SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)

Page 11

by @smauta




Wasa wasa yau lily satin ta daya gidan babani yadda babani ta tsara kuwa hakan akai duk wani aikin gidan babani lily keyinshi har sai ta baka tausayi gashi idan zatayima Sarah kira dubu bata daukar wayar ta,Sarah bata taba fushi da ita ba irin haka ba………..



Gogan kuwa tun daya baro gidan nan bashi da wani sauran sukuni wurin aikin ma yaje ya dauko leave kullum yana kwance gida zuciyarsa na namashi wani irin ciwo,ya sakan kance da lamarin ubangiji tabbas ta tabbata yanason lily so mai tsanani amma kashhh soyayya taimashi yankan kauna………..




Yanzun ma shiri yake zaije wurin sufyan dan duk dunia ba wanda yake fadama matsalolin shi samada sufyan shima ɗin kuma koda bai fada mashi ba yana gane aminin shi idan yana cikin damuwa,bayan yagama shirin tsaf wayar sufyan ya kira ilai kuwa yana dauka ya fara tsokanar namijin duniya tazuru mai abun ban mamaki🤣……….

Sufyan kana ina,ina gida zaka fita?a'a yau ranar madam ce bazanje shop ba gaskiya, okay on my way Allah ya kawoka lfy,tunda yaji ya tsokani abokin nashi bai kula shi tabbas yasan yana cikin damuwa ne haka kurum yaji ranshi baya mashi dadi shimaa ba dauki wasu lokutta ba adam ya iso gidan sufyan sun gaisa da iyalinshi sannan suka zauna zaman tattaunawa…………..




Kaifa haka kake ni da anceman ka mutu wlh nasan damuwa ce tayi ajalin ka haba adam kashe kanka zakayi abu na damunka bakasan kuma ka fada ba,Adam ya kira sunanshi da ido kawai ya kalli sufyan kamar ya rushe da kuka yakeji,dan Allah ka fadaman damuwar ka ninasan ba lafiya ba tunda naji muryar ka a waya………..




Kalli yadda ka tara gashi ba aski duk kazama wani iri wai meke damunka fisabilillahi nima nan kazo ka tasani gaba kana kallo,ya adam ya numfasa yace sufyan ina sonta banso ina ganin kowa tareda ita amma batajin magana batada kunya ko kadan unfortunately kuma yanzu aure zasuyi mata………..




Labarin gizo bai wuce na koki shi dama ya dade da sanin adam yanason lily amma yaki yarda da hakan,gudun kar yayi dariya ya kuleshi yasa sufyan yace meyasa bazamuje mu samu abby da maganar ba,gida bata koshi ba ai bazaa bada a dawa ba,a nawa tunanin adam muyima abby magana hakan yayi………….




Girgiza mashi kai yayi banso yazama nine silar rugujewar farin ciki lily,na taso dason farantama lily a rayuwata sufyan kasan yadda nakeson lily, Sufyan ya gumtse dariyar shi yace a'a ai kullum cewa kake kanwar ka ce😂nikuma nasan kana sonta wlh,lily tanason wanda zata aura sosai…………




Yima abby magana zaisa ta kara tsanata bayan wacce takeyi a baya,inaga sufyan zan hakura lily dama ba matata bace bazan taba zama silar rugujewar farin cikin ƙanwata ba Allah ya basu zaman lafiya kawai ya idasa maganar,ranshi na mashi wani irin zugi………….




Zuwa yaushe ne za'ayi bikin nata wlh i don't know nadaiji babani tace a gaggauta nan ya labarta mashi komai daya faru Sufyan nata daria dama lilyn nan taka dangerous kullum muna school sai an kawo maka kashedin ta,amma wani hanzari ba gudu ba,inajinka,mezai hana kaima adam kayi aure hakan zaisa kamance da damuwar lily kwana kusa………….





Nafara tunanin haka nima amma duk wadda nayi yunkurin tunkara nakanji a raina kamar zan cuceta zuciyar tawa har yanzu ta kasa yadda da abinda nakeso in yardar mata,shegen kaya wai yau adam kaine ke dogon zance haka, soyayya sirrin Allah 😂😂😂💔……………….






Zan cigaba da tayaka da addu'a Ina Shaa Allah zaka dace,kayi hakuri dan Allah ka cire damuwar nan a ranka ci abinci mutashi muje a aske maka wannan gashin naka duk kayi buzu buzu wani kala dakai,sufyan thank u amma i can't eat…….



Karya ne wlh yadda naganka a wnn condition nasan ko abinci kirki bakaci,kaci abinci kawai ina zuwa,dakyar adam yadan tsakuri abincin nan haka ya barshi tare suka fito Sufyan ya ansa tukin har wurin mai askin su a tare akai masu askin daga nan suka wuce Majalisar su ta matasa yanaso dai duk dan abokin nashi yadan zama fresh,adam kuma yana binshi ne kawai sbd karfin hali yake………




PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏....SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……