BABAN KAWATA

Chapter 21

by @smauta

Kawu labaran kawu labaran, labaran kamar kiranka akeyi fa waka sani a kaduna badai ni ba kawu labaran dukkansu suka juyo dede tace manaraaaaaaa😳😳😳😳kece????



Da gudu manar tayo kan dede ina kaka dan Allah tana ina taji sauki kawu labaran yace ke dan kaniyar ki ina kika shiga anata nemanki kin tadama kowa hankali ni shiyasa dama da akace za'a kaiki kasar waje ban yarda ba wallahi dan bata tarbiyya sukeyi ke har kin san kimasu dede wayau ki gudu kiki dawowa yau koni ko ke cikin asibitin nan bari kiga...........





Daga bayan manar kawu labaran yaji ance a'a malam ana uzuri mana irin na rayuwa ina kakar take?kai kace kawu labaran yasan khalil yace yallabai sannu ko kaikuma daga ina manar ya nuna mashi da hannu tare muke ,sai lokacin dede tace tare kuke kamar yaya wannan diyar fa bacewa tayi mun kusa sati ana nemanta sanadin haka ne ma ciwon yayarmu ya tsananta sosai,manar tayi karaf tace dede shine wanda ya tsince ni muje wurin kaka, hannunta na cikin na dede suka dumfari dogon dakin................





Kakace kwance akan gado an saka mata robar cin abinci idonta rufe tana bacci,da gudu manar tayo gadon kawu labaran ya riko ta ke karki fadama yaya mana gatanan da ranta bata mutu ba kuka manar keyi wiwiwi dede na aikin lallashi shi ko gogan tsaye yake kyam gefen gadon yana kallon kaka tausayin tsohuwar ya lullube shi sosai...........




Ba abinda yake tunawa a yanzu sai iyayenshi haka yayi jinyar su har mai rabawa ta raba su, tausayin kaka da manar ya kara zama cikin ranshi,kawu labaran ya kalla bismillah to to ranka ya dade sallama yayi ma dede har sunkai kofa dede tace kawu na'am dan zo kaji,bari dai in dawo a'a kazo dan Allah tsakanin dede da kawu labaran sako da sako suke basa jituwa tunda sukazo asibitin nan cikin saida hali suke kowa ya sansu🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣






Kaga mutumin nan bamu sanshi ba nasanka da shegen son abun duniya kaje ka saki baki ka gaya mashi komi irin wannan masu kudin ba abun yarda ba ne yanzu kaji anyi tsafi da mutum abunka da mutumin kauye yace ke dede tsafi kuma yanzu wannan din matsafi ne,dede ce ta buga salati tana sallallami kaini karka jaman cewa nayi ba abin yarda bane ta ina nace tsafi yake............




Sai lokacin manar ta dago tace dede mutumin kirki bamai cutarwa bane,nima shine ya taimakeni ta kwashe labarin tun daga zuwanta Abuja har yau kawu labaran yace kashhh kinga duk wanda ya gado zuciya irin taki dede yayi asara a rayuwarki idan baki hada tuggu da munafurci ba baki samun cikakken kwanciyar hankali.........




Makira kinganshi akwai alamar kuɗi kin kirani nan kuf kuf ki kitsaman kilbibi ki shiga tai tayinki,yo kawu daga taimako ai halinka nasani yana iya shaka maka kudi wallahi in nemeka kaura wambai kabar ni da marar lafiya kaikuma ka haya tudu ka kara aure da kudin gayama wanda baisan halin ka ba 😹.............





Ki fita idona dede in rufe inji ni ba yayan ki bane amma da wannan shegen bakin naki kamar an bugo karya ta taga kisani gaba kinaman iskanci Allah yasa ya bada kudin ma bazaa bada ba,kawu labaran dan Allah kuyi hakuri kubar fadan nan kaka fa batada lafiya,ke yarinya mi kikasani uwarki ce zataiman alkunku na mata bari inje naji shikuma dami yazo............




Dede ce ta dafe kai sannan tace manar inji dai wannan mutumin taimakokin kawai yayi baice yana sonki ba gaban ta ne ya fadi da kyar tace eh dede, to Alhamdulillahi dan kuwa muddin ya kebe da labaran Alkur'anin Allah labarin da dana yanzu sai ya gayamashi kindai san halin labaran idon shi idon abun duniya duwainiyar shi har kyarma take🤣🤣kai dede easy yayanki ne fa,manar ta lumfasa kawai sannan tace Allah kyauta dan duk abinda dede ta fada kan kawu labaran ba ragi ba ƙari komai zai iya aikatawa😹😹






Gaban reception kawu labaran ya samu khalil yazo yanata fada kan abinda dede tayi mashi wuri suka zauna a karo na biyu kenan da khalil ya kara gaishe da kawu labaran duk da bawani girman shi yayi sosai amma ya girmama shi,kawu labaran ne ya muskuta yace yanzu yarinyar nan manara take gayamana kaine ka ceceta Alhaji mungode mungode sosai wallahi munan hankali duk ya tashi munsa barayin dajin nan ne sukayi garkuwa da ita wlh tashin hankalin da muka shiga ne yasa ka ganmu nan asibiti yayar tamu ba lafiya dama wannan mummunan labari ya riske mu shine fa ciwo ya tsananta.............





Surutun kawu ya isheshi ya lumfasa kawai me akeyi mata a nan din yanzu?bakomai allura ce sukace za'ayi mata wallahi wallahi Alhaji ba kudin drip ne kawai nan suke zazzaga mata wani fegi ne ma na kanwata dede ta bada jingina dasune nan muketa jalaulautawa,to kawu wane likita ne ke dubata?????




Bai kuwa dade da barin wurinta ba yana Ofishin shi,to kawu naga kamar kaine babba kwarai nine kuwa ranka ya dade murmushi khalil yayi yace sunana khalil ahhh kaci babban suna khalilul rahaman,inaso nima dan Allah kusani cikin samun ladar kakar inaso a maida ta Abuja a nema mata lafiya acan kamar can zaifi nake gani,khalilu Abuja nan ma mun kasa balle Abuja kabarmu nan din dai,a'a bance zaka bayar da komai ba yardar ku nake nema kawai...........





Maganar dede tadawo ma kawu labaran yace to khalilu bani kadai keda hakki kan yaya ba akwai kanwata dede kaiman lamuni inje yanzu in fada mata duk hukuncin da muka yanke zakajini bakomai kawu nima bari in fita wajen asibitin nan zan samu abinda zanci lokacin da zan dawo sai inji kome kuka yanke Allah ya bata lafiya yasa zakkar jiki ne amin............





Sunan zaune gaban kaka kawu labaran ya taho kamar zai tashi sama harara dede ta balla mashi minene kuma taso taso ba inda zanje ayita nan inaji gayamata yadda sukayi da khalil yayi tace kaime kace mashi?bance komi ba nace ya bari in shawar ceki to nidai gaskiya ban yarda ba ya bamusan mutum ba yace zai daukemu har Abuja mu bishi muyi hakuri kawai abinda ke garemu muyi amfani dashi ai cuta ba mutuwa bace amma gaskiya labaran ban fa yarda ba a dauki yaya har Abuja ba,kayya kinji matsalolin ki dede har damu za'a tafi fa ba ita kadai ba sai muyi zaune ga sauki Allah ya aiko mana to nidai bazanje ba kuma itama yayar bazaa dauke ta saidai ka bishi ku tafi inyi ubanmi idan na bishi ahh labaran a auna taka zuciyar mana daga ganin mutum yanzu duk kabi ka rikice zaka fara saida halin naka............




Manar ce ta kalli dede taga bilhakki dagske take,dede mutumin nan fa nasanshi da dadewa ba abinda zai faru sai alheri kiyi hakuri dede bamu zaki duba ba ita mai ciwon zaki duba dan Allah karki bari damar nan ta wuce,gallamata harara tayi ke ina kika sanshi da har kikasan bazai cutar damu ba daga taimakon naki,zubewa kasa tayi ta kamo hannun dede wallahi Allah dagske nike dede khalil ne ya dawo ya samu manar tsugunne gaban dede,kawu labaran yace ahhh harka dawo bismillah ke bashi kujerar can mana ya zauna,koda ya zauna dede kara tsuke fuskar ta tayi kamm to khalilu yar uwata dai tace bata yarda ba nikuma banida ikon barin a dauki yaya ni kadai.............




Mama ya kira sunan dede kallon shi tayi na'am kasa ya sauko yace dan Allah ki dubi girman Allah ki bari nima in samu ladar jinyar nan,ki duba ya nuna mata manar dake zaune kan gado tana kuka makomarta zaki duba bani ba,farin cikin ta yana gaba sannan lafiyar kaka itace ginshiki a gareta tunda na taimaketa nasan akwai wani bond mai karfi tsakanin su bance baza ku iya kulawa da ita ba anan a'a can dinne keda kwararrun likitoci zuwa É—aya a gano meke damunta kar ku zauna nan cuta daban magani daban idan ta rasa rayuwar ta mama zaki iya shiga cikin wanda manar fa zata ce kece sila dan Allah ki duba lamarin nan wallahi banzo nan dan in cuceku ba saidai kawai in taimaka maku..........




Zuciyar dede ta karaya ta kalli manar din da har lokacin kuka takeyi manara na'am goge hawayen naki na yarda Allah yasa yaya ta dawo da kafarta, mungode sosai da kulawar ka garemu sai lokacin ya koma kan kujerar shima ya zauna sosai nine da godia mama kawu inane office din likitan?zamu iya zuwa ko ?????????






       ABUJA NIGERIA......