SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)
Page 12
by @smauta
A kan hanyar shi ta zuwa asibitin ya kira Mama ya fada mata halin da ake ciki,bayan ya kaita asibitin an shiga da lily dakin gaggawa saiga mama da sarah sun iso mamace ta kalli adam ba abinda yakeyi sai zufa kai lafiya? Ina lilyn take???da ido yayi mata alamun inda take gaba ɗaya karfin shi ya ƙare raunin shi yana saurin bayyana muddin akan lily ne shiyasa ganinta a wani hali yasashi shiga yanayi matuka…………….
Kusan hour daya aka dauka sannan aka fito da lilyn dakin hutu aka wuce da ita wata nurse ce ta kalli mama tace Dr nasan ganinku mama kam hankalin ta baya jikin ta adam bisu kaji me zasuce Innalillahi nashiga ukku sannu lily kome akeyi lily naji amma ba bakin magana da ido kawai take bin su mama da kallo………..
Office dinda Dr yake ciki adam ya nufa bismillah da kyar ya zauna yadda kanshi ke sara mashi,yan rubuce rubucen shi yagama sannan ya dago ya kalli adam ya kuke da ita she's my sister,kai likita ya jinjina prescription ya bashi tana bukatar wadannan,and da Allah duk wani abu dazai sa ta wahala ayi avoiding dinshi kar ayi over working dinta……………
Har ya taso zai fita ya kalli Dr amma jikin nata normal likitan yace ahh alhamdulillah matsala ce kawai irinta MP dinta ne yadan bata wahala and nagano harda rashin samun isashen hutu ne,bai kara cewa komai ba ya fito ya baro masa office dinsa,shaaa pharmacy ya wuce ya rankato magungunan da aka rubuta masu………..
A gefen su kuwa lily ta kama hannun Sarah ta rike gammm mama nata aikin jera mata sannu,sai lokacin ma mama ta tuno da abby ta kirashi ta sanar dashi halin da ake ciki,to ya kike ganin jikin?da sauki nurse din ma data kawota tace kila zuwa dare ma a sallame ta, Allah ya bata lfy Abby kadai yace………….. har yanzu knn Abby bai huce ba?????
Sannu da zuwa ya adam sai lokacin lily ta dago kanta karaf idonshi cikin nata lokacin daya wata wutar son lily ta kara ruruwa a zuciyar adam,da kyar ya dake namijin dunia ya kalleta da kyau da fuskar nan tashi ba yabo ba fallasa ya jikin?alama tai mashi da kai da sauki, magungunan ya ajiye ya kalli mama me za'a siyo mata?…………..
Lily me kikeso a siyo maki kici kisha magani drip din yakusa karewa mama bakina ba appetite ban iyacin komai fa,a'a kefa tsiyar ki knn rashin cin abinci kaga adam siyo mata anything abu liquid amma mai sanyi sosai kaji, okayyyyy kadai yace yaci reverse sai mota,bai zame ko ina ba sai wani supermarket cigaba da jido youghut yayi yaji wayar shi na ringing mamace…………..
Kanaji ummmm dama kanaji inata magana mama an not feeling okay me kike needing ne? sanitary pads,a wayance yace mene hakan?bansani ba ka siyo mana shi duk ta batama masu gado sarah taje ta siyo mana nine zan siyo wnn abun,adam idan ka sawo mutuwa zakayi?kit ya latse wayar shifa shiyasa bai shiga harkokin mata saboda irin wnn aiken yada girmanshi aganshi yana wani sayen pad😂………………
Baiko siyo pad din ba haka ya dawo da ledoji niki niki,satar kallon gadon yayi yanaso ya tabbatar da abinda mama tace ilai kuwa kallon farko ya hango jini akan white bedsheets din,mama ce ta bude ledar ina pad din lily kuwa kmr kasa ta bude tashige takeji dan ita a duniya ba abinda take kunya sama da ace period takeyi…………..
Dakiya yazo mashi yace mama ina sarah ne dan Allah,na aiketa gida ta dauko mana kaya ita da wa?ita kadai mana mama kinsan abby fa baison yaran nan na hawan mota su kadai wai idan basu hau mota ba taya zasu kware,In Shaa Allahu zata dawo lafiya dama ga mai rawar kai nan amma sarah nasan zatayi tuki cikin natsuwa da yardar Allah……………
Motar shi yakoma yayi dailing wayar sarah bugu ukku ta dauka hello ya adam Yes where are you?ina gida kin isa gidan ne bakidaiyi gudu a titin ba,eh yaya ammmm ammmmm yace amma takai cikin cokali yayi ta maza yace ki zo mata da pad idan kina dawowa kunada shi a gida ko zaki tsaya ki siyo?eh akwai anan amma dai bashida yawa okay lemme dash your account…………Irin ku akeso babban yaya adinga dashing account din ƙanne😂😂🫰
Saida Sarah ta tsaya ta dafama lily indomie ta fito kenan wayar mama tashigo tace babani ce ta kira tanaso itama tazo asibitin hankalinta yaki kwanciya kije ku taho to mama gidan babani ta isa,a shirye ta sameta suka rungudo asibiti tana shigowa ta dinga salati tana sallallami,ke fatima ki yadda kika koke kamar farar audiga dama haka takeyi ne ke mamansu baki taba gayaman ba,a'a babani gaskiya bata taba irin haka ba,adam na gefe yai caraf yace Dr yace tana aikin wahala ne shiya jawo hakan…………….
Wayyo ni Allah na adamu dana kashe jikata da kaina gani nayi bata iya komai ba sai don jiki ga aure na karatowa duk girman gidan nan ita ke share shi ta goge taimana abinci sannu jikalle aibansan haka abun yake ba,kai adamu ummmm kace naam ne wani ummmm uwa bamaguje…………
Mama am leaving to shikenan sannu tun kafin asan za'a haifi ubanka nima de turancin nan na iyashi ni zaka juyama harshe,sarah da lily suka kwashe da dariya lily tace to meyace? ja'ira primary har aji bakwai nayi miyace kuwa cewa yayi yagaji da suturu yanajin tace haka shi kanshi baisan lokacin da ya murmusa ba kawai ya fice……………
Har bayan isha suna asibitin saida dr night yazo ya sallamesu,tunda adam yakoma gida bai huta ba dan kwalwar shi tsaye take tana mai aikin tunani ya saka wancan ya fidda wancan ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji dadi,wata zuciyar tana bashi courage na ya fito fili ya fadama lily abinda ke ranshi wata zuciyar kuma tana kwabar shi da yin hakan🙂↕️🙂↕️🙂↕️🙂↕️🙂↕️🙂↕️🙂↕️………………
Mama ce ta kirashi ta fada mashi an sallamesu yazo ya maida babani gida,dagashi sai jallabiya ya iso asibitin duk sun haɗa yan kayayyakin su,dayake shi period kamar ciwon karya yadda yaga lily nata daria idan ba shiya kawota asibitin ba sai yacema karya take,anzo bakin mota mama tace lily kije da Adam gidan babani ko,kwalkwal tayi da ido babani tace keeee rabani da diyan ku na zamani……………..
Daga sata aiki ta koma haka wlh ku koma da abunku tunda tazo banida hutu gidan nan bakina har tsawo ya kara yanzu ma adamu na zuwa zan sashi ya dauko mata kayanta nida fatima sai a ziyara karta mace ace babani ce 😂😂 dadi har cikin ran lily kuwa sukai mata bankwana kowa ya shige motar su sai gida kare yasha taba 🤣………..
Mi kake nufi tsofai tsofai dani nice zan hada mata kayan ta wannan diya kazama ce adamu ko dan kamfai ta cire sai in isketa ta jeraman su kan gado kai kace wata kasuwar gwanjo ta bude😂 akwatin ta na nan da wayar ta akan gadon kwaso mata su ka kai mata abunta,dakin ya shiga ilai kuwa ga bra nan baje akan gadon kallo daya yayima cups din ya dauke kai, cigaba da tattara kayan yayi tunda yake a rayuwarsa dakuma girman sa hannun shi bai taba shafa bra ba balle har ya riketa sai yau……………..
Yana daf da daukar wayar ta yaji tana vibration idon shi akan number mai kiran da akaima saving da dan aljanna❤️😍 ko ba'a gayamashi yasan waye Alhaji najib ne,silent ya maida wayar ya tulla ta aljihu ya fito jaye da akwatin a tsaitsaye yayi bankwana da kakar tasu ya fito bai zama ko ina ba sai shawarma kings dukka gidan ya siyoma kowa sannan ya nufo gidan nasu…………
A parlourn Mama ya tarar da kowa harda abby daya dawo lily na kwance kan cinyar mama tagama ba abby hakuri tana yan kwallan ta yashigo,sarah tayi saurin tashi ta anso kayan hannunshi har tsakiyar parlour ya kawo akwatin abby ya kalleshi sannu da kokari kaida kakai kayan kuma kaika kwasosu dukkan su kowa daria yayi a gefen abby ya zauna kujerar da ke facing tasu lily……………….
Sarah ta fara fiddo shawarma wayyo Allah yaya mungode dama kwana biyu kwadayinta nake wlh lily tai zumbur ta tashi uwar kwadai,an kawoma marar lafiya baki bari ma in buda ke rugiya wnn shawarma nufinki ke daya zakici ta?ya adam dan Allah ba tawa bace?lily ta jefo mashi tambayar a bazata samun kanshi yayi da ansa mata eh,Abby ya saci kallon shi duk yazama wani cool…………
To bani abuna kinji mama ce ta raba gardamar tace kowa yaci guda daya sauran da ta rage taki ce,sai lokacin ya tuno da wayar ta yasa hannu a aljihu ya ciro wayar bai kula ta ba kawai yace take,Sarah ansoman dan Allah kafafuna a rike suke wlh kafin Sarah ta mike ya taso da kanshi har gabanta ya dora mata wayar a cinya ya wuce sama abun shi😅😅😅😅 gaskiya ya adam kazama lallausa baby………………….
PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹..SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……