Chapter 20
by @smauta
Hannun manar ya kama gam kamar wanda za'a kwace masa ita,me kikeyi anan labe kike mana da jajayen idanuwanta ta kalle shi labe akan kakata kai kanka da ba hurumin ka ba ka shigo bare ni,kuma ni tunda nazo bazuyiman wannan bayanin ba sai kaine zaayima wannan bayanin,lumfawa yayi sannan ya kara kallon ta da kyau yace baki basu damar suyi maki bayanin ba kinzo kinata masu kuka kamar wadda akacemawa an sace kaka............
Ranka ya dade hakane wlh munyi munyi tayi shiru amma yarinyar nan ta tubure tunda ta iso kuka kawai takeyi takicin komai yasan za'a rina fada ma dayayi mata a gidan shi kin cin abincin tayi saida yunwa ta kurota,manar da kukanta tace na'am kinga yanzu dare yayi ko zamuje mu samu hotel in kwana gobe da safe zanzo sai muje kaduna tare kin yarda?
Make masa kafada tayi alamar a'a to fadaman ya kikeso ayi?mu tafi yanzu duk kansu suka zaro ido daya na dare fa saura minti sha biyar kiyi hakuri kinji baby girl gobe da sassafe dakaina zan dawo na dauke ki amma da sharadi daya sai kinci abinci🙄na koshi bakison zuwa wurin kaka?
Ina so to sai kinci abinci baban Ibrahim na tsaye yana kallon ikon Allah manar sai narkewa take ala dole shagwaba takeyi,to ai babu abinci a gidan inje in siyo maki? gyada kai kawai tayi alamar eh hannu yaba baban Ibrahim sukayi sallama ya nemi alfarma zaije hotel dinda zaya kwana ya samomata abinci yarinya ce kar ulcer ta kamata,hakane bakomai Allah ya dawo daku lafiya amin.........
Wani babban hotel suka samu anan suleja jakar kayanshi Idris yakai masa daki ya fito oga muje Idris jeka ka kwanta kawai zanje dakaina direct kitchen dinsu yaje an haɗa masa komai shi suke jira karba yayi ya saka mota ko minti 20 baiba ya karaso kofar gidan wayar idris dake hannunta ya kira ta dauka fito gani a waje kadai ya fada, maman Ibrahim na zaune ta zubama sarautar Allah ido tace Alhajin ne yazo?eh to muje in rakaki bakin soro nasan yanzu dai baban Ibrahim yayi bacci...........
Duk ruwa ne a kwance kofar gidan ta tsallako shi tazo har bakin motar hannu tasa a hankali ta budo motar sannan tashigo wani kamshin sa ne daya daki hancinta a take natsuwa ta ragaya a ranta,shurun shuru akai na tsawon wasu mintina kafin daga bisani ya fiddo mata abinci ta wutsiyar ido take kallon lafiyayyar shinkafar da coslow ga naman kaza a same, Bismillah daya ambata ta dawo da ita hayyacin ta hannun sa rike da cokali dab da bakinta.............
Kamar geliya ta bude bakin ta zuba mata abincin a hankali a hankali yake bata abincin saida takusa cinye shi tass sannan tace nakoshi makaleta kafada yayi shima irin nata naki wayon nan wannan guntun magen wa zaki barmashi?to kai bazaka ci ba?banacin abinci mai nauyi da dare manar meyasa?s takaice kawai yace mata girma..........
Fesss ta share abincin nan ya bata ruwa tana cikin sha wayar shi ta dauki ringing dagashi har ita dukkansu screen na wayar suka kalla,har wayar ta kusa tsinkewa bai dauka ba gefe guda ta kalla ka dauka ana kiranka fa baice komai ba hannu yasaka ya dauki wayar kasheta yayi gaba daya.........
Zan koma gida nagode, murmushi yayi ƙasan ranshi,karfe 7 ki shirya zanzo mu wuce kaduna wani makokon bakin ciki ya tasoma manar karkada kanta kawai tayi ko arzikin sallama bai samu ba haka ta fito tashige gidan maman Ibrahim, motar shi ya halba bai zame ko ina sai hotel jikin na dauke da gajia wanka da hutu kadai su yake bukata a yanzu............
Tun asuba manar da wankan ta dawo dakin maman Ibrahim karfe shidda na safe ta shude bakwai ta hau kan lokacin ta ba khalil ba labarin shi ga wayar idris dake hannunta itama ta mutu tunda aka fara ruwan nan suka dauke wutar lantarki ba'a maido masu ba, kamar tayi tsuntsuwa takeji kawai ta tafi ruwan kokon ma kasa sha tayi burinta daya a yanzu bai wuce taganta akan hanyar tafiya ba...........
Firgigi ya farka da salati dauke a bakin shi,wayar shi dake gefe ya jawo 8:40am number Idris ya lalubo switch off gabanshi ya fadi cillar da wayar yayi ya fada toilet gurguje ya fito ya shirya cikin wata dakekiyar shadda ash ya saka takalmi da hula ya feshe jikinshi da turare kayanshi ya ya haɗa komai ya fito dakin dake next dashi yayi knocking idris ya bude kofar cikin shirin shi tsaf barka da safia oga yawwa.........
Jakar shi ya karba check-out sukayi har bakin mota sannan ya kalli Idris ka koma Abuja akwai aikin da zakayiman kaida jude zan saka maka kudi a account dinka nima yau zan dawo abuja In Shaa Allah, Allah ya tsare hanya oga amin gudu yake tsalawa har Allah ya kawo shi kofar gidan su Ibrahim wani yaro yagani s kofar gidan shiga gidan nan kace ana sallama da manar...........
A bakin kofar shiga gidan yaron yace wai ance ana sallama da manar maman Ibrahim dake duke bakin murhu ne tace gatanan zuwa fito manar inaga shine yazo fa,bari kukan nan dama nace maki kila wani abun ya tsaida shi ga malam sun fita kuma da yace tare zasuje can kadunar, manar dai ta cika tai fammmmm sallama tayi ma maman Ibrahim ta fito..........
Yana jingine bakin motar yaga fitowar ta fuskar nan murtuk ba alamar murmushi a tareda ita shima baya juya yashiga motar shiga tayi ya tada motar saida ya dauki hanya sosai ta tabbatar da tafiyar za'ayi sannan tace ina kwana banza yayi da ita ya cigaba da ba motar shi wuta tafiya suke kamar bazasu kai ba ya samu wani gari ya parker gaban wani restaurant order abinci yayi masu sannan ya fito........
Ledar abincin ya dora mata akan cinya ya kunna motar hannu ta saka ta bude sandwich ne da sauran tarkacen snacks faraci tayi yana kallon ta ta gefen ido yadda take cin abincin nata hankali a kwance gab da 11 na safe suka karaso kaduna wani farin cikin rahama ya mamaye zuciyar ta koba komai yau zatayi tozali da farin cikin ta...........
Rage gudun motar yayi yanata bin hanya har suka iso babban asibiti dake anan cikin kadunar yana cikin gyara parking wayar shi ta dauki tsuwwa kallon wayar tayi number jiya ce dai bashida niyyar daukar wayar yauma hannu tasa da sauri ta daga kiran speaker ta maida wayar muryar mace ta fito rangadau kallon kallo sukayi ma juna........
Hello bakaji na ne? kara matsar masa tayi da wayar wurin bakin shi alamar yayi magana, hannu ya saka ya amsa wayar kit ya latse kiran ta waiga gefe a kufule idonta yayo mata zooming dede da kawu labaran suna tafe ana surutu da sauri tace wlh gasucan bude ni bude ni.....