SANADIN HIJIRA

Page 50

by @ummufadeela01

*SANADIN HIJIRA*
     

       BY


Ummu Fadeela


Chapter 49/50


"He... hel... help" shi ne abun da bakina ke fada ina kakkarwa da cigaba da damkeshi tamkar zan koma cikin cikinshi.
Daya daga cikin likitan ne, da alama yana da zafin rai, ya tunkaroni da niyyar yi mani allurar, amma Al'ameen ya mishi wani kallo da fadin, "Stop!" Cakk kuwa ya tsaya. Sauran suka hau kallon-kallo, dukkansu mamaki da al'ajab fal ransu.


Hannuna ya warware daga rikon da nai mishi, ya juyo dani gaba muna facing juna. Har lokacin shock na ganina a wajen bai bar fuskarshi ba. "You! Ke ce? Ko dai resemblance ne? Me kike yi a nan?"


"Ni ce... Ina ka kai min Maahh kuka tafi kuka barni rayuwa tana ta bugun kwallo da ni?"


"Answer my question first, me kike yi a nan?"


"Ban sani ba, ban sani ba nima. 

Kawai sun kawo ni, kuma sun ce bargon da ke cikin kashina za a kwashe a dasawa yarsu. 


Sun ce ni baiwa ce, kudi suka sanya suka sayeni, dan haka dole in bi umarninsu, bani da zabi sai yadda suka yi da ni. 

Sun kawo ni nan, kuma shi ne na gankaaa..." 

Na fashe da kuka ina durkushewa gabanshi.


Illahirin likitocin da ke dakin sakato suka yi suna kallonmu; kasancewar da Hausa muke magana, ba kowa ya ji mu ba, in ka dauke Musty da ke ta jujjuya maganganun da abokinshi da yarinyar ke yi. 

"Su waye, a ina suke?" 


Hannu na shiga jujjuyawa, "Ban sani ba."


Wayar gaggawa likitan Elisha ya yi. Cikin minti daya sai ga Mom da Jack biye da ita a baya. 

"An gama ne d..." 

Maganarta ne ya katse sakamakon ganina da ta yi durkushe gabanshi. Kamar zata kifa ta karaso garemu, ta sanya hannu zata kamoni. 


Cikin kaushin murya ya ce, "Ko da wasa kada ki yarda ki taba ta. I mean even by mistake don't dare you touch her" 

Kamar ba shi ya yi maganar ba, yana sosa habarshi, tunani kala-kala na rige-rigen shiga kwanyarshi.


"Kai waye da zaka hanani tabata?"


"Waya baki izinin amfani da wani bangare na jikinta?" 


Shi ma ya watso mata tambayar ba tare da ya bata amsar tata tambayar ba.


Kasake Mom ta yi kafin ta zuge jakarta, ta zaro takardar da suka yi signing dukkansu, ta jefawa Al'ameen a fuska, a fusace ta ce, "Da amincewarta, bayan sun gama cin makudan kudin da na basu, ita da iyayenta."


Tsawon minti daya yana duba littafin da kuma signing da yarinyar ta yi, ya dago kanshi yana kallonta. 


Tun bai yi magana ba na fara girgiza mishi kai. 

"Ban san na menene ba! Kawai sanya ni dole suka yi in yi sign, wallahi ban sani ba, sanya ni suka yi." 

Jack yana jingine da bango idanunshi a lumshe; bai san me yake ji ba, abun da kawai ya sani shi ne, yana farin ciki da tsaikon da aka samu. Yes, yana farin ciki.
Da sauri ya bude idon jin abun da Al'ameen yake fada. 

"Zaku amsa kiran hukuma bisa laifin safarar bil'adama da amfani da sassan jiki ba tare da amincewar mai shi ba." 


Daga haka ya damki hannuna ya fara jana da karfin gaske yana barin dakin tiyatar, fuskar nan tamkar bai taba dariya ba.


Wani irin kukan kura Mom ta yi kafin ta afkawa Al'ameen, ita ma ta janyo daya hannuna ta fara ja tana dawar da ni baya. 

Jin suna kokarin balle min hannaye ya sa ni fara turjewa. Wani stern look Al'ameen ya bai wa Mom da fadin, "Sakarta!" Bata sake ni ba kuwa, ta cigaba da jana. 


A daidai lokacin kuma aka bude kofar, jami'an 'yan sanda suka shigo sakamakon security alert da wani Dr ya danna.


"You're under arrest!" Cewar jami'i dake gaba yana daga handcuff da nunawa Amin a saitin fuskarshi. Wani kalan murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi yana kallon dan sandan, ya zaro ID card nashi shi ma, sannan ya ce, "Ga wacce zaku kama kafin mu iso in shigar da kara."


Dukkansu suna zaune cikin ofishin kowa ka gani rai a bace. Mai rubuta statement din ya dago yana kallon Al'ameen, "Uhmmm, go on."
Lumshe ido ya yi ya bude, "Ina tuhumarta da laifin human trafficking and human harvesting organs, lallai muna bukatar zuwa kotu." A tare duk suka dago suka kalleshi. Musty ya yi karfin halin cewa, "B..." Daga mishi hannu Amin ya yi cikin wani irin fushin da bai taba saninsa da shi ba. "You know nothing about her, Musty. Just stay quiet! Idan ba zaka iya ba, kawai ka fita a nan."
Kasancewar Turai sun san hakkin da darajar dan Adam, suna girmamashi, tuni labarin ya dauki hankali. Yayin da Mom ta shiga tashin hankali mara misali lokacin da aka turata cell. Bincike ake babu kakkautawa; ba don kasancewar Aminu soja ba, sai don su a can ba sa wasa da hakkin dan Adam ba irin kasata ba. Duk girma da kimar da Jack ke da shi a kasar, haka aka kamashi shi ma bayan ya auno Magajiya da ya tabbatar da a wajenta suka dauko Fannah. Ita ma aka garkameta a cell, sai muzurai take da nanata kalmar *Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un*. Cikin kwana biyu komai ya rikice ya jagulewa Mom, yayin da Jack zuciyarshi ke wasuwasin waye wannan da ya dage a kan yarinyar haka. An gama shirya komai, sai shirin shiga kotu a washegari.
"Kina da lauya ko lauyan gwamnati za a baki?" Dan sandan ya mata tambaya a karo na uku. Dago jajayen idanunshi ta yi tana kallonshi ta ce, "Ina bukatar waya in kira shi."
"Shi waye lauyan naki?" Gyada kai kawai ta yi tana kara dafe kanta da take jin kamar zai tsage gida biyu. Bayan minti biyu dan sandan ya dawo rike da waya ya mika mata ta amsa, shi kuma ya ja tunga ya tsaya. Kallon 'ka bani waje' ta mashi lokacin da lambobin da ta loda cikin wayar suka fara tafiya. "Sorry ma'am, ina bakin aikina ne."
Cikin tausashiya kuma zakakkiyar muryarshi ya furta, "Assalamu'alaikum!" Dan jimmm Mom ta yi jin muryarshi. "Assalamu'alaikum!" Ya kuma fada a karo na biyu.
"Hello Daddy!" Iya abun da ta fada kenan, ta fashe da matsanancin kuka kamar yarinya karama. Sosai ya shiga mamaki, ko a mafarki ba zai gaza gane muryarta ba. "Mariya, ke ce? What's happening? Me ya sa ki kuka?"
"Daddy, I seriously need your help, ina..." Kusan minti biyu tana magana.
"Ohk, share hawaye ki daina kuka, ina zuwa..." Bai dauki lamarinta da wasa ba, cikin kasa da awa biyu ya shigo station din. Tana zaune bisa benci, shi kuma saman wata kujera da aka ajiye mishi, ga mai tsaronsu kikam dake gefe. "Mariya, tell me the whole truth. Na sanki sarai, fadi gaskiyar abun da ya faru." Iya gaskiyar ta fada masa. "Yanzu ina shi Jabirun, ina Aishar?" Nuna gefen da aka ajiye Jack ta yi tana share hawaye ta ce, "Lisha kuma tana hospital karkashin kulawar likitanta."
"Abun da nake so da ke yanzu, ki kwantar da hankalinki. Zan shiga cikin lamarin, ohk?" Gyada kai Mom ta yi kafin jiki a sanyaye ta bishi da kallo har ya bacewa ganinta. Ya dade yana magana da Jack har sai da mai tsaronsu ya ce, "Sir, lokacin da aka debar maku ya cika." Sannan ya tafi bayan Jack ya bashi full details da ya tambayeshi...
Kallo daya ya mishi ya ganeshi; yaron nan ne da suka hadu a filin jirgi ranar da ya dawo kasar daga doguwar tafiyar da ya yi. "Ba ka ce komai ba Son. Ba don su ba, domin girman Allah ka janye case dinnan muyi sulhu a gida. Tsakanin uwar da dan dukkansu ba halinsu kenan ba; zafi da radadin ciwo da yarinyar ke ciki ya sanyasu aikata hakan. Plsss Son, ka min wannan alfarmar." Ya kare da hade hannayenshi waje daya.
Wani irin kunya ne ya saukarwa Al'ameen a karo na ba adadi ganin tsoho sa'an babanshi yana rokarshi. To shi wanne irin zuciya ne da shi da bazai yafe ba, duk kuwa da cewa ya dau abun da zafi da farko? Dago kai ya yi suka hada ido, gabanshi ya kuma yankewa ya fadi kamar yadda yake ji tun dazu idan sun hada ido.
"Na yafe Abbah, kuma zan je har station din in janye, amma yarinya ba zata koma hannunsu ba. Kuma bazan barta hannun hukumomin shige da fice ba; da kaina zan mayar da ita gida in hannuntata ga iyayenta."
"Masha Allah! Ubangiji ya dubi lamarinka, Allah yai maka albarka gabanka da bayanka. Menene sunanka?" Al'ameen da ya ji wani irin sanyi yana ratsa dukkan gabban jikinsa ya amsa da "Amin" a sanyaye, zuciyarshi na tambayar, 'Me yasa Abeey bai taba min irin addu'o'innan ba?' Dago kai ya kuma yi ya sauke cikin na dattijon da ke kallonshi cike da murmushi ya ce, "Aminullahi."
"Masha Allah, Allah ya amintar da kai."
A hankali nake tafiya. Tun ranar da ya kawoni gidan nake zaune a daki, ko falo ban taba lekawa ba sai yanzu da na gaji da zama na fito. Ganin mutane zaune a falon ya sa ni tsugunnawa can karshe, na gaida dattijon dake sanye da babbar riga har da rawani, da ka ganshi ka ga cikakken malami. "Ita ce wannan?" Al'ameen ya gyada mishi kai.
"Masha Allahu! Amma zamanta a nan bai kamaceku ba, ko zaka kaita can gidana tunda akwai mata da yara sa'anninta sai tafi sakewa, nake gani. Kafin lokacin komawarku can kasar taku ina ma kace?"
"Nigeria," ya fada a takaice. Dan jimm ya yi sai kuma ya murmusa ya ce, "Kasar da nake da muradin zuwa amma Allah bai kaini ba, watakila ta dalilinka watarana zan je." Murmushi kawai Al'ameen ya yi.
Kamar yadda ya bukata, tare da shi da Amin din muka tafi gaba daya. Gidan babbane sosai mai cike da mutane kala daban-daban; Turawa, Larabawa, Asians, har da 'yan uwa bakaken fata akwai. Abun mamaki, karatun addini ake sosai da wani babban masallaci a wajen. Ina ta mamaki dama akwai musulmai a nan? Dama akwai masallaci amma ban taba jin kiran salla ba?
A hannun wata babbar mace aka damkani, ya mata bayanin zan kasance da su na wani gajeren lokaci. Sosai ta karammani kuma ta rikeni hannu bibbiyu. Nan na saje cikin jama'a, sai aikin girkawa da saukewa ake ana fitarwa waje. Lallai wannan gida akwai karamci, kova ka gani yana nan-nan da dan uwanshi.
Al'ameen yana wajen har aka gabatar da sallar Isha, ya ga yadda wajen yake kuma sosai hankalinshi ya kwanta da mutumin da duk sanda zai dago sai ya kamashi yana satar kallonshi. Murmushi kawai yake ya cigaba da karantar da daliban da ke gabanshi.
Taxi Al'ameen ya hau har cikin asibitin ya maida shi. "Capt, ka min shiru! Me hadinka da yarinyar nan? A ina ka santa? Yanzu kuma ina ka kaita? Don't put yourself in trouble faaa!" Musty ya karishe cike da gargadi. Bai ce mishi komai ba ya nufi daki. "Ohk, ga shege na magana shi ne kake tagiyarka ko? To ai shikenan. Matarka tana ta kiran wayarka da ka jefar."
Shi sai a lokacin ya tuna ya ce mata zai kirata. Yau kwana biyu kenan tun da yarinyar ta dawo apartment nasu, bai kara bi ta kan Badar ba; tunda sharing daki suke da Musty, ya barwa Fannah nashi, and bai son waya da ita gaban mutane sanin halinta...
"Sojana, saura kadan hawan jini ya kamani. Kawai rashin sanin hanya ne amma da tuni ka ganni a Spain! Na yi kewarka kamar zan hauka, my Soja."
Lumshe ido ya yi ya bude, murya ciki-ciki ya ce, "Badarrr!" Wani irin yarrr ta ji a jikinta the way ya ambaci sunan, ya taba ta sosai. Yana matse filon da ke hannunshi da karfin gaske don gujewa yanayin da yake ji yana yawo cikin jininsa, ya ce, "Tell me something."
"Like?" Ta fada da sigar tambaya.
"Just tell me something special da zai kwantar min da hankali." Rikicewa ta yi, tana mikewa tsaye ta fara kai-kawo; me zata sanar da Soja yau da zai sanya shi farin ciki? Wani tsalle ta daka tuna wani abu ta ce, "Sojana!"
"Hmmmmm," ya fada, wani sanyi yake ji yana ratsashi kamar zazzabi zai rufeshi, dan haka ya kuma matse filon yana janyo duvet da kafarshi ya rufe kusa da guiwarshi. Sai kuma ta yi shiru jin yanayinshi. "Sojana!"
"Uhhmmmmm," ya kuma fada. "You want something ne?"
Kamar tana gabanshi ya gyada kai still a hankali ya ce, "I want you, ke nake bukata."
Kamar zata taka rawa don dadi, cikin shagwaba ta ce, "Da gaske Sojana? Shi yasa na ke ce zan bika mu taho tare amma kace zan taho daga baya. Kana isowa kuma kace babu fili yanzu, da ba muna tare ba?"
"Uhhmmmm," kawai ya kuma fada, dan ba zata taba fahimtar halin da yake cikin ba. Hira ta dinga mishi tun yana fahimtarta har bacci ya fara daukarshi, sannan ya mata sallama...
Kamar yadda ya yi alkawari, washegari da kanshi yaje station ya janye case din aka saki su Mom kamar yadda ya yi alkawari...
A daddafe suka kara sati a kasar. Su da suka tafi da niyyar yin wata shiga, sai gasu cikin kwana goma sun fara shirin dawowa; musamman aikin da za a yi wa Elisha ne zai rikesu daman, tunda an canza lokacin kuma babu amfanin zamansu...
"Zamu yi kewarki, Fannah!" Suka fada lokacin da aka gama sanya tarin kayayyakin da na samu a gidan cikin booth din taxi da ya zo da shi. Ina daga musu hannu na ce, "Nima zan yi kewarku sosai." Cikin satin nan sosai muka shaku da su. Addu'o'i sosai Abbah—kamar yadda na ji ake kiranshi a gidan—ya mana, sannan muka dauki hanyan filin jirgi.
"Ina wuni!" Na fada ina kai kaina kasa. Bai amsa ba, na kuma fadin, "Wajen Maahh zaka kaini ko?" Still bai amsani ba. Na dago kaina a zatona bai ji ni bane; ilai kuwa hankalinshi na kan wayarshi da yake operating. Har muka iso filin jirgin bai ce komai ba, nima ban kara yunkurin cewa ba. Amma kasan raina fal murna, zan ga Maahh dita da har yanzu ban yarda cewa ta rasu ba...
Surprisingly, Al'ameen yake kallon ma'aikacin filin jirgin, kafin ya nuna kanshi. Ya ma kasa furta ko kalma daya. Fahimtar hakan yasa ma'aikacin cewa, "Tabbas sir, sai ta nuna mana takardun izinin shigowarta kasar nan kafin ma ta samu izinin fita."
Shafa kanshi ya yi yana lumshe ido da budewa. Awa uku kenan yana ta cuku-cukun cikin airport din amma abu ya gagara. Ganin zasu yi missing flight ne ya sa Al'ameen cewa su Musty su tafi kawai. Tun awa daya da suka wuce jirginsu ya tashi amma har yanzu babu wani labari.
A gajiye ya dawo kusa dani yana bani wani irin kallo da na gaza fassarashi, ya ce, "Ke yanzu ya zan yi dake ne? Kince paspot dinki yana wajen waccar Magajiyar." Gyada mishi kai na yi. Hannu ya yarfar, "Gashi an tusa keyarta gida Nigeria dan fara fuskantar shari'a."
Langwabar da kai na yi, hawaye na bin fuskata, na bude baki zan fara kuka. A fusace ya ce, "Karki fara! Da me zan ji? Da zafin kan da kike hada min duk sadda kaddara ta hadani da ke? Ko da wannan kukan naki mai cin rai?" Ya fada rai a bace yana zaro wayarshi da ta dauki ringing.