AMEEENATOU 'YAR KAKA

FREE PAGE-11

by @xayyeesherthulhumaerath

_*KALAMAN SOYAYYA🤍*_

_Aduk in da zaka kasance ina so ka tuna da cewa Ina sonka, Kuma bana fatan bari, kasan dalili? Kai ne hasken rayuwata zan kasance da farinciki ne kawai in har ina tare da kai, ina kaunar ka_

_________

"Zan ci yana bani abaki ai haka yayu suke ma kanne ko?"ta karasa maganar tana goge hawayen fuskarta.

Kaka ta ce, "Muje Ciki dai."

Suna zuwa falo kuwa suka tarar da Al-ameen zaune yana aiki a system.

Aminatou ce taje ta zauna kusa da shi tana, "Onkul Ka zo mu ci abinci ka bani abaki kaji Allah yaso ma nikam dazu fa ban ganka ba rufe idanuna na yi nikam bab ga komai ba kaji ko."

Hajiya ce ta shigo da sallama tana, "To Ameenatou ga abincinki in bai isheki ba sai akaro.

Ihu tasa tana , "Kaka? Kaka? Kaka kin gani dan abincinnan mai na ci bare in ba hanjin ciki da hantar kwakwalwata Kaka Ni da Onkul kuma zamu ci fa tab wallahi ni akaro Mana."

Karaf Kaka ta ce, "Yoo daman ban da jarabbabiyar rowa wannan dan abinci wa zai ci? Kar ki manta fa ina sane da yadda aka auroki kamar tsinken gazari amman yanzu anzo anci ba iyaka sai hawa kamar fulawa, a tarihin danginku kaf tun daga yayan kakan kakanki ba wadda ta shiga gidan arziki sai ke ko ince ma ku da aka barwa gadon tusa? To ahir wallahi dibo mata abinci iya son ranta ta fiki gadara da gidan."

Ameenatou ta kyalkyale da dariya, "Laaa Kaka daman ana gadon tusane?"

Kaka ta murza ido kan ta ce, "Yoo ba ga shi kinji ba,ban da tusa ba abun da gidansu suka iya yanzu ma Allah rabamu da wannan tusa dan in tayita ina ga sai mun suma sau tamanin batare da sanin inda muke ba."

Tsaki Al-ameen ya yi,yana kokarin tashi.

Kaka ta ce, "Kai Ja'iri ni kake yi yiwa tsaki dan gyatumarka, kana sunkuyar da kai kamar munafikin kwarto har ni za'a kawowa raini a cikin gidan d'ana ni da idan na so zan iya hana kowa zama a cikin gidan nan. Ace daga zuwar yarinya har anfara yi mata hassada da ba'kin ciki abincin ma ba za'a saka mata wanda za taci ta 'koshi ba. Shi kuma wannan me zubin aljanun yana min tsaki saboda ya raina ni"

Dariya Ameenatou tayi sai kuma lokaci guda ta d'aure fuska ganin Al-ameen ya bud'e 'kofa ya fita ta fashe da wani irin kuka tare da kwanciya a 'kasa tana birgima kamar wacce taji wani mummunan labari, lokaci guda hankalin Kaka ya tashi dan a tunanin wani abu ya faru da Ameenatoun.

Hajiya Babba dake tsaye a gefe ma ta matsu kusa tana 'kokarin ta'ba Ameenatou, da sauri Kaka ta karasa kusa ta bige hannun Hajiya Babban ta fara magana cikin kuka tana fadin "Ba ga irinta nan ba anyiwa yarinya mugunta, yanzu haka ma mayu suka kamata dama tunda muka shigo gidannan na ga ana nuna alamun ba'ayi murna da zuwarmu ba, wayyo ni Indo na shiga uku ya zanyi da ha'k'kin marainiya"

Gefen zani ta saka ta fyace majina ta cigaba da cewa''Kin tsaya kina kallona ne ba zaki wuce ki kiramin d'ana ba yazo asan wacce za'ayi dan ni ba zan lamunce haka ba."

Jiki a sanyaye Hajiya Babba ta mi'ke za ta fita sai dai kafin ta 'karasa ta jiyo murya Ameenatou tana magana cikin shesshe'ka ta ce" Ni fa Kaka ba abinda aka yi kawai yunwa ce inaji yasin kamar hanjin cikina zasu tsinke na mutu haka nakeji."

Kaka ce ta mi'kar da ita zauna ta ce" Bayani zakiyi ai 'yar lelena ga abinci maza kici a 'karo miki dan wannan ba isarki zaiyi ba nasani."

Kuka Ameenatou ta fashe da shi tana fad'in" Ni wallahi ba zanci ba tare da Onkul Al-ameen za mu ci ya dinga bani a baki."

Shiru Kaka tayi kafin ta ce'' Yo ai wannan ba wata matsala bace bari a kirashi ya baki ai kema 'kanwarsa ce"

Kallon Hajiya Babba tayi wacce ke tsaye tana kallon sangarta irin na Ameenatou, Kaka tace"Ke Mero maza je ki kiramin yaron nan Ameenu ya zo ya baiwa 'yar uwarsa abinci a baki."

Cike da ladabi Hajiya Babba ta ce" Mama yanzu kamar Ameenatou ace sai Al-ameen ya bata abinci a baki saboda sangarta ina gani hakan kamar bai dace bawai dan wani abu ba sai dan saboda girmanta yanzu ai abun kunya ne wani ba'ko ya shigo ya tarar ana bata a abinci a baki ba ciwo ba komai kawai dan shagwaba."

Aikuwa me neman kuka an jefe shi da kashin awakai, nan Kaka ta fara surfa bala'i tana fad'in Hajiya Babba ta raina ta daga zuwa gidan d'anta zata fara zaginta, hakuri Hajiyar ke bata amma Kaka ta runtse ido sai masifa take yi.

"Yoo zan ga yau ni da ke wayafi wani mahimmaci awajen Audu in kuma ke kika bani Nonon da na shayar da shi sai ki fadamun." Ameenatou dake gefe ganin fad'an Kaka ba tsayawa zaiyi ba ya sa ta isa ga plate din abinci ta fara ci hannu baka hannu kwarya dan abincin ya mata dad'i sosai farar shinkaface da miya wacce taji had'i ga nama, hakan yasa bata ko 'kara kallon inda Kaka ke tsaye ba bare tasan me take fad'a.

Hayaniyar da Kaka ke yi ne ya fito da Hajiya 'Karama, ta taho tana rangaji kamar wata matashiyar budurwa dan ita irin matan nan ne ta suke wayayyu, batare da ta kula Kaka ba take tambayar abinda ya faru ko da Hajiya Babba ta fad'a mata yadda akayi sai ta ta'be baki ta fara magana cikin isa ta ce" Banda abinki Mama ta ina Al-ameen zai fara bawa wannan 'kazamar abinci a baki ai hakanma ba zai yiwu ba gaskiya dan idan ya taba wannan kazantar kila kwana zaiyi a asibiti dan kwalera ce zata kama shi."

Ameenatou ta kwalara ihu da sai da ya karade ilahirin gidan.

Kaka ta...................

*Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments*

_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER *** SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 4:28 PM] ***: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

****

_RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_