MATAR GIDA PAGE 17
MATAR GIDA 017
SHUUKRAN/022
P17
Laƙaci guda Ɗalha ya ji kansa ya sara masa ɓacin rai haɗe da damuwa sun haɗu masa lokaci guda,yanzu haka bai san da wanda zai fara ba da Fauziyya da ta haɗa garin tuwo da mangyaɗa a guri ɗaya ko da su Sudais da Suhail da sun hargitsa parlour da kayan wasa, ga Ummu Abiha ta kwaso kayan ƙwalliyar Amirah ta fidda su,yana cikin wannan tunanin ya jiyu murya Afef yana ihu tare da faɗin ''Dady kaga Rayyan yana dukana ban yi masa komai ba" tsabar ɓacin rai Ɗalha bai san sanda ya fita daga kitchen ba bayan sigar sa parlour bai tsaya ɓata lokaci ba ya finciko Rayyan dake kan Afef yana kai masa naushi,bulala Ɗalha ya samu ya zane Rayyan da kyau tun tafiyar Amirah bai taɓa dukan yaran ba sai Fauziyya ita ma sau ɗaya ya daketa da Sumayya da ta yi masa kashi a wando dan kawai ya ce baza ta tafi makaranta da hijab biyu ba,sai yau da ya zane Rayyan tunda ya zane Rayyan duka yaran sun nitsu cif kamar basa gidan tun karfe goma Ɗalha ya fara aiyukan gida daga dafawa yaran abin kare zuwa gyaran gida da wankin bathroom nasa da na yaran duka,karfe sha biyu da mintina arba'in na rana Ɗalha ya gama aiyukan gida da wankan yara gaba ɗaya,ba ƙaramin gajiya ya yi ba ga wani zufa da ya hada,bai samu damar yin breakfast ba sai karfe sha ɗaya da mintina ashirin na rana,bayan ya gama breakfast ne ya cewa yaran su yi sallah bayan sun idar da sallah,nan cikin parlour ya zauna tare da yaran ya dauki laptop ɗinsa da waya ya fara aiki daga gida tun karfe takwas na safe ya kira ogansa ya faɗa masa cewar ba zai samu damar zuwa aiki yau ba zai yi aiki daga gida ogansa ya ce babu matsala saboda kusan duka mutanen kamfanin sun san matarsa bata gidansa ba'a san inda take ba,Ɗalha na cikin aiki ne ogansa ya kirasa kan wani project inda ya ce yana buƙatar sa hannu Ɗalha saboda haka zai aika masa da file ɗin a gida ya sa hannu Ɗalha ya ce ''babu damuwa ya cigaba da aiki cikin laptop,Ɗalha na cikin aiki ne yaran sun fara hayaniya hakan yasa Ɗalha ya ce duk sun kwanta su yi barci a nan parlour babu musu duk suka kwanta amma banda Suhail da Fauziyya ita dai Fauziyya wasa take da tarkacen kayan wasanta,shi kuwa Suhail ya kafe Ɗalha da ido na wasu ƴan sakanni inda Ɗalha hankalinsa na kan laptop yana aiki kawai ya jiyu murya Suhail ya ce ''barcin me zamu yi kuma?"
A hankali Ɗalha ya ɗago kansa yana aikawa Suhail wani mugun kallo har Suhail ya buɗe baki da niyya sake yiwa mahaifinsa wata tambayar ganin kallon da Ɗalha ke masa yasa ya ja bakinsa ya yi shiru bai sake cewa komai ba a hankali ya kwanta tare da rintsa idanunsa,Ɗalha na nan zaune yana aiki Allah ya taimake duk yaran sun yi barci har Fauziyya amma banda Suhail dake wasa da yatsunsa,wayar Ɗalha ce ta yi ƙara alamar shigar kira Ɗalha ya duba ya ga ogansa ne ke kira ba tare da ɓata lokaci ba ya amsa kiran nan ogansa ya shida masa cewa yana kofar gida ya fita ya sa hannu a file ɗin tsabar mamaki Ɗalha bai san sanda ya ce ''yes sir'' daga haka ya kashe wayar bai yi tunanin ogansa zai kawo file ɗin da kansa ba ba tare da ɓata lokaci ya tashi da niyyar fita zuwa waje ya sami ogansa,lokaci guda kuma yaji yana buƙatar shiga bathroom ya kama ruwa hakan yasa ya nufi hanyar ɗakinsa,Suhail dake kwance yana jin duk wayar da Ɗalha ke yi bayan shigar Ɗalha ɗaki Suhail ya tashi zaune gaba ɗaya ya gaji da kwanciyar hakan ya tashi ya nufi hanyar fita daga parlour har kofar gida ya fita nan yaga motar ogan Ɗalha Suhail ya kafe babban mutumin me kimanin shekaru sittin da biyar a duniya da ido hankalin mutumin ne ya dawo kan Suhail,tsananin kamannin Suhail da Ɗalha yasa kallo ɗaya mutumin ya yiwa Suhail ya fahimci ɗan Ɗalha ne hakan yasa ya yiwa Suhail alama da hannu cewar ya zo babu musu Suhail ya tako har inda mutumin ke tsaye mutumin ya miƙo masa hannu shima Suhail ya miƙo hannusa suka yi musabaha cike da girmama Suhail ya ce ''ina wuni'' mutumin ya amsa masa tare da faɗaɗa murmushi ya ce ''how are you son?" Suhail ya ce ''l'm fine thank you sir'' yaji daɗi da yaga yaron ya amsa masa ba tare da kuskure ba ya ɗan yi ƙasa da murya ya ce ''where is your father?" Suhail ya ce ''he is inside'' mutumin ya ce ''ok go and tell him he has a visitor waiting'' da gudu Suhail ya koma cikin gida tun daga parlour yana ihu kiran ''Dady..Dady you have a visitor he is outside'' Ɗalha dake cikin bathroom ya yi mamakin jin muryar Suhail a wannan lokacin a tunaninsa ya yi barci,jin shiru ba'a amsa sa ba yasa Suhail shiga ɗakin Ɗalha,motsin ruwa da ya ji cikin bathroom ya tabbatar masa Dadinsa na bathroom har kofar bathroom ya tako ya ce ''Dady wani mutum ya zo wajen ka yana waje yana jiran ka'' Ɗalha bai ce masa komai ba kawai ya kankare murya ya ce ''uhmmm'' da wani irin gudu Suhail ya fito daga ɗakin bai tsaya ko ina ba sai kofar gida bayan ya isa wajen motar mutumin na kallonsa har sannan fuskarsa dauke da murmushi ya ce ''ina baban naka?" Suhail dake mayar da numfashi ya ɗago idonsa ya kalle mutumin ya ce ''wai kuma yana kashi ka jirasa har sai ya gama'' ba iya ogan Ɗalha ba har direbansa dake zaune cikin mota ya yi mamakin amsar da Suhail ya basu ogan Ɗalha ya sosa kai tare da faɗin ''okay kid'' daidai lokacin Ɗalha ya ƙaraso wajen a kunnensa Suhail ya ce yana kashi,a kunyace ya ƙaraso har inda ogansa ke tsaye cike da girmamawa suka gaisa ogansa ya miƙo masa file zai sa hannu kenan Suhail ya ce ''Dady har ka gama kashin?" da wani irin sauri Ɗalha ya kalle Suhail dake tsaye kusa da ogansa hannusa cikin na ogan Ɗalha yana wasa Ɗalha bai iya cewa komai ba ya mayar da hankali kan file ɗin yana duba wajajen da ya kamata ya sa hannu matsayinsa na manajar kamfanin, ƙaɗan ya rage ya sa hannu wajen daracta wato ogansa wanda shine mamallakin kamfanin ogan Ɗalha ya ce ''you talk too much kid'' shi kuwa direban sai faman danna dariyarsa yake Ɗalha kuwa ji ya yi kamar ƙasa ta buɗe ya shiga tsabar kunya,bayan ya gama sa hannu ne ya miƙawa ogan nasa file ɗin daga haka suka yi sallama da juna Ɗalha ya kama hannu Suhail zuwa cikin gida yayin da ogansa ya shiga mota direbansa ya ja motar suka bar wajen,bayan shigar Ɗalha da Suhail ciki waje Ɗalha ya samu ya zauna ya ce Suhail ya zauna gefensa babu musu Suhail ya zauna nan Ɗalha ya shiga yi masa nasiha kan abinda ya yi Ɗalha ya nuna masa rashin dacewar hakan ya kuma nuna masa hakan kuskure ne babba sannan kar ya sake yin haka sosai nasihar ta shiga Suhail ya kuma gane ya yi kuskure bayan Ɗalha ya gama masa nasiha ne ya ce ''Dady l'm sorry ba zan sake ba'' Ɗalha ya ce ''is okay''
Karfe biyar na yamma daidai Amirah ce tare da Rumaisa zaune kofar kitchen ɗin Rumaisa suna aikin abincin dare yadda Amirah ke jajjagen kayan miya cikin turmi ita kuma Rumaisa na can bakin murhu tana tana talgen tuwo bayan Rumaisa ta gama talgen tuwo ne ta mayar da dubanta ga Amirah da ta gama jajjagen kayan miya yanzu tana wanke kifin da za'a sa a miya Rumaisa ta debi ruwa cikin randar roba dake cikin kitchen da dauraye hannuta tare da share hannu da wata ƙaramar towel dake saƙale jikin ƙosa dake manne jikin bangon kitchen,tun misalin ƙarfe huɗu da suka fara aikin abinci Rumaisa ke bawa Amirah shawarwari kan yadda zata kula da gidanta da kuma yadda zata tsara rayuwar ƴaƴanta,mayar da dubanta ta yi ga Amirah ta ce ''ki na jina Amirah?" Amirah ta ce ''eh'' Rumaisa ta ce ''tarbiyyar yara tana wahala kuma tana sauƙi sauƙinta kuwa shine in kin iya tsara komai cikin tsare kin koyawa yaranki abubuwa a ƙananan shekaru ba sai sun girma ba,kin ga kamar Sudais dake da shekaru takwas wallahi da wata uwar ce da tuni ya iya yiwa ƙaninsa wanka za ki ga ya iya sharan gida har wanke wanke kin san Allah wasu har girki zasu iya barin sa ya yi musamman in shi ɗin ya kasance mace irin dafa indomie da taliya haka,da wata ce tuni ta koya masa,sannan kin yi magana kan yadda suke ɓata gida da kin gyara zasu ɓata a nan dai naga laifin ki,in zasu ɓata gida sau goma ki sa su gyara,ko za su saki magana haka za ki ta fama suna yi kina gyara masu kafin wani lokaci za ki ga sun iya,maganar watsa kayan makaranta da sun dawo su watsa jakar makaranta a can takalmi a nan gyara masu za ki yi,ya zamana akwai inda zasu riƙa zuba takalma da sun dawo gida,jakar makaranta akwai wajen ajiye shi haka ma uniform da sun dawo su cire su su zuba waje ɗaya duk wa'inan abubuwan ke za ki tsara masu,ita kuma Ummu Abiha ko tana so ko bata so ki sa ta dole tana taya ki wanke wanke da sauran ayyuka a kitchen'' shiru Rumaisa ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''dole zasu sa ki magana amma haka za ki daure ki yi ta magana har su iya abinda ki ke son su iya,kuma ki dage da yi masu addu'a da kuma nasiha wani lokaci ki yi nasiha wani lokaci ki rarrashi su wani lokaci kuma ki sa masu hannu amma fa sai in ki yi ta fama basu ji ba sai ki sa masu hannu,kuma kar ki yi wasa da addu'ar abu na karshe ki yi ki jan su jiki su zama tamkar ƙawayen ki ne su da abokan ki musamman yanzu da mijinki zai maki kishiya dan Allah ki danne zuciyarki,masu iya magana sun ce duk wacce bata zauna gida ɗaya da kishiya ba to ba'a yi mata kishiya ba,wacce aka haɗa ta gida ɗaya da kishiya ita aka yiwa kishiya''
SHUUKRAN/022