FreeArewaPen original
AMEEENATOU 'YAR KAKA
- 1views
- 43chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
NobleWriter
Sample · FREE PAGE-1/2
Wata tsohuwa ce zaune akan kujera 'yar tsugunno tana tankad'e garin masara, a cikin wata 'katuwar 'kwarya. "Oh! Ni Indo, ko ina Ameenatu ta tsaya ne? A ce tun almuru mutum ya fita har yanzu shiru." Shiru ta yi kamar wacce ake fad'awa amsa, wani gutun tsaki ta ja ta ce, "Ni ma na cika mantuwa halin Ameenatu sai dai wanda ba da shi Ibro da Hansai suka haifeta ba, yarinya sai ka ce rainon kaka." Tankad'enta ta ci gaba hankali kwance, ba tare da damuwar komai ba har ta gama, ta mi'ke ta shiga madafa. Kamar wacce aka jefo ta shigo a guje ta bi ta kan 'kwaryan ta yi d'aki, baki bud'e tsohuwar ke kallon garin da ke zube a 'kasa, sannan ta bi sahun 'kafafunta da kallo, tana shirin magana ta ji sallama daga zaure, tana tsaye a inda take ta bada umarnin a shigo, ta hau 'ko'karin tattara garinta da ke 'kasa.Ganin mutanen da suka shigo yasa ta d'agowa tare da mai da fus...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.