FREE PAGE-12
_*KALAMAN SOYAYYA🤍*_
_Ba kyau ko dukiya zan so ba zan sokana saboda ka daukeni tamkar sarauniya, hakan na bani tabbacin cewa babu wata da zata iya kasancewa acikin zuciyarka bayan ni, ina sonka ina kaunar aduk inda kake ka tuna cewa kai ne farincikina_
_*Oyoyo Harbeebbty Zeey Er Mutan Zazzau🥰🥰🥰💃💃💃 Tabbas ina cikin farincikin dawowarki*_
_*🎂🎂🎂Appy bornday Anty Zee (African Black Coffe) admins din Shahararrun Novel Allah ya karawa rayuwa albarka)*_
___________
Tuni Ameenatou ta hau birgima ta jefar da plate ɗin abinci, ta fara kakkafe ido tamkar wata mai aljanu tana faɗin, "Wayyo Allah Kaka wallahi yasin wannan Ƙaraman Hajiya ce ko wace suke kiranta Mayya ce ta kamani, Wayyo zata kashe ni." Ameeenatou ta kwallara wani gigitaccen ƙara dai dai lokacin da Daddy ya shigo gate ɗin gidan, domin ya fita ya ɗan siyo musu yan kayayyakin da zasu bukata kafin gobe in Allah ya kaimu, ko gama gyara parking baiyi ba ya fito daga motar yayi cikin gida da gudu. Dai dai lokacin da Kaka ke saka na ta ihun ta nufi Ameenatou tana faɗin, "Wallahi Zulai kike ko waye sai kin sakamun kurwan jikata, dama ai na ji tarihin dangin ku an ce kaf Mayu ne saboda Maitanku ma kuka ƙi Auruwa shine aka laƙaba ma Ɗa na, to wallahi jikata ta fi ƙarfin ki kurwan ta kur, ki zo kawai ki tsallaka ta tashi."
Daddy ne da Al'ameeen suka shigo a ruɗe suna tanbayar lafiya. "Yauwa gara da Allah ya kawo ka Audu." Kaka ta faɗa ta kakalo wasu hawayen, tana face majina.
Gaba ɗaya Daddy ya ruɗe ya isa gurin kaka da Ameenatou yana tambayar kaka lafiya.
"Ina fa lafiya Audu garin jajibe-jajibe irin naka kaje ka Auro mana Mayya, gashinan ta kama Ameenatou." Kaka ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka tana cigaba da jijjiga Ameenatou.
Ita ko Hajiya ƙarama bata taɓa zaton sharin su kaka da wannan figigiyar yarinyar ya kai haka ba, Tabbas sai ta yi maganin su kuwa.
Gaba ɗaya Hajiya Babba ta kasa motsi saboda da ganin sharri irin na Ameeenatou ƙiri-ƙiri domun ganin idon ta ta ga Ameeenatou na ma Hajiya Ƙarama gwalo da dariyar mugunta.
"Wai Audu tsayawa kayi kana kallon ta ba zaka ɗauki mataki ba har sai jikata marainiyar Allah ta mutu ne."
Kaka ta ƙarra saka kuka tana sallallami wai matan Audu sun asire mata yaro dole ta zo ta neman mai taimako tun wuri tun kafin su rabata da shi.
"Ba dan na tuba ba tabbas yau da kunga asirin asali mu da muke mai da mutane kashi ma, to wallahi ahir dinku."
Gaba ɗaya sun ishi Al'ameen ji yake kamar ya kwashe su ya mai da ƙauye, don shi irin mutanen nan ne da bai son hayaniya ya dawo ko hutawa bai yi ba ya haɗu da jaraban su kaka, tsaki ya yi ya juya zai fita, Kaka ta wuf ta sha gabanshi.
"Ka ga wanda kayi ma tsaki nan gasunan tsaye da Audu da Mero, saboda baƙin hali an tsotsa a Nonon Uwa kana ganin ƴar uwar ka rai a hannun Allah Matar Uban ka ta kama mata kurwa Amma kake tsaki zaka fita to ba in da zaka sai Ameeenatou ta tashi eheee."
Kaka ta ƙarisa maganar tana fiki-fiki da ido.
"Audu in har na isa da kai ka sa Zulai ta tsallake Ameenatou, bayan ta tsallake ta kuma ta tashi sai ka rubuta mata takardar saki ta ƙara gaba don ba zamu zauna sa zuri'ar mayu ba, in kuma kaki ni yau a matsayina na uwar ka sai na ɗaga ma Nono kabi duniya eheee."
Gaba ɗaya yan falon sai da suka razana da batun kaka, ban da Ameenatou da ita matuƙar murna tayi, maganar kaka kuma yayi dai dai da shigowar Hassana da Hussaina ƴaƴan Hajiya ƙarama sun dawo daga makaranta, sosai suka razana suma da maganar kaka.
*************************
*ƘAUYE*
"Wallahi Furera ina ta kewar guggo Ameenatou, ita ko tana can Binni tana cin daɗin ta."
"Ke dai bari kawai Lantana ai ji nake kamar nima nayi tsuntsuwa in ganni a Binni ɗin nan."
"Waya ga Fure a Binnni, Tab." Lantana ta faɗa tana kwashewa da dariya.
"Ki ce dai waya ganmu a Binni ni da ke, kin ji ta shi mu shiga gari muga ina muka nufa ni duk zaman ma ya isheni fa." "Uhmmm ki bari kawai ai Ameenatou ta fara bamu kewa tun yanzu, na san da tana nan da tuni mun shiga gari.
*************************
"Audu baka ji mai na ce ba ne wai."?
"Naji Inna Amma don Allah ki soke maganar sakin nan zata tsallaka Ameeenatou, insha Allah zata tashi."
Daddy ya ƙarasa maganar ya na mai durkusawa a gaban Inna. Gaba ɗaya yaran gidan sai suka ji sun tsani Ameeenatou don duk ita ce silar komai.
"Kai Auduuuu Alllah............!
*in ga ruwan comment sai ku ga ruwan typing*.
*TEAM ƊIN AMEEENATOU GAFA AMEEENATOU TA ISO BINNI DAGA ZUWA TA FARA DA MATAN GIDA.*🤣🤣🤣
LITTAFINA NA KUƊI NE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER *** SANNAN TA MAGANA TA WHATSAAP TA NUMBER, KO KUMA A TURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abbdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU ALL, SHARE&COMMENT FISABILILLAH🥰
*Urs Xayyeesherthuo*💜 [12/1, 4:28 PM] ***: ***
°°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
****
_RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_