JA DA BAYA...

Rudin zamanip

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 22✍️*

***

Tsaye take acikin dakin nata Wanda yaji kayan more rayuwa, kudin da aka narkar a wannan daki nata kadai yaci aba wasu mutane da dama jarin da zai ishesu kulawa da rayuwarsu.

Sai dai Kash a wannan zamanin shuwagabanninmu Babu abinda suka suka sani se kansu,su Gina yayansu,da jikokinsu,Amma rayuwar talaka ko ohoo.

Kamar yadda ta Saba arayuwar tata,kamar kullin Rawar ta take cikin Jin dadi da walwa, saidai amatasayin yar musulma, bawai rawar bace ma abin damuwar yanayin suturar jikinta ce abin duba, domin kuwa Babu abinda ba'a gani ajikin nata rigar da ke jikinta iyakarta cibiyarta, hakan wandon Wanda yayi matukar kama jikinta, Shima iyakarsa kwaurin ta.

Meerah kenan Shaharriyar Yar TikTok ce Wanda tayi shura akafafen sada zumunta,sannan ba Wani abune take sawa a shafin face video na Raye-Raye.

 ko wanka zatayi Wani sa'in se tayi video ta daura, da towel ma video takeyi Wanda aganinta daidai.

Meerah na daga cikin 'yan TikTok da suka samu karbuwa sosai saboda bidiyoyin raye-raye da rungume rumgume da take yawan sakawa a shafin nata.

Bidiyoyinta suna samun dubban views da likes kowace rana, kuma hakan ya sa ta zama sananniya musamman tsakanin matasa masu amfani da TikTok, sannan Kuma irinta masu bibiyarta.

Abin da ya fi jawo hankali a shafinta shi ne yadda take yin raye-raye da kuma Saka ko wace sutura da bata dace ba, Wanda Sam baiyi kama da dabiu na musulma Kuma ba haushiya ba,wanda wasu ke ganin "ba su dace a al'adunmu na bahaushe ba da Kuma addininmu gaba daya.  

Wannan ne ya sa ta samu mabiya masu yawa, tare da samun suka daga wani bangare na jama'a, domin kuwa wasu suna yaba mata yayin da wasu ke Allah Wadai da ita.

Abu ne na zahiri Wanda al'ummar mu sukeyi na son zuciya yau ko tsirara mace zata fito tana video madadin a mutane su kyamata abin, to se ansamu Wanda wannan abu su shine yayi musu, zakaga har zuga me aikata wannan abu akeyi ana fadin komai yayi, tare da danna masa like, Wanda hakan shine yake basu gwarin gwiwar cigaba.

Wasu suna cewa Meerah tana "nuna baiwarta ne kawai, kuma tana bin trend din duniya, Wanda da yawa sun shagala da hakan har ya zamana kamar ma sun manta mutuwa", sannan kuma suna ganin ya kamata ta yi la'akari da al'adu da addini wajen zabin abin da zata saka a media tunda hakan ya zame ma al'umma jiki.

To kamar yadda ta saba, yau ma tsaye take tana yin bidiyon nata, ta juya Nan ta juya can surar tata Mai matukar daukar hankali Wanda tashi take rinjayar mabiyan nata, yanzu dinma wanka zata shiga shine ta tsaya nunawa duniya yadda zata shiga wankan.

Camera ta kafa sannan tayi video din nata, Bayan ta gama, ta karasa wajen camera din ta kashe.  
Kallon bidiyon tayi daga farko har ƙarshe tare da furta "Wow I'm hot lady fa"  
Ta sake kallon sa dakyau tana ganin haduwar ta da yadda in ta daura video din mutane zasu kalla sosai duniya zata Kara Saninta, se da ta murmusa sannan ta fara editing na video din, Bayan ta gama, ta ɗora shi a shafinta tare da kashe wayar tata kirar iphone 17 tashige toilet din.

Ta bata lokaci Mai tsawo gurin wankan nata,Wanda zallar sabulan da take amfani dasu kadai kasan yar gata ce, wacce ta amsa gatan gata.

Da Dan guntun towel din da da kadan ya wuce mazaunan ta tafito daga bathroom din,bakin gadon ta zauna tare da daukar.  
Waya tana kira Mai kula da ita, Wanda cikin yan sakanni ta karaso dakin tarar da ita tayi zaune abakin gadon nata gaisheta tayi cikin matukar girmamawa, tare da tsunnawa a kasa kamar zatayi mata sudaja.  
Ko kallonta batayi ba, hakan yasa ta mike ta karasa gaban mirror din tafara dakko abubuwan dazata gyara meerah din.  
Mayukan ta masu tsananin kyau da tsada take bin ko Ina na jikin meerah din tana shafa mata, sabida tsananin gata wai katuwar budurwa kamar wannan zatayi wanka ace Mai bazata iya Shafawa jikinta ba se an sha fa mata Dan gata.

Haka tagama shafa mata, sannan ta tashi ta dakko kayan dazata Saka mata, Hadi da turarika masu dadin kamshin da tsada.  

Ita kuwa gwanar ana gyarata tana hakimce tana sha fa wayar tata, karanta comments ɗin da suke shigowa wayar ta ta takeyi tana murmushi sosai. da Jin dadin yadda mutane irinta ke ta Koda surarta ta.

Wasu suna yabawa, yayin da wasu kuma suna mata dariya, wasu kuma suna mata nasiha, wasu kuwa Allah Wadai.  
Wanda ita Sam bata tsayawa duba comment na masu Yi mata nasihar ma domin kuwa Shaharar da take samu ta riga ta zama wani ɓangare na rayuwarta, Sam bata ganin illar hakan, tunda duniya na yayinta.  

Amma abin da ba ta sani ba shi ne, rayuwar da take nunawa a kafafen sada zumunta shine abinda zai cuci rayuwar ta.

Kamar an tsikareta ta shiga media tana search game da sunan sa ko zata samu Wani abu a game dashi.

tunda suka hadu har zuwa yanzu zuciyarta bata huta da tunanin sa ba.  
Ko bacci ta kwanta setayi mafarkin sa tun daga ranar da ta daura idanuwanta akansa.

Ita din ba Ma'abociyar kallon kwallo ba ce Amma ta sanshi awasu lokutan Wanda bazaka samu hotonsa Wanda Babu face mask ba, sedai in Yana filin wasa, to anan ne fuskarsa take bayyane, Amma bayannan ko Wani family nasa yadaura hotonsa yawanci fuskarsa rufe take.

Shiyasa ranar ta da fara kallon fuskarsa taji cewa bawani se shi.

Dan Wani irin kaunar sa Hadi da sha'awarsa ne ya riske ta Nan take,Wani irin wutar kaunarsa na sake ruruwa a zuciyarta inta Tina idanuwansa da Kuma bakinsa.

Gajiya tayi ta kwanciyar tana tunaninsa yasa ta tashi a gadon na ta ta fito zuwa babban falon gidan inda ta tarar da mahaifiyarta na zaune suna kallon labarai ga mahaifinta agefe suna Hira.  

Babu ko sallama da yar rigarta wacce take iyakar gwiwarta ta karasa ta kwanta a jikin mahaifin nata, hannu yasa Yana shafa kanta cikin kauna da kulawa tare da tambayarta "  
My baby me kike bukata?
naganki yanzu ba walwala bayan dazu naganki you are so happy!  
Cikin tabara ta Bude Baki tace "dad I love him, I want to marry him".  
Wow, Wani Mai sa'an ne kyakykyawar yarinyata takeso?  
Wanene ubansa a kasar?  
Dan gwamnan inane kokuwa Dan sarkin Wani gari ne?  
Iyehhh princess dina ta fada soyayya ya jero mata wadannan tambayoyin.

ita kuwa tana ta Kara lafewa ajikinsa.  

Itama mommy abinda take fada kenan, cikin Jin daddy princess dinsu tana son wani har tana batun aurensa Dan gidan waye?  
Cikin One week ayi komai agama!  
Meerah kuwa cikin yakinin iyayen nata zasu aura mata shi, tunda tasan bata taba neman abu a duniya ta rasa ba ta budi Baki tace"  
Dad sunan sa Ayzaan Mai rabo, (the lion)

Ai cikin Wani irin matukar fargabar sunan da ta ambata Alhaji Gali Wanda baisan ma ya tureta daga jikinsa ba ya mike Wani irin mummunar faduwar gaba na riskar sa Nan take yamike tare ta fadin"  
Whattt  
Ayzaan Muhammad Mai rabo kike nufi?????????