HASASHEN SOYAYYA

Hs 36

by @legendspen

Bayan sati uku. 

Zaman Bhatool da Senate a gidan Mom ya daure, Bhatool ta canja ta yi kyau ta yi ƙiba, haka shima Senate ya yi ƙiba abunsa. Kasancewar a part daban suke gidan kamar gidansu su kaɗai, Jannah sun zo bayan an yi mata baiko an kuma saka lokacin aurensu, amma Amrah ba ta samu zuwa gidan Mom ba. 

Sai da su Bhatool su ka yi wata biyu cif a gidan Mom sanan suka fara shirin komawa gidansu, daga Bhatool ɗin har Senate babu wani dake ɗaukin komawa gidan nasu, tun da nan babu wani da su ka rasa, rayuwa suke kamar gidansu. 

Da yamma Senate ya dauke ta, sai da su ka fara zuwa gidan Yaya Karima su ka yi ma ta sallama sanan suka huce gida wajen Umma, Bhatool na ganin Umma ta ce sai ta kwana gidan. Sai da Umma ta yi mata jan ido sanan ta bi Mijinta suka tafi, lokacin dare ya yi sosai suna shiga gida kwanciya kawai su ka yi. 

Washe gari. 

Ko da Bhatool ta buɗe idonta ba ta sami Senate a ɗakin ba, a fili taja tsaki sannan ta ta shi ta nufi bayi ta ɗaura alwala ta yi sallah, ran ta duk a ɓace na yadda Senate ya tashi ya ƙyaleta. 

A daddafe ta yi sallah ta koma sabida yadda ta ji cikin ta na ma ta ƙugi alaman yunwa, ta rasa wanan cin abincin da ta ke kwana biyu na mene?, ganin har tara na kusa wucewa ya sa ta lallaɓa ta ta shi ta fito falo, ta yi matuƙar mamakim ganin senate zaune kan dinning yana breakfast, amma sai ta kawar da mamakin ta hanyar cewa. "Shine ko ka ce ma fito ko?." Banza ya yi da ita ya ci gaba da cin abincinsa, takowa ta yi zuwa wajen dinning ɗin ta fara kokarim ta ɓa plast ɗin shayin amma sai ta ji shafal kamar babu komai a ciki. "Ina nawa tea ɗin?." 

"Ni zan dafa miki?." Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. "Wai mene haka, me na yi kuma daga safiyar?." 

"Kawau kin je kina wani baccin asara, baki san ki yi wa mijin girki ba, haka kika ga Mom na yi?, idan ku haka ake a gidanku mu namu gidan ba haka ba ne?." Wani irin abu Bhatool ta ji ya soketa a ƙirji. "Wai idan haka ta ga ana yi a gidansu, shi ba haka ake yi a nasu gidanba, zagin ta yake ko me, so yake ya ce ita ba ta ta so tarar da mahaifinta a raye ba ko me?." Cike da ɓacin rai ta ce. "Usman, zan juri komai, amma ba zan juri hulaƙamci da cin mutunci ba." 

"Did you just called me Usman?." Ya faɗa a tsawace. "Yes! Kai baka ji kunyar yi wa uwata rashin mutunci ba, sai ni zan ji kunyar kiran sunanka?." 

"Lallai Bhatool, ashe haka kike? Allah a fili, fir'auna a zuci, kin yi asara kuwa wallahi." 

"Ai idan akwai mai fuska biyu Senate bai huce kai ba, ka manta da duk irin abu da ka ce kafin ka aureni; amma duk ka watsar. A can gidan Mom ne kawai kake nuna mun kulawa ko soyayya, amma idan muna namu gidan babu komai sai hulaƙanci da cin mutunci." 

"Matsa ki ba ni waje kafin na tsinka miki mari anan wajen." Ya faɗa yana kauda kai. "Mari fa, da ba ƙara ba wallahi." Ta faɗa tana barin wajen, ta koma cikim ɗaki. "Wai wanan wane irim aure ne, daman haka ake zaman auren, yau fari gobe baƙi? To ni bazan iya ba." Ta faɗa tana ɗaukar wayarta. "Kawai ya sake ni na koma gidan ubana na yi zamana." Ta ƙara faɗa tana danna lambar Yaya Karima, Yaya Karima dake zaune ɗaki tana ganin kiran Bhatool sai da gabanta ya faɗi, jiki a sanyaye ta amsa wayar. "Hello Bhatool." 

"Na'am Yaya ina kwana?."

"Lafiya kalau, ya gida, ya mai gidan." 

"Yaya wai daman haka ake zaman aure?." Bhatool ta tambaya ba tare da ta amsa ma ta wayancan tambayoyin ba. "Me ya faru kuma?." 

"Kinga na ta shi da safe na ga baya ɗakin, kuka na ji cikina yana kukan yunwa, daƙyar na iya komawa na kwanta yanzu kuma na ƙara ta shi zanje kitchen na yi girki na gan shi yana breakfast." 

"Ya ga kina bacci ne shi yasa bai tashe ki ba." Yaya Karima ta katse ta. "Ki bari na kai ki mana Yaya." 

"To na bari." Nan ta hau zayyana mata duk abinda ya faru, har da marin da ya ce zai ma ta. "Kai Bhatool mari fa, anya ba ƙarya kike ba?." 

"A kan mene zan masa ƙarya, wallahi Yaya dagaske na ke miki, Senate ba ya sona, idan muma gidan Mom ne yake nuna mun kulawa." 

"Kin san me Bhatool, abu na farko sai kin yi hakuri, sanan ki dai na mayar masa da magana, ko me ya ce ki yi hakuri ko da zaki mayar mai da amsa sao ki faɗa mai ta cikin sigar soyayya da sanyi, ba wai yana  magana da ƙarfi ba kina yi ke ma." 

"Ni da Yaya kawai ya sakeni." 

"Bhatool wai saki abun so ne?." 

"Ni ban sani ba, kawai dai senate bai san darajar mace ba." 

"Yanzu kina ji Bhatool, zamu gwada shi sau uku, idan bai tsallake ba sai na sa ya sake ki."

"Amma Yaya fa ina son shi." 

"To yanzu Bhatool, ki bi wayanna abubuwan guda uku da zan lissafa miki, nasan shima zai dawo son ki." 

"Tom Yaya." 

"Yanzu kina ji, da farko dai ki yi mai banza kar ki kulashi, ki je kitchen ki yi breakfast ɗin ki ki ci sosai da sosai, sanan da rana ki tabbatar kin yi girki da wuri kin kai masa idan kuma bayanan ki tabbatar kin masa na dare, idan kuka zo kwanciya sai ki ba shi hakuri ki ce masa In sh Allahu hak bazai sake faruwa ba, amfanin yi mai shiru yanzu shine, zuciyarshi tana cikin fushi yanzu, amma zuwa anjima ta sakko." 

"Tom Yaya na gode."

"Ba komai Bhatool, saura na biyu." 

"Tom ina jinki."

"Ki tabbatar baki ƙara samun irin wanan matsalal da shi ba, duk abinda ya ce miki ki yi, to ki yi." 

"Shi ke nan Yaya, sai me?." 

"Rashin kunya, kar ki ƙara masa rashin kunya ko kiran sunansa kai tsaye." 

"Tom Yaya in sha Allah."

"Allah yabaku zaman lafiya." 

"Amin mun gode." Bhatool ta faɗa tare da ta shi, ba ta same shi a falon ba da alama ma baya gidan, kitchen ta nufa ta ɗora abinda zata yi karin kummalo da shi, bayan ta gama ne ta dawo ta yi ɗan gyare-gyaren ta kafin mai aikin ta ta zo. 

Bayan ta gama abinda za ta yi ne ta hau online, su ka fara chatting da Amrah take tambayarta ta dawo, ta ce Eyh, nan ta ce ma ta za ta shigo daga makaranta, amma kusa fara jarrabawa. 

Tana zaune wajen ƙarfe uku da rabi ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayarta, kaman ba zata duba ba dai ta jawo wayar. Saƙone daga Senate.

Ɓuɗe saƙon ta yi ta fara karantawa. 

"Barka da rana masoyiyah ta Bhatool, ina fatan kin wuni cikin ƙoshin lafiya, ina mai matuƙar baki haƙuri a kan abinda ya faru ɗazu, ina so na sanar miki cewa, ina sonki, ina ƙaunarki, ban san wani abu da zan yi a duniya ba inda babu ke a cikinta." 

Murmushi Bhatool ta yi bayan ta gama karanta saƙon, sanan ta fara mayar masa da amsa. 

"Nima ina sonka mijinah, ina kuma baka haƙuri akan rashin fahimtar ka da na yi, kai nake so ka kaɗai, kai ne rayuwata, kai ne farin cikinah." 

Take ta mayar masa da amsa, zuciyarta fari tas har ta ma manta da wani abu da ya faru, take wani ƙarin ƙarfi ya zo ma ta, ta ta shi ta shiga haɗa ma sa abincin dare. Ta kusa minti goma a kitchen ɗin tana faman tunanin me zata da fa masa, daƙyar ta iya tuno lokacin da ya ce ma ta. "Ina son dambun kus-kus, ayi shi da miyar ƙwai." Ai kuwa ba shiri ta shiga haɗa dambun kus-kus da miyar ƙwai, daga nan ta shiga haɗa masa lemon kankana, sai wajen biyar da rabi ta kamalla komai lokacin kuma Amrah ta ce da ita ta ƙaraso, sai sa ta gama kwashe komai nasa a plast sanan ta kai cikin wata warm high, ita kuma bata taɓa barin abin ciki ya yi san yi. Sanan ta bar ragowar a cikin kula, har sai da Amrah ta ƙara kiranta a kan ta gaji da jira. 

Bayan ta danna ƙararrawar ne masu gadin suka bar Amrah ta shigo, ita kuma Bhatool ta shiga ɗaki ta hau gyara jikinta, duk da ba ta yi wanka ba, ta bari sai darw kafin ya dawo. 

A kan kujera tasami Amrah zaune ta haɗe rai. "Lafiya kamar wacca aka aikoma da saƙon mutuwa?."  Bhatool ta tambayeta. "Haba wannan mistiyatan masu gadin naku mana, sun fiya iskanci wallahi." Amrah ta faɗa. "Yi hakuri Amrah." Bhatool ta faɗa tana zama. "Kema kin wani shanya mutane." 

"Wallahi ina ɗakine, yanzu na sauke girki ina son gyara jikina ne, da wanka ma zan shiga ma." 

"Eyh sai dake Amarya, kin san wai Jannah ta faɗamun an kusa kawo kuɗin ta jiya." 

"Sai jiya ta faɗa miki Amrah, ni fa tun ina gidan nan." 

"Wai me ya kai ki gidansu ne?."