FREE PAGE-13
_*KALAMAN SOYAYYA🤍*_ _Zan So mukasance tare ne kawai da son ranka inko baka bukata na zabi bawa zuciyata hakuri duk radadin ko kunar da za ta ji,amman ina so ka sani,kar ka manta ina kaunarka har cikin raina._
_*TEAM AMEENATOU AYI KARO-KARO ASIYA MATA ABUNNAN FA🤭KO CIKO NE SAI AYI*_
_*MY GROUP MEMBERS ANTIES MASU SHARHI BARKA 😁SU GOGGOS MASU ƊUMAMA GROUP DAN ALLAH ABAMU WAJE MU SARARA😒✋*_
"Aradun Allah ko da Malam ne zai dawo yau ba Zan Yarda Zulai ta ci gaba da zama agidannan ba." Cewar Kaka tana fiki-fiki da ido kamar jinjirar munafika.
Dady ya rasa abun fadi kawai yana kallon ikon Allah duk anyi shiru a falon.
Kaka ta numfasa kan ta ce, "Ince so kake sai ta gama tsotse mata jinin bata tsallaketa ba? To maza ki tsallake mun jika komai ma ya biyo daga baya."
Dady ya kalli Hajiya Karama kan ta ce, "ki tsallaketa dan Allah."
Kamar ba za ta yi ba can kuma ta tuna abun da bata zato ma kaka zata iya abu mafiyin tunanin kowa.
Hakan yasa ta tsallake Ameenatou.
Tana tsallake ta kuwa ta ta shi tana attishawa tana, "Kaka, Kaka ki zo ta sakeni,Wallahi ta sake ni, Wayo kwakwalwar wuyana zafi anan ta shakeni kaka mutuwa zan yi shikenan wuyane ina jin ta kwashe hanjin wuyan."
Riketa Kaka tayi tana hawaye da shekan majina, "Yi Hakuri Ameenatou na kin warke ba za ta kara kamaki ba kin san bana son maganar mutuwannan na fada miki ban so wallahi Ba za ki mutu ki barni ba aradu da ki mutu gwanda mun Audu ya mutu ma."
Ta juya tana kallon Dady "Ka na gani kana kallo Matarka zata cinye mun jika? 'Yar 'Yar Uwarka amman ko ajikinka an riga an shanyeka ko? To ahir na ce rubuta mata takarda saki Hamsin dan uku ya yi kadan ina kallo."
Dady ya kalli Kaka araunace yake fadin, "Inna Dan Allah kiyi hakuri bana so kiyi fushi ki bata dama zata gyara kuskurenta."
"Iyeeee, na ce Iyeee Ashe ma ban isa da kai ba,yoo ko Malam Mahaifinka kafin ya bar duniya bana fada ya ja bare kai na ce ka saketa tun kafin in tarwatsa gidannan."
Ameenatou ce ta ce, "Umm Kaka Kin san miye? Kin ga ita ta girka abincin can kuma ya yi dadi abarta tana mana girki irin wannan in ta kuma kamani sai mu korata ko?"
Kaka ta ce, "kun ga 'Yar Albarka an cuceta kuma ta yafe dake batai gadon bakin hali ba, tabbas yau kun ci sa'ar Ameenatou ne amman da yau sai Dai ka zaɓa ko zulai ko ni Indo."
Ficewa Al-ameen ya yi, ya yin da Hassana da Hussaina su ma suka nufi dakinsu.
Kowa ya watse afalon anbar daga Ameenatou sai kaka.
Kaka ta ce, "Yoo ni naga gyatumar fitina wato duk kowa ya yi daki anbarmu afalo gamu filajin ko? To ba a isa ba, ina kike Mero,mero,mero na ce ki fito nan."
Hajiya Babba ta fito tana, "Inna Gani." Ta karasa maganar tana durkusawa gabanta.
Kaka ta ce, "Ince mu anan kukeso mu dawwama Bama da dakin zamane?"
"Aa Inna ga daki can angyara har kayan ku ma ankai can."
Kaka ta ce, "To maza amun iso ga dakin nima inje in kwanta a kushin kamar kowa."
Sai da Hajiya ta kaisu kan ta dawo dakinta.
Ameenatou tsalle ta fara kan gadon tana waƙa, "Tab Kaka Ai bani ba kauye yasin kin ga gadon nan da di inaga irinsu ne a aljanna."
Kaka ta latsa katifar , "Ba Shakka wannan abu kwai dadin zama kana lumewa kamar ka samu naman dawisu."
A dakin suka hini har dare sai kai masu abinci aka yi, ban da tabe-tabe ba abun da Ameenatou take yi.
Washegari.
Ameenatou ta fita tana zagawa wani daki ta hango.
Dakin Nauwara da Nusaiba, dake Nusaiba na bording bata gidan ita ko Nauwara tana aiki sai dare take dawowa in ta fita tun safe.
Nauwara ta shiga wanka ta ciro kayan da zata sa harda su bra da pant Ameenatou ta shige dakin ba abun da idonta ya fara kaiwa sai kan bra din.
Dauka tayi tana dariya sannan ta daura kan kirjinta , "Aradun Allah zan nunawa Onkul Al-ameen ya siyamun wannan abun saka Nonon ai nima na girma jibeshi ba laushi harda kushin aciki."
Nauwara na fitowa da Mamakinta ta tsaya kallon Ameenatou tana, "Lafiya? meya kawoki dakinnan?"
Washe baki tayi tana, "Ni ce Ameenatou da Kaka mu ka zo kuma."
Murmushi Nauwara tai kam ta ce, "Welcome Ameenatou ta ajiyamun kayan in sa ko?"
Ameenatou ta ce, "Aa ina Zuwa bara inje inunawa Onkul nima ya siya mun ina sa Nono ciki."
Kallonta tai sama da kasa bata ga kirjin da za asawa bra ba kawai ta kyalkyale da dariya.
Ita ko Ameenatou ko ajikinta yafawa tai a kirjinta tana tafiya tana kallo har ta isa bangaren Al-ameen.
Kwance yake yana sharbam barci hankalinsa kwance.
Dukansa ta fara yi tana, "Onkul tashi ka siyamun wannan ka tashi ka siyamun."
Yana bude ido.....
*Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments*
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER *** SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_
_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 4:28 PM] ***: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
****
_RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_