FREE PAGE-3
_*XAYYEESHERTHUO FANS CLUB ARADU SHARHINKU NA TAHIYA DANI🤣🥰💃💃INA YINKU IRIN SOSAI DINNAN*
Taci karo da mai tallen alewa.
Tsayawa tai kamar kamila.
"Ina kwana Baba mai alewa?"
Washe baki ya yi,yana "lafiya yar nan,na nawa za abaki?"
"Ni fa da yawa ina so daman kakace ta ce in siyo za ta yi sadaka."
Mai alewa son kudi anji banza.
Tuni ya sauke alewa kasa yana washe baki, "ma sha Allah ki ce yau bani ba wahala anyi an gama duka zan bar miki jaka biyu."
Ameenatou ta washe baki.
"Tab ni dai sai dai in zaka bari jaka daya ai sari zan yi ma."
"Haba yar nan alewar fa ba wani riba duka kudinta kenan."
Ameenatou ta ce, "Shikenan, Shikenan to wallahi na fasa siya." Ta karasa maganar tana kokarin tafiya.
"Haba 'yata ayi haka kuwa? To zo na bar miki jaka daya da rabi,bara ajuye miki aleda."
(Alewar da dukanta ba ta kai na jaka dayan ba ma amman dan son zuciya za a saida jaka daya da rabi,hhhh Alhaji baba anga bati adole za ama 'ya wayo)
"Yawwa to zubamun aleda nikam sauri ina yi kar kakata tamun fada."
"Yi hakuri yar nan yanzu ma kuwa zan sa miki."
Mai alewa harda yar wakarsa yana murna yau ya ci ganima ya zuba aleda tare da mika mata.
"Yawwa yammata bani kudin to."
Kallon cikin ledar tayi kan ta ce, "to rufe idonka ni karka kallemun kudina da yawa kaka tace kar inna ciro kudi gaban mutune."
Rufe idon ya yi yana , "Yo ai da gaskiyar kakarki duniyar nan ce yanzu sam ba yarda."
Kallon tai ta tintsire da dariya.
"Aradu alewar nan taka kwai zaki."
"Bari kawai 'yar nan ai kadan ma kikaji sai kin sha farar can Aradu har wani gardi take."
Yana cikin maganar nan ta zame jikinta ahankali tana dariya.
"wai baki gama ciro kudin bane? Ha'ah wannan kaka taki kwai wayo Aradu zan fa bude idona ni kam."
Shiru dai ba alamar motsi bare maganar Ameenatou.
Bude idon da zai yi ba alewa ba Ameenatou ba kudi.
Suman tsaye ya yi yana.
"Ina ki ke ne? Wai ina ki ke ne? Ince yau gamo nayi da aljana,na shiga uku kudina ."
Zama ya yi awajen kawai ya fara kuka wiwiwi. Majina na bin hawaye.
Lekosa ta yi tana dariya.
"Wayyo cikina,ji tsoho na kuka, wayyo Allahna." Kara lekasa tai tana shan alewa tana dariya.
Alhaji Baba mai alewa kuwa kukansa yake yana, "Allah ya isana wallahi,muguwa ja'irar yarinya,Ba zan yafe ba,wallahi ba zan yafe ba koma Aljannarce."
Ganin yaki tashi yasa Ameenatou fara ihu tana.
"Kai Malam,Kai Malam na ce kai Malam." Cikin murya mai tsoratarwa.
Waige-waige ya fara ko zai ga inda ake kiran na shi ammman ina sautin magana kawai yake ji batare da alamun mutum ba.
Ci gaba da magana tayi, "ka bar mana gida,na ce ka bar mana gida in ba haka ba ina daf da shigewa jikinka na fadama zan shiga zan shiga."
Nan da nan cikin tsoho duri ruwa kan kace miye ya fara fitsari a zaune.
Da ta kuma wata kara bai san lokacin da ya zura da wani mugun gudu ba.
AMEENATOU na fitowa dan dariya har da rike ciki tana kwantawa, mussamman inta kalli gun da ya yi fitsari.
Gidan su Furera ta shige tana shan alewarta da yar wake tana dariya.
Innar Furare gwanar kwadayi ta ce, "Ah Ameenatou me aka samo mana ne?"
Murguɗa mata baki ta yi kan ta ce, "Alawar Aljanuce na tsinta a hanya in kuma za ki sha to."
Zaro ido Innar Furare tai , "tab yi hakuri Ameenatou wallahi na koshi ni tsoron Aljanu nake."
Ta kalli Furera , "Ke Zo muje gun tumbiɗa dan wallahi kifi na ke son ci."
Furera ta ce, "Haba Ameenatou dazu fa kina gani da kyar muka sha yanzu in aka kama mu fa."
"Ke dallah bana son iskanci in an samo ma wa yafi ci ina kece da shegen baki kamar sabuwar akuya zauna kar kije ita ma lantanar bani zuwa gidansu Amma ku sani bani ba ku agarinnan kowa ya kama hanyar gabansa,banziya mai idon agwagwi."
Furera ta ji Maganar rabuwa Da Ameenatou tuni ta yi karamar murya, "Goggo Ameenatou dan Allah kiyi hakuri kinji,kar azo tafiya binni ace bani."
Washe baki Ameenatou tayi domin ba abun da ke faranta mata rai fiye da ace Goggo uwa uba kuma ayi maganar birni.
"Kin ci sa'a wallahi yarinya, Allah raya min ke mu sha biki a birni yasin,hhh jeki kiramun Lantus tun yanzu zan mai da ku yan gayu kan Kawu Audu yazo kai mu binni ke Fures ita Lantus."
Lantana zata fita Ameenatou ta ce, "Dalla dawo wawiya ba ki ce mun kin gode ba."
"Na gode Goggo Ameenatou."
"Yawwa yi sauri kuje ku dawo aradu yau tumbiɗa zai sha yasa."
Bai fi minti biyu ba kuwa sai ga Fures da Lantus an shigo.
Ameenatou ta ce, "yawwa wallahi ku goyani mutafi tunda Jiddah matar police ma kawayenta goyata suke."
Ba yadda suka iya haka suka saba Ameenatou abaya tana shan alewarta suna gani ta hana.
"Fures wallahi kibar hadiye yawo ma dan ba sammiki zan ba,ke kam kinyi gadon kwadayi wallahi innarki kamar kuda yaga suga haka take."
Ba abun su tanka ba ta ce asauketa ba ita ba su.
Suna isa gun tumbiɗa Ameenatou ta sauko tana , "Yaya Tumbiɗa wallahi kaf garinnan ka fi kowa iya suyan kifi,har mafarki na yi jiya fa inaci."
Washe baki tumbiɗa ya yi kan ya ce, "Yoo ai na jima da sani kin ga fa har yan binni zuwa suke saye."
Jansa da hira ta fara tana ɗiba Lantana na karɓa.
Duk atunaninsu tumbiɗa bai san me suke ba.
Tumbiɗa irin lutayen mazannanne karfafa masu kirar samudawa.
Sai da ya bari suka diba son ransu suna kokarin fita ya janyo kofar shagon.
Ameenatou ta ce, "Yaya Tumbiɗa zamu tafi ne fa."
Dariyar mugunta ya fara.
"In kinga kun fita agidannan to na maidaku kifaye ne na gasa na siyar."
Jikin Ameenatou ya duri ruwa.
Su Lantana kuwa hawayene kawai ke kwarara.
Tumbiɗa ya ce, "dake Zan fara Ameenatou ina tunaninki duk ban san me kuke mun bane,gani banza ko? Maza zo nan inna maidaki kifin na ga yadda za ki ci ai."
Ameenatou ta gama tsorata baba mai alewaa kawai ta tuna sai ga fitsari ita ma ya fara kwararowa, can kuma ta ce, "Yaya tumbiɗa ba ka ce kana sona ba rannan? Wallahi zan aureka kaji."
"Dagaske zaki aureni?."
Ehmna na fada jiki na rawa.
Washe baki ya yi,"yawwa to ku tafi da kifin da kuka diba duka ga kari ma sai na zo mu zanta ko Amaryar."
Ita ma ta washe baki , "eh sai kazo."
Tana amshewa suka fice adari .
Dan neman Jaraba ta dawo tana, "tumbiɗa mai tumbin giwa wallahi karya nake ma ba zan aureka ba,tab ji ka fa kazami kullum wari wallahi bana sonka wayo na ma ysin." Tana gani ya taso ta zura aguje tana mai gwalo.
Biyota ya yi tana gudu yana yi gashi shi jiki ba kadan ba har tsayawa kallonsa take tana dariya.
Gajiya ya yi ya tsaya yana haki, "zaki sani wallahi ba abun da zai hanani aurenki agarinnan nan da sati daya."
Turo masa baya tai tana.
"Fada ma Duwaisatu ba dai ni ba."
Furera da lantana kuwa sun jima da isa gidan kaka.
Tana shiga suka fara dariya.
Kaka ta ce, "Ya naji zarni wake zarni acikinku kuma?"
Ameenatou ta kalli su Lantana, "wallahi in baku bar mun dariya ba kwalelanku kifinnan,Kaka nice na yi fitsari kuma wallahi ba zan cire kayannan ba jiya fa nasa tab, Tumbiɗa ne ya turfamu ban san sanda na sake masa fitsari ba."
Sallamar da akayine ya katse ma su magana.
"Kaka ga shi kawu Audu ne ya kirawo waya akawo miki."
Amsa tai tana , "to fa Malam Audu da yammacinnan Allah sa dai lafiya."
"Shallo,shallo na ce kana ji na ko?"
"Ina Jinki Inna,ina wuni ina gajiya ya aiki."
"Yoo ni ka daga murya wannan abu naku ba wani nake ba,ehhh fa muna lafiya ya iyalan gidan fatan duk lahiya?"
Ameenatou ta ce, "Kaka kice abawa Okul Al-ameen zan ji muryarsa."
"Toh toh Audu abawa Al-ameen Yar uwarsa na son jin muryarsa."
Dadyne ya mikawa Al-ameen wayar yana "ga shi Ameenatou za ta ma magana."
Rai bace ya karba dan yasan in yaki karba yanzu zai jawa kan shi jidali Yar da bai taba gani ba ta nanike masa.
"Shallo Okul ka mun magana kaji."
Al-ameen ya ce, "kina lafiya?"
Bai jira ta amsa ba ya datse wayar tare da mikawa Dady yana ba network,jin tsanar yarinyar yake ji har ransa mara dalili duk da cewa bai taba ganin ta ba.
Ameenatou kuwa ta dage sai magana take taji shiru
Kuka ta fara, "Kaka ni wallahi ban gama jin muryarsa ba abun ya dauke ni akiranmu shi ni wallahi ban yarda ba."
Birgima ta fara yi akasa tana akira mata Al-ameen
23/10/2021
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER *** SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_
_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 3:23 PM] ***: ***
*IN KINA NA FARKON KAR KI SHIGA WANNAN PLS🙏*
°°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
****
_RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_