CHAPTER 6
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske.
Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.
SHAFI NA SHIDA
Yana dukanta, tana dukansa, ta zage karfinta ta mannasa da bango tana buga kansa cikin zafin zuciya. Tun Sufyan na iya ramawa har ya gagara, janta ya dunga yi suna zuwa daidai kofar toilet. Ya fada ciki da sauri ya kulle kofar.
Numfarfashi yake yana fadin, “Ba fa tsoronki nake ba, kawai tausayinki nake ji, domin na san in na zage karfina zan iya miki dukan mutuwa.”
Farida na nishi a bakin kofar ta fara bugawa. “Karyar banza kawai! In ba tsoro ba ka bude mana a gwada. Ai ni bana so ka ji tausayina, araba rainin kawai.”
Jin kansa ya yi yana yi masa nauyi. Ya daga kansa ya kalli fuskarsa a madubi; goshinsa ya kumbura sumtum ga jini.
Dafewa ya yi yana yi masa azaba, Farida ta ci gaba da buga kofar.
Ya ce, “Mahaukaciya kawai, ba zan bude ba din.”
“Matsoracin banza, ai da ka bude din dai.”
Ta karasa maganar tana ficewa daga dakin. Dakinta ta nufa, taje ta cire kayan da ke jikinta, ta saka na barci kafin ta kwanta.
Sai da ya leka ta jikin kofar ya tabbatar da Farida ta fita, sannan ya bude kofar a sulale. Yana tafiya a hankali kamar sabon marawo ya danna sakata a kofar shiga dakinsa. Ajiyar zuciya ya yi yana cewa, “Wannan ingarmar ai sai ta kashe mutum. Karfi kamar basamuden zaki, bala’i, washhh.”
Ya karasa yana dafe goshinsa.
Hawa gadonsa ya yi yana yamutse fuska. “Wallahi tasa duk jikina ciwo yake min. Muguwar banza kawai. Ni dai an cuceni, an aura min namiji, namijin ma ingarma.”
Ya karasa maganar yana jan jikinsa a hankali ya kwanta.
Tun asuba yake jiyo motsin Farida a falo, yana so ya fita ya je masallaci amma tsoro ya hana shi, ganin yake idan ya fita za ta kara damƙarsa. Hakan ya sa ya gwammace ya yi sallarsa a ɗakin.
Ya gama shiryawa tsaf, P-Cap ya sa akansa ya rufe inda goshin nasa ya yi kulu, wajen ƙarfe takwas zai tafi school ɗin da suke da lectures. Ya ji alamun babu kowa a falon, hakan ya sa ya buɗe ƙofarsa a hankali, yana tafiya kamar wanda ba zai yi ba. Waigawar da zai yi, sai ya ga Farida zaune a kan kujera, ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana shan shayi.
Gabansa ne ya yi mummunan faɗuwa, a zuciyarsa yana ji kamar ya koma ciki. Can kuma sai ya make zuciyarsa ta fara raya masa, “Kada ka nuna mata kana jin tsoronta fa, lagonka za ta samu wallahi. Ka zama namiji.”
Take ya canja yanayi yana gyaran murya.
Dago kai Farida ta yi, ta ga yana kallonta. Ta ce, “Ya wannan kallon fa?”
Sufyan ya yi guntuwar dariya cikin ƙarfin hali ya ce, “Ya kamar ya? Me zan kalla? Baƙar fuska ko kuma katon goshi? Ai ke ba ki da abin kallo. Inda hali ma, da kin daina saka kanki cikin sahun mata, don wallahi kin fi kama da maza, a mazan ma munana.” Ya faɗi hakan yana fita daga ɗakin.
Farida ta kasa ce masa komai illa binsa da kallo.
Yana fita ta tashi ta tafi ɗaki, zama ta yi kan kujerar mirror tana kallon kanta.
“Da gaske na san ni mummuna ce, dukkanin maganganun da Sufyan ke faɗa a kaina gaskiya ne.”
Ta kalli jikinta.
“Ni ba kyaun fuska ba, kuma ba kyaun dirin jiki ba. Na tabbatar kila Yah Ahmad ma da ke nuna min cewa ina da kyau, kila don kawai ya kwantar min da hankalina. Ni kaina ban yi wa kaina kyau ba, to ta yaya zan yi wa wasu? Na san babu wanda zai so mace mummuna kamar ni.”
Ta ƙarasa faɗin hakan tana share hawayen da ke kwarara daga fuskarta. Wayarta ce ta fara ringing, ta ɗaga.
“Hello Azima.”
“Naam, Farida, gani a wajen gidanki, ki fito.”
Ko amsa ba ta yi ba, ta aje wayar. Tashi Farida ta yi da sauri, farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta fita da gudu. Tana zuwa ta rungume Azima.
Azima ta taɓe baki, “Na yi fushi ai, tunda ba za ki faɗa min an yi aurenki da Sufyan ba sai da na je gida kawai aka ce min kina nan ai.”
Farida ta ce, “Umm, mu shiga ciki dai.” Ta ƙarasa maganar tana riƙe mata hannu.
Shiga ciki suka yi, suka zauna a falo.
Cikin fara’a Farida ta ce, “Kawata, yaushe a gari?”
Azima ta gyara zama kafin ta ce, “Jiya da ke mun samu hutu a office, shi ne na ce bara in zo in ganki, amma sai kuma na ji zancen aure, kuma ba zato ba tsammani.”
Idanun Farida sun cika da hawaye ta ce, “Azima, arasa wanda za a haɗa ni da shi sai Sufyan? Kanina fa kanina ne Azima, na goyasa a bayana Ko dai suna tunanin ba zan auru ba ne? Suna tunanin babu namijin da zai so ni bayan Yah Ahmad?”
Share mata hawaye Azima ta fara yi ta ce, “Batun Kanin nan fa ki sa shi a gefe yanzu Farida, Sufyan mijinki ne, ko kin manta manzon Allah SAW da Sayyada Khadija ne? Sannan kuma batun ko ana ganin baza ki auru ba babu wannan maganar. Ai babu macen da take rasa masoyi a duniya, kar ki ƙara faɗa.”
Farida ta yi ajiyar zuciya tana faɗin, “Amma dai ke kin fi kowa sanin cewa tun muna makaranta ake kushe min halitta, ake faɗin cewa ni mummuna ce, har akwai masu danganta ni da biri. Kuma gashi yanzu kullum ma abin da nake fara karyawa da shi a gidan nan shi ne zagi da rashin mutunci. Har cemin namiji Sufyan ya yi. To ni da halitta kaina? Don Allah!” Farida ta ƙarasa tana fashewa da kuka.
Rugumarta Azima ta yi tana shafa mata sannan ta ce,”Har yanzu ba za ki bar saka damuwar furucin mutane a ranki ba? Mutane su suka yi ki? Ba su suka halliceki ba kuma mutane ba sa taba rasa abun fada a duk yadda zaka kasance.”
Cikin muryar kuka ta ce,”Shiyasa fa na daurawa kaina sanya nikaf a duk lokacin da zan fita, saboda gudun bacin rai, gudun tozarci, bani na yi kaina ba fa Azima nima zan so ace ina da kyawun nan amma kullum ni kenan cikin rayuwar rufe jiki da fuska.”
Azima ta numfasa,”Wallahi har yanzu bakya son kanki Farida, da zaki so kanki baza ki bi ta maganar mutane ba, ba za ki jira su ce kina da kyau ba kafin ki ji dadi, da tuni kin kudurta a ranki cewa ke ma mai kyau ce a yadda Allah ya yi ki, ke ta mussamance, kyawunki baya bukatar bayyana a zahiri a zuciya yake kuma zuciyoyin mutane kike shiga kina faranta masu, da nice ke ba zan sa nikaf ko wani abu ba wai in rufe kaina don zan shiga mutane aa shiga zanyi kamar kowa in karfafawa kaina gwiwa cewa ni mai kyau ce a duniyata babu wacce ta fini ni kadai ce.”
Juya kai Farida ta yi tana kallon Azima ta ce,”Chab, da hijab da nikaf dinma ya aka kare ba zan iya ba, barni cikin rufawa kaina asiri kawai.” Ta tashi tana share hawaye kafin ta ci gaba da fadin,”Kin ga na dameki da surutu bara in kawo miki ko drinks ne kafin a daura girki.”
Girgiza kai Azima ta yi tana, “Ai ba matsalarki kenan ba, kya son yarda da kanki.”
Zuwa Farida ta yi ta ɗauko mata Coke da ruwa ta kawo mata, ta zauna tana faɗin, “Ya to, me za a dafa miki?”
Azima ta ce, “Ba komai, ni a ƙoshe ma nake. Ni kam ya batun aikinki ne? An miki promotion ai ina fatan ba wani matsala?”
Farida ta numfasa kafin ta ce, “E, to ina fatan hakan. Ina so ma in shiga school ɗin, jiya ne nake da classes ban samu damar zuwa ba, amma gobe zan je. Zan ƙoƙarta wajen ganin komai ya tafi daidai.”
Azima ta ce, “To Allah ya bada Saa.”
•••
Suna zaune a class ana yi musu lecture, biron Sufyan ne ya faɗi. Ya durƙusa zai ɗauko, kenan P-Cap ɗin da ke kansa ita ma ta faɗi.
Habib ya ce, “Kai Sufy, ya haka? Me ya sa meka a goshi kuma?”
Sufyan ya yi sauri ya ɗauko ya maida kansa.
Habib ya kyalkyale da dariya, “Ni fa yau ban gane maka ba. Ko dai an je eya ne da amarya ta maujeka?”
Sufyan ya yi tsaki, “Allah tir! In haɗa jiki da wannan bogazar.”
Habib ya ce, “To yane, bani labari me ta aikata maka ne haka?”
Sufyan ya ce, “Dambe muka yi, kasan ko ma tana da jarababben ƙarfi, shine damke ni a bango ta dunga buga min goshi.”
Me Habib zai yi ban da dariya har yana durƙusa ƙasan desk.
Sufyan ya tunkuresa yana, “Dalla ka nutsu, kar wannan ɗan wahalan ya fiddamu mana.”
Cikin muryar dariya Habib ya ce, “Yasin ka rama kawai, kar ka bari ta ci banza.”
Sufyan ya ce, “Ta ya to? Ina zan iya da wannan abar?”
Habib ya ja kunnensa ya faɗa masa magana, dukansu suka yi dariya suna tafawa.
Ranar da wuri Sufyan ya koma gidan, ya tarar Inno ta kira Farida a waya tana faɗa mata abubuwan da za ta yi da yadda za ta yi, akan tana jin zazzabi ba za ta iya fitowa ba.
Ya ji daɗi sosai da ya tabbatar Inno ba za ta zo gidan ba, shiyasa ma yana sallar Isha ya kulle gidan, ya shiga kitchen ya dafa shayinsa, ya sa abunsa ya zauna a falo ya kulla kallo.
Farida ta fito daga ɗaki, ita ma ta shiga kitchen ɗin. Shayin ta dafa, ta yi toasting bread ta haɗa, ta fito. Har za ta shiga ɗakinta kuma sai ta dawo ta zauna a falon, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana sha, tana ci.
Ji ta yi kanta ya fara juyawa tana fita daga hayyacinta, ga wani irin zafi da ta fara ji. Ƙoƙarin tashi daga kujerar da take yi ta gagara, sai kawai ta sa hannu ta zame zanin da ke jikinta, daga ita sai pant, cinyoyinta a buɗe awaje, nama na rawa. Sufyan ya yi kamar bai san tana yi ba.
Daga kan kujerar ta zame ta yi a ƙasa. A lokacin ya kalleta yana sakin wata dariyar mugunta, sannan ya…
***