AMARYAR GADO

CHAPTER 7

by @xayyeesherthulhumaerath

AMARYAR GADO

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

AISHA SANI ABDULLAHI

Xayyeesherthul-humaerath

©️2026

 

Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske. 

 

Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.

 

SHAFI NA BAKWAI

 

Ya janyota, ta zame ta faɗi ƙasa. Da ganin ta zame cikin sauƙi, sai ya kyalkyale da dariya. Ya durƙusa gabanta, rigar da ke jikinta ya cire mata, ya zaga ta bayan ma ya cire mata breziya, sannan ya durƙusa gabanta ya zare mata pant ɗin da ke jikinta.

 

Ya tsaya ya kalle ta, ya saki dariyar basawa kafin ya ƙara durƙusa gabanta. Breast ɗinta ya fara ja da hannu kamar yana tatsan nonon saniya, ya ce, “Kambala’i kamfani kenan, yoo! Ke wannan in shanuwa ce ke, ai masu ke na cikin alƙairi. Ji wasu samudawan kaya.”

 

Ja ya dunga yi yana sheƙewa da dariyar mugunta, ita kuwa ta gama ficewa a hayyacinta.

 

Bayan ya gama da kirjin, ya koma kan cinyoyinta inda nama ke rawa, yana duka. In ya daka naman ya yi rawa, sai ya ƙara kyalkyalewa da dariya, “Wato ke dai ta ko’ina nama ce a cike, yoo! Wannan kika kwanta kan mutum, ai daina numfashi zai yi.”

 

Haka ya ci gaba da mata, ya ja nan, ya ja can, ya daki nan, ya mari can.

 

Sai da ya yi mai isarsa sannan ya tashi, ya ƙara janta a ƙasa, sannan ya buɗe ta da kyau ta yi plat. Ya ɗauki wayarsa yana yi mata hotuna da bidiyo. Sai da ya dauka son ransa sannan ya tsaya yana kallonta. Ya ce,

 

 

“Gaskiya Habib ɗan duniya ne, gashi nan cikin ruwan sanyi na rama mafiyin yadda ta mun ma, gaba kya kuma.” Ya karasa maganar yana shigewa dakinsa.

 

A tsakar falon nan Farida ta kwana kan tais, sai da sanyin asuba ya fara shiga jikinta kafin ta farka. Kokarin tashi ta fara yi, ta ji gabadaya jikinta ya yi mata nauyi, ko ina ta motsa ciwo. Dakyar ta dafa kujerar da ke gefenta ta tashi ta zauna.

 

Kallon jikinta ta yi ta ganta tsirara Mamakin kasancewarta a haka kuma wajen ta fara yi tana kokarin tuna me ya faru. Ta dai tuna zamanta a falon, sai kuma ta fara ganin Sufyan dishi-dishi a gabanta yana dariya, daga nan kuma ta kasa tuna komai.

 

“Lallai ma komai ya sameni, yaron can ne ya tsara, kuma wallahi sai na rama tunda shi ba zai yi hankali ba.” Ta karasa maganar tana kara dafa kujerar. Da kyar ta tashi ta dau zaninta ta daura ta janyo pant da sauran kayan tana tafiya tana kama bango, ta shige dakinta sanyin wajeb ya gama kashe mata jiki.

 

Wanka ta shiga ta yi don ya rage mata tsamin jikin, ta duba ko ina dai bata ga alamun ya mata wani abu ba ta yi hamdala sannan ta dauro alwala. Bayan ta yi sallah, duba jakarta ta yi ta ga Declo Pain, ta dauka ta sha, sannan ta ja jiki ta hau gadon ta koma barci.

 

Har Sufyan ya tashi ya shirya ya fita, Farida bata tashi daga barcinta ba sai wajen tara ta farka. Da sauri ta tashi ta dafa indomie ta ci, sannan ta ƙara wanke jikinta ta shafa mai.

 

Doguwar rigar material ta ɗauka ta sanya, Navy blue mai adon fari, sannan ta ɗauki hijab ɗinta, shi ma Navy blue har ƙasa, ta sanya. Ta ɗauki nikaf ɗinta ta daidaita shi a fuskarta, ta dauko safarta da bakin crocs tasa, tukunna ta feshe jikinta da turare. Ta ɗauki jakarta da wayarta ta fita da sauri.

 

Gidansu ta fara zuwa ta gaida su Mama, sannan ta wuce gidan Inno, dake motarta. Na gidan ba a maida mata ce ba.

 

Tana shiga ta tarar da Baba a falon Inno suna hira. Ta yi sallama ta shiga ta gaida su. Bayan sun gaisa ne Baba ya tambaya, “Ya mai gidan naki? Fatan dai komai lafiya ko?”

 

Kafin Farida ta yi magana, Inno ta katseta da faɗin, “Yoo, lafiyar kenan, amma fa Kulu bata kyauta min ba. Tana son tada min da husuma wai ace sam bata koyawa Faridatu yadda za ta tarairayi namiji ba? Ai tunda ka yi tafiya bayan an ɗaura musu auren nan, kullum sai na je gidan na nuna wa Faridatu abubuwan rayuwar aure, hum.”

 

Baba ya girgiza kai ya ce, “To, Allah ya kyauta.”

 

Farida ta ce, “Dama zan koma wajen aiki ne, na zo ɗaukan motata.” Ta ƙarasa maganar tana tashi.

 

Inno ta ce, “Aa, dakata kafin ki tafi ki karɓi saƙonki ki sa a jaka. Ga alimun ɗinnan na siyo miki.” Inno ta kalli Baba Haruna ta ce, “Kasan irinsu masu jikin nan sai ana sa abin kawar da warin hammata, musamman yanzu da ta yi aure. Ai sai a ɗauki haƙƙin Sufuyanu ko? Don dai wari ba daɗi a gare shi ba yana daga cikin lamuran husuma.” Ta ƙarasa maganar tana gantsarar goro.

 

Alla-alla Farida take ta karɓa, ta samu ta fice daga ɗakin. Tana karɓa kuwa, da sauri ta tashi.

 

Baba Haruna ya ce, “Allah ya tsare, a lura wajen tuƙi.”

 

Ta amsa da, “Amin,” tana ficewa daga ɗakin.

 

Shiga motarta ta yi ta kunna redio tana sauraren Unity FM, tana driving cikin nutsuwa har ta isa cikin University of Jos. Duba wayarta ta yi, taga wani class take da shi. Bayan ta yi parking sannan ta fito, kai tsaye ta nufi bangaren ‘yan Computer Science.

 

Daidai lokacin time dinta ya fara, lecturer ɗin da ke ciki ya gama kenan ya fito. Suka gaisa, tukunna ta shiga ita ma.

 

Tana shiga class ɗin, ya yi shiru kamar an dauke ruwa, ganin sabuwar lecturer ɗin da ba su saba gani ba. Jin wannan shirun yasa Sufyan ya daga kansa. Yana daga kai suka yi ido biyu da Farida, gabansa ne ya yi mummunan faduwa. Ya fara taɓa Habib yana cewa,

 

“Kai, kamar Farida fa.”

 

Gyaran muryar da ta yi ne ya katse Habib da bai samu damar amsawa ba. Gaisheta sauran ’yan class ɗin suka yi ta amsa, sannan ta ce,

 

“Barkanmu dai. Sunana Farida Harun Abdullahi. Na san kila ba kowa ne a nan ya san ni ba, saboda ina daukar iya ’yan 100 da 200 Level ne, sai kuma wannan shekarar aka samu ci gaba har da ku, ma’ana ’yan 300 Level. Daga yanzu ni ce zan fara daukarku CSC 312, ma’ana Computer Networks.

 

“Ina da tsari, ina da dokoki, wanda in har kuka yi kokarin kiyaye su, to ba za mu taba samun wata matsala da ku ba. Na farko, bana son surutu a lokacin da nake lectures. Sannan idan na riga mutum shiga class, ba zai shiga ba. Bana son raini, dukkaninmu a nan mun yi girman da za mu guji bacin rai. 

Sannan ni fa a class dina ba a wasa, dole kowa ya gane komai. Ina da yawan tambayoyi har sai na gamsu cewa na gane abin da ake koya, don bana shirin zama mai dumama benci.

So, ina fatan mu zama friends yadda dukanmu za mu ji dadin juna, okay?”

 

Amsa mata suka yi da, “Yes, Mah.”

 

Farida ta ce, “Alright, bara mu fara.”

 

Sufyan ya ce, “Ji shegen iyayi! Wai a rasa wa za a kawo mana sai wannan bunsurar? Tur, ni gaba ɗaya raina ya ɓaci wallahi. Kar ta bi ta raina ni.”

 

Habib ya ce, “Wallahi kuwa! Da ma dai an barta ta ci gaba da riƙe yaran, amma mu ai mun mata girma. Ina faɗa miki, da kanta za ta gudu. Ai ’yan department ɗin nan ba kanwar lasa ba ne, ka sani.”

 

Dariya Sufyan ya yi yana tafawa.

 

“Kuma fa mazan ma ya suke kare da mu, bare ita mace.”

 

Suka ci gaba da surutu, ita kuwa Farida ta ci gaba da musu lecture kamar ba ta jin abin da suke faɗa.

 

Ta ce, “Gabatarwa: Computer Networks.

 

Ma’anar Computer Network

 

Computer Network wani haɗi ne na kwamfutoci biyu ko fiye, ko wasu na’urorin kwamfuta, waɗanda aka haɗa domin su iya sadarwa da juna da kuma raba albarkatu (resources) kamar bayanai (data), fayiloli (files), printer, applications da internet connection.

 

Computer Network yana ba na’urori damar aika (send), karɓa (receive), da musayar bayanai (exchange information) da juna.

 

Misali:

 

Idan aka haɗa kwamfutocin da ke cikin Computer Laboratory wuri guda, ta yadda za su iya raba fayiloli ko amfani da printer guda ɗaya, to waɗannan kwamfutocin sun samar da Computer Network.

 

In conclusion, a computer network is simply the connection of two or more computing devices together for the purpose of communication and resource sharing. The devices connected to the network can send, receive and exchange information with one another.

 

For example, computers connected in a computer laboratory that share files or a printer form a computer network.

 

Shiru ta yi na ’yan sa’o’i kafin ta ci gaba da faɗin,

 

“So, you should remember that the two major purposes of a computer network are communication and resource sharing. Ina fatan kun gane?”

 

Suka amsa da yes Mah.

Farida ta ce,”Alright to akwai mai tambaya?”

Suka kara amsawa da fadin,”No Mah.”

 

“Okay, hakan ya yi yanzu ina ganin mun gama class din yau.”

 

Ta na karasa faɗin hakan, idonta ya sauka daidai kan Sufyan da Habib da suke ta zabga surutunsu hankali kwance.

 

Gyaran murya ta yi tana kallonsu ta ce, “Hey you…”

 

Kau da kai duka suka yi kamar ba su san tana yi ba.

 

Ta ƙara magana, “Hey, second to the last seat, am I not talking to you?”

 

Ƙara kawar da kai Sufyan ya yi, kamar bai san abin da take faɗa ba.

 

Habib ya nuna kansa, “Ni?”

 

Farida ta girgiza kai. “No, wannan farin zabiyan abokin naka.”

 

Juyawa ’yan class ɗin suka yi, ana kallon Sufyan ana dariya.

 

Farida ta katse su da faɗin, “One class, please. And you, Mr. Man, ka ɗan tashi tsaye ko.”

 

Tashi ya yi, ba don ya so ba, yana kallon ƙasa.

 

Farida ta ce, “Please, can you help us and define Computer Network?”

 

Gaban Sufyan ya yi durus, don shi tun da ta fara lecture ɗin babu abin da ya saurara, bare ya fahimta.

 

Ya yi shiru.

 

Farida ta ce, “Eheen, muna jiranka fa.”

 

Fara sosa ƙeya Sufyan ya yi yana mutsu-mutsu, sannan ya taɓa Habib.

 

Habib ya kawar da hannunsa yana cewa, “Please, kar ka ja zamin. Ni ma ban sani ba.”

 

Farida ta yi gyaran murya. “Eheen, duk kunnuwanmu kai suke saurare.”

 

Sufyan ya numfasa, yana ƙara sosa ƙeyarsa, sannan ya ce,

 

“Computer Network is when computers are connected together so they can help each other… especially when one of them is tired.”

 

Yana karasa faɗa, gaba ɗaya class ɗin suka fashe da dariya.

 

Farida kuwa ta zuba masa ido na wasu daƙiƙu, kafin ta ce,

 

“Interesting…”

 

Ta ɗan karkata kai.

 

“Since when do computers get tired, Mr. Man?”