Chapter 1
by @zmchubado
MUTUNCIN 'YA MACE....!
Rubutawa:
Zainab Muhammad Chubaɗo
Hafsat Mustapha (ƴar mutan Nija)
Gargaɗi: ba mu yarda wani ko wata ya juya mana wannan labarin ba tareda izinin mu ba, duk wanda yayi haka tabbas za mu haɗu da shi a gaban hukuma saboda muna da haƙƙin mallaka a hukumance.
Bismillahirramanurrahim
page: 1
A zaune take ta Rabka uban tagumi idanunta duk sun caɓe da Hawaye wanda ke zubowa akan kumatunta. tunanin halin da take ciki ne ke ƙara mata yawan zubar hawayen ba tareda ta iya dakatar dasu ba, cikin yanayi na rashin sanin madafa Asma'u ta miƙe cikin hanzari tana gyara zaman hijjabin dake jikinta. fita tayi zuwa farfajiyar madedaicin gidan wanda ke ɗauke da tarin shuke-shuke na alfarma, bata tsaya a ko ina ba se'a gaban ƙaramar Motar Samfurin Camry, a hankali ta buɗe motar ta shiga ta zauna sannan tayi mata key ta nufi Ƙofar fita daga Babbar Ƙofar Gidan.
Cike da girmamawa mai-Gadin Get ɗin ya buɗewa Asma'u Ƙofar ta Fice daga Gidan cikin Hanzari kamar za ta tashi Sama, duk tsawon lokacin da Asma'u ta ɗauka a Motar tana tafiya har Lokacin bata dena kukan da take ba harta iso ƙofar Gidansu ta tsaida Motar, Sam ba ta damu da Hawayen dake zubowa daga idanunta ba a haka ta fito daga motar ta shiga wani Ƙaramin Gida dako ƙofar kirki babu sai Labulan Buhu, Babu kowa a tsakar Gidan sai wata dattijuwar Mata wadda ba zata wuce shekaru Sittin a duniya ba daga ɗan nesa da Dattijuwar kuma wata matace itama wadda bazata Wuce Shekaru Arba'in ba, Dattijuwar dake Zaune akan Tabarma tana shafa magani a ƙafarta wadda ta kumbura alamar ciwo ta ɗago kai tana kallon Asma'u baki a sake tace," Yau naga tsigalalliyar yarinya, babu sallama za ki shigowa mutame gida ki tsaya kinayi mana kuka saboda janyowa kai Masifa Asma'u? To wllhi Aniyarki sai dai ta biki, mudai ba za muga kuka ba duniya da lahira kinji na gaya miki." saikuma ta fashe da kuka tana maida kallonta ga wannam matar dake can nesa da ita tana gyara itacen dake cikin Murhu tace,"yanzu Talatu kullum Haka Asma'u zata dinga shigo mana gida babu sallama se kuka? Dama irin tarbiyar da kukai mata kenan keda Haruna Talatu?
Talatu wadda ke shirin Fara tankaɗan Garin tuwon dake gabanta ta tsaya tana Kallon Gwaggo wadda keta faman matsar ido baki buɗe tace "Wace Asma'un kike nufi Gwaggo?. Ta faɗi hakan tana fitowa da hanzari daga ɗakin girkin hannunta ɗauke da Rariyar tankaɗen Garin
Asma'u na ganin Innarta ta nufota da gudu ta Rugumeta tana mai Ƙara sautin kukanta tace "Inna Don girman Allah ki taimaka min kar na faɗa ga halaka Inna, wallahi idan har ba'a Raba Aurena da Sulaiman ba zai sa na kai kaina wutar jahannama da ƙafata Inna!! Don girman Allah ku sa ya aikomin da takardar Saki na Roƙeku. Gabakiɗayansu salati suka saka daga Inna har Gwaggo wadda tai mitsi-mitsi da ido tana shirin fara bala'i cike da masifa Inna ta hankaɗe Asma'u daga jikinta tace "Asma'u Ashe bakida hankali ban saniba? Auren naki kikeso ki kashe sabida wani banzan dalilinki marar amfani? To wllh ki sani muddin kika kaso wannan Auren wallahi bada yawuna b...."Nima kaina bada yawuna ba kuma wallahi a sanadin hakan saina tsine miki!! Malam Madu Mahaifin Asma'u dake ƙoƙarin shigowa tsakar gidan ya katse Talatu ta hanyar faɗar hakan cikin ɓacin rai da kumfar baki, duk yanda Asma'u taso ta fahimtar da iyayenta akan matsalarta da mijinta sulaiman sam sukaƙi bata damar hakan dan dole ta haƙura, haka iyayen nata da kakarta Gwaggo suka dinga surfa mata masifa duk dan abinda Sulaiman ɗin yake aiko musu dashi na yau da gobe.
Jikin Asma'u a mace ta fito daga gidan tana ƙara sautin kukanta a haka ta shiga motarta ta koma gida cike da Rashin sanin makama akan matsalar tata, idan har zata iya tunawa dai-dai yau watan Sulaiman Goma cif da tafiya kwatano ba tare da ya dawo gida ya duba lafiyarta ba, ko babu komai ai yasan akwai haƙƙinta da addini ya ɗora masa a wuyanta taya yake tunanin zata iya rayuwa a hakan bayan itama lafiyayyiya ce kamar ko wacce mace, tabbas ya zama wajibi a gareta ta samawa kanta mafita don bazata iya zama a cikin wannan masifar da take ciki ba a gidan Sulaiman.
Tana isa Gida Hijjabin jikinta kawai ta cire tareda zubewa a kan ɗaya daga cikin kujerun dake falon tana sauke numfashi tamkar wadda ta gwabza tseran gudu da ingarman doki maji ƙarfi, a hankali ta fara jiyo sallama daga ƙofar falon miƙewa tayi ta isa bakin ƙofar falon tana amsa sallamar da ta jin, Bashir Mai wanki ta gani hannunsa ɗauke da gogaggun kayanta dariya tayi wadda ta baiyana fararen haƙoranta tace "Maraba Bashir shigo mana. ta faɗa tana gyara masa hanyar da ze Raɓa ya wuce da kayan, yana shiga ya ajiye kayan tareda rissinawa ya gaisheta sannan ya fice.
Gabaɗaya Asma'u ji tayi kamar zata kurma ihu sabida baƙin ciki bayan fitar Bashir mai wanki, wayarta ta ɗauka dake gefanta ta shiga kiran Hafsat ƙawarta, hafsat na ɗagawa Asma'u ta fashe mata da kuka tace " waiyo Hafsa na shiga uku kasheni kawai Sulaiman ke son yi har yanzu yaƙi ya dawo tunda ya tafi kullum indan nai masa maganar halin danake ciki se yace shi neman kuɗinsa ne a gabansa ba maganar kwanciya da mace ba Hafsat ya zanyi don Allah? Su inna suma sunƙi su goyamin Baya na Roƙeki Hafsat kiban shawara!
Ajiyar zuciya Hafsat ta sauke sannan tace "kwantar da hankalinki tunda sunƙi baki goyan baya akan matsalarki ni nan zan samo miki mafita kamar yanda na samowa kaina, yanzu dai zan samo miki ƙwayar maganin danake amfani da ita inyaso indan kin shiga wannan yanayin saiki sakawa wanda kike ganin ze iya magance miki matsalarki a lemo yasha inyaso saiki biya buƙatarki dashi, kinganin nan Asma"u mai gadina kullum nake ɗirkawa ƙwaya ya biya min buƙata ta tunda mai gidan nawa shi aiki yafi masa komai amfani a Rayuwarsa, don haka seki san abinyi tun wuri.
Shiru Asma'u tayi tareda jan fasali tace "to shikenan ƙawata sekinzo goben.
Washe gari kamar yanda Hafsat ta faɗa hakance ta kasance tunda sanyin Safiya ta kawowa Asama'u ƙwayar maganin da sukai magana, sosai jikin Asma'u yay sanyi kamar bazata iya ba amma saida Hafsa tasan yanda tai ta tura mata wannan muguwar ɗabi'ar ta aikata Zinah! Hafsat na Fita Asma'u ta shiga ɗakin girkinta ta ƙurawa flacks ɗin shayin Bashir mai wanki idanu, bata da wani zabi haka ta ɓallo maganin har guda uku ta zuba masa a ciki tareda girgizawa sannan ta ɗauka ta nifi waje da flacks ɗin da kuma soyayyen dankalin dayaji uban ƙwai, har ƙofar ɗakinsa taje sannan ta fara sallama Bashir ɗin ya fito yana taje sumar kansa, a nan take taji wani babban al'amari ya tsirga mata a tareda Bashir ɗin
Durƙusawa yayi har ƙasa cike da girmamawa ya fara gaisheta, a dan hanzarce ta amsa masa tareda miƙa masa flacks ɗin fuskarta ɗauke da murmushi ta juya zuwa ɓangarenta, tana barin gurin Bashir ya koma ɗakinsa tareda zama ya buɗe farantin dake rufe ruf ya fara cin dankalin tareda tsiyaya Ruwan shayin dayasha madara da Milo a kofi ya fara kurɓa cikin nishaɗi, a haka Bashir ya shanye shayin tas har yana lasar baki.
Gama shan shayin nasa ke da wuya kimanin ƴan mutuna sai labarin ya canza nan fa Bashir ya dinga juyi a tsakar ɗakin kamar zai mutu sabida tasirin wannan ƙwayar mai bijiro da zazzafar shi'awa da Asma'u ta zuba masa a shayin, kafin kace me tuni Bashir ya fara haɗa zufa sharkaf tamkar wanda aka watsama ruwa, a haka cikin wannan yanayin Asma'u ta shigo ɗakin ta sameshi se juyi yake yi hannunsa dafe da mararsa wadda yake ji kamar zata fashe, sam bata sha wahala akan Bashir ba ya bata haɗin kai tunda dama shima a buƙace yake.
Daga yanayin da jikin Bashir ɗin ke rawa zaka fahimci shi ɗin baƙone a wannan lamari, amma sam hakan besa Asma'u ta gaza wajen samun biyan buƙatar kanta ba kusan itace ma take jan ragamar lamarin abinka da wadda ta daɗe tana ɗagon buƙatarta har tsahon wata goma cif ba tareda namiji ya kwanta da ita ba. A wannan ranar Asma'u ta maida Bashir cikakken namiji kuma me lafiya.
Koda suka samu nutsuwa sam Bashir ya kasa kallon tsakiyar idonta sabida kunya musamman ma daya kanta kwance tsirara a saman katifarsa, Asma'u kuwa murmushi ta sakar masa me kashe zuciya ba tareda tayi magana ba ta sake jawoshi jikinta suka kuma afkawa duniyar sama jannati. Tun daga wannan ranar da Asma'u ta samu biyan buƙatar ta A gurin Bashir Shknan qulla alakar aikata masha'arsu, idan tana buƙatarsa ma basai ta saka masa ƙwayar magani ba dakansa zaizo har kan Gadon Aurenta yay zina da ita, a haka suka shafe watanni suna cin mutuncin Aure harta manta da batun wani Sulaiman dake can yana naiman kuɗi a kwatano, abinda be sani ba shine yana can kwatano shi kuma Bashir Yana kwatane Masa mata
BAUCHI STATE
A hankali take tafiya sanyeda dogon hijabinta maroon colour wanda ya saukar mata har idon sawunta, ƙafarta sanye take cikin wani flat ɗin takalmi Wanda ya kasance maroon Shima daga yanda take ɗaga ƙafafunta kaɗai zaka fahimci ita ɗin ɗiyace me tarbiya da kuma nutsu, daga kallon farko idan kai mata bazaka kirata gajeriya ba Sabida Sumaiyya irin dogayen matan nan ne masu mtsakaicin tsayi da kuma tsarin halitta.
A nitse cikin takunta ta iso ƙofar babban gidansu wanda ya kasance irin fasalin ginin masu kuɗin da ɗinnan, yanayin fuskarta ne ya canza kaɗan sabida gajiyar dake tareda ita a madadin ta nufi maine ƙofar gidan senaga ta nufi wata babbar ƙofa ta shiga da sallama, nan take kakkyawar fuskarta ta yalwata da wani qayataccen murmushi wanda ya ƙara fallasa sirrin kyanta, falo ne babba wanda aka Ƙawata da kujeru masu kyan gaske babu mutane dayawa a falon se wani dattijo wanda ke sanye cikin farar alkyabba irinta malamai, kansa a ɗaure yake da farin rawani wanda yay dedai da haibar fuskarsa.
Gefansa kuma wasu magidantan maza ne kimanin su shida ko wannensu ya buɗe littafin dake gabansa, da alama karatu sukeyi cike da girmamawa Sumaiyya ta ƙarasa gurin daga can gefan shaik ta zauna tana ƙawa wadata murmushinta tace " sannu baba na dawo daga islamiya ne shine nace bazan shiga gida ba senazo na ganka tukunna.
Dattijon da Sumayya ta kira Baba Yay murmushi yace "Masha Allah ubangiji yay miki albarka maza tashi ki shiga ciki nima ina nan shigowa. A kunyace ta miƙe tabar falon har ɗaya daga cikin ɗalin Shaike ɗin na tsokanarta yace" Sumayyah ƴar babanta. Murmushi shaike yayi sannan sukaci gaba da karatun da sukeyi.
Tana shiga cikin gidan Samirah Qanwarta ta nufota da gudu harda tsallents tace "yaya Sumy yau bayan kin tafi makaranta governor yazo ya kawowa baba wata takarda wai gobe zaki fara attending lectures ɗinki a schl. Gaban sumaiyya ne yay wata irin bugawa nan take ta fashe da kuka ta nufi ɗakinsu da gudu ta murza key, a wannan ranar sumaiyya kusan kwana tayi tana kuka kuma sam taqi buɗe qofar ɗakin har garin Allah ya waye, sabida a rayuwarta sam ta tsani abinda zesa tayi nisa da Babanta!!!
Tunda sanyin safiya me girma gwamna ya turo motar daza'a tafi da Sumayya.
SUMAIYYA AHMAD MUKTAR shine cikakken sunanta, d'iya ga wani shaharrarren malamin addinin musulunci mai suna Sheikh Ahmad Mukhtar Azare, Fitaccen limamin garin Azare kenan dake Cikin jihar Bauchi. Sumayya ita ce d'iya ta kusan goma sha uku awajen mahaifin ta domin kuwa Allah ya albarkaci Sheikh Ahmad da tarin ya'ya maza da mata.
Duk cikin ya'yansa guda goma sha biyar, Sumayya ita ce mafi soyuwar d'iya dayake jinta har ransa da duk wata gab'a da jini ke gudana ajikinsa kasancewar tana masa biyayya sosai, ga hankali da nutsuwa, uwa uba ga ilimi.Tayi makarantar Noziri da kuma Frimari d'inta a Abdullahi Memorial School Azare, sannan taje gaba tayi sakandiri d'inta a Ummul Qura Science Academy Secondary School Azare.
A cikin wannan tsukun ne Sumayya ta samu gurbin karatu a Babbar jami'ar ATBU a inda suka bata cos d'in data zab'a wato 'Biochemistry' tare da taimakon Gwamnar jihar Bauchi wanda ya kasance amini kuma dalibi awajen Sheikh Ahmad, shine ya tsaya mata har ta samu Shiga wannan jami'a.
A lokacin da aka gama komai na tafiyar ta makaranta sun ci kuka sosai da Sheikh kasancewar wannan shine karo na farko A rayuwarta da zata bar gida da nufin ta tafi makarantar kwana, awajen yar'uwarta mai suna Yaya Basira zata zauna wacce take aure anan cikin garin Bauchin har ta kare karatun nata wanda rututun shekaru ne har biyar.
Sheikh Kalli sumaiyya yace"Sumayya ina fatar ba sai na sake tsayawa b'ata lokaci wajen miki nasiha ba sanin da nayi na cewa ke d'in nutsasstsiyar yarinya ce kuma kowa na shaidar hakan, sai dai ance tunatarwa nada matuk'ar muhimmanci." Saukar da ajiyar yayi kan ya cigaba"Sumayya abu na farko da zan sake tunatar dake akai shine, inaso ki sanya tsoron Allah ya zamto shine abu na kan gaba gaba arayuwarki, idan kikai haka to kuwa ina mai tabbatar miki da cewa ba zaki tab'a tab'ewa ba domin kuwa shi tsoron Allah guzuri ne na zuwa lahira, abu na biyu kiyi k'ok'arin k'yautata mu'amalarki da jama'a don ayanzu ne zaki soma cud'anya da mutane daban daban masu banbancin addini da kabila.Girman kai, alfahari, raina mutane da tinkaho cikin magana da aiki suna halakar da dan adam, kuma su kai shi ga zama kaskantacce a idon dukkan masu imani, dan haka ina mai zaburar dake ki zamo mai sauk'in kai da tawali'u, mai girmama kowa cikin mu'amala, mai kulawa da mutumcin jama'a.Sannan abu na k'arshe kuma mafi daraja da muhimmaci shine MUTUNCINKI NA 'YA MACE...
Yana kaiwa nan a maganarsa kuka yaci mugun k'arfinsa wanda hakan ya ida karyar da zuciyar Sumayya, ita ma ta sake rushewa da wani sabon kukan ganin mahaifin nata ya shigo da b'angare mai matuk'ar muhimmanci, ya cigaba da magana yana nunata da 'yar yatsa, yatsar sai rawa take"Lallai ki sani MUTUNCIN 'YA MACE babban jarabawa ne a gareta, ki zamo mace wacce ta san mutuncin kanta da na iyayenta, ki kauracewa duk mutumin da kikasan zai ja har mutuncinki ya zub'e, ki kuma lura da duk abubuwan da zaisa sunanki ya b'aci, domin zubar mutunci yana tab'a ahalinka, ki san cewa saka sutura masu mutunci yana daga cikin yadda ake gane cewa wannan tana da mutunci kuma daga gidan mutuncin ta fito, sab'aninta kuma wato mummunar shiga, sharri ne me girman gaske gare ta da kuma al'umma gaba daya,kuma babu abinda zai kiyaye mutuncin 'ya mace face hijabin ta da kunyar ta, hijabin ki ya dunga tuna miki da addinin ki akodayaushe, sannan kuma ga wannan al'qur'ani mai girma ki yawaita karanta ta dan waraka ce daga dukkan kunci da damuwa..." haka dai ya cigaba da mata nasihu kafin sukai bankwana.
ATBU BAUCHI..
Sumayya ta fara makarantar ta lafiya ba tare da wani matsala ba, k'awayenta sune Amina da Khadijah, kuma ba laifi suma sun fito ne daga gidan mutunci, A hostel suke zama ita kuma daga gida take zuwa.Haka mai girma gwamna Alhaji Aliyu Rufa'i bata manta irin halaccin da yayi mata kuma yake kan mata ba domin kuwa nauyin karatun ta shi ya dauke, ta kan kai masa ziyara tare da iyalensa lokaci zuwa lokaci.Awani zuwa data tab'a yi ne suka had'u da babban dansa Fu'ad wanda bai wani jima da kare karatunsa a cairo ba, gashi har ya samu aiki a CBN, kai tsaye ya nuna yana son Sumayya sabida sosai nutsuwar ta ya tafi da imaninsa.
Abu na farko da Sumayya ta fara lura dashi awannan babban jami'ar shine, yawancin 'yan mata na siyar da mutuncin kansu awajen marasa imanin malaman makarantar ne ba don komai ba sai don su samu su ketare jarabawa, babban abun tak'aicin wai harda wasu matan auren suma sun jefa kansu cikin wannan halakar wanda ak'arshe ma yawancinsu basu kai ga cimma buri akan dalilin da har yasa suka zab'i zubar da mutuncin kan nasu akai.
Wani abun tashin hankali suna shekara ta uku sai ga Amina da ciki, ashe tasha mu'amala da wani cos laccara nasu domin ta samu ta ketare cos d'insa dake matuk'ar bata wahala, wanda tun ashekararsu ta farko ta kasa wuce shi, gashi har sun kai shekara ta uku wanda in har bata samu ta ketare shi ba to tabbas zata koma baya, shine ta zab'i siyar masa da mutuncin kanta domin samun grade.Sumayya tasha kuka tamk'ar ranta zai fita, kai kace ko ita akai wa wannan cin zarafi da keta, sai cewa take"Amina meyasa ? meyasa kika zab'i zubar da mutuncin kanki akan abun duniya ?" Amsar Amina agareta shine"Sumayya kibar dora ayar tambaya akan kaddara ta! ki jira naki domin kuwa ko wani bawa baya tashi fad'o wa cikin duniyan nan ba tare da takaddar zanen kadarorinsa dunkule ahannu ba." Wannan magana sosai ta tsayawa Sumayya arai, sai jikinta yayi matuk'ar sanyi.
Jarabawar rayuwar Sumayya ya safko mata ne akan gab'a mai wuya alokacin tana matakin k'arshe, abun nufi anan shine, abunda ta gani akurkusa da ita kuma take jin jita jita akansa wai shine ayau ya kusanto inda take, wato wani cos laccara mai suna Dr.Garba Gana shine ya sata gaba yana nema ta mallaka masa kanta sannan ya taimaka mata ta ketare cos d'insa da mutane ke kuka dashi, in kuwa ba haka ba zata fad'i kuma wannan cos d'in dole zai sa ta dawo wata shekarar. Alokacin daya k'ira ta ofishinsa yana sanar da ita wannan bukata tasa, miyau ta watsa masa akan fuska tana kuka tace"Allah ya kiyaye in siyar da mutuncin kaina akan abun duniya,ka sani ni Sumayya bazan yi gangancin kai kaina jahannama akan kwalin makaranta ba, Allahna shine zai tsaya mun domin wajensa zan kai kararka." Tana gama fad'in hakan tabar ofis d'in da gudu tana kuka, shi kuma ya bita da dariyar keta yana fad'in"Ashe yarinya kin shirya dawowa wata shekarar kenan don babu makawa in baki bani had'in kai ba ya zama dole insa ki fad'i."
Abu kamar wasa sai da Dr.Gana ya fadar da Sumayya don taki yi masa yadda yake so, sannan kuma taki gayawa kowa hatta da Fu'ad, sai tayi k'ok'arin barin ma ciki damuwar ta.In ka ganta kamar ba Sumayya ba ta rame ta lalace sabida damuwar data mata yawa, gashi ashekarar akaso ayi bikin aurensu da Fu'ad, sai kuma ta samu matsala, yanzu fa sai wata shekarar in har ta samu ta ketare kenan zata yi bankwana da makarantar.Sheikh kamar zai haukace mata don shi matsalar shi daya, baya son fad'i wa arayuwarsa, basu tab'a samun sab'ani da mafi soyuwar d'iyar tasa ba sai akan wannan batu, Sumayya tayi kuka sosai kamar ranta zai fita ganin mahaifin nata yayi fushi da ita sosai gashi ita kuma taki gaya musu abunda ke faruwa ta tsaya zurfin ciki.
Shiyasa aka ce in kana cikin damuwa kayi k'ok'arin sanar da wani amintacce domin samun mafita, to ita sam Sumayya tunanin hakan gabaki daya ya fita k'wak'walwar ta, kanta ya cunkushe yayi duhu, ta rasa mafita, burin ta ayanzu bai wuci ta samu ta ketare wannan cos d'in ba, hakan yasa tayi shahad'a ta kai kanta ga Dr.Gana take ce masa ta amince yayi duk yadda yake so da ita muddin zai bata markinta ta wuce, sosai yayi dariya yana kallon ta yace"hahaha dama ai nasan duk taurin kanki dole zaki dawo gareni don kina da bukatar sa hannun Dr.Gana kafin ki samu har ki iya yin bankwana da wannan makarantar, to yanzu sai kije ki shirya zuwa takwas d'in dare mu had'u aharabar Villa hotel."
Commet
And
Share
2sters✍️ H/C