya ce,"Ehh wallahi Baffa." 

 

Baffa ya gyaɗa kansa a hankali. 

 

"Sannan ka tabbatar babu abin da ka ƙara ko ka rage?" 

 

"Wallahi babu abin da na ƙara, sai ma wanda na rage." 

 

Baffa ya yi ɗan jim. Sai ya maida kallonsa kan Fullo. 

 

"Ke." 

 

Kallon nasa ya zaburar da ita. 

"Na'am Baffa." 

Ta amsa da tsananin rawar murya. 

 

"Kafin yau kin taɓa gaya wa wani wannan maganar?" 

 

Ta girgiza kai. 

"A'a." 

"Shi ɗin ya taɓa ce miki ki ɓoye wani abu?" 

 

"A'a." 

 

"To me ya sa kika ɓoye komai? Ba ki san kasada kika dinga yi da rayuwarki ba?" 

 

Hawaye suka sake cika mata ido. 

"Ai bana son a ce ni ce na yi asirin. Kuma da na san shi ɗin mutumin kirki ne, ba zai yi musu komai ba, shi ne na yi ta addu'a Allah ya dinga taimakona akan komai." 

 

Wannan karon babu wanda ya yi magana. Har Mum ta ɗago ta kalleta. Fullo ta cigaba da magana cikin rawar murya. 

 

"Na dinga addu'a ne kawai Allah ya kare shi, nima ya kare ni. Idan na yi yunƙurin zan faɗa sai tsoro ya kama ni. Wallahi ban taɓa sanin kalar asiri ba sai a lokacin, kuma na rantse da Allah ba ni na yi masa ba." 

 

Ta share hawayenta da bayan hannunta. Kalaman nata suka sake saukar da wani irin shiru. 

Hajiya Madina ta lumshe ido. Ta ji zuciyarta na ƙara narkewa da yanayin da ba zai faɗu ba. Yarinya ƙarama haka ta ɗauki irin wannan nauyin ita kaɗai? Duk tsawon lokacin da suka ɗauka tare, bata taɓa faɗa mata akwai wata matsala haka ba. 

 

Ta iya bi ta warware aikin asiri ba don kanta ba. Ba don anfanin wani na ta ba. Sai don kawai ta kare rayuwar wani. Wani da bata da haɗin komai da shi. 

Baffa ya sauke numfashi. A karon farko tun da aka zauna, ya ji zuciyarsa ta ɗan yi sanyi, kuma ta sassautu. Sai dai ba sanyi akan Muhammad ba. Sanyi akan Fullo. Idan akwai abin da ya rage masa tantancewa, ba daga gareta ba ne. Sai daga wajen waɗanda yake son sanin sun yi wa ɗansa asiri. 

 

To akan me? Me ya yi musu? Kuma su waye? Tambayoyin suka yi masa layi a cikin zuciya, kowacce tana jiran amsa. Sai ya maida kallonsa kan Turaki. 

 

"Akwai abin da tunanina ya ke bani Muhammad." 

 

Turaki ya kafe Mahaifinsa da ido. 

 

"Ina so ka ɗauki kanka tamkar kana cikin kotu ne. Ba kana amsawa a matsayin ɗana ba ne yanzu. Ka ɗauki kanka a gaban Alƙalin da baka taɓa sani ba." 

 

Wannan kalma ta sa Turaki ya haɗiye yawun bakinsa. Baffa ya cigaba,"Ina so na yi magana da limamin da ka ce shi ya ɗaura maka aure. Ba da mahaifin yarinyar ba." 

 

Turaki ya ɗan ɗago kai. 

 

"Idan abin da ka faɗa gaskiya ne..." 

 

Baffa ya numfasa. Idanunsa suka kafe akan fuskar Turaki. 

 

"Muhammad zan ji daɗi. Zan samu natsuwa a ƙalla baka lalata rayuwarka akan Mace ba, a ƙalla ba zan yi danasanin haihuwarka ba, a ƙalla ba zaka yi ajalina lokacina bai yi ba..." 

 

Sai ya ɗan karkatar da kansa. 

"Amma idan akasin haka ne..." 

 

Muryarsa ta yi sanyi. Sanyi mai ɗauke da barazana. 

 

"Wallahi ba zaka taɓa jin daɗina ba." 

 

Ya ɗan ja dogon numfashi ya sauke. 

"Zaka ji dama baka sanni ba." 

Ya sake yin shiru na ɗan lokaci, sannan kalmar ƙarshe ta fito a hankali. 

 

"Sai ka ƙwammaci dama ba ni na haifeka ba." 

 

Kalaman suka sauka kan Turaki kamar saukar guduma. 

"Baffa..." 

 

Ya yi saurin dakatar da shi,"Ba ka da abin da zaka ce min yanzu. Ni dai kawai na sanar maka zan yi magana da Limamin da ya ɗaura maka aure." 

 

Turaki ya dinga jin kamar komai zai zamar masa tsanani. Domin ya san abin da Baffa yake nufi. Ba wai yana tsoron hukuncin da mahaifinsa zai ɗauka ba ne. Yana tsoron rasa mutumin da ya ɗauka a matsayin ginshiƙin rayuwarsa. Domin kuwa yana fargabar Liman ma ya kasance tamkar Hayyo, ya ƙaryata zancen auren bisa son zuciya da rashin tsoron Allah. Ya zai yi kenan? Shikenan zargin iyayensa akan Lalata yake da Fullo zai tabbata? 

 

Sai ya ji zuciyarsa ta buga. Ya san maganar Baffa ba barazana ba ce. Alƙawari ne. Alƙawarin Alƙali Dikko. Kuma duk wanda ya san Baffa, ya san idan ya ce zai gano gaskiya, to ko a ƙarƙashin dutse ne, sai ya fiddo ta. 

 

"Baffa, ba zaka kama ni da yi maka ƙarya ba in sha Allahu. Yanzu..." 

 

Baffa ya katse shi kamar ya riga ya san abin da yake shirin faɗa. 

 

"Ai idan kana da sauran hankali, a cikin haukar da ka san ka aikata, dole zaka ajiye lambar wayar wanda ya tsaya maka ko." 

 

Turaki ya numfasa. 

 

"Baffa, ba ma iyaka lambar waya ba. Har da shaidar da ta fi lambar waya ina da ita, in sha Allahu zata zama hujja." 

 

Kalaman suka sa Baffa ya lumshe ido. Ya ɗaga hannu ya dafe goshinsa, yana jin kansa kamar na shirin tsagewa. Hajiya Madina ta lura da yanayin nasa. 

Kafin ta ƙarasa gare shi, Hajiya Ramla ta riga ta isa. 

 

"Ya isa." 

 

Hajiya Madina ta faɗa cikin sanyin murya. 

"Ku je sai da safe." 

 

Babu wanda ya ƙara magana. Turaki da Bello suka miƙe a hankali, jikinsu a mace. Bakinsu na ta jera sannu ga Baffa, amma Baffa bai samu ƙarfin amsawa ba. Ƙafafun Turaki kamar ba za su fice a ɗakin ba, amma bisa dole ya fita, zuciyarsa na ta ƙara tamkewa akan kukan Fullo. 

 

Ciwon kan Baffa ne yake neman tashi. Ya jima ransa bai ɓaci kamar yau ba. Ya jima bai taɓa jin kansa ya ƙulle kamar yau ba. 

Irin ƙullewar da mutum yake zaune da tarin tambayoyi a lokaci guda, amma hankalinsa ya kasa kama ko guda ɗaya. 

Ya san akwai abin da yake buƙatar fahimta. Amma a yau dai ba zai iya ba.  

 

Kuma a can ƙarƙashin dukkan wannan abubuwan da suka faru, akwai rikicin da yake tsoron faruwarsa a gaba. 

Mahaifiyarsa! Bai san yadda lamarin zai kaya ba idan mahaifiyarsa ta ji wannan labarin. Ya san yadda take ciki da Turaki. Za ta ɗauka da gayya aka aura masa Fullo. Babu wani zancen ma zata fahimce su. 

Tun da dama Iyayensa Mata ba su taɓa son aurensa da Ilham ba, so zata ɗauki hakan a matsayin wani sabon shiri da aka ƙulla masa. 

 

Haka ma Ƴan uwansa, ta yaya za su karɓi wannan lamarin? Wanne kallo wacca Fahimta za su yiwa Muhammad?  

Me ya sa ɗansa ya ga ya fi dacewa ya ɗaura wa kansa aure ba tare da ya sanar da ko ɗaya daga cikin iyayensa ba? Yana nufin ya ishi kansa a rayuwa kenan? 

 

Tarin tambayoyin suka riƙa zagaye masa kai. Ya ji kamar yau Muhammad ya buɗe masa wata ƙofa ce da yake tsoron abin da zai tarar a bayan ta. 

Ya riga ya san irin maganganun da za su fito. Sai dai ya yi haƙuri da duk maganganun masu ɗaci da Muhammad ya janyo musu. 

Sunansa! Martabarsa! Darajarsa! Shikenan duk Muhammad ya watsar masa da su. 

 

Hajiya Madina ta lura da yadda yake ƙara dafe kansa. Ta shiga ɗakinsa da sauri ta buɗe drawer ɗinsa. Ta ɗauko magungunansa. 

 

"Ka samu ka sha wannan. Kuma don Allah ka bawa zuciyarka nutsuwa da haƙuri. Ka godewa ubangiji da yasa auren Sunnah Ɗanka ya yi ba akasin hakan ba." 

 

Ya karɓa ba tare da musu ba. Sai dai kafin ya sha sai da ya ce mata,"Madina mutum mai laifi babu kalar kalaman da ba zai faɗa ba domin kare kansa. Zan samu nutsuwa Madina, amma idan na samu ƙwaƙwƙwarar Shaida akan Auren nasa. Ki daina ƙoƙarin kare Yaronki, ki bi bayan gaskiya kamar yadda ɗayar Babar tasa ta tsaya akan shaidar da idanunta suka gani." 

 

Bayan ya sha maganin, suka kama shi suka kai shi ɗaki. Duk da cewa ya kwanta kuma ƙwaƙwalarsa na buƙatar hutawa, amma sai ya zamto gangar jikinsa ce kawai ta kwanta, ban da tunaninsa da kwanciyar hankalinsa. 

 

A parlon kuwa Fullo har yanzu tana zaune a inda take. Kukanta sai ƙaruwa yake yi. Hajiya Ramla ta tsaya gabanta cikin ɓacin rai ta ce,"Tashi mu je." 

 

Fullo ta ɗago kanta. Hawaye sun wanke mata fuska sosai, ta yi yunƙurin miƙewa. Hajiya Ramla ta kalleta daga sama har ƙasa. Sai ɓacin rai ya sake tasowa mata. 

 

"Shashasha." 

 

Fullo ta sunkuyar da kanta. 

 

"Da kika ga ya tafi da ke ɗaki, kika bi shi baki turje ba, baki da hankali ne? Kin san abin da ake nufi da namiji da mace su keɓe?" 

 

Fullo ta yi shiru. 

 

"Kin san ai ke ba muharramarsa ba ce ko? Har kika iya yarda ya rungumeki a jikinsa." 

 

Ta faɗa tana ɗaga murya sosai. 

 

"Kin san irin abin da hakan zai iya jawo miki?" 

 

Fullo ta fara girgiza kai cikin kuka, tsoro na kamata sosai. 

 

"Mum..." 

 

"Kar ki wani ce min Mum. A haka kamar mai wayo, kamar kina da hankali, ina yabonki sallah ashe ko alwala baki iya ba. Ni duk zancen asirin da kika yi ma ban kama ko ɗaya ba, daga ke har shi ɗin maƙaryatan banza ne." 

 

Muryarta ta ɗan yi sanyi na daƙiƙa, amma fushin bai ragu ba. 

 

"Abin da ya fi damuna, har yanzu bamu da tabbacin aurensa da yake ambata akanki, da kika biye masa a yanayin da na riske ku, shaiɗan ya fi ƙarfinsa wani babban abu ya gifta a tsakaninku, shikenan kun jefa mu cikin bala'i da tashin hankali.... Ke yarinya ce. Ba ki san namiji ba, ba ki san inda kuskure ɗaya akan Namiji zai kai ki ba." 

 

Ta sauke numfashi mai nauyi. Hajiya Madina dai na gefe ta zauna kan kujera. Wayarta tana hannunta. Ta kira wayar Kaka ne tana shaida mata cewa, don Allah su daure gobe su shigo, Baffa na son yin magana da su.  

 

Ta ɗan yi shiru tana sauraron Kaka daga can ɓangaren. 

 

"Kada ki damu Kaka, ba wani abu ne da zai sa ki firgita ba. Magana ce kawai da muke son mu zauna mu fahimta tare. Wani abu ya faru tsakaninmu da ku mai ɗaure kai." 

 

Sun ɗan jima a wayar kafin suka yi sallama. Hajiya Ramla dai har lokacin na ta yiwa Fullo faɗa, da nuna mata illar biyewa Turaki da ta yi. Kuma har sa'ilin duk bayan abin da ta ji, ta kasa samun natsuwa da kwanciyar hankali kamar dai Baffan. Ba zata taɓa gamsuwa da batun auren nan ba har sai ta samu ƙwaƙwƙwarar shaida, don a yanzu duk wasu kalamai da ta ji daga bakin Ɗanta, kalaman kare kai ne kawai. 

 

Fatanta ya zama da gaske ya aureta ɗin. Kuma ya zama wannan ne karon farko da ya tarfeta a cikin ɗakinsa, sannan wani babban lamari bai riga ya wanzu a tsakaninsu ba. Domin idan su sun fahimta, mutane ba za su fahimta ba, kuma tana gudun bakin mutane akan rayuwar ɗanta. 

 

A WASHE GARI… 

Ummi dai kallon ƴarta kawai take yi. Kallon da mamaki ya cika shi, tsoro kuma ya kasa barinsa. Har yanzu ba ta gama fahimtar irin haɗarin da yarinyarta ke faɗin ta jefa kanta ciki ba. Ta yaya ɗan mutum ba aljani ba zai shiga irin wannan lamarin da kansa, ya ɗauki nauyin da zai iya kai shi ga halaka, sannan ya yi shiru ya bar komai akansa kamar ba ƙatuwar matsala ba? 

 

A tashin hankali take tun ɗazu da Baffa yake cewa za su ji bayani daga bakin ƴar su. Kanta ya ɗaure da farko, amma zuwa yanzu wani irin takaici da baƙin ciki ne ke damunta. Kuma babban baƙin cikinta bai wuce yadda Fullo take faɗar komai cikin nutsuwa, kamar tana bayar da labarin wata ƙaramar matsala da ta faru a wasan yarinta. 

 

Da ace ba a gaban waɗannan mutanen suke ba, da ace daga ita sai ƴarta ne a ɗakin... Wallahi mari ne zai fara sauka a kan fuskarta, sai ta tabbatar ta fashe mata baki, kafin ta samu ikon ci gaba da bayanin cewa tausayi ne yasa ta yi rashin hankalin da take kira da sunan taimako ne ta yi. 

 

Ta yaya za ta saka kanta a cikin irin wannan haɗarin? Yo ko ubanta ne ta yi masa wannan sadaukarwar? Wa ye shi Turakin  a wajenta don ubanta. Ai ko Abdulhamid da suke ciki guda iyakar abin da zata masa kenan.  Lallai bata san mahaukaciya ta haifa ba sai yanzu. 

 

Wannan ba taimako ba ne a wurinta. Wauta ce. Wauta mai iya kashe mutum ma kuwa. Kuma Ummi mamakin ma yadda aka yi take raye ne cikin ƙoshin lafiya har yanzu, ko da yake addu'a bata bar komai ba, cikin nema musu kariyar Allah take ko da bata tare da su, amma tana da tabbacin duk abubuwan da Fullo ta lissafa tayi, ba yin kanta ba ne, sai dai idan tana da wasu motsi akanta da suka shige mata gaba. 

 

Ita fa tun a jiyan da Kaka ta sanar mata da saƙon Hajiya Madina, haka kawai ta ji hankalinta bai kwanta ba, cike da fargaba ta kwanta. Shi ya sa gari na wayewa suka doko sammako suka taho. Don bata jin za su iya kaiwa ƙarfe sha biyun rana kamar yadda Hajiya Madina ta sanar mata a jiyan. 

 

Daga ita har Kaka, kowa na ɗauke da nasa tunanin akan lamarin Fullo.  

Kuma bata gama fita daga Shock ɗin asirin da ƴarta ta yi ta kasada da rayuwarta wajen karyawa ba, furucin Baffan ya ƙara sakata jin ta girgiza a saman kujerar da take zaune. Wai Turaki ya auri ƴarta, sannan mafi mamakin ma Hayyo ne ya aura masa ita, anya zata kama wannan zancen? Aure? Kuma Hayyo ya ɗaura auren? A mafarki amma ko. Haka ƙwaƙwalwarta ke ta juya mata zancen da take jinsa kamar almara.