SHI SO DABAN YAKE

Babi na biyar:

by @dijensy



5



  Jidda ta shafe hour ɗaya da kusan rabi kafin ta gama shiryawa ,cikin atampa daga kayanta ta saka ta amsheta mai haske ce ruwan ɗorawa da ratsin ja mai maroon da baƙi Hassan ya shigo ya tarar da ita ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya daga gefen gado Hassan ko haɗa ido da ita nauyi yake ji fuskarsa ba yabo ba fallasa “Kin shirya mu je?”Ya tambayaa tausashe ba tare da ta ce masa komai ba ta miƙe tsaye tana yafa mayafi a kafaɗa suka fito Anty Ruƙayya na uwar ɗaki da Shafiha taji sallamarsu fuskarta da faraa ta fito tana ƙoƙarin shinfiɗa carpet Jidda ta samu kujera mai cin mutum ɗaya tayi zamanta a yayinda Hassan ya zauna daga ƙasan yaƙi komawa kan carpet ɗin da ta shinfiɗa.”Anty Ruƙayya kun kwana lafiya?”Ya gaisheta tana amsawa da “Lafiya lau” tana kallon Jidda kamar bata so ta furta “Ina kwana”.


 “Lafiya lau an tashi lafiya ya kwanan baƙon waje?”Ta ƙarashe da tambayarta “Cikeda kewar gida”Jiddan ta amsa rai a haɗe Anty Ruƙayya ta murmusa tana kallonta ko ba a faɗa mata ba ta san yarinya ce shakaf Jidda sabida haka dole ta mata uzuri baƙunta kuwa dole zatayi.Anty Ruƙayya tayi tunani a ranta.


 “Allah ya haɗa kawunanku ya baku zaman lafiya da rayuwa mai ɗorewa tare Allah ya albarkaci aurenku ameen”.Hassan ya amsa da ameen  cikeda jin kunya yana shafa goshi da tafin hannu “Mun gode da ɗawainiya Allah ya biyaki”Ya furta Jidda ta jefesa da kallo kafin ta sauke idonta kan Anty Ruƙayya da ta sunkuyi da kai “Wace ɗawainiya kuma in banda abinka Uncle idan tana buƙatar abu tayi magana dan Allah ko aikene ga yara ki faɗa zasi maki nima idan kina buƙatar wani abu gani a kusa in sha Allah”.Anty Ruƙayya ta faɗa Hassan ya mata godiya kafin ya tashi ya yayi mata sallama yana fita Shafiha sai ɓuya take ta ga baƙuwar fuska yana kiranta taƙi zuwa ta maƙale jikin babarta Jidda ta tashi ta fice tana binsa kamar jela suka koma ɗakinsu ta tsaya zangangan ko zama basuyi na “Na biya maka taka buƙatar saura tawa maganarmu ta jiya”.Ta furta tana kallonsa  ya kasa ko ɗagowa yayi shiru na yan sakanni Hassan da kyar ya ɗan ɗago ya dubeta yana haɗa ido da ita ya kawar bai saba haɗa ido da mace ba wani kwarjin balai yaji ta masa dukda cewa ya fita tsaho “Zan iya samun wata alfarmar ki yi min haƙuri ki bani lokaci ko da kwana uku ne zan yi shawara kinji?”


  Wani kallo ta jefo masa “Bazan iya ba na rantse ko kwana bazan sake iya yi gidannan ba na baka nan da anjima zaka zo ka tarar bana cikin ɗakinnan”.Ta furta tana wucewa ta zauna gefen gadon ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya kamar kububuwa Hassan ba tare dayace komai ba ya juya jiki a sanyaye ya fita.


  “Ko kafi ƙuda naci sai ka sakeni wawan banza kai ba ka yarda ba kayi mata ko ? okayy”.Ta ƙarashe maganar tana jinjina kai don kwata kwata bata hango zamanta da shi ba.



    Jidda ta cigaba da zama tana ta shawarar yadda zatayi ta tafi muddin bai dawo sun yita ta ƙare ba sai saƙe-saƙe take daga baya ta shingiɗa kan gadon tana tuna wayarta da ace Umma bata ƙwace ba da tuni ta na ɗan dannawa ranta ne ya sake ɓaci tuna irin yadda lokaci ɗaya rayuwa ta canja mata tayi kewar Baba dama komai zai dawo dai dai.Hassan fitar da yayi ya shiga shago ba abinda yake sai saƙe saƙe ya rasa ya zai yi da lamarin Jidda daga baya kawai ya ɗaga hannu yayi addua da roƙon Allah ya kawo masa mafita.Har rana tayi ya kasa komawa gidan ,Anty Ruƙayya kuwa tuni ta fito ta haɗa girkin rana almajirin da take aike tuni ta bashi cefanan kayan da zai sayo mata rayayyar shinkafa da miya tayi ta haɗa kayan cabbage da karas ta shirya musu ,ta jima tana tsammanin shigowar Hassan ɗin bata ga alamar yana nan ba ta ɗauka tray da kanta ta kwankwasa ɗakin tana tasowa Jidda ta buɗe tayi tsammanin daman ita ce don har yunwa ta fara lallasata Anty Ruƙayya tayi murmushi tana miƙa mata “Kiyi haƙuri yara basu dawo daga makaranta ba fatan zaman bai dameki ba ke kaɗai”.Ta faɗa jidda bata ce komai ba ta karɓe mata abinci Anty Ruƙayya  ta mata sallama ta tafi Jidda ta shigo ciki tana ajje tray ta buɗe warmer wani ƙamshi ya doki hancinta nan ta zuba abinci ta sa cokali ta ci ta yi hani’an ta sha ruwa tana komawa gado kwanciyarta tayi wani bacci mai daɗi ya kwasheta.A hankali ta ji murya a kanta ana kiran sunanta ta buɗe idanunta Hassan ta gani tsaye ta yi zumbur ta tashi tana ja baya haɗi da ɗago kai tana kallonsa rai a haɗe “Ki gafarceni na tashe ki Baba ne ya zo ya na son magana da ke”Ta ji muryar Hassa tana kallonsa “Baba?”Ya giɗa mata kai yana tsakar gida Jidda ta sauri ta faɗa banɗaki tana wanke baki da fuska ta yafo mayafi a ka tana bin bayan Hassan sai a sannan ta ga alamar yamma ce liƙis ko asr ba tayi ba ta tsuguna ta gaishe da Baba ta kasa haɗa ido dashi wani tsoronsa take ji gefe guda take kalla bayan ta gaisheshi yana zaune kan wata kujera mai ɗan tsaho da suka bashi ya zauna a soro ko ciki bai shigo ba  ya dubeta bayan ya amsata karo na farko tun bayan abinda ya faru bai sake saurarar maganarta ba sai yanzun da ya amsa gaisuwarta.


  “Dalilin zuwa na nan nazo ne na ja maki kunne Jidda ,daga rana irin mai kama ta yau yadda na damƙaki hannun mijinki Hassan bana son jin wani tsaiko ko koke,kamar yadda kike ‘ya gurina shima Hassan ɗana ne sabida haka kada kaji nauyin tunkarata idan Jidda ta ƙi biyayya ga aurenku ka zo ka sameni ba kina ganin ba na ganinki ba idan kikai ba dai dai ba ma zan sani kuma a gaban mijin naki zan hukuntaki”.


   Jidda tana sunkuye da kai Baba yake mata faɗa a gaban Hassan don shi ya buƙaci da ya tsaya shima yana tsugune ya sa su a gaba sama da minti talatin Jidda harda hawaye don wani ɗaci da take ji maganganun Baba tamkar sadakarta ya bayar gabadaya a maganarsa ba wani abu wai shi Hassan ya kula da ita kawai faɗan a kanta ne kacokar har ya gama ya sa ta tashi ta shiga ciki ta wuce tana komawa ɗaki komai ya jagule mata lissafi da yasa ta fara tunanin ko Hassan ne ya kai ƙararta don ta ga alamar sumumu kasam ne wajen minti biyar kafin Hassan ya shigo ciki ta kallesa da rinannun idanunta “Kai ka faɗa masa abinda na ce maka?”Ta tambayesa cikin sigar tuhuma.


 Kai ya girgiza da sauri ya shiga rantse mata batare da ta tsaya ta sauraresa ba ta shiga banɗaki ta rufo ƙofar da ƙarfi sai da ta gama sharar hawayenta ta fito tana mai ɗakko darduma ta shinfiɗa tana ta da sallah  bayan ta idar ba jimawa aka yi maghriba ta tashi tayi ta ji motsin shigowar Hassan ta ƙi ko juyowa.Fahimtar cewa ta idar ya sa shi kewaya ya ajje ledar fruit salad da ya siyo mata ɗaya ya kaiwa su Anty ya kawo mata ɗaya ya zauna da tazara a tsakaninsu amma ba yawa taƙi kallon inda yake kansa a sunkuye.


 “kiyi haƙuri nasan ni mai lefine amma ina so ki sani wallahi ban kira Baba na kai ƙararki wajensa ba”.Ya faɗa.


  “Karka damu kanka bada haƙurin na mene?ni baka min komai ba”.Jidda ta faɗa ta tashi ta ninke dardumar ta wuce ta ajje a cikin wardrobe ta ɗakko akwatinta kaf kayan ciki ta ciro ta jera wardrobe ɗin tana rufewa ta ɗauka tana miƙewa kan gadon ta tsaya Hassan da ya fahimci me zatayi ya buƙata da ta bashi ya ɗora mata kan wardrobe ɗin kallo ɗaya ta masa ta sauke akwatin ya karɓa ya ɗora mata ya fita masallaci yaje yayi isha yana ta nazarin sauyin yanayinta lokaci guda hakan na nufin ta ja ye maganar sakin?  dawowarsa ya tarar Anty Ruƙayya ta kawo mata abincin dare yaci ko bai ci ba bai shafeta ba tunda ta zuba ta ci ta yi isha ruwan flask ta juye a bokitin banɗaki tayi wanka ta fito ɗankwalin atamparta da shi tayi zani Jidda ba ko kunya santalan santalan cinyoyinta a waje ta fito daga banɗakin  ta wucesa da ɗaurin ƙirjinta ta tsallake ta ƙarasa wajen wardrobe ta ciro kayan bacci doguwar riga ta zira itama iyakacinta cinya ta haura kan gadon tana kwantawa ta juya baya ,kwanukan ya tattara ya kai waje saida ya ɗauraye kamar koyaushe ya kai kitchen ya dawo Jidda ta daɗe ido biyu lambo tayi tana jiran ya gwada yin wani abu da bai mata daɗi ba a daren nan sai ya ga tijara indai har aurene ya yi sa amma jalala yanzu ya fara gani rantsuwar da ya dinga mata ɗazu ta gano wani rauni a  tare dashi yadda baya iya haɗa ido da ita ɗinnan ya tabbatar mata da Hassan ɗin ba mai zafin kai bane don haka cikin ruwan sanyi take son horashi na amsawa aurenta da yayi da kansa sai ya gaji ya saketa don kanshi.Hassan sai can ta ji motsinsa ɗan zirin kusa da wardrobe yayi shinfiɗa ya kwanta bayan ya rufo musu ƙofa ta rufe idanunta….





Arewapen