MATAR GIDA PAGE 18
MATAR GIDA 018
SHUUKRAN/022
P18
Shiru Amirah ta yi tana sauraron Rumaisa,Rumaisa ta ce ''aiy kin ce min gida ɗaya zaku zauna da kishiyar taki'' Amirah ta ce ''eh haka ne tun sati biyu da suka wuce naga yana ta gyara a ɗaya bangaren ban kawo kamai ba a tunanin wasu ƙudaɗen ya samu yasa yake gyara ban san aure zai yi ba'' Rumaisa ta ce ''wani ɓangare?bayan ɓangaren ki ya gina wani ne?kin san na yi kwana biyu rabona da gidan ki''Amirah ta ce ''a'a bangari biyu ne haɗe waje ɗaya da kin shiga gidan akwai wata babban parlour haɗe da kitchen da kuma daining space sai bangare na dake gefen dama ɗakuna huɗu ne kowanne da bathroom sai parlour da kitchen da kuma daining space hakama ɗaya bangaren dake gefen hagu,daya bangare dake gefen hagu zai sa amaryar'' Rumaisa ta sauke ajiyar zuciya ta ce ''kinga kuwa sai kin so haɗuwa da ita shawarar da zan ba ki daga ranar da amarya ta tare ki hana yaranki zama a babban parlour kin san wasu amaren da an auro su zasu yi ta nuna maki su miji ke so a gaban ki da ƴaƴanki zata rungume shi wata gangariyar ma a gaban ƴaƴanki zata masa kiss,to ki rufawa kan ki asiri duk yadda za'a yi kar ki bari tana zama waje ɗaya da yaranki sai an kwana biyu in ta haihu ɗaya ko biyu,haka zalika kitchen ki kwashi duk wasu kayayyakin ki dake babban kitchen ki maida su kitchen ɗin ki ki rinƙa girkin ki cikin kitchen ɗinki ya kamata ki bata space sosai ita da mijin naki amma in amarya taki me hankali ce za ki iya zama da yaran ki a babban parlour,wata gangariyar fa kuna zaune a parlour sai ki ga ta haye kafar miji ita a dole ga matar so to wallahi Amirah ki nitsu sosai ki fahimci irin matar da mijinki zai aura,abu na gaba duk yadda za'a yi ki nunawa ƴaƴanki ita ma uwa ce gare su duk yadda za'a yi kar kisa su raina ta ki danne zuciyarki ki yi hakuri ki ƙara hakuri'' shiru Amirah ta yi tana nazarin maganganun Rumaisa ganin Amirah ta yi shiru yasa Rumaisa daukar tukunyar miya ta daura a kan ɗaya murhun gawaye bayan tukunyar ta yi zafi Rumaisa ta zuba mai kafin ta daura da kin ga ni yara uku gareni bayan dafa abinci bana wani aiki a gidan nan babban ɗana yana da shekaru sha uku mai bi da shi mace ce tana da shekaru goma sai karamin shekarunsa bakwai komai su ke yiwa kansu aikin abinci ma wata rana Yasmin ke yi'' shiru Rumaisa ta yi yayin da ta zuba kayan miya a mai da ya fara zafi bata sake yiwa Amirah magana ba saida ta gama haɗa miya ta rufe tukunyar miyar kafin ta mayar da hankali kan Amirah ta ce ''wai ni kam me yasa ba kay planing ne?" murmushi Amirah ta yi kafin ta ce ''babu wanda ban gwada ba amma sam ta ƙi amshi jikina ban sani ba ko jinina ya yi karfi ne'' Rumaisa ta ce ''ikon Allah to Allah ya raya maki su ya yi masu albarka'' Amirah ta amsa da ''ameen'' daga haka bata sake cewa komai ba can ta kalle Rumaisa da ta gama tuƙa tuwon masara ta ce ''ina da wata magana da nake son yi da ke''Rumaisa ta ce ''ina ji'' ta faɗa tare da daukan ledar tuwo ta fara buɗewa shiru Amirah ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''bana son komawa gidan Ɗalha har cikin zuciyata bana son zama da shi'' baki sake Rumaisa ke kallon ta can ta ce ''ba ki son zama da shi da wa za ki zauna? auren ki ke son kashewa gaba ɗaya ko yaya? tsakani da Allah duk wannan dogon lakca da na yi maki ki ce ba ki son zama da shi kenan babu amfanin ba ki shawara,a tunanin ki in kin fita a gidan za ki samu wani nan kusa? to bari ki ji in kika kuskura kika kashi auren ki wallahi za ki yi dogon zawarci ƴaƴa bakwai gareki fa ki bar ganin nonuwanki basu gama kwanciya ba wallahi ki sani rashin ƙiba da kuma halittar da Allah ya yi maki kyau yasa nonuwanki har yanzu suna tsaye kuma ɗan ƙananu ne wallahi da rabta rabta ne da tuni sun kwanta,da kin kwanta sun gangaro maki har hammata,kuma ki sani duk haihuwar ki da kanki ki ka haife su ba'a taɓa maki aiki ba wallahi kin gama buɗewa,haka kawai ji min mata da wata zance mallama ki shirya za ki koma ɗakinki kin dai ji na faɗa maki,na yi maki oda kayan mata daga Sokoto na dubu arba'in saboda haka ki shirya gidan Ɗalha kaman kin koma'' Amirah na shirin magana Rumaisa ta ce ''matasalar Ɗalha raina ƙokarin ki da yawan hantararki da kuma yawan korafi da yake,a iya fahimtata bai iya magana ba,amma to ya za ki yi tunda Allah ya haɗa ki da shi ga yara,tsakani da Allah wace zata riƙe maki yara har bakwai wallahi ki sani babu wannan matar ko ba ki koma dan Allah ba ai kay koma dan ƴaƴanki,mijinki ba ya dukan ki baya zagin ki yana ba ki abinci yana biya wa yaransa kuɗin makaranta kin kuwa san mata nawa ke zama da mazajensu alhali basa basu abinci kuma basu damu da karatun ƴaƴansu ba?"
Amirah ta yi shiru tana sauraron Rumaisa,can ta ce ''kullum fa cewa yake zai sake ni da wani abu ya haɗa ni da shi sai ya ce zai sake ni,abu bai kai ya kawo ba zai ce shi fa zai iya sakina a ko da yaushi'' Rumaisa ta ce ''good kullum yana faɗa yanzu kuma ya yi,kina tunanin yanzu bai yi nadama ba ai kin gama burgi ni tunda kin tafi kin bar masa yara ki koya masa hankali kin kuma kashe waya babu wanda ya san inda kike yau kwananki biyu a gidan nan kin ji na tambaye ki yaushi za ki tafi ban tambaye ki ba saboda ina son hankalin ki ya ƙara kwanta kafin muyi maganar komawar ki,duk matar da kika gani zaune gidan miji wallahi hakuri ne ya zaunar da ita kin dauka ki kaɗai miji ke wulakanta kawai dai na wani ya fi na wani ne,haka duk zamu yi hakuri mu zauna tunda zaman ibada muke aljannah muke nima ina ruwanki da wulakacin miji in Allah ya taimake ki kina da ƴan ƙudaɗen ki ai shikenan ya je ya yi ta iskancinsa shi ya sani,abubuwa biyar zuwa shidda ne in namiji ke yi bazan cewa mace ta zauna ba miji me duka da kuma mazinaci,ɗan luwaɗi,ɓarawo,shaye shaye,caca,mazinaci da ɗan luwaɗi zasu dauko maki ciwo su kashe ki da ƙuruciyarki haka zalika miji mai duka wata rana zai iya maki bugun da zai zama ajalinki ko ya kassaraki da duka,ɓarawo ya jawa ƴaƴanki abin gore,ɗan shaye shaye kuwa in kika haifi mace kafin ta samu miji sai an yi da gaske,ɗan caca kina zaune cikin gida zai ce ki fita ya sa gida a caca kuma an ci shi,kin ga kuwa bai kamata a zauna da iri irin wa'inan mazajen ba saboda haka ki gode Allah Amirah'' nan take Amirah ta ji jikinta ya yi sanyi duk abinda Rumaisa ta faɗa gaskiya ne cikin zuciyarta ta yiwa Allah godiya,shiru ne ya biyu baya na wasu ƴan mintina Rumaisa ce ta yi magana ta ce ''yaushe ne auren nasa'' jiki babu kwari Amirah ta ce ''saura sati biyu'' shiru Rumaisa ta yi na wasu ƴan mintina kafin ta ce ''kinga kuwa ya kamata ki koma kafin auren'' da sauri Amirah ta ɗaga kai ta kalle Rumaisa,Rumaisa ta ce ''eh ya kamata ki koma ba ki san halin da ƴaƴanki suke ciki ba ba ki san ya ya karatun su yake ba,suna zuwa makarantar ko basu zuwa ba ki sani ba,a sani na dai gaba ɗaya garin Kaduna ba ki da dangi ko ɗaya haka ma mijinki kanwarsa kaɗai ke aure garin nan,kin ga kuwa shi ke kula da yaran'' Rumaisa ta yi shiru na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''hakuri za ki yi Amirah ki koma wajen ƴaƴanki ko dan karatun su da tarbiyyar su'' shiru Amirah ta yi kafin ta ce ''okay'' ba da son ranta zata koma gidan ba zata koma ne saboda yaranta Rumaisa ta fahimce Amirah bata son komawa amma haka ta shiga rarrashinta da bata misalai iri iri har Allah yasa ta shawo kanta,bayan sallar magrib Rumaisa da Amirah tare da yaran Rumaisa da Yasmin na zaune tsakar gida suna cin abinci nepa suka kawo wuta nan take hasken nepa ya gauraye farfajiyar gidan duk suka yi hamdala Rumaisa ce ta cewa Yasmin da ta gama cin abinci ta sa mata waya a chaji Yasmin ta amsa da to suna cikin cin abinci ne mijin Rumaisa ya shigo bakinsa dauke da sallama duk yaran sun tashi suna masa oyoyo tare da ƙarɓar kayan hannusa,tun zuwan Amirah yau fata ganin fuskar mijin Rumaisa bata taɓa ganinsa ba kullum kafin ta fita daga ɗaki ya fita kasuwa in ya dawo da yamma kuma tana ɗaki,cike da girmamawa ta gaishe shi ya amsa mata bayan shigarsa ɗaki ne Rumaisa ta tashi ta bi bayansa,ba'a dau lokaci ba ta fito hannuta riƙe da wata leda mai ɗan girma ta wuce ɗakin da Amirah ta sauka ta ajiye ledar,bayan sallar isha'i Rumaisa ta shigo ɗakin Amirah hannunta riƙe gwangwanin madara madaidaici,ta tarar Amirah har ta kwanta inda ta ajiye ledar ɗaxu ta dauko ta ajiye gaban Amirah waje ta samu ta zauna kafin ta mayar da dubanta ga Amirah ta ce ''Malama tashi wajen ki na zo'' tunda Rumaisa ta fita daga ɗakin mijinta ta wuce ɗakin Amirah da leda Amirah ta gane maganin mata ne,jiki babu kwari Amirah ta yunƙura ta tashi zaune tana kallon Rumaisa ta ce ''barcin ma baza ki bari na yi cikin salama ba'' Rumaisa ta ce ''kan ki ake ji,ga wannan magungunan mata ne a ciki ga madara nan ta faɗa tana nuna wa Amirah gwangawnin madara ta ce ''ke ba yarinya ba ce shekarar ki tara a gidan miji kallo ɗaya za ki masu za ki gane na sha da madara za kuma ki gane wanda za ki cusa yauwa ni bazan tsaya bata lokaci ba,kin ga tafiyata zan je kula da mijina sai da safe'' Rumaisa na gama faɗin haka ta fita daga ɗakin cike da mamaki Amirah ta bi bayan Rumaisa da ido
SHUUKRAN/022