SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)
Page 14
by @smauta
Jiya su aunty yafindo suka iso gidan abby domin fara shirye shiryen bikin lilyn kowa yayi busy mama dasu aunty yafindo sun bazama kasuwa hadoma lily lefe dan kuwa Alhaji najib kudi ya saki ba yan kadan ba almost done sai abinda ba'a rasa ba su gama gobe sukeson fafutukar siyan kayan gida,sai gab magriba suka dawo har lokacin kuwa lily da sarah basu dawo ba sunacan neman fabric da lily zata saka a cocktail party dinta……………
Karcat suma suka dawo aunty yafindo ta kallesu idan baku ba mu andai samo komai ko? Babu wanda lily kema shagwaba taji kamar mahaifiyarta na raye sama da aunty yafindo fadowa jikinta tayi ni wlh nagaji,da wuri haka har kin sare biki ya gaji haka yar lele saikin daure kuyi dai kugama next week ko kofar gida bazaki fita ba sbd gyara In Shaa Allahu zamu gama kafin lokacin………..
Mama ya gajiya ku akwaita fa kuje kuci abinci kuyi sallah anjima zamuje daku a fara duba kayan abby ya bayar da kuɗin idan kunyi sallah kuje keda sarah kuyo godiya ko,to mama nan sukabar kayan da suka sawo din sukai sama kowa da tashiga alwala cikinsu da wanka ta hado sbd zafin garin suka idar sungama cin abinci ne lily tace suje gun abbyn………………
Shigar su keda wuya suka tarar da ya adam da abbyn kamar ma magana sukeyi,har zasu koma abby yace su shigo yau kusan sati hudu kenan bai karasa idon shi a na lily duk abinda zai hadashi da ita yayi backing dinshi saboda peace na zuciyarsa,Abby barka da dare hajia saratu manyan mata haka abby ke kiranta duk lokacin da yake cikin nishadi Abby ina wuni lafiya lau sarah baby,lily ma tace abby ina wuni lafiya lau………..
Amarya har wani kyallin goshi take adam kagani,baiso abby yasashi a maganar su ba dan tunda suka shigo baiko kalli kanshi ba,da kyar ya dago idonshi sukayi 2 👀 kirjin shi ya fadi ji kake rasssssssss,ya adam ina wuni suka gaishe shi a tare lafiya kawai yace abby na lura da shi tsaf da yanayin shi godia suka fara jera ma abby da addu'a yaji dadi sosai yasa masu albarka sannan suka fice………….
Abby ya maido hankalinshi tsaf akan adam yace inajin ka yayi shiru ba magana nake dakai ba abby Allah dagske nake ni banida wasu kudi da zan bayar a yanzu,bakadasu kace fa a dake yace eh banida su wanda ke gareka fa sai lokacin ya dago yace abby kudina bana haka bane fa,bangane ba adam idan banida rai kaiba mai aurar dasu bane wazai masu kayan daki sama dakai kai ba uba bane a garesu……………
A'a inaji rannan tana cewa niba uba bane a wurinta meyasa yanzu za'a titsiyeni ace sai nayi mata kaya na abu abby banida su nadaice abincin da zaaci wurin biki zanyi amma kayan daki dan Allah kayi hakuri idanun nan sun kada sunyi jawur,kalleni da kyau ka maimaita man abinda kace kara sunkuyar da kanshi kasa yayi yace kayi hakuri Abby………….
Shikenan bakomai abincin ma mun gode zaka iya tafiya,salaf salaf ya baroma abbyn parlour ya fito bai zame ko ina ba sai majalisar su galaxy ne ya fara tsokanar shi Gwarzon maza namijin dunia,adam yace mazaaaaaa suka wani kashe duk matsalar daya kwaso a gida fitar da ake cafkewa anan ta mantar dashi adam mutum ne mai zaɓe idan ya yarda dakai hmmmm zakasha mamaki……......
Angama sayen komai satin bikin ake jira kawai aje ahau jera yau aka tashi kuma aunty yafindo ta fara aikinta macece no nonsense gyara ta farama lily ta ciki ta waje yau kawai da akai dilke bakuga yadda yarinyar ta kara murjewa ba ta fito fesssss magungunan su na Fulani kala kala take bankama lily,wani ta iya sha ta sauki wani kuma sai anyi dagasken gaske take ansa gida yayi busy mama da sarah kansu a chargy yake da ka gansu kasan ba'a natse suke ba hidima ce up and down ba abinda zamuce sai fatan alheri lily💃💃💃……………….
Mutanen gembu sun idasa isowa gida ya ɗinke har jere anyo,jibi kuma za'a fara hidimar bikin,sarah yane amarya dan Allah zoki rakani ina? Dan aljanna ne yazo yauga bara'uba dama nike rakaki idan yazo a'a wlh ni kawai tsoron shi nakeyi kinga abubuwan da yakeyiman?ina nagani kuwa ɗanyen jini ai saida tsohon engine kije kawai Allah tsare idan da rabon ya farkeki tun gida ai kinyi bayani dama wannan tsaffin da shegiyar jarabar tsiya😁😁😁kinga ni kwanciya zanyi ba inda zanje da kinga yana shirin maki wani abu kawai ki kwaso a guje,wai me yazo yi maki da daren nan sauran kudin nan nace ya kawoman sarah tace okayyyyy hakane saikin dawo to…………………
Kwas yar kwalisar ta haka ta fito ta window dakinshi yake kallon ta tana tafiyar nan tata fesssss hasken gidan ya hasketa wani kyau ta kara a idon sa A'uzubillah ya furta jin ya fara sake sake kan matar da ba tashi ba,adam kenan,harta bacema ganin shi sannan ya saki labule kobaa fada mashi yasan waye yazo mijinta ne,wata zuciyar tace shikenan kanaji kana kallo yarinyar daka raina kayi dakon soyayyar ta shekaru ashirin da shidda nan da jibi wani zai maka iyaka da ita ta har abada??????????………………………
HAUSAWA SUKA CE RANA BATA KARYA SAIDAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA🫰💃💃💃💃 A YAUNE ZAA FARA GUDANAR DA SHAGALIN BIKIN FATIMA LILY DA ALHAJI NAJIB…………. COCKTAIL PARTY
Amarya ce fa taci ƙurus ga yarinya beauty pro na hango tsaye akan wannan kyakkyawar fuskar tata tagama tsara mata kwalliya ya Allahu maganin mai tsafi Allah yayi halitta,shakikan kawayen lilyn ne anan gida da sarah suna jiran amarya tagama shiryawa ga motoci can mijin ta ya bada akaisu meena event center inda za'ayi taron na kece raini,koda suka gama kasa suka sauko aka yi masu hotuna da iyayensu harda abby dan manya sunce bazasuje wani cocktail party…………………..
Adam ne yashigo gidan yanzu daga office yana parking ya hango tawagar amarya na fitowa kin fitowa yayi yana kallon su tana ta safa da marwa a filin parking na gidan nasu,from no where yaji wani abu mai dumi nabin fuskar bi da sauri yasa hannu ya shafo da mamakin shi sai yaga hawaye ne ya daki stairing motar yace noooooooooooooooooooooooooooo😅🫰🫰haba ya adam nidai nace yessssssssssssssssss sabon jini saida tsohon engine 🤣 🤣 🤣…………………
Kukan shi ya rizga cikin motar nan yafi minti arba'in bai fito tuni sun ma dade da tafiya yunwar cikin shi ta fiddo shi daga motar ya kwaso laptop dinshi sukayi kicibus da abby na fitowa daga sashen mama gefe ya koma ya saita natsuwar shi barka da dare, yawwaaaaaa wai ina ka shiga ne badai sai yanzu ka dawo ba? wallahi kuwa abby wasu ayyukan ne suka kunnoman kai ba lokaci yanzu ma a gajiye nake wlh, Allah ya taimaka kaji yasa albarka a nemanka kaji Ameen…………
Mamace ta fito ta gansu tsaye bakin kofa daman kana nan yafindo nata neman ka,wlh mama office ne suka sani gaba aiki nake kullum wani zane ne yakeda gyara kuma ranar Friday mukeso muyi submitting mama tace friday jibi kenan eh mama Allah ya taimaka ai llokacin dana fita nasan baku tashi ba shi yasa kawai na wuce, yanzu kuma shigowata gidan kenan na tsaya gurin abby idan nayi wanka na huta zan shigo,mama tace to Allah yasa,abby dama wurinka nazo gani maman yara,munyi tuya an mance da albasa masu curtains ne suka kirani kasan nace maka sasu kawai nayi su dinka munyi rabin payment bamu idasa ba sunada sauran 1.2 hannun mu shine nace bari in fada maka fa har ansa curtains bamu ida biyan kuɗin ba……………..
Maman yara ba'a tausayina duk nema na na shekara nawa zaki cinye keda diyar son nan taki to abby ya za'ayi Allah de ya karo arziki da wadata da lafiya, mungode wlh Allah ya biyaka da aljanna abby Amin,kallon adam yayi yace Adam na'am kaba mamanku kudin data bukata nayi exceeding limit dina na yau,ammmm abby kar kaiman maganar komai kudi nace ka tura ba neman baasi ba,kasa magana yayi jijiyoyin kanshi na fitowa rado rado yace okay,mama ta juya ta shige gida shima ya yunkura zaibi bayan ta Abby yace…………..
Adam na'am fito a mutum dinka muyi magana ta tsakanin da da mahaifi wacce ba boyo ko kunya a cikin ta wacce ba tsoro ko shakku a cikinta wacce zuciya zata fadi gaskiya baki yayi alƙalancin fadar gaskiya kuma,YAUSHE KA FARA SON FATIMA BANSANI BA?????????????????????????????????
ƘARA ƘAƘA ƘAƘA GA AKUYA GA KURA LET'S GO MU HADU A NEXT PAGE 🫰💃💃💃💃💃💃💃💃
PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹...SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……