BIYU A ƊAYA

Chapter 14

by @barista

BIYU A ƊAYA 
    (Don't judge a book by its cover)


Page 14

Sayyada barrister 
***
YOTA 13 
TEAM FIVE INK LEGENDS 


Zaune ta ke har wannan lokacin tana sharar ƙwalla, zazzaɓi yana neman rufe ta ga kuma jini dake zuba daga tafin ƙafarta, tana so ta mik'e amma ta kasa saboda yanayin da take ciki. Bata taɓa sanin rashin imanin Aunty Laraba ya kai haka ba sai yau, duk da ta san basa shiri amma bata san haka ta ke sanar ta ba sai yau, taƙi taimaka mata, bayan kuma taga halin da ta ke ciki....

"Ke Bilqees!"

Ta ji muryar Alaja daga waje tana tun karo ɗakin, nan tsoro ya sake kamata shikenan yau kashinta ya bushe, Alaja ta sake bankaɗo Kofar tare da cewa 

"Ni za ki zubar wa mutunci, ni za ki yi wa rashin hankali, ki ɗagawa customers nawa hankalin, ki janyo min asara"

"ALAJA don Allah ki yi hakuri, ba da gangan na aikata ba, ban san ya abin ya faru ba, kawai ina shirin kai masa shayin ne na zame na faɗi.....

"Ferme ta bouche!"

Alaja ta faɗa cikin ɗaga murya ranta yana ci gaba da ɓaci, ta ce shut you mouth, ta rufe mata baki, nan Bilqees ta ƙame bakinta tana hawaye, Alaja ta ci gaba da cewa

"Na gaji Bilqees na gaji, a wata ɗaya asara nawa ki ka jawo min, akan wane dalili za ki ta yi min asara, mugunta ne ko iskanci ne"

"Je suis de'sole Maa"

I'm sorry Maa, ta faɗa mata tayi hakuri, don in ba wannan kalmar ba bata san me zata ce ba...

"Hakuri! Sau nawa ki ke aikata laifukan kuma ki bani hakuri na hakura kuma bayan kwanaki ki sake aikatawa, don haka yau kin kai ni bango"

"Alaja ni ma na ji ciwo, ki gani jini ƙafata ke fitarwa ka ƙuna da ruwa shayin ya yi min, me zai sa na yi miki mugunta bayan ni ma zan cutu"

"Ki mutu Bilqees ba ƙuna ba, ina ma gaba ɗaya ruwan ya zube miki a jikin ki kowa ma ya huta da wannan takaicin...

Kuka Bilqees ke yi, yau ta tabbatar da Alaja bata da imani, maimakon ta taimaka mata take kiran mata mutuwa.....

Dr Waahab bai samu nutsuwar cin abinci ba, gashi ruwan shayin da ya taɓa masa hannayensa yaji suna ɗanƙo ya goge da tissue amma har wannan lokacin bai daina danƙon suger ba, ya mik'e tare da sanya wayarsa da wallet nasa cikin Aljihun rigar coat da ya ɗaura a saman farar rigar dake jikinsa, a nutse ya bar wajen, yana ɗan dube dube ko zai hango in da zai samu ruwa, ganin security dake zaune bakin ƙofar shigowa dining area yasa ya iso wajensa tare da cewa 

"Sannu, Ina buƙatar inda zan samu ruwa na wanke hannaye na"

"Ok za ka iya fita waje akwai fanfo amma yana baya, sai dai ka shiga toilet dake side ɗin nan"

Ya nuna masa bangaren Server's, Dr Waahab ya ce

"Ok thanks"

Ya shigo bangaren Server's, mamaki yake yi, ganin haɗaɗɗen restaurant irin wannan, koman su gwanin sha'awa, ya iso bakin ƙofar da aka rubuta TOILET, ya sauke numfashi ya buɗe ya shiga fes da shi ba datti sai ma ƙamshin Detol dake tashi, ya wanke hannunsa tare da ɗan shafa ruwa a inda ruwan shayin ya ɓata yana gogewa, sannan ya fito yana ƙoƙarin barin wajen yaji hayaniya na tashi daga ƙofar dake kusa da toilet ɗin, kamar kuka ma ake yi, wata zuciyar ta ce Dr Waahab kayi tafiyar ka, wannan abin bai shafeka ba, wata zuciyar kuma ta ce ko dai taimako me shi yake nema...

Ya juyo a hankali ya iso bakin ƙofar ya tsaya, ganin ƙofar a buɗe take yasa ya ƙarasa shigowa sai yaga mamallakiyar restaurant ɗin ce da wannan yarinyar da ta ke kawo masa shayi ne, wacce ta faɗi ɗazu garin kawowa....

"Don Allah ALAJA ki yi hakuri ba zan sake ba, na yarda in na sake ki kore ni, amma yanzu ki taimaka min jinin ya tsaya"

"Ba zan taimaka miki ba, asarar nawa ki ka yi min, yau ba zan tausaya miki ba Bilqees sai dai ƙafarki ta ruɓe"

"Ki yi hakuri Maa tsautsayi ne kuma na yi miki alkawarin ba zan sake ba"

"Tsautsayi ko, za ki ga tsautsayi Bilqees in na riƙe kuɗin ki na wata biyu na biya asarar da ki ka janyo min"

"A'a ALAJA kada ki yi min haka, da kuɗin muka dogara, don Allah kada ki hanani albashina...

Nocking da suka ji ne yasa suka juya suna kallon kofar, duk da kofar a buɗe ta ke, hakan bai hana Dr Waahab Waseem KIRAWA neman izini ba. Shi bai cika shiga abin da bai shafe sa ba, amma kuma sai zuciyarsa ke raya masa ya shiga cikin wannan maganar ko ba komai saboda buƙatar shi yarinyar ta shiga wannan halin. 

"Me yake faruwa ne anan?"

Ya tambaya a hankali yana rarraba idanuwa a kansu, ya kalli Alaja wacce ta zuba masa idanuwa da mamakin ganin shigowar sa, bata taɓa tunanin zai wani zai iya shigowa ba, ballantana wannan mutumin, kasancewar customers basa shigowa wannan ɓangaren, Dr Waahab ganin jini da yake zuba a ƙafar Bilqees yasa ya iso inda ta ke ya rage tsawonsa, ya cire coat nasa ya ajiye kan seat tare da cewa Alaja 

"Bani tissue"

Da sauri ALAJA ta fito ta ɗauko tissue tare da miƙa masa, ya karɓa nan ya soma goge jinin, sai da ya tabbatar ya goge babu jini ko kaɗan sannan ya nemi Detol ta kawo ya goge ƙafar dashi don ya san ba lallai ne ya samu kayan aiki ba. Bilqees ta kura masa idanu tana kallon sa, da farko taji tsoro amma ganin cikin ƙwarewa ya tsaida mata jinin dake ƙafarta, yasa ta kawar da tsoron taji ɗan sauƙi da ya wanke ƙafar, ya mik'e tsaya, ya kalli Alaja tare da cewa 

"Riƙe albashi don ma'aikaci ya yi laifi hakan ba daidai bane, da ana yin haka ke ma ba za ki kai wannan matsayin ba"

Jikin Alaja ya yi sanye kenan ya ji abin da suke tattaunawa, ya ci gaba da cewa

"Kamar yadda ki ka ce abin ya faru ne cikin rashin sani, to bai dace ki riƙe mata albashi ba, ki bata hakkin ta"

"Yallaɓai daman so nake na sorata ta sabi da gaba"

"Zan biya asarar da ta yi miki, ki bata hakkin ta na aiki da ta yi miki"

Bilqees da tun da ya fara magana ta kafe shi da idanuwa tana kallon sa cike da mamaki, jin ALAJA ba zata riƙe albashinta ba yasa ta yi farin ciki, amma jin shi zai biya asarar da ta yi wa ALAJA yasa ta mamaki da al'ajabi, tun da ta ke ba a taɓa yi mata makamancin abin da wannan mutumin ya yi mata ba....

"Bani account details naki"

Ya faɗa a lokacin ya ɗauki coat nasa ya saka tare da ciro wayar, ganin bata motsa ba ya sa shi cewa

"Anan zan biya saboda bana so asan da hakan"

Ta ba shi, har zai fice kuma ya tsaya tare da tura mata kuɗaɗen da suka girgiza Alaja ta ce Bilqees ta basu waje, ta mik'e a hankali ta fice, Alaja tayi magana cikin farin ciki 

"Ai kuɗaɗen sun fi ƙarfin asarar da ta yi min"

"Ba damuwa ki yi amfani dasu amma kada ki riƙe mata albashi"

"Ba zan riƙe ba Yallaɓai to amma in kana neman abokiyar ɗebe kewa sai ta dinga zuwa hotel ɗin"

Cikin rashin fahimta ya ce

"Kamar yaya?"

"Yallaɓai sai ka huta da ita"

Wani kallo da ya watsawa Alaja shi sai da ta yi baya kamar zata faɗi, saboda kwarjinin sa, taja gajerun ƙafafunta da suke shirin kadata ta tsaya, da mamaki ta ke dubansa ko dai bai ji abin da ta ce bane, ta ce

"Yallaɓai ba sai ka biya ba, kawai ku wuce yanzu ma, in ma gobe ne shikenan"

"Dakata!"

DR Waahab ya faɗa cikin ɓacin rai da ɗaga murya, ba a taɓa yi masa irin wannan cin mutuncin ba, wai shi ya kwana da macen da ba halaliyarsa ba, ina never.....

ALAJA ganin ɓacin rai ƙarara akan fuskarsa yasa cikin sauri ta ce

"Ah ina nufin ta dinga taimaka maka, wajen gyara gyara da.....

"Zan tura miki kuɗin amma ki sani daga kaina kin daina wannan tunanin, ni ba irin maza marasa kamun kai bane da suke barin lahirar su saboda irin ku. Ni Abdulwahab Waseem KIRAWA sai nasa kin yi nadamar furta min wannan ƙazamin rayuwar"

ALAJA ta girgiza da wannan al'amari, wanene wannan mutumin? Ta yi masa tayin abin da ya gagari sauran Alhazawa amma shi ya ce baya so ko kyauta ne, amma jin furucinsa na cewa sai ta yi nadama yasa ta ji tsoron kada ya tona mata asiri, har zai yi magana kuma ya fice cikin ɓacin rai, ya shigo dining area ganin duk suna nishaɗi yasa ya saki ransa kada su fahimci wani abu, ya zauna da ƙyar yake iya cin abinci sai ya ji komai ya fice masa a kai, mamaki da takaici suka rufe shi, daman abin da ake aikatawa a wannan wajen cin abinci! Ya lumahe idanunsa na wasu lokuta sannan ya buɗe, ganin sun fara shirin tafiya yasa shima ya mik'e....

ALAJA kam ta bushe a tsaye, ta kasa barin wajen, bata taɓa jin irin wannan yanayin a tare da ita ba sai yau, to me yasa? Wanene wannan? Me yasa ya biya kuɗin asarar da ta yi? Ta fahimci yana da kirki, mutum ne me taimako amma me yasa yaƙi karɓan tayin da tayi masa? Da gaske ne shi saftatacce, kenan shi RUWA ne su kuma WUTA! Bata samu amsar tambayoyin ta ba har ta bar wajen ta koma ɗakinta....

Bilqees tana zaune a Corido, ta kurawa ƙafarta idanu tana kallon ƙafar kamar yau ne ta fara ganinta, mamakin mutumin da ya taimake ta tayi, ta ɓarar masa da shayin da yake ɓukata, bai ɗau zafi ba, bayyi mata faɗa ba kamar yadda sauran customers nasu suke yi, da sun yi kuskure su yi ta faɗa suna aibata restaurant ɗin amma shi har ya taimake ta, kuma ya biya kuɗin asarar da ta yi. Jin hayaniyar fitan su yasa ta mik'e tana ɗan kishingiɗa wa ta fito a lokacin babu sun fita daga dining area, ta iso reception nan ma sun fice, ta fito farfajiyar restaurant ta tadda suna ƙoƙarin shiga motar ta iso tare da cewa 

"Yallaɓai! Yallaɓai! Yallaɓai"

Kusan sau uku ta faɗa, ragowar da basu ƙarasa cikin motar ba suka tsaya, ganin ma'aikaciyar RESTAURANT ɗin ne yasa Dr Isma'il cewa

"Wane Yallaɓai?"

Ta nuna Dr Waahab da yatsa, ganin haka yasa sauran shige wa mota, Dr Waahab kamar ya shige motar yake ji amma kuma ya tsaya, ya tako zuwa inda take tsaye, ya sanya hannayensa cikin Aljihun coat nasa yana kallonta ta hasken fitilar dake wajen. Bilqees da kuzarinta ta fito amma tsayuwar da ta yi a gabansa yasa ta nemi kuzarin ta rasa, sabar kwarjinin da yake dashi....

"Mene ne?"

Shine abin da ya furta, tunowa da ya yi da abin da me restaurant ɗin ta faɗa masa akanta yasa yana ganinta ransa ya ɓaci, Bilqees jin muryar sa da tambayar ta da yayi yasa jikinta ya soma rawa, muryarta na rawa ta ce

"Ka yi hakuri"

"Hakuri! Akan menene?"

Da ƙyar ta haɗiyi yawun da ya tsaya mata a maƙoshi ta ce

"Na ɓata maka cin abincin daren ka"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Ai ya wuce"

"Na... Na... Gode?"

Ta sake faɗa muryar na rawa. 

"Saboda mene ne ki ke gode min?"

"Ka taimake ni"

"Saboda Allah nayi"

"Na sani, ba a taɓa yi min irin wannan ba shi yasa nazo na gode maka"

Ya kalleta sama da ƙasa, ya fahimci wannan salo ne na son ta shige masa jiki, wato ra'ayin sa take ja, babu tantama turota Oganniyar ta tayi....

Murmushin gefen laɓɓa ya yi, a nutse ya ce

"Don na taimake ki yau ba shi ne yake nufin zan din ga yi kullum ba, iya yau ne kawai, saboda haka sai ki maida hankali kan aiki ki san me ki ke yi, by then....

Ya ɗan yi shiru na wani lokaci sannan ya ci gaba da cewa

"Bana buƙatar mu sake tsayuwa irin wannan, kada ki sake tsaida ni cikin yan'uwana don wata buƙatar ki"

Ya juya da nufin barin wajen yaji sauƙar muryar tana cewa

"Kamar yadda ka taimake ni yau, ubangiji ya ci gaba da haskaka rayuwar ka, yasa ka cika duk wani muradin ka na alkhairi, ya saka maka da alkhairi, ya ci gaba da buɗa maka, ya yalwata arzikinka"

Chak ya tsaya, gaba ɗaya ta ɗaure masa jijiyoyin jikinsa ya ɗau wasu sakonni yana juya kalaman, sannan ya juyo, mamakin daga inda suke fitowa yake yi, zai yi magana ta yi saurin shigewa reception, ya sauke numfashi tare da furta a fili 

"Ameen!"

Ya dawo cikin mota, basu ɓata lokaci ba suka koma hotel.

Bilqees tana shigowa ta wuce ɓangaren Server's ta ɗauki jakarta, tana ƙoƙarin barin wajen sai ta hango abu a ajiye daga gefe, ta saka hannu ta ɗauka, wallet ne, da mamaki ta buɗe kuɗaɗen ne a ciki sai kuma ID card kusan uku guda ɗaya ta zaru tana kallo Dr Abdulwahab Waseem KIRAWA haka taga sunan, ta maimaita kusan sau uku sannan idanunta suka sauka kan hoton dake jikin ganin wannan mutumin ne da ya taimake ta, ta tuna ya cire coat nasa ya ajiye a daidai wannan wajen a lokacin da yake goge mata ciwon ta. Daman likita ne! ...

"Ke sai ki fito mu tafi gida"

Taji muryar Alaja don haka ta saka wallet ɗin cikin jakarta, ta yi sauri ta fito, ta tadda sauran a farfajiyar restaurant ɗin, suka fito bakin gate kusa da titi suka tsaya suka tari mashin suka hau ya kawo su gida...


DR Waahab Waseem KIRAWA suna isowa cikin hotel ya wuce masaukinsa yana shiga ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet ya sakarwa kansa shower ya jima a hakan sai da ya sami nutsuwa sannan ya ɗaura towel ya fito, ya shirya cikin jallabiya ruwan ƙasa ya shafe jikinsa da turare kamar yadda yake yi kamin ya kwanta, sannan ya haura kan bed ya mik'e tare da lumshe idanunsa duk abubuwan da suka faru dashi ɗazu suka dinga zuwar masa, musamman addu'ar da ma'aikaciyar RESTAURANT ta yi masa, ya jima yana tunani sannan bacci ya yi awun gaba da shi....

Bilqees tana kwance bayan tayi shirin kwanciya, sai da tasha pain relief sannan ta kwanta....

"Bilqees"

"Na'am Mama"

"Me yasa me ki a ƙafarki kamar kina ɗingisawa tun da kika dawo"

Kasancewar bata ɓoyewa mamarta komai ta ce

"Na taka glass ne"

"Glass! Garin yaya?"

"Uhm Mama yau ma na kuma yi wa ALAJA ɓarna"

"Na meye kenan?"

"Ina bakin da na baki labarin za ayi to ɗaya daga cikin ɓakin ne ya ce yana buƙatar shayi, garin kai masa ne na ɓarar har na taka glass na cups ɗin da suka fashe"

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Me yake damunki Bilqees kin san halin ALAJA yanzu sai ta ɗau zafi"

"Ai ta ce za ta riƙe albashi na, amma wannan mutumin ya biya"

"Ya biya? Wane ne shi?"

"Ko sunan sa ban sani ba, ya ce kada a riƙe min kuɗi na"

"Ikon Allah, amma Alaja bai dace ta karɓi kuɗi a hannunsa ba, bayan ta san baya da alaƙa damu"

"Shi kam ya biya"

"To an gode Allah ya ninka masa abin da ya bada, amma ke ma ki dinga mai da hankali"

"To Mama, ya ma yada wallet nasa na tsinta har da kuɗi a ciki"

"Ikon Allah to kina komawa gobe ki yi maza ki kai masa"

"Ai anan restaurant suke cin abinci safe da dare, da yazo zan ba shi"

"Yawwa sai ki adana waje me kyau"

"Tam kuma fa likita ne"

"Likita! Anan yake da zama kenan?"

"A'a ba anan bane bari na duba naga ɗan wacce ƙasa ne"

"To me za ki yi da ƙasar"

Bilqees ta miƙa hannu ta ɗauko jakar ta fiddo da wallet ɗin ta fiddo da duk ID card dake ciki, ta duba National ID card nasa taga Nigeria da sauri ta ce

"Ɗan Nigeria ne"

"Nigeria!"

Cewar Maman Bilqees, Bilqees ta duba na wajen aiki ta ce

"Lah kiga wani sunan gari wai BORNO"

Ta faɗa tana dariya, Mama ta ce

"BORNO!"

"Eh Mama sunan sa ba Abdulwahab was...



___________________

Ayi hakuri kwana biyu zazzaɓi ya hanani typing amma yanzu Alhamdulillah.

Na gode fan's da kira da kuma chat na yi mini fatan samun lafiya.


Ayi comments sannan ayi sharing fisabilillah