FREE PAGE-15
_nayi mistake fejin baya maimakon 14 nasa 13 so take note wannan 15 ne dayan 13 din 14_
_*Afwan Ameenatou fans bana da lafiya ne kuka ji shiru🙏*_
_*Wannan fejin naku ne Harbeebbty da Aminiyata Ada kuji dadinku kadan domin namijin jajircewata yasa na baku fejinnan mai kama da ku😁*_
Free Page na daf da karewa wa inda suka biya sun huta😆 _____
Dai dai isowan wani mai mashine gashi ya shigo da gudu, Al'ameen bai san lokacin da ya dira a motar ba ko rufewa baiyi ba ya janyo Ameeenatou suka tafi tamkar zasu faɗi gaba ɗayan su yayi sauri ya dafe Motar ta tashi.
Wiki-wiki Ameenatou tayi da ido ta lafe a jikin shi, tuni har Mutane sun fara taruwa kowa na tofa albarkacin bakin shi, finciko ta yayi ya jefa a Mota yana huce ya shige Motar bai saurari Mutanen da ke gurin ba ya figi Motar ya harba kan Titi, Sai da sukayi tafiya mai Nisa ba wanda yayi magana a cikin su gaba ɗaya Ameenatou a tsorace ta ke don ta sadaƙar da mashine ɗin nan ya bige ta sai tayi rugu-rugu, kawai Hausi ta tuna maƙociyar su da Mashine ya bige sai dai a ka cire mata ƙafa, tana gama wannan tunani sai kawai ta fashe da kuka.
Parking Al'ameen ya yi dai dai wani guri da ba Mutane, ya fito a fusace ya jawo ta ya wanke ta da Mari, yana faɗin, "ke wacce irin mahaukaciya ce yanzu da Mashine ɗin ca ya bigeki fa,! banza wawiya ƴar ƙauye kawai,! kuma wallahi ko ki mun shiru ko in tafi in barki a gurin nan masu satan mutane su harbeki kowa ya huta da jaraba, kawai Daddy ya tashi ya jawo mana Annoba a gida.!
"Onkle ya fa isheka don ba tsoron ka nake ji ba da zaka tasani kana mun masifa, kuma Yasin muka koma gida sai na faɗa ka da kaka ba dai ni ka mara ba, wallahi sai na ce ka mun shegen duka, ka turani titi kuma wai Mota ya kasheni saboda ba ka ƙauna ta."
Ameenatou ta ƙarasa maganar tana juyawa ta shige mota ta cigaba da kukan ta.
Takaici gaba ɗaya ya gama cika Al'ameen ya rasa mai zai ma yarinyar nan ya huce ne, ji yayi har kan shi ya fara ciwo don shi har ga Allah bai son dogon magana balle hayaniya amma wannan mayyar yarinyar ta sa shi yana ta buɗe murya a titi.
Komawa motar yayi ya ja ya kama hanyar komawa gida da ita yace sai dai duk abun da zai faru ya faru, Muryan ta yaji tana cewa.
"Onkle ya zaka maidani gida baka siyamun rigar Nonon ba.?
Banza yayi da ita, da ta fasa wani uban ihu ta tuma akan kujerar Motaar bai san lokacin da ya taka wani wawan birki ba, kaɗan ya rage ya bigi na bayan shi.
"Wayyo Allah na ni Al'ameen yau Allah ya haɗani da jaraba.!
wani tunani ne ya zo mishi a rai sai ya juya Motar ya nufi Asibitin shi da ita, ita kuma ta cigaba da birgima da bige-bige a motar kamar mahaukaciya.
Suna isa ya fito ya buɗe gurin da take ya jawo ta yayi hanyar Office ɗin shi da ita, Sister Surayya ce ta hangoshi da sauri ta taɓo wacce take kusa da ita ta ce, "Sister Rukky ga mutumin ki can ya shigo da wata ƴar ƙauyen yarinya, yanzu ya shige Office ɗin shi."
"Uhmm ni wallahi na haƙura da Doctor Ameeen kullum ina bin shi yana wulaƙanta ni."
Wayar ta ce tayi ƙara da take ajiye a tebur ɗin gaban ta, jawo wayar ta yi, zaro ido tayi ganin mai kiran na ta.
"kinga wai yau ni Doctor Ameeen ke kira da ma yana da Number ta ne.?
Ta faɗa fuskar ta ɗauke da mamaki.
" To ki ɗauka mana kar ta yanke kin san bai kira biyu shi."
Da sauri Rukky ta ɗauka ta kara a kunnen ta.
Amsa sallamar da tai mai yayi ya ce mata, "ki zo Office ɗina ina son ganin ki."
Yana gama faɗa mata haka ya katse kiran.
"Kin ji wai yana son gani na bari inje in ji."
"Ok sai kin dawo."
"Ke Meena ki mun shiru wallahi ko yanzun nan in miki Allura."
Ai bai gama rufe baki ba Ameenatou ta ɗauke wuta, don duk rashin jin ta Allah ya saka mata tsoron Allura.
"Alhamdulillah yarinya tun da na gano lagon ki kin shiga uku kuwa, mara kunyar ƙarya."
Duk a zuciyar shi Al'ameen yake wannan maganar, bai gama tunani ba sai ga Rukky ta shigo tana wani karairaya kamar zata karye dama gata ita ta tafi kaman one sai fuska ta ci bleching ga kafar ta da hannun ta baƙinƙirin.
Tun da ta shigo Ameenatou ke kallon ta, can da ta tuntsire da dariya har ta na faɗuwa ƙasa daga kujera, gaba ɗaya suka bita da kallo suna mamakin mai ya bata dariya haka.
Ita ko in ta ɗago ta ƙara kallon Ruƙayya sai ta ƙara kwashewa da dariya.
"Meeenah! will u shut up! ya zaki ta samu gaba kina mana dariya kamar kin ga mahaukata.!
Al'ameen ya ƙara sa maganar cikin fushi.
"To Onkle ba dole in dariya ba naga abun dariya, dama a mutane ma akwai Muchiya da zani ban sani ba, gani nayi wannan Matar tayi kama da muchiyar kaka da take tuka mana tuwo, kuma wai ƙonewa tayi naga fuskarta fari kafan ta da hannun ta baƙi."?
Ameenatou ta ƙarasa maganar tana kara kwashewa da dariya.
Gaba daya kunya ya lulluɓe Al'ameen saboda irin tijarar da Ameenatou take ma Rukky ya rasa ma mai zai ce mata.
Ita ko Rukky ji take a duniya ba'a taɓa mata cin mutunci irin wannan ba, gashi yarinya ƙarama tana muzanta ta a gaban wanda ta fi so duk duniya, a yau taji tana da ta sanin yin bleaching, da sauri ta juya zata fita Al'ameen ya miƙe da sauri ya bita yana kiran ta, "Rukky please ki tsaya kiji don Allah."
Ko waigowa ba tayi ba, riƙe kanshi yayi da yaji yana sara mai ya koma Office ɗin, samun ta yayi tana ɗaɗɗaga takardun da ke kan tebur ɗin office ɗin.
"Meeeeeenah! wai ke baki san darajar ɗan adam ba ne, baki da hankali wannan ba ta girmeki ba."
"To ni ina ruwa na, ni na ce ta zo tana ma fari da ido tana wani girgiza jiki kamman sandar suluka shine naji ta ban haushi kuma naga kana kallon ta meyasa ni bazaka kalleni ba, ban fita kyau ba ma ni ƴar duma duman Kaka Nono ne kawai ta fini kuma ni ma ya fara fitowa kuma bari ka ganshi."
Ta miƙe tana ƙoƙarin ɗaga mai riga.
"Ke baki da hankali ne na ce miki ina son gani ne.?
"Wallahi ni sai na nuna ma."
Dafa kai Al'ameen yayi saboda tsananin sara mai da kan na shi ke yi..........✍️✍️✍️
TEAM AMEEENATOU HOW MARKET🤣🤣🤣
ni dai na fece Ameeenatouo tabbas tafi ƙarfi na nan fa kishi Ameenatou kaka keyi ikon Allah🤣🤣🤔🤔🏃♀️🏃♀️🏃♀️
IN GA RUWAN COMMENT KU GA RUWAN TYPING YASIN🙄🙄
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER *** SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_
_*Urs Xayyeeshert[12/2, 10:01 AM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
****
_RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_