SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)
Page 13
by @smauta
Abby ne ya biya bayanshi zuwa nashi sashen mama ta kalli su sarah idan kungama sarah karku barman parlour kaca kaca ke kuma kisha maganin ki ku kwanta da wuri to mama saida safe tayi masu tabi abby a baya,a daki ta tarar da Abby nashirin shiga wanka tashigo sannu da dawowa ta kara mashi ya ansa ya koma gefen gadon shi ya zauna koda ya zauna mama tagane alamun akwai magana a tare da shi ita gefen gadon ta nemi wuri ta zauna………….
Maman yara na'am abby,wani abu ne yake damuna sosai gameda adam gaban mama ya fadi sosai ɗa da uwa sai Allah tace Allah dai yasa lafiya ahh lafiya lau gameda da maganar da muka tabayi dake ne da dadewa,ehhh magane itace yauma ta kara tasoman amma dawani sabon salo kuma kara matsowa mama tayi kusa da abby tace me kenan abokan adam sunzo har office sun sameni da maganar amma ba tareda sanin shi kanshi adam din ba………………
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai mama ke nanatawa a ranta dan itama kanta ta lura da yanayi da adam din yashiga a kwanakin nan yana cikin wata makauniyar soyayya ne,Abby bai idasa maganar shi ba mama ta sauko kasa ta kama kafar abby tace dan Allah dan son annabi abby yau dai rana daya ka cikama adam burin shi nason lily,duk da bai fito fili ya nuna ba a matsayina na mahaifiya gareshi kayiman wannan alfarmar………………
Abby ya kalli mama sosai yace maman yara bansan ki da wannan halin na son kai ba amma saboda adam zaki ari hijabin da ba taki ba ki rataya a wuyanki da wane ido kikeso in kalli,in hanata zabin ranta in tirsasa mata auren wanda nasan bataso saboda wata maslaha ta ɗana?idan auren yazo baiyi karko ba ya sakoman yarinya ko tayi mashi wani abun fa dukkansu ya'ya nane ta dawo gidana tana zawarci kuma ɗana na ciki yai mata haka…………
A gaskiya ki canza tunani ban taso an tauyeman hakkina ko daya ba bazanso in tauye ma yarana hakkin su,shi babba ne yasan hakuri yasan kuma daidai yasan kuma haramun ne ma a yanzu nema cikin nema idan har ba wancan ne ya janye ba,yayi hakuri ya samo wata matar lily Allah ya kaddara ba tashi bace, Wallahi maman yara muddin kikaga naba adam auren lily saidai in najib ne da kanshi yace baya sonta……………….
Banida tabbacin son da yakema lily idan sonta yake da gskia ya tun kareni mana ya fadaman niba mahaifin shi bane?har abokanshi suka gane son ta yake yakuma ansa masu da eh hakan ne amma ya kasa fitowa ya fadaman,zurfin cikin shi yaja mashi gashinan kuma ganin idon shi zan aurar da ita wata kila daga kanta idan yaga abinda yakeso yayi saurin furtawa ina mashi fatan samun mata tagari da zata kula dashi itakuma lily Allah ya tabbatar mana da alheri amin…………………
Mama ta numfasa tace amin,abby ya kamota ya zaunar da ita gefen shi tana guntun hawaye na tausayin danta Abby da kanshi ya goge mata kiyi hakuri,idan fatima rabon adam ne sai kiga ya aureta idan kuma Allah ya hukunta ba aure tsakanin su kar muyi ma Allah shishshigi mu sakankance kawai mubar mashi zabi,zabin Allah shine daidai kawai……………….
A gefen Adam kuwa bacci ne ya faskara a idon shi rutsum ya kasa rufe idonshi daya rufe screen din wayar lily yake gani dan aljanna❤️😍,sai juye juye yakeyi yana tunanin yanzu haka fa tanacan batada lafiya suna waya da wannan tsohon banzar tsaki yaketa jerowa tunani yaki karewa ya tashi toilet yashiga ya dauro alwala yahau darduma yacigaba da gayama Allah kukan shi🥹……………..
Tunanin adam kuma bai tsallake ba ilai ga lilyn nan lafe a gado tana tsinkar fure da dan tsohon ta yanata fadan danmi ba'a sanar dashi batada lafiya ba,tanawa kashe murya take lallashin abun nata har ya sauko mar'atussaliha na'am dan aljanna kinsan yadda nakeson ki kuwa?nasani soyayyar da mukema juna daban take Allah ne shaidar zukatanmu yasan muna ma juna soyayya ta gaskiya da gaskiya………………..
Ya maganar gidan kuwa ohhhhh sorry kinsan namanta ban tura maki ba tun da safe engr ya turoman almost done fa cabinet ne kuke cemashi ko meye ma?kai dan aljanna kitchen cabinet yawaa to shi kadai ya rage jibi zaa saka na ƙagu in ganki cikin gidan nan kin zama mallakina na zama baki😁🙈🙈 uhummmm lily ta kare fuskar ta kmr yana ganinta ta kasa magana…………………
Nifa banison kunyar nan mar'atussaliha baki fara jin kunya ta ba saida kikaga bikin ya taho,ban yarda ba kunyar nan ki barota gida kina kunyata taya zaki kula da mijinki,to dan aljanna nadaina yayi murmushi ki kwanta kiyi bacci gobe idan kinji karfin jikin sai inji idan zan iya zuwa umm tohm bye bye i love you 😘 i love you too matata sleep tight……………
Yana kashe wayar tayi mata mirgina kan gadon ta tafkama sarah bugu a hannu tace wayyo sarah soyayya dadi soyayya ruwan zuma🤣🤣🤣dan aljanna duniya neeeeeeeeeeeee ke yarinya kizo gidanmu kiyi course din soyayya keda zakiyi auren age mate saikin dage,naji bakomai da in auri tsoho gwara dai yasir dina ajinmu daya kuma na gayamaki ya girmeni fa yabani 2 years…………
Yo shekara biyu girma ne mtswww🤣 ajinku daya dai yanzu dai in ya kira kina daukar wayar ko ina ruwanki niban iya rashin kunyar ki ba gaisawa kawai muke ya kashe😁😁😁naga auren ku ke kunya shi kunya munafukai akai auren kar in ganki da ciki Sarah tace idan munzoyi ki hanamu 🤣🤣🤣………….
Ahhhh wlh kan mage ya waye duk soyayyar yasir dince yasa ina fada kina fada to ya san ranki keni na ƙagara kiyi auren kona huta da dumi wlh dana tafi zakiyi kewata wayarta da take latsawa ta karkato mata tace kalli gidan ya turoman da sauri sarah ta matso kai Ma Shaa Allah inyehhh wlh kinyi goshi haka sukaita firar su har bacci ya kwashe su koda sarah ta tashi tasan lily na fashin sallah bata tasheta ba………………
Sai wurin 10 lily ta farka ta kalli agogon dakinsu kai haka nayi bacci sosai dama batasa ran ganin sarah a gefenta ba ga wata malalaciyar yunwa tanaji, toilet tashiga tayo brush ta wanko fuskar ta tayo parlour,tun tana saukowa idonshi ya sauka akanta daga sama har kasa yake kare mata kallo kurrrrr idon nan nashi dasuke kama da maijin bacci a idonta ogiyar batasan yanayi ba……………
Daga ita sai rigar bacci da kadan ta ɗara cinyar ta,babu ko bra a jikinta daga saman rigar kana hango tudun boobs dinta da suke cirr babu ko bra,tana gaf da saukowa benen ne ta fara kwala sarah kira sarahhhhhh sarah baby matar mijinta ta tashi kizo kibani abinci am hungryyyyyyy………….
Kirjin ya adam ne ya tsananta bugawa bai taba ganin lily a irin wannan shigar ba sai yau ita kuma a nata tunanin tasan yanzu bakowa gidan duk sun wuce office gogan kuwa soyayya tasa yadan dauki hutun dole, tsakiyar parlour tashigo ta kara bude murya ke sarahhhhhhhhhhh bata ida sauke zancen ba idonta suka sauka akan shi dake zaune a dinning table yanacin chips………………..
Kirjinta ne ya buga lokaci daya kuma dakiyar ta da Allah yaimata ta halitta tazo mata ta kara take fuskar nan ya adam good morning,wallahi baiji me tace ba yashiga wata duniyar tunani da imagination🤣🤣😅saida ta kara maimaitawa yace lafiya kwana tayi zata shige kitchen ya kalli yadda mazaunan ke wani juyawa yace ke ina zakije haka?………….
Kitchen ta bashi ansa jeki rufe jikinki idan wani yashigo ya sameki a haka fa? Zumburar baki tayi ta juya ya kara kallon bayan ta sai lokacin ya lura da yadda rigar tata ma tayi staining bata sani ba,tana gaf da hawa sama sarah ta fito tace ke daga ina kuma wlh yunwa nakeji kawoman abinda kikayi indan ci zansha magani okay to……………
Gefen inda ta tashi ta kalla taga alamar staining rigar ta tajawo tana dubawa tace Innalillahi daidai sarah na shigowa lafiya?dalla kinga ashe nayi staining baki gayaman ba nagani wlh gaban ya adam din ne zance maki kinyi staining kin fito waje rabinki zindir kinsan kuma yana gidan,ohhh Allah nice rabina a zindir 🤣🤣🤣………………
Sarah ta cigaba da cewa wlh da mama ta ganki kinsan saita bigeki kawai saiki sauko haka to waike ina ruwanki keda kike fitar haka fa saini aini babu aure tsakanina da ya adam ohhhh saini kenan tayi wata shewa tace yadda kike dashi nima haka nike yo in banda abinki nan mezaa gani ace ana so wurina,ohor maki nidai nagayamaki kidaina gaskia…………
Ke sarah ubanki warning kikeman dalla mikoman wayata ana kira yanzu haka wannan tsohon naki ne ohooo dai ɗanyen jini kamata sai tsohon engine 🤣🤣🤣❤️ Allah ya shirya ki kalmar banza bakinki ba wuya eh din bani karta tsinke…………
PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹.......SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……