SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)
Bonus page
by @smauta
Yau lily ta tashi da wani matsanancin ciwon ciki,a gefe guda kuma sufyan ne da abokinsu galaxy sukaje har office din abby akan maganar adam da lily ba tareda sun nemi shawarar shi ba🙄,abby tass yana sauraron su suka gama mashi bayani ya kalli sufyan dakyau yace…………..
Sufyan na'am Abby inaso ku saurareni dakyau dani da maman adam mun dade da sanin adam yanason lily amma nayi alkawarin muddin bashi ya kawoman kanshi bazan taba aura mashi fatima ba,banida tabbacin wani kalar so yake mata,haka itama lily bazan taba aura mata wanda ranta baya so ba…………
Hakika ku abokai nagari ne da zakuga dan uwanku a damuwa ku nemo mashi mafita amma yanzu kuma is too late dan nariga da na bada lily,kuma ita ta kawoman zabinta da kanta zanbi kuma zabinta dan in farantamata, dukkan ku kunsani lily marainiya ce,banida wani buri daya wuce inga farin cikin ta har karshen rayuwata………
Inason dana adam kamar yadda itama nakeson ta amma kowane su inaso yayi rayuwa ta farin ciki ba tareda tauyema kowa hakkin shi ba, tabbas yanzu idan na bijiroma lily da auren Adam ba karamar rigima zaayi ba wacce daga ƙarshe nasan bazata haifar man da ɗa mai ido ba,kamar yadda kukazo a mamadin adam, nima a matsayina na mahaifi dukkan gareku ina mai baku hakuri……….
Abinda kukazoman dashi bamai yiyuwa bane na bada lily yanzu haka saura wata biyu a daura mata aure kamar yadda mahaifiyata ta umurceni da ayi hakan,naji dadi sosai,kuma kuyita sashi a addu'a a wasu lokutan zakaso abu amma kuma yazo ba alkhairin ka bane a wani lokacin kuma zakaki abu wannan abun da kaki kuma shine alkhairin ka………..
Kuma tayani bashi hakuri duk da kunceman baisan zakuzo ba,mun fita zamanin da ake danne yaya mata yanzu kowace mace yanci gareta,yancin yasa ta kawoman wanda takeso kuma nayi bincike akanshi sosai baida wata matsalar da zatasa a fasa aure kuma shima yanason ta,muyi masu fatan alheri da tabbatuwar zaman lafiya a tareda su shikuma Allah ya bashi wacce ta fita, ameen Abby a tare suka amsa tabbas abby uba nagari ne da baiso ya danne hakkin kowa,haka sukai mashi sallama suka fito ƙafafu sagaleeeeeee………………
Ohh innalillahi ni zainabu abu ke diyar nan mike mugani babani ce tsaye kan lily daketa murkususu, Assalamu alaikum kai Alhamdulillah adamu daukar man yarinyar nan kuje asibiti tsanki take tun safe na bata jike jike amma abun yaci tura,bai tsaya jin sauran zancen babani ba ya idasa gaban gadon da lily ke kwance ya sunkuceta sai mota……..
PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹...SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……