SAUTIN KARSHE

Chapter 26

by @amanarcool323

SAUTIN ƘARSHE

BY AMANARCOOL

YOTA/021

Under Yota's Amazing Pens 

Book 1 

Page 26


Tsayuwa ta yi a gurin, ta saki baki tana bin kayan da kallo cikin mamakin waye wannan ya aiko musu da waɗannan kaya haka, cikin natsuwa Aliyu ya fito daga ɗaki, ya kalli ƙofar ɗakin Inna, wani abu mai zafi ya ji ya soki zuciyarsa, ya tuna yadda ya ji Ma'u na yunƙurin amai. Dubansa ya mayar ga kayan, sai da ya ƙare musu kallo sannan ya ɗago da kansa ya kalli Inna ya ce "Waɗannan kayan fa daga ina?" 

Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Yanzun nan yara suka shiga da su wai in ji wani ya ce a kawo sadaka ce." Aliyu ya ƙara kallon kayan da kyau, ya ce "Inna kuma sai ki karɓa ba tare da kin san ko waye ba?" Cikin damuwa ta ce "Gadanga ai ba su ma tsaya suka jin abin da zan zance ba suka bar gidan." Shiru ya yi bai ce komai ba, ya taka a hankali ya fita ƙofar gidan. Wani maƙocinsu ya gani sai murna yake yi yana washe baki. Mutumin na ganin Aliyu ya nufo shi yana faɗin "Aliyu yau kaga abin arzikin da ya same mu a unguwar nan? Wani bawan Allah ne ya zo ya raba mana abinci hadda kuɗaɗe, ka ga nawa dubu ɗari aka ba ni. Kodayake naga har gidanku ma an kai wannan abin alherin." Aliyu ya yi murmushi ya ce "Allah ya saka masa da alkhairi" daga haka ya koma cikin gida. 

Har yanzu Inna na tsaye a inda ya bar ta, yana shigowa ya ce "Inna bari a shiga da kayan nan ciki, ashe ba nan gidan kaɗai a ka bawa wannan kayan ba hadda gidan Malam Musa" ya yi maganar yana ɗaukar kayan ya fara shigar da su cikin ɗakin Inna.

Inna ta ce "Ikon Allah, to waye wannan mutumin da zai zo ya yi kyauta mai yawa haka? To ko ma dai waye Allah ya saka masa da alkhairi, irin mutane nan ne da basu son a san su, sun fi son suyi komai domin Allah." Ta yi maganar tana kallon Ma'u dake zaune ta sunkuyar da kai ta ce "Gadanga sai ka karɓi kuɗin nan ka ɗan ƙara sayo mana wasu abubuwan da zamu buƙata sauran canjin kuma sai ka riƙe." Aliyu ya girgiza kai tare da faɗin "A'a ba zan karɓi ko sisi ba, zan dai yi sayayyar kamar yadda kika buƙata, ki ajiye kuɗin anjima zan karɓa in yo." Daga haka ya fice daga ɗakin, yana fita Inna ta sake juya kuɗin, ta ce "Kuɗin sai ƙamshi suke yi, Allah ya saka da alkhairi" ta ce tana ajiye kuɗin saman cinyar Ma'u ta fice da sauri domin ta duba girkin da ta ji alamun ya fara ƙauri. Sai da gabanta ya faɗi da aka ajiye mata kuɗin nan. A hankali ta ɗauki kuɗin tana juya su, a kan hancinta ta kara su ta shinshina ƙamshin da ta ji suna yi. Lumshe idanunta ta yi tana ambaton sunan Allah, lokaci ɗaya hawaye suka dinga zubo mata ta gefen idonta.

.....

Bayan sati huɗu, Sudais ya ɗan fara sakin jikinsa kaɗan, ya mayar da hankalinsa a kan aikinsa da kuma kasuwancinsa. Sai dai duk da haka damuwar mutuwar Ilham da yadda ta rasa ranta yana nan danƙare a cikin zuciyarsa, kuma yana kan bincike ta ƙarƙashin ƙasa game da abin da ya yi sanadiyar mutuwarta. 
Yana zaune a cikin office ɗinsa yana duba wasu takardu, aka sanar da shi zuwan su Alhaji Badaru, izinin shigowa ya basu, bakinsu ɗauke da sallama suka shigo office ɗin. A hankali ya ɗago da kansa ya kalle su, tare da amsa sallamar. Zama suka yi, Sudais ya gaishe da su cikin girmamawa. Tare da tambayarsu ya harkoki? 

"Alhamdulillah" cewar Alhaji Hali. 

Sudais ya ce "Ma sha Allah, ya waccan aikin da ake yi, ina fatan babu wata matsala? Duk da naga an yi nisa a aikin sosai." 

Alhaji Badaru ya nisa ya ce "Alhamdulillah, aiki an kammala shi gabaɗaya, mun je mun duba, komai an yi shi a tsare, gidajen sun yi kyau sosai da sosai."

Sudais ya jingina da kujerarsa, ya sauke ajiyar zuciya, ya ce "Alhamdulillah, wannan babban ci gaba ne a gare mu bakiɗaya, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya ci gaba da dafa mana." 

Alhaji Badaru ya ce "Wannan gaskiya ne, Amin ya hayyu ya ƙayyum, yanzu ina ganin ya kamata mu fara tunanin mataki na gaba."

Sudais ya kalle shi ya ce "Mataki na gaba? To ina sauraren ku."
Alhaji Hali ya gyara zamansa, sannan ya fara magana "Yanzu tun da an kammala wannan ginin, abin da ya rage shi ne, mu fara fitar da sanarwa a kan gidajen, saboda masu buƙatar saya, da yadda za a saka farashin kuɗinsu, har zuwa yadda za a karɓi kuɗin, waɗannan abubuwan suna buƙatar mu tsara su da kyau."

Jinjina kai Sudais ya yi. Ya sauke numfashi kafin ya ce "Ni ma na yi tunanin hakan, za mu fitar da sanarwa in sha Allah, zan yi magana da mai kula da wannan sashen, daga nan sai mu bayyana videon gidajen da farashinsu, duk wanda yake da buƙatar saya sai ya tuntube mu."

Alhaji Badaru ya yi wani irin murmushi, ya kalli Alhaji Hali kafin ya maida dubansa ga Sudais ya ce "Da sunan kamfanin nan kenan za a yi tallar?"

Sudais ya tsaya yana kallonsa, kafin a hankali ya ce "Eh, ai haka muka tsara tun farko."

Jinjina kai ya yi ya ce "Tabbas haka ne, ba wai ina nufin ba haka ba ne." Sudais ya yi shiru bai ce musu komai ba.

Alhaji Hali ya ce "Sudais abin da Alhaji Badaru yake nufi shi ne, mutanen da za su nuna son gidajen nan suna da yawa, musamman idan suka ga daga wannan kamfanin ne, to ya kamata a ɗan yi taka tsan-tsan."

Sudais ya kalle su da kyau ya yi murmushi, ya ce "Amma ai wannan ba sabon abu ba ne a gurinmu, mun san aikinmu, kuma mun san yadda muke tsara komai ya tafi yadda ake buƙata, to in dan wannan ka da ku samu damuwa."

Alhaji Hali ya ce "Babu damuwa, Allah ya shige mana gaba ya hana mu jin kunya a ko ina muka shiga."

Sudais ya ce "Amin ya hayyu ya ƙayyum" sai dai kalamansu sun nuna kamar akwai wata magana da ba sa son faɗar ta kai tsaye. Nan suka ci gaba da tattauna yadda abubuwan za su kasance.

....

Cikin tsananin ɓacin rai yake kallon yaran da alamun su ya nuna riƙaƙƙun ƴan ta'adda ne, idanunsa sun yi jajur saboda masifar da yake ciki. Muryarsa har ba ta fita tsabar ɓacin rai, ya ce "Allah ya wadaran wannan aiki na ku, wallahi ban ga ranarsa ba, me ye amfanin ku idan har ba za ku iya yi mini aikina kamar yadda na buƙata? Inda na aike ku da ban, inda kuka je kuka yi aiki da ban. Ba ku da hankali ne? Ko kuma baku ji ƙauyen da na ambata ba ne? A kan me za ku je inda ban aike ko ba, gashi yanzu kun saka ni a matsala, Malam ya tabbatar mini da abin da kuka aikata wani ya ganku. Ya yi ƙoƙarin magance matsalar amma abin ya gagara."

Cikin girmamawa babban cikin su ya ce "Ka yi haƙuri Oga, wallahi akasi aka samu ne, na yi tunanin inda muka je can ne ka aike mu, sannan na yi mamakin da aka ce wani mahaluki yaga abin da muka aikata. Amma muna mai ba ka gaƙuri Oga in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba." 

Cikin takaici ya ce "Dalla rufe mini baki, bayan kun jawo mini matsala wane haƙuri za ku ba ni kuma, maza ku ɓace mini da gani ba na buƙatar ganinku a yanzu." Sum-sum kamar wasu munafukai suka bar gurin. 

Suna fita ɗaya daga cikin su ya ce "Boss wai waye ya ga abin da muka aikata a ranar ne? Ko dai wann.." Cikin ɗaga Boss ya daka masa tsawa yana faɗin "Rufe mini baki, ko so kake yi ya ji abin da ka faɗa? Salon ya kira ka kai kuma bakinka baya iya riƙe sirri tsaf za ka sanar da shi abin da ya faru." 

"Tuba nake Boss, kawai na tuna abin da muka yi a gurin ne, kai amma ranar mun samu la..." Kallon da ya yi masa ne ya sa yin shiru da bakinsa.

Suna fita ya ciro wayarsa ya kira Malam, bugu biyu ya ɗaga, tun kafin ya yi magana ya ce "Malam yanzu ya ake ciki ne? Gabaɗaya hankalina a tashe yake, ba na son a samu matsala."

Malamin ya ce "Ka kwantar da hankalinki, ina nan ina ƙoƙarin gano inda abin nan yake, sai na yi ƙoƙarin gano shi sai wani duhu ya zo ya mamaye hasken da na fara gani. Amma zan juya akalar aikin zuwa wani ɓangaren." Ajiyar zuciya ya sauke cikin damuwa ya ce "To shikenan Malam sai na jika." Daga haka ya ajiye wayar yana tsaki.

....

Sosai jama'ar gari suke yabon kyawawan halayen Alhaji Sardauna tare da ƙara yi masa godiya akan irin taimakon da yake yi, yanzu haka ma ya ɗauki nauyin karatun yara hamsin a ƙasar waje waɗanda suke da burin yin karatu amma basu da zarafin yinsa. Ya ƙara saka sababbin kayan aiki a Asibitin daya buɗa, gidan marayun nan an ƙara gyara shi da ƙawata shi. Duk wani abu na jin daɗi bakin gwargwado ya kai musu shi, ga marasa ƙarfi da almajirai daya yake ta tallafa musu. Sosai jama'a suke ƙaunarsa. Har a kafafen sada zumunta yabonsa ake yi.

Yana zaune a katafaren falonsa Zuhura ta fito cikin shirinta na zuwa aiki. Bayan ta gaishe shi ne ta ce "Abbi na zo ne in yi maka sallama, zan wuce gurin aiki."

Ya kalle ta yana murmushi ya ce "To shikenan Zuhurata, Allah ya kai ki lafiya, yau dutin dare za a yi kenan?"

Ta ce "Eh Abbi, bari in wuce kar in makara." Ya ce "To ya yi, Allah ya tsare hanya. Ki kula sosai Zuhura, sannan ki dinga saka mini ido akan yadda ake gudanar da aiki a Asibitin nan, ko kaɗan kika ga wani abu da ba daidai ba ki sanar da ni." Zuhura ta sauke numfashi ta ce "Abbi kamar name fa?" 

Ya kalle ta da kyau ya ce "Zuhura na gina Asibitin nan ne domin taimakawa marasa ƙarfi, ya zamana aikin da duk za a yi musu dubu ɗari a wata Asibitin idan suka zo nan za su samu sassauci sosai, ta yadda ba zai wuce a yi karɓi dubu ashirin ba a hannunsu, to kinga irin wannan sai ana yi ana saka ido sosai ga waɗanda aka bar ragamar aikin a gurinsu, ba wai ina nufin ki dinga tuhumarsu ba, ko kuma ina zarginsu ba, a'a ina so ki sa ka ido da kyau ki kula da yadda ake gudanar da aikin, ko in ce ku gudanar da shi." Shiru ta yi tana kallon Abbin nata, kamar ta faɗa masa wasu abubuwan da take lura da su, amma sanin halinsa na zai iya tambayarta tana da hujja ya sa ta yi shiru, ta ce "To shikenan Abbi, in sha Allah zan dinga lura."

Ya ce "To shikenan Allah ya yi miki albarka"

Ta amsa da Amin, sannan ta yi masa sallama ta fita.

....

Cikin Ma'u ya fara tasawa kaɗan, yanzu yana da watanni huɗu da ƴan kwanaki, gabaɗaya ta rame ta ƙara haske, da ma gashi ita ba wata ƙiba ce da ita ba. Tun da cikin nan ya bayyana a jikinta ta daina fita ko nan da ƙofar gida ne, kullum tana ɗaki a kwance, ko da maƙota sun shigo gidan ba ganinta suke yi ba, Jamila ba ƙaramar damuwa ta shiga ba na ganin halin damuwar da ƙawarta take ciki. Duk da ba ta san ainahin abin da yake damun Ma'un ba, saboda duk lokacin da za ta zo gidan a cikin hijabi take iska ta, hakan bai dame ta ba duk a tunaninta damuwar abin da ya faru da ita ne da kuma rashin da suka yi duk ya dawo da ita haka. Tun tana zuwa a kai a kai, yanzu kuma ta rage saboda yadda ta ga Aliyu ya ɗan fara sakin jiki da ita. 

Dare ya yi sosai, tana kwance kamar kullum, idanunta a buɗe tana kallon sama, saboda rashin baccin da take fama da shi idan dare ya yi. 
Ganin ta yi hasken fitar ɗakin ya ɗauke, a hankali ta ji hucin mutum a kusa da ita. "Waye?" Ta tambaya ba tare da ta yi magana da ƙarfi ba.

Haske fuskarta aka yi da fitalar ƙaramar waya, "Waye?" Ta sake tambaya

"Ni ne" aka ba ta amsa.

"Kai ne wa?"

"Uban yaron da yake cikinki mana, ko ba ki gane ni ba?" Shiru ta yi tana shaƙar ƙamshin turaren da take ji, kuma da alama daga gurinsa ƙamshin yake fita.



Mun kusa kammala book 1, book 2 na kuɗi ne, ga mai buƙatar ci gaba da bibiyar wannan littafin zai iya tura 1k ɗinsa, 1019533255 Nafisa Muhammad UBA, sai a tura mini shaidar biya.


Amanarcool 
***