Page 49
💫MARYAMA💫
By
Ummu Fadeela
49
Da hannu biyu na toshe bakina da karfin gaske dan kar ihun da nake shirin kurmawa ya fito, daga ciki suka cigaba da magana ba tare da sun san cewa akwai mutum a wajen ba, John ya ce, "Oga ina tabbatar maka ba kananan kudi wadannan zuka zukan yan matan zasu kawo ba, mussaman the girl that used to wear hijabi, chaii omo kamar ita ta hallici kanta wannan idan fitinannun larabawan nan suka sameta ai kakarmu ta yanke saka, kuma sai ka gama morar abinka ka tsammana muma mun gwada kafun ka jefa masu ita". Ya kare da sakin wata dariyar.
"You are very stupid John!
An fada maka ni wawa ne?
You kno I don't do women. kafi kowa sanin wannan, and ban sanya kudadena na saye su dan in ringa ba mazan Dubai su suna tsakuro mini 50,0O0dollars ko 10,000dollars ba
Na sa kudadena a kansu ne dan in samu riba fiye da tunanin mai tunani.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un dama sayen mu Abdallah yayi?
To a wajen wa ya saye mu din, ya ya hausar ya saye mu yake?
Ta ya zai sayemu sai kace mun zama albasa ko kuma ince zamanin cinikin bayi.
Kunnuwata baza su iya jure jin abin da suke fada ba, dan haka da rarrafe na koma dakin da muka fito hannu na daura aka sai dai na kasa yin kukan sai harbawa da kirjina ke yi.
Ban taba tsammanin haka zai kasance da ni ba a kasar da ba ni kadai ba, yan mata da dama a kasata nigeria suke da burin zuwanta.
Na yi zaton zuwa ta Dubai zai zamto sanadiyyar cikar burina da dauwamammen farin ciki a gareni da dangina na har abada
Sai gashi daga shigowata kasar ko kwana daya banyi ba na fara cin karo da tashin hankali da masifa,."Ya Allah" na fada ina ganin Chioma dake ta kakari.
Magana Abdallah ya cigaba da yi da dan sauri sauri. "Na kawo su nanne dan samun cigaban harkokina, kasan mata shaidanu ne barinma kyawawan mata, kaji tsoron Allah kaji tsoron kyakkyawar mace, idan ka sanya irinsu a gaba zakayi succeding a lamurranka. yanzu ita waccar bakaga amfanin da ta mana ba? So haka zanke amfani dasu wajen safarar koken nawa wadda zai kawo mana billlions of dollars a saukake ba tare da bincike ba".
Gyada kai John ya yi yace, "Thats my oga" yana jinjinawa Abdallah,...yadda naga rana haka naga wannan daren mai cike da tarin da na sani wacce hausawa suka ce keyace.
Washe gari misalin karfe shida Abdallah ya shigo dauke da wani katon baho irin na wankan jarirai, da wani abu a dayar hannunshi da ban gama tantance menene ba, cike da fara'a yace min, "Morning baby!how was your first night at Dubai city?" ya tambayen yana murmushin, yayinda nake ganin murmushin nashi tamkar kuka ko uffan bance mashi ba,wani mutum ne ya shigo tare da John wanda zuwa yanzu na gama fahimtar cewa shine na hannun daman Abdallah.
Baby kije palour ga dr zai duba jikin Chioma ya fada yana kafe ni da idanunsa. Kamar jira nake dama kyet na fice daga dakin.
Bansan mai suka yiwa Chioma ba, na ga dai sun jima a dakin kafin daga bisani suka fito dauke da wannan bahon wanda ke dauke da wani abu mai dan banzan wari dan da suka iso tsakiyar palon inda nake zaune sai da na toshe hancina da bakin mayafin rigata kamar yadda dukkansu fuskarsu ke dauke da facemask kana hannayensu sanye cikin handgloves."Mai ya ke faruwa ne?" nai wa kaina tambayar da babu mai bani amsa.
Kafin Maryama ta samo mai bata amsa mu bari mu nemo amsar, abin da ya faru kuwa shine lokacin da Chioma ta amsa kiran Abdallah a lagos har wani da ya shigo ya basu lemo a kofi suka sha, daga nan ta fice a hayyacinta, dan kwaya ce aka sanya mata mai karfin gaske a cikin lemon da ya fi karfin kanta, da wannan damar suka yi amfani wajen sanyata ta had'iyi hodar ibliss da suke son fitarwa Dubai ba tare da an kamasu ba.wannan ne yasa ta fita a hayyacinta dan bata saba ba sannan kuma sun dura mata fiye da kima, yanzun kuwa wani magani suka bata inda koken din da suka dura mata ya fito ta hanyar bayan gida, so shine suka tare a baho dan zuwa su gyara shi su cire koken nasu a rabawa masu saye,.(Ya Subhanallah, jama'a duniya ta zo karshe ada ana safarar hodar iblis ne ta hanyar sanya shi cikin kayayyaki a wuce dashi ba tare da jami'an tsaro sun gano ba, aka zo aka koma tsaga jikin mutane a tura a cikin ciki a dinke idan ka iso inda ake bukata a kara yima mutum aiki a fitar, yanzu kuma zamani yazo da wani sauyi hadiya kawai zakayi duk binciken na'ura bai isa gano kana dauke da wannan mugunyar abu ba, idan ka kaita inda ake bukata, magani kawai ake hadiya mutum ya kasayar dashi, Ya Salam, Allah ka tsare mu ka tsare mana zuriyarmu da imaninmu.)
Cike da damuwa na mike na koma dakin kwance na samu Chioma tana baccinta peacefully kamar ba ita ce ta kwana murkususu tamkar mai shirin bakuntar lahira ba, dakin na bi da kallo wai ko zan ga wani abu da zai nuna min abinda suka aikata,sai dai yadda na bar dakin haka na sameshi, sai dai warin dake tashi irin wadda naji lokacinda suka iske ni falo,room freshner dake kan mirror na dauka na zazzage gaba daya kwalbar a dakin sannan na wuce toilet da tunanin ko Chioma tayi using toilet din batayi flushing ba, tas na samu wajen har wani daukar ido yake tsabar walkiya, dan haka wanka kawai nayo na fito daure da towel da na samu a bathroom din, a tsanake na shirya cikin abaya kamar ko yaushe na zauna hadi da yin tagumi yayinda na fada duniyar tunani.
Sai wajajen karfe sha daya Chioma ta farka, rass ta tashi abinta kamar babu abinda ya sameta sai rashin kardin jiki da take ji kadan kadan, duk yadda ta so funa abinda ya sameta kasawa tayi, dan haka ta share kawai gami da shiga bathroom ta hada ruwa mai dan zafi ta silla wankanta tass ta fito ta kimtsa cikin wandon da da kadan ya wuce mazaunanta sai wata yololuwar riga da dashi da babu duk daya,zako zakon faratanta ta gyara sannan ta matso tana tashina a inda nayi bacci daga zaune ba tare da na sani ba kasancewar daren jiya ban samu baccinba ko kadan.."Morning Marama".
Ta fada tana sake min lallausan murmushi, "Morning Chioma, ya jikin naki?".kallon rashin fahimta ta min hadi da tambayata da idanu "jiki kuma".Murmushi nayi ina basarwa nace, "Ohh sorry, i mean ya gajiyar hanya?" itama dariyar tayi tace, "Ahh dukanmu ne ai wannan, gashi dai finally mun shigo Dubai, ohhh my dream city,ina fada maki sai nayi shekara goma banje naija ba, kudi kawai zan riga turawa parents nawa su gina man katoton mansion da duk sadda naje zan sauka a can, sannan zan ke saran kaya irin na matan arewa laces shadda da kuma irin rigar da kike sawa dinnan ina turawa arewa ba karamar Madam zan dawo ba fa hmmm,". Ta karishe tana hada hannu waje guda gami da rufe idanunta.
A karon farko na ji wasu hawaye masu dumi sun wanke min fuska ba tare da na san da fitar suba, sosai ta bani tausayi bata san cewa mu yanzu a matsayin bayi muke ba, bata san cewa duk kudin da Abdallah ya kashe a kanmu bashi ne mu zamu biya ba..., iyayena, ko wanne hali suke ciki?. "Haaan,Marama why are you crying?"ta tambayeni ganin hawayen dake bin kuncina..."Nothing Chioma, muje palo na gaji da zama dakin nan seriuos,".
Zaune muka tadda Abdallah a dining area hannunshi rike da cup dake ta turiri, ko ba'a fada ba nasan hot coffe ne a ciki hannunshi daya kuma rike da waya idanunshi na kallon wayar.
Dagowa yayi jin alamar fitowarmu, murmushi ne ya bayyana saman fuskarshi lokacin da muka hada idanu, yayinda ni kuma kirjina ya bada sautin dammmm dan wani irin tsoro mai hade da tsanarshi ce ta dirar min,take kunnuwata suka fara bitar maganganunsu na jiya da dare.
Tasowa yayi yana ajiye cup dake hannunshi ya matso garemu kadan, yana kallona har cikin ido ya ce, "Morning princess,fatan kin tashi lafiya ya gajiyar hanya?"
Komai bance masa ba sai bugawar da kirjina keyi na tsananin tsoronshi, juyawa yayi kan Chioma ya mata magana da yarensu na igbo wanda da alama gaisuwa sukayi, sannan ya nuna mana hanyar Dining area yace muje muyi breakfast, babu musu kuwa muka dunguma dan gaba daya dama jin cikin nake tamkar an yashe min shi rabona da cin wani abu tun a jirgi mun iso kuma tashin hankalin da nake ciki bai barni na ci komai ba dan haka muka nufi wajen muka ja kujeru gami da zama.
Da ido Abdallah yabi su, kafun da baya baya Abdallah ya koma cikin falon ya zube cikin daya daga kujerun da suka kawata wajen.
Baya harkar mata ko kadan, a ganinshi mata shaidanu ne shiyasa ma ake amfani dasu wajen harkalla masu yawa, amma yanzu ganin Irin shigar da Chioma tayi da yadda manya manyan mazaunanta yake juyawa idan tana tafiya ga shafaffun cinyoyinta mai cike da tsoka sumul sumul sun sa shi jin wani abu yana yawo a cikin jininshi lumshe idanu ya yi yana kaiwa kwance saman kujerar.
Abincine kala kala a wajen, abin mamaki kuma yawanci irin abincinmu ne na nigeria don haka kowa ya diba abinda yake son ci muka fara aikawa cikinmu hakkinshi, babu abinda ke tashi wajen sai karar cokula....
wasa wasa muka kwashe wata guda cur a Dubai ba tare da mun leka koda wajen gidan ba, kullum muna cikin gida a kulle sai dai muci muyi wanka da bacci. Abdallah kuma ina ganin tun washe garin zuwanmu sau biyu na kara ganinshi a bakin cook na gidan nake jin wai sun tafi Singapore shida sauran yaranshi,..
Jikinmu ya karayin shar shar dashi kasancewar zama waje daya da kuma hutu ga rabar AC, wata daya ya wuce, wata biyu ya wuce wata uku ya shigo babu Abdallah babu labarinshi daga mu sai cook da yake zuwa ya mana girki shima yana gamawa yake tafiya muka dai a gida, babu inda muka sani gabas da yamma kudu da arewa balle mu fita.
Sannu kan hankali muka nemi mai girki shima muka daina ganinsa, kamar daukewar ruwan sama haka ya daina zuwa, ya zama saidai mu shiga kitchen mu girka abin da zamuci da kanmu, zara bata barin dami dama to hakance ta kasance damu,wayar gari mukayi gaba daya abincin gidan ya kare, hatta ruwan da zamusha na toilet muke tarewa, rayuwar tayi mana kunci ga yunwa ga rashin sanin inda muke, sau tari mun gwada attempting fita amma babu abin da muke ganewa dole mu dawo gidan muci gaba da zama, munyi kuka har kamar hawayenmu zai tsaya gashi babu wadda ya sai sim card na dubai a cikinmmu,gaba daya mun jeme mun bushe kamar wadanda yaki ya cinyesu, har gwara Chioma ma ta fini kuzari amma ni Maryama bambancina da skeleton kadan ne.
Wata rana bayan shafe wattani shida babu Abdallah, kuma kusan kwanaki goma da karewar abincin gidan,muna kwance shame shame a palo tamkar gawarwaki kwatsam sai ga Abdallah sun shigo kamar an jehosu shida yaranshi, duk da irin yankwanewar da mukayi sai naga kamar mun fisu kyan gani tsabar yadda suka kode yawancinsu suna dauke da tabo har a fuskarsu. Amma na Abdallah yafi zama worst dan har da jini ke diga a damtsen hannunsa da kuma gefen cikinsa.
Turuss suka yi a palon suna kallonmu sai kuma da dan sauri sauri ya fara magana, ku tashi maza maza ku hanzarta fitar da kayanku yanzu zamu bar gidannan da akwai matsala, daga haka ya fara taku cike da izza zai bar wajen, "Oga ya kamata a cire maka bullet dinnan ayi dressing na wajen inba haka ba there's problem you know".
A fusace Abdallah ya juyo daga tafiyar da ya keyi yana bankawa wanda yayi maganar wani mugun kallo kafin yace, "You are very stupid John, kai har kana da lokacin zama ka cire bullet? ka manta abinda ke gabanmu ko?wllh duk wadda ya kara minti biyar bai dauki duk abin da yake bukata ba a gidannan thats the end of him, dan tafiya zan yi in barshi."
Daga haka ya juya yaci gaba da tafiya da sauri sauri kamar zai tashi sama amma deep down ji yake kamar zai mutu dan azabar da yake ji..."Ku tashi ku dau kayayyakinku zamu bar gidan nan yanzu, inba haka ba babu mai karajin koda labarinku ne a duniyar nan.
Cikina ne ya bada sautin kulululu jin abin da mutumin ya fada, sai dai wannan ba na yunwa bane na tsananin tashin hankali ne, dan a take na nemi yunwar da na keji na rasa.
"Ya Ilahi, have mercy on me"na fada kuka na kufce min, kafun in ankara babu kowa palon, hatta Chioma ta wuce bedroom dan daukar abin bukatarta. Da kyar na iya mikewa ina jin jiri yana kwasata luuuuu na tafi baya zan fadi Abdallah da fitowarshi kenan yayi azamar cafkoni na fada saman damtsen hannunshi mai dauke da harbin bindiga,rumtse idanu yayi da karfi, bai gama jin azabar hannun ba gangar jikina ya sauka saman gefen cikinsa inda nanma ke dauke da rauni,"Wasshhhhh" ya furta yana kokarin sakeni, a daidai lokacin ne kuma karar SIREN na yan sanda ya cika illahirin anguwar kafun daga bisani muka fara jiyo karar harbe harbe..........