SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)
Page 15
by @smauta
Duk wani process yabi har ya shigo dakin shi hand luggage dinshi ya bude ya zaro charger wayar shi yayi plugging kenan kiran sufyan ya shigo,adam ya dauka yada kirana tsakar dare haka mijin aure,wata dariya sufyan yayi yace 1/0 yauni kaci wasan kenan,shima adam din dariyar yayi yace ya ake ciki ya Madam………..
Tana lafiya madam ya hidima,dan tsaki yayi hidima alhamdulillah,Ma Shaa Allah kira nayi dama in tmby ka gobe zamuje daurin auren dan kasan fa muma tayaka kishi mukeyi bazan je daurin auren nan naji ana ambatar sunan wani ba naka ba,hmmmmm kirana kayi dan kaciman mutunci……………
Nidin banza yadda kace haka za'ayi, Sufyan na'am wlh banyi niyyar zuwa wurin daurin auren nan ba ni kaina amma matsalar cikin gidanmu zaayi shi,muddin banje ba zai zama abun magana a kuma fara zargina kan abinda banso kowa yasaman baki akanshi, sufyan yace haka ne amma ya za'ayi kaddara ce ta riga fata……………..
In Shaa Allah kaima zaka yi aure kayi rayuwa tajin dadi kamar kowa anya kuwa?sosai kana wasa da hukuncin ubangiji a'a to fatana dakai kawai adam ka dage da addu'a itace takobin mumini duk yadda rayuwa tazo cikin zafi ko kunci muddin ana tuna Allah a cikinta sai kaga komai ya lafa…………
Duk da ban taba shiga irin halinda kake ciki a yanzu ba a yanayin ka yana nunaman kana cikin damuwa amma inda nagodema Allah kai mutum ne daba kowa ke iya gane menene asalin damuwar ka ba zaka iya ɓoye damuwar ka ba tareda an ankare da hakan ba, abinda nakeso dakai kacigaba da hakan karka fasa Ina Shaa Allahu,kaine da nasara abokina……………….
Adam Adam,ummmm meye wai naji kayi shuru bakomai sufyan na fara deciding wani abu ne mene shi bayan bikin nan zanyi requesting a office su maidani branch dinmu dake lagos in dagama kanon kafa koda na tsawon 6 month brain dita ta huta lokacin da zan dawo nasan duk wata damuwa da nake ciki a lokacin ko bata tafi ba ta ragu kuma na samu change of environment………………
Banki ta taka ba hakan da kayi shine abinda ya dace kuma itace hanya ta farko da zata saka ka fara healing ba tareda tunanin lily ba,amma gida za'a yarda yesss zance kawai daga office ne suka bukaci hakan ba zama na dindindin bane sufyan 6 month zan nema idan tamun dadi na cike shekarar sai in dawo ko?yayi Allah yasa haka shi yafi zama alheri…………..
Ameen,kana ina ne gani a tahir gidan ya cika ne da mata sunata hayaniya shiyasa na baro gidan idan kurar ta lafa zan koma,goben sai muzo tanan mu wuce tare ko eh Allah ya kaimu goben Ameen ya rabbi,suka katse wayar ya jona chargy ya fita waje neman abinda zaici ya kwanta dan wnn sinasir din kadan yaci idan dari yayi bayacin abinci mai nauyi kafaji turawa🤣…………………..
Sarah dake da lily kuje dakin yayanku ku kwana mana sukuma kawayen naku saiku bar masu dakin naku,ina yayan yaje ne kinsan halin shi wai gida cike da mata yayi hijira to shikenan bari mukoma can,sarah taje ta kira lily wacce duk an wanke fuskar nan tace mata mama tace sukoma dakin ya adam su kwana🙄shikuma yana ina yo………………..
Mamatace ba'a gidan zaya kwana ba,bari in dauko wayata toh sai muje,wayar ta kawai ta dauko basu zame ko ina ba sai dakin shi a bude yake wani sanyin rahama ne ya dakesu ga wannan lallausan kamshi nashi na tashi daga ko ina a sassan dakin,lily jikin ta yayi sanyi shigowar ta dakin kamar an zare mata wani noti a jikinta………….
Kamar yau ta fara shigowa dakin haka taji kalle kalle takeyi kmr mai neman wani abu a dakin sarah ce ta kalleta ke wai lafiyar ki kuwa,from no where kawai taji wasu zafafan hawaye na fita a idonta da sauri ta rungume yar uwarta kam kam tana kuka mai tsuma zuciya tun tana tsaye harta gagara tsayawa saida sarah ta zaunar da ita haba mana lily kuka kuma kina cikin farin ciki gskia ba girmanki bane…………….
Lily ta shaki lumfashi ta kalli Sarah da kyau ba girmana bane me kukan?eh mana amarya da farin ciki aka santa bada kunci ba,rabuwa fa zanyi da gida to ba kinason shi ba ahhhh jiman wata karyar iskanci nan kikecemun kin kagara ai maki aure ki huta ranar tazo tun yau kin sare,kinga addua kawai zaki cigaba da yi Allah ya albarkaci rayuwar auren ki,burin duk wata diya mace knn a duniya aure……………..
Haka sarah ta cigaba da lallashin lily hatta saki kwance suke akan gadon sunata yar firar su akan yadda cocktail party dinsu ya bada ma'ana,aini wlh naji haushi da baizo ba shiyasa yanata kirana naki dauka,haba kekuwa ki mashi uzuri babba kamar shi a cocktail party ba aji amma zai aureni 😂 har ya nemi ya cire wando gabana ko😂😂😩wnn kuma itace sunnah ta auren kema ita kike kwadayi………..
Kima bar wnn tunanin wlh to nabari uwata saratu hoto ne dama naso muyi da kayan tunda baizo ba shikenan,gobe anyimana na daurin aure,wai gobe kamar yanzu nifa matar aure ce ko Sarah,kwarai kuwa har mun sender ki gidan miji ma,wata shewa suka dauka a tare ni kaza wai amarya a taho a baroni ni kadai sarah tace kwarai daga ke sai halinki😂🙏🙏🙏🙏…………
PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹...SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……