Page 6.
by @zeeykumurya
*BARA A KUFAI*
*Zeey Kumurya*
6.
*BRIGHT PENS*
YOTA ID 003
Bismillahir rahmanir rahim.
Ɗiban ruwan da Saudat ta yi da aikin da Mama ta dinga tula mata ya saka washegari ta tashi da ciwon baya, tsabar gajiya da kwanciyar da ba ta yi da wuri ba sai da ta makara a sallar asuba, da ƙyar ta iya daurewa ta yi azkar ta sake komawa bacci.
Cikin baccin ta ji wani irin sanyi ya ratsa fuskarta zuwa wuyanta, a firgice ta tashi zaune tana ambaton sunan Allah. Yaya Mardiyya ta gani riƙe da kofin ruwa a hannunta tana huci da harararta, ruwan da yake fuskarta ta goge sannan ta dube ta a raunane ta ce. "Yanzu Yaya ba za ki iya tashi na ba sai dai ki watsa mini ruwan sanyi?"
"Na watsa ɗin, don ubanki kin san akwai abubuwa da yawa a gidan nan amma shi ne za ki zo kika kwanta bacci, kowa ya tashi yana abin da ya dace amma ban da ke hamshaƙiya, to tashi ki karɓo markaɗen waina, tun ɗazu mutane suna jin yunwa an rasa mai karɓowa." Ba ta ce komai ba ta miƙe ta gyara hijabin jikinta, wani irin sarawa ta ji kanta ya yi mata, amma a haka ta fita tana taune baki ta ɗauko markaɗen, ga ciwon gaɓoɓi da take jin shi har cikin ƙashinta.
Tun daga wannan farkawar ta fara bautuwa, ita ce aike da ɗauko abubuwa tana miƙa wa masu girki, ita ce rainon Affan da Afrah ƴar gidan Yaya Mardiyya, hakan ya sa duk ta ficiccike ta ƙara dagulewa, munin da ake ganin ta da shi ya ƙara fitowa, ga tsangwama daga gurin ƴan'uwan Mama, a gurin familyn Abba kawai take samun sauƙi, hakan ya sa take fakar ido ta shiga toilet ta ci kuka ta ƙoshi, kukan rashin Abbanta, da a yanzu take jin wata irin kewar shi.
Da yamma aka fara hada-hadar tafiya Mother's event, ta ci sa'a an ba ta kati guda ɗaya kacal nata, cikin kayan fitar bikin da Mama ta yi mata ta ɗauki lace ɗaya ta saka, ta yi ɗaurinta daidai ita ta yafa babban mayafi akai, duk da girmansa kuma ya rufe mata ko'ina amma sai da ta ji wani iri, ta riga ta saba da saka hijabinta, ta fi sakewa a cikinsa. Ta ɗauki jakarta kalar mayafin ta zura wayarta keypad a ciki da pass da ƴan canjinta, ba ta fita ba saboda jama'a ta yi zamanta a ɗakin, tana jira sai an ragu, don mutum ce ita da ba ta son mutane kwata-kwata, wanda wasu suke ganin duhun kai ne da ƙauyanci, ita kuma haka kawai ta tsinci kanta Allah ya yi ta, idan ta shiga cikin taro duk sai ta takura musamman idan ana kallon ta. Azkar ɗin yamma da ba ta samu ta yi ba saboda hidima ta zauna tana yi. Kamar yaƙi haka ta jiyo muryar Yaya Mardiyya tana ta ƙwala mata kira, gabanta ne ya faɗi, amma haka ta daure ta leƙa ta window tana faɗin. "Ga ni nan Yaya." A fusace Yaya Mardiyyan ta ce. "Dalla Malama fito, ki zo ɗakin Mama tana neman ki." Daga haka ta juya ta koma, Saudat ta bi bayanta da kallo, ta sha kwalliya cikin wani tsadadden lace mai kyau da ya dace da kyakkyawan ɗinki, ga make up an yi mata, farar fatarta ta sha ja da baƙin lalle, ta yi kyau sosai da sosai. Sai da ta ɓace wa idanun Saudat sannan ta sauke numfashi jiki a sanyaye ta fito ta bi bayanta, ita duk a zatonta kaya iri ɗaya za su saka dukansu, tunda ta ga Mama ce ta faɗa mata ranar da za ta saka kowanne kaya lokacin da ta ba ta, a ɗarare take ratsa mutane har ta ƙarasa ɗakin Mama.
"Kina fitar da ni kunya Mardiyya, kina kankaro mini mutunci yadda ya kamata, haka nake son na ga kun fito fes shar da ku yadda babu mai raina ku, na san duk taƙamar dangin matar Zubair ba su isa sun kere ku a kyau ba."
Abin da kunnuwanta suka fara jiyowa mata kenan tare da sakin shewarsu. Kamar wadda aka yi wa duka haka ta yi sallama ta shiga, ba su kula ta ba har ta samu guri ta rakuɓe kamar baƙuwa tana kallon Shamsiyya da take faɗin. "Aiko jiyan ma ba su fi mu da komai ba Mama, na san dai kayan jikinsu sun fi namu tsada amma ba su fi mu yin kyau ba." Mama ta ce. "Yau ma hakan ce za ta kasance in sha Allah, wannan uban lace ɗin naku mai tsada na san ba su isa sun saka wanda ya fi shi ba, ai abun zuciya ce ba dukiya ba, ku yi maza ku ƙarasa ku tafi, tun ɗazu Salma take yo waya an gama yi mata kwalliya, na san idan mutane suka ji kun tafi za su fi ba da himmar tafiya, Allah ya yi muku albarka ya ci gaba da rufa muku asiri kuna ba wa maƙiya assignment, yadda na ji jiya ana labarin bikin nan a social media da yaba kyawun da kuka yi wallahi ba ƙaramin farinciki na yi ba, da ma ni burina kenan a rayuwa, na yi abu duniya ta yaba a yi ta zancensa."
"Aiko yau ma sai ya fi na jiya in sha Allah, don wannan kayan naki ba ƙaramin assignment za ki bayar ba, ni na faɗa miki Mama za ki sha mamakin yadda za a yi ta yawo da hotunanki ana ga Maman amarya ga Maman Ango."
Murmushi Mama ta yi cikin alfahari ta ce. "Bikin 'ya'ya biyu idan ban baza capacity ba ai ba kanta" Da azarɓaɓi Shamsiyya ta ce. "Ƙwarai Mamanmu maganin kukanmu."
Sai a lokacin Mama ta dubi Saudat, take fara'ar fuskarta ta ɗauke, ta ja tsaki a kufule ta ce. "Don Allah ku taya ni ganin wannan shashashar? Ke me ya sa wai duk yadda aka so a yi abin arziƙi da ke sai kin kauce ne? Mene ne wannan? Gidan mutuwa za ki ko maƙabarta? To sauke mayafin nan kafaɗa don ubanki, bagidajiyar banza kawai." Da sauri Saudat ta mayar da mayafin kafaɗa. Shamsiyya ta kwashe da dariyar izgilanci, tana dariyar ta ce. "To ai gara ma ta bar shi a kan wallahi , ji wani ɗauri fa don Allah kamar mai shirin ɗaukar buhun siminti, gaskiya Yaya Mardiyya ba ƙaramin taimakonmu kika yi ba da kika ce kar mu yi kaya iri ɗaya da ita." A yangance Yaya Mardiyya ta ce. "Ban shirya kwasar baƙinciki ba ne, Familyn Darling za su zo, suna ganin kayanmu iri ɗaya za su gane ƙanwata ce, to wa ya aike ni bare ya ce na daɗe? Yadda ban bari sun san ta ba har yanzu to a yi ta zama a haka." Shamsiyya ta ce. "Wallahi fa, ni dai sun sassan ta wasu har maƙotana ma, to ba yadda zan yi tunda ba a sauyawa tuwo suna." Mama ta ce. "Haƙuri za mu ci gaba da yi, tunda hannunka ba ya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar."
Idanun Saudat cike da ƙwalla ta yi ƙasa da kanta, furucin Mama na yawo a cikin kanta yana dukan zuciyarta, ita ba wani mummunan abu take aikatawa ba amma ta zama abar ɓoyewa a cikin ahalinta, ta zama abar yin haƙuri da ita, da bayan hannunta ta share hawayen da ya zubo mata, duk yadda ta so ta saba da wannan rayuwar amma ta kasa, ba ta da wani buri da mafarki a duniya sai na ganin Mama ta ja ta a jiki, ta so ta kamar sauran ƴan'uwanta amma abu ya ci tura, duk abin da ta saka ta ba ta yi mata musu, ba ta jayayya da ita, amma ba za ta iya tuna ranar da Mama ta saka mata albarka ba, sai dai ta ji tana saka wa su Yaya Mardiyya.
Aikin haɗa kayan su Shamsiyya da ƴaƴansu Mama ta saka ta, ta ajiye komai a inda ya dace ta rufe mata ɗakin. A motar Yaya Mardiyya suka tafi, Afrah da Affan duk suna kan cinyarta, suna shiga cikin hall ɗin ta nemi kujera ta zauna, su kuwa ba zama, suna ta yawo suna gaisawa da mutane tare da ɗaukar hotuna. Da amarya Salma ta zo suka je suka shigo da ita, haka aka ci gaba da gudanar da shagalin ranar, su Shamsiyya ana ta rawar kai da zuba liƙi, sai kirarin yayyan Amarya kuma ƙannen Ango MC take kwarara musu.
Duk wanda ya ga Saudat suka gaisa sai ya yi mata ciwon bakin zaman da ta yi.
"Ke ga ƴan'uwanki suna can suna warkajaminsu amma ke kin zo nan kin zauna."
"Oh! Sauda wai sai yaushe za ki waye ne? Yanzu bikin ƙanwar taki ma ba za ki saki jiki a yi buduri da ke ba?"
"Wai ke Saudat wacce iri ce ne ke? Anya kuwa kina da cikakkiyar lafiya? Wannan duhun kan ya yi yawa, ya kamata a bincike ki, don abubuwan da kike ko a zamanin kakanni ba a yi kamar su ba."
Ire-iren maganganun mutane kenan a kanta, hakan ya sa ta daure duk yadda take ji na rashin son shiga mutane ta ba wa wasu cousin ɗinta su Affan ta nufi inda su Yaya Mardiyya suke hotuna tare da Mama da ƙawayenta, da murmushi ta ƙarasa bayan ta gyara mayafin jikinta a ƙoƙarinta na burge su, Mama da Yaya Mardiyya da Yaya Zubair da Shamsiyya da Salma da angonta da amaryar Yaya Zubair ta ga sun jeru, da sauri ta matsa ita ma ta tsaya a kusa da Shamsiyya fahimtar hoton iya na ƴan gida ne.
Kamar wadda aka tsikara da wuta haka Yaya Mardiyya ta zabura ta ce wa masu ɗaukar hoton su dakata, a tsawace ta dubi Saudat ta ce. "Ɗan fita, idan aka gama yi mana wannan sai ki shigo." Yaya Zubair yana harararta ya ce. "Dalla koma gefe, kin wani nadakamo ɗauri kin taho zungwi-zungwi." Kamar kazar da aka watsawa ruwan zafi haka ta ja ƙafafuwanta da suka yi mata sanyi ƙalau ta koma gefe ta tsaya, wata irin kunya ce ta kama ta kamar za ta nutse, ga idon mutane duk ya yo kanta, tana kallon Mama ta bi ta da wani irin kallo tare da girgiza kai cikin takaici.
"Rabu da su, zo mu je ni a yi mana a wayata." Cewar wata maƙociyarsu da suka yi makaranta tare da Yaya Mardiyya tana kama hannunta.
Ita dai Saudat bin ta kawai take amma jin ta take kamar ana yawo da ita a kan iska, kanta a ƙasa ta kasa ɗago da shi, idanunta ya cika taf da hawaye, har aka yi musu hoton da Rasheeda aka gama ba ta san me ake ba, saboda baƙincikin da yake danƙare a cikin ranta, wannan kyarar da dizga ta ko a gaban waye ya saka ba ta shiga cikin ƴan'uwan nata a irin wannan gaɓar, amma mutane ba sa ganewa, sai su yi ta ganin kamar ita ce take ware kanta.
"Kar ki yi kuka Saudat, kin ga taro ne kar hankalin mutane ya dawo kanki, ki daure ki yi haƙuri watarana sai labari, na ɗauka ai zuwa yanzu kin saba da halinsu Mardiyya."
Kamar wadda aka tunzura haka ta kece da wani irin kuka mara sauti, jikinta ya kama tsuma, ta ƙanƙame hannun Rasheeda a cikin nata. Cikin tausayawa Rasheeda ta rungume ta, ta ce. "Ki yi shiru don Allah, kar kanki ya yi ciwo." Da ƙyar ta lallaɓa ta ta yi shiru, ita kam ko kaɗan ba ta ganin munin Saudat da mutane suke faɗa, hasalima kalar fatarta ba ƙaramin kyau take yi mata, ga ta da nagartattun halaye, yadda su Mardiyya suke tsangwamar ta ba ƙaramin mamaki yake ba ta ba, don ita ba ta ga aibu akan saka hijab da rashin gayu da Saudat ta zaɓa wa rayuwarta ba, a kullum tana faɗa musu kowa da yadda Allah ya yi shi, don su suna da wayewa sosai bai kamata su dinga yi mata haka ba.
Har aka gama cin bikin ranar aka gama zuciyar Saudat ba ta daina yi mata ƙuna ba, washegari ranar wuni tun safe aka tura ta shagon mai ɗinki karɓowa su Shamsiyya kayan da za su saka a ranar, tun a lokacin kuma ta fahimci ranar ma sun ware ta ba kaya iri ɗaya za su saka ba. Sai bayan Azhar ta dawo ta kawo musu, ta samu abinci ta ci ta yi sallah ta sulale zuwa gidansu ƙawarta Hasina, domin ta tuna mata ta shirya da wuri su tafi tare, wataƙila idan da Hasinan ta fi jin daɗin event ɗin tunda za ta samu ƙawar hira, kati ɗaya da ma aka ba ta ta gayyaci wani, shi ne ta ba wa Hasinan.
Hasinah tana aiki tana yi wa Amma mita da ƙunƙuni, ita kuma tana tausar ta da saka mata albarka Saudat ta yi sallama a gidan, sai ta ji sun burge ta, ta ji dama ita ce suke haka da mahaifiyarta, don Hasinah kamar wata ƙaramar yarinya sai zuba taɓara take.
Da fara'a Amma ta tarɓe ta tana faɗin. "A'a'a'a, ƴan biki ne yau a gidan namu? Ai ɗazu nake cikiyarki Hasinah ta ce kuna ta shan ebem shi ya sa kwana biyu ba ki leƙo mu ba." Fuska a keɓe Hasina ta yi caraf ta ce. "Gaskiya Amma kina bayar da ni wallahi, tun ɗazu na ce ki je ki canza zanin nan amma ba ki canza ba, ga shi nan har ƙawata ta zo ta same ki a haka, yanzu kuma kin ƙara kwafsawa kin ce wai ebem, fisabilillahi me ya haɗa event da ebem? Da wata ce ba Saudat ɗin ba ma haka za ki ba ni kunya kenan? Kowa ya san Uwata ba ta yi boko ba." Murmushi Amma ta yi ta ce. "Hasina kenan, Allah ya shirya mini ke, to ya ake cewa ai sai ki gyara mini." Cuna baki ta yi ba ta ce komai ba, Amma ta miƙa wa Saudat kujera, ta karɓa da sauri cikin risinawa tare da yi mata godiya, ɗaki Amma ta nufa tana faɗin bari ta kawo mata ruwa. Fuska babu walwala Saudat ta dubi Hasina ta ce. "Ki daina abin da kike yi Hasina ba shi da kyau, Amma mahaifiyarki ce ba, bai kamata ki dinga damuwa da duk yadda za a zo a gan ta ba tunda ba wani mugun abun aka ga tana yi ba." A kufule Hasina ta ce. "Kya faɗi haka mana tunda ku Mamanku ƴar gayu ce, ba kuma ke ce za a zo gidanku a ka gan ta kamar almajira ba."
"Kai Hasina! Amman ce kamar alamjira?"
"Ai kin ji abin da na ce."
"To Uwa uwa ce dai ko yaya take, kuma wallahi Amma Uwa ce da kowanne ɗa zai so ya zo a ɗanta, ba ruwanta da duniya, ga ibada ga rashin shiga abin da bai dame ta ba, ki duba yadda take wuni a tsaye duk dan ta inganta rayuwarku, burinta ku samu nagartacciyar rayuwa kuma kar ku yi kukan rashin komai."
Baki Hasina ta taɓe ta ce. "Na ji kar ki ishe ni uwar wa'azi, ni mantawa ma na yi ashe duk jirgi ɗaya ne ya kwaso ku."
Haka suke kullum idan suka haɗu sai sun haura sun sauko saboda bambancin halayya da suke da ita, a ƙarshe sai Saudat ta yi shiru ta ƙyale Hasina, wadda tun farko take ɗaukar komai da zafi, saɓanin Saudat da gaskiya kawai take faɗa mata cikin tausasa harshe. A islamiyya suka haɗu ajinsu ɗaya, ita Hasina tana ƙawance da Saudat ne saboda ta ga suna da rufin asiri, Islamiyyar kuma yawanci ƴaƴan masu da shi ne a cikinta, to sun raina ajinta ba sa kula ta, shi ya sa ta riƙe Saudat ɗin, ko ba komai tana zuwa gidansu ta samu background ta yi hotuna. Ita kuma Saudat da ma duk inda ta je ba ta da farinjini, to islamiyyar ma haka ne, kowa kyarar ta yake, sai Hasinan ce kawai take kula ta, har suka yi sauka kuma ƙawancen nasu bai watse ba sun ci gaba.
Da za ta tafi Hasina ta yi mata rakiya, a hanya sun tsallaka rukunin masu kuɗi kafin su ƙarasa layinsu Saudat suka zo ƙofar wani danƙareren gida, baki a washe Hasina ta ce. "Ji gida har gida, gaskiya masu kuɗi sun ji daɗi, su ci mai kyau su sha mai kyau su kwanta a mai kyau, gida biyu ne fa nan ake haɗe shi, masu gidan ba su daɗe da tarewa ba, an ce mai gidan babban ɗan siyasa ne." Kallon ta kawai Saudat ta yi, jikinta har rawa yake wajen zuba bayani.
"Da za a bar mu wallahi sai na shiga ciki na ƙara kashe kwarkwatar idona, don na san cikin ma ba ƙaramin haɗuwa zai yi ba, jibi fa hawa uku ne, wai! Aljannar duniya..."
Fafaro wata mota da aka yi aka shigo layin a guje kamar za ta kwashe su ya katse wa Hasina zubar da take ba shiri, a rikice suka kauce Saudat na furta. "Subhanallah! Innalillahi!" Ganin a ƙofar gidan nan motar ta tsaya ya saka Hasina faɗin. "Ah dole koma waye ya yi haka? Wannan daula da kuke ciki ai dole ku ci duniyarku da tsinke, Allah dai ya nuna mini ranar da zan shiga wannan gidan, dole ma na yi ƙawa a cikinsa ko ta halin ƙaƙa." Guntun murmushi Saudat ta yi ta ce. "Ki ce idan alkhairi."
"To da da sharri na ce? Uwar iya da ba a iya miki."
"Allah ya ba ki haƙuri."
Saudat ta faɗa cikin son gajarta zancen.
Tare suka ce gurin bikin kamar yadda Saudat ta so, yau ma neman guri ta yi ta zauna ba ta yi azarɓaɓin komai ba gudun kar su dizga ta kamar jiya, Haseena ce dai tana daga gaba-gaba tana aikin yin hotuna da videos, da ta koma gida kuwa har sai da Amma ta yi bacci ta bar ta saboda yadda take ta labarin haɗuwar event ɗin da abubuwan da aka gudanar, ta saka status ya fi 20 kamar bikin na gidansu ne.
Washegari aka yi dinner, ankon da ƙawayen amarya da ƴan'uwa suka yi shi aka yi wa Saudat ta saka, su kuma su Yaya Mardiyya da Shamsiyya suka yi nasu daban, an yi dinner ta gani ta faɗa an ɓarar da Naira.
Ranar ɗaurin aure tun kafin asuba da ta tashi ba ta koma ba, sai da aka gama duk wani aikin abinci sannan ta yi wanka wajen shaɗaya da rabi. Ta shirya cikin shadda pich colour, ta yi ɗaurinta simple ta yafa mayafi. Tana kallo ana ta hotuna amma ko tunkarar gurin ba ta yi ba, don yau ta tashi da farinciki saboda biki ya zo ƙarshe, za ta samu ta huta kuma su Yaya Mardiyya za su koma gidajensu, Yaya Zubair da Salma za su tare a gidajensu su ma, gidan zai koma daga ita sai Mama, ta san ko yaya ne za ta samu salama tunda uban hantara da kyarar ta ya bar gidan.
Parloun da Abbansu yake saukar baƙi kafin ya rasu Mama ta aike ta kai wa wasu baƙi abinci.
"Ki yi abu da jiki Da'alla, ki yi sauri ki miƙa musu, ƴaƴan Baba Gali ne, ki zuba musu komai ishashshe ki saka nama sosai."
Abin da Maman take ta maimaita mata kenan, ta san kuma dalili, saboda mahaifinsu yana da kuɗi ne, su ma duk sun girma sun tara nasu arziƙin.
Da takatsantsan sosai take tafiya saboda nauyin kayan hannunta da ta jera a kan tire, a bakin ƙofar parloun ta tsaya ta yi sallama, ba ta san an amsa ba ko ba a amsa ba saboda a cike yake da matasan maza, suna ta hayaniya ana hira cikin raha. Tana sa kai za ta shiga ta ji an fesa mata hayaƙi a fuska, da sauri ta kawar da kanta don ta tsani warin taba, amma kamar da gayya ta ji an ƙara bula mata shi, duk yadda ta so ta dire tiren a ƙasa amma ya faskara, saboda ƙwarewar da ta yi ta fara tari, ba ta san ya aka yi ba sai jin ƙarar faɗuwar fulasai da plates ɗin da ta haɗo da su ta ji a ƙasa.
*#Zeey Kumurya*
*#****